KWARTON SARKI

3-4

by @oumhairan1

**KWARTON SARKI*



*Oum Hairan*


*3-4*
Ji Azeemah tayi anyi mata ɗaukar amarya ta buɗe baki zata yi ihu akasa wani abu aka rufe mata baki tanaji amma bata isa tayi magana ba  nan suka juya suka nufi wata ɓoyayyiyar hanya  ita dai Batasan ina suka nufa ba saida aka shiga da ita ciki sannan ta fara ganewa cikin tsananin mamaki ta rinƙa kallon sashin ba tare da ance mata komai aka fice aka barta ta mike da sauri ta cire abinda aka rufe mata baki dashi ta fito daga dakin da aka kaita tayi Turus ganin Mamallakin sashin tsaye  jikin window tayi baya da sauri zata juya “Azeemah!" taji ya kira sunanta ta tsaya Cak ya tako cikin takunsa me cike da iko da isa yace “Meye ya hanaki zuwa kiyi aikinki yau?" cikin mamaki tayi ƙasa da kanta tace “Ranka ya daɗe kaine jiya kace min baka buƙatar hayaniya kana son kaɗaici" yana takawa zuwa elevetor yace “Kuma nace har da ke?" cikin sanyin jiki tace “Ban fahimta bane Allah ya baka hakuri" Murmushi yayi yace “Ki shiga ciki ki gyaramin ɗaki" So take tayi magana saidai tasan halin yarima Hameen bai ƙaunar yawan magana  Shiyasa ta mike tabi bayansa ta Elevetor ɗin ta shiga babban parlourn nasa akwaishi da tsafta komai nasa tsaf yake kamar mace.
ɗakin baccin ta shiga ta fara gyarawa kamar yanda ya bata umarni tana tsaka da gyaran ya shigo ya tsaya jikin ƙofa ya zuba mata ido Batasan dashi a wajen ba don haka hijjab na Jikinta ma cireshi tayi dagowar da zatayi bayanta gama suka haɗa ido yana maƙale da hannunsa a ƙirjinsa tayi saurin ɗaukar Hijjab nata ta saka tace “Na kammala ranka ya daɗe" baiji me tace ba saboda ya tafi duniyar tunani har Saida ta sake magana sannan ya taka ya shiga bathroom yace “Inason wanka ki haɗamin ruwa" sakin baki tayi tace “Ruwa kuma?" saurin binsa tayi da sauri tayi baya ganinsa tsaye dagashi sai boxes takai bakin ƙofa ya kirata ta tsaya ya taka ya isa inda jacuzzin yake yace “Me nace kiyi?" cikin in...ina tace “Ruwan wanka Amma ganinka nayi a haka" juyowa yayi ya zuba idanunsa a kanta ya tayi saurin ƙasa da kanta ya tako ya iso gareta yace “Meye don kin ganni a haka?" cikin tsoro tace “Babu kyau tsoro Nakeji......" cafkar hannunta yayi ya janyota ta faɗa jikinsa ya ɗora hannunsa a ƙugunta yace “Haka fah?" rintse Idsnunta tayi ƙirjinta na bugawa da ƙarfi ya sake ta yace “A takaice ke ɗin mallakina ce Azeemah    na fansheki matsayin Kuyangata.........


*for more info.....*
*****

*Oum Hairan*