KWARTON SARKI

1-2

by @oumhairan1

*KWARTON SARKI*


*Oum Hairan*


*1-2*
Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu Akbar!!!..... Kiran sallar Magrib ya cika kowacce kusurwa ta wannan masarautar A lokaci guda kuma zuciyoyin wasu ɓangarori na mutanen dake hidima a wannan masarauta cike yake da zullumi da faɗuwar gaba, can nesa na hango wasu kyawawan yammata guda biyu zaune cikin tagumi na taka garesu a hankali cikin son jin abinda yasa kowa yake kasancewa a wannan hali na damuwa idan akace la'asar ta kawo jiki har zuwa wayewar gari wani abin mamaki ba mazan ba ba matan ba kowa a wannan zullumin yake kwana, Ɗaya cikin yammata tace “Azeemah nifa na tsorata da kallon da naga tsegumin gidanan yanayi mana ɗazu Kinsan Naji bayin daula suna cewa duk mace da taga idon tsegumi yana yawo a kanta to shakka babu ko matar aure ce sai an samu labarin wani wanda har yanzu ba'a gane waye ba ya haura gidansu yayi mata fyaɗe kuma abinda ike bawa Kowa tsoro ba'a sanin sanda yake zuwa sai bayan ya gama abinda Zaiyi idan budurwa ce aganta  a yanayin tashin hankali idan matar aure ce kuma taji alama" Sauke iska Azeemah tayi tace “Hinde duk Bama wannan ba wai shi wannan KWARTON waye da duk tsaro da iko na wannan masarauta aka kasa ganoshi Kinsan wani abu da yake bani mamaki Ance bayacin ƙananun yara  kuma Ance duk macen da yaci so ɗaya to bazata ƙara jin daɗin wani namiji ba sai shi duk Bama wannan ba ance wai ba'a iya ganinsa saidai kawai kaji ya garƙama maka kaciyarsa cikin Durinka idan kuwa akayi rashin Sa'a ma fuskarsa ta bayyana to a wata halitta daban zaka gani ba mutum ba"
Kama hannun Azeemah Hinde tayi tace “Kin san me?" girgiza mata kai tayi Hinde tace “Nifa inason naga wannan mutumin na daina jin wai wai amma kuwa wai sarki Fadal ya san da wannan abin da ke faruwa a ƙasarsa" dariya Azeemah tayi tace “Nifa ina ganin yasan komai saboda Wataran Naji Kaka Ajuzi na cewa ta fita ɗiban magani taga wani mutum ya fito daga sassan sarki da tayi ihu sai wani mutum ya kamata zai murɗe mata wuya daƙyar Saida tayi alƙawarin bazata faɗa ba sannan ya barta ta tafi bayan ya zaneta da dorinar Dawaki" Jinjina kai Hinde tayi tace “To ke yau me ya hanaki zuwa sassan yarima ne naga yinin yau gabaɗaya bakije ba" shafa gefen fuskar ta tayi tace “Yace baya buƙatar hayaniya ne yau yana son kaɗaici" haka suka ci gaba da hirarsu dake a ɓoye suke a wani lambu babu wanda ya gansu sai bayan Isha suka bi ta wata siririyar hanya suka nufi gidajen uwayensu suna tafe sukaji ana cin uban gudu ana cewa “Kowa yayi ta kansa Kura ta tsinke....." Habawa ai dukkansu suka tattare zani suka fara cin uban gudu kamar Zasu tashi sama"............ 

*for more info....*
*****

*Oum Hairan*