Page 17&18
🤍🔥✅ ★★★
#ANNEH POV
Kwananta biyu aka sallamota bawai don ta gama warware wa ba saidan sallamar data naima da kanta. Tunda ta dawo cikin matan gidan babu wanda ya ko leƙo inda take, duk da kuwa cewar suna sane Amma baƙin hali da sama Rai wahala ya sanya babu wanda ya kalli inda take. Ita kuwa samm ba su bane a gabanta ɓatan ƴar tane kawai damuwanta, duk irin uban fari da jikin da take da a cikin kwanaki uku babu shi ga duhun da farar fatarta da sirka. Kasancewar jikinta da suffarsu irin na cikakkun larabawan nan ne wani irin kyau da haiba Anne ke dashi. Wannan shine kyau nata da yanayin kyawun jikinta shi yafi komai ƙona zuciyarsu abokan zaman nata. Tana zaune saman darduma tayi irin kifa kan nan na rashin samun nutsuwar zuciya. Yanzu a wanne hali *DIDI* take dama haka rashin ɗa a kusa dakai yake?, Dama haka ko wacce uwa take ji idan tana a irin halin da take?. Toma wai miya haɗa *DIDI'ƊINTA* ta wannan AK ɗin? Ak is a known criminal in Lagos, ta gagari kowa he is a kidnapper as well as an arm robber. "Ya ALLAH ya ARRAHAMANU ka kare min *DIDI* aduk inda take ka bayyana min ita cikin amincinka ya zul'Arshim majeed" Wani irin suya zuciyarta take mata yau inama ace tana da Asali? Inama ace tana wata ko wani ɗan uwan, yau inama ace tana da mahaifiyar da babu abinda zai hana ta rungume ta tayi kuka, tayi kuka iyaka kuka tayi kuka me sunan kuka ko zuciyarta ta samu salama da nutsuwa. Cikin zubda hawaye ta furta _"SHIN WACECENI?"_
Kamar daga sama taji Muryar maman haidar tana furta. *"KEBA KOWA BACE face tsintacciya mara asali mara galihu ƴar tsintuwa wacce uwarta tayi cikin shegenta ta hullar a bola"*
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfin bala'i tana jin yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa. "YA RABB!" Ta faɗa tana wani irin fesar da iska ta cikin bakinta me zafi. Kamar daga sama taji ƙarar shigowar sako a wayar *DIDI'ƊINTA* Sake kulle idanuwan tayi kafin jikinta na rawa da janyo wayar data zame mata tamkar itane meerah'ɗinta. Hannunta har karkarwa yake wajen buɗe saƙon domin gani take a kowanne loƙaci kan iya turo saƙon bayyanar meerah'ɗinta ne ta cikin wayar. Sai dai kash!..... Saƙon ma bai hada hanya da kidnapper's ɗin ba, saƙo ne da akan turo mata duk shekarar duniya na zagayowar ranar haihuwarta ta wata ɓoyayyar Number. Ga abinda sakon ya ƙunsa. *_ OHhhhh On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world’s most amazing woman. Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my JAAN my SUNSHINE, If anyone is deserving of all the happiness in the world, it’s you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being. Happy birthday 4ever❤️ Barka da zagayowar ranar haihuwa my JAAN May your birthday be filled with joyful moment❤️_* Tun bata kai ƙarshe ba taji wasu zafafan hawaye suna bin gefen kumatunta *"ALHAMDULILLAH"* Ta faɗa cikin wani irin amon murya Incheerfully. "ABTINI MEERAH, I Missed her with All my heart ANNE ki kaini wurin beloved Nima" Raiha ta cikin muryan da yaci kuka sosai. "DIDI adda'armu take da bukata yanzu Raiha kici gaba dama addanki adda'a Allah ya bayyana mana ita cikin amincinsa.....
Da sauri Hajiya Hajiya umma dake tsaye tun ɗazun ta sanya bayan hannunta tana sharce ruwan hawayen tausayin Anne'n, Wacce ta kasance itane tamkar uwaa ga Anne'n. Domin wani irin girma take bata irin na ƳA da UWA. Labulen ta tura tare da shiga ɗakin da sallama kasa amsata duk suka yi domin rumgume junansu sukayi suna wani irin kuka me tsuma zuciya. Zaune takai kan ɗaya daga cikin kujerun parloun. "Shin dama ashe idan Allah ya jarrabi bawansa da wata ƙaddarar kuka ake AYSHATUL HUMAIRA?, Allah ake miƙama dukkan al'amurran ata kai kuka a gareshi domin shine buwayi gagara misali mai kowa mai komai! Ce ALHAMDULILLAH" "ALHAMDULILLAH" Ta sake maimaita wa cikin ɗacin murya, kafin ta kife kanta saman ƙafafun Hajiya umma cikin wani irin raunin murya ta shiga faɗin. “Ni ma ina da buri ina da mafarkai irin na kowacce ƴa mace ina da burin na rayu tare da ƴaƴana ba kamar yadda nawa IYAYEN suka zabi wulaƙantar dani ba. sai dai kash ƙaddara ta shata min liyi da hakan ta sanja min nata salon yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi babu yacce na iya. Ni musulma mace me ƙarɓar ko wacce iriyar aduk yadda tazo min. Daga loƙacin da Akayi kidnapping DIDI sai tsoro da fargabar me zai faru ya tasoni gaba! Amma dana tuna Allahu buwayi gagara misali sai tsoron hakan ya fita a raina. Zuwa yanxun yaci ace na daina ma ko wacce iriyar ƙaddara kuka UMMA idan nai duba da yadda zanen tawa ƙaddarar ta kasance min. Kenan ƙaddarar ɓatan DIDI Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da ɗaure kai. Wata kalar ƙaddara ce mai rikitarwa shimfiɗa ce wacce take tafe da nata salon. Yaushe wannan rufaffen sirrin dake shimfiɗe a cikin zuciyata! Zai fito fili?, A cikin ko wacce rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa toni a wanne mizanin nake? Mabuɗin kowacce ƙofa makulli ne sai dai Ni tawa ƙofar wani irin wawakeken rami ne wanda aduk loƙacin da wani yayi yunƙurin bi ta cikinsa yake ruftawa dashi. Shin Me nama nawa IYAYEN da suka zabi wulaƙantar dani? Ki bani Amsata UMMA!!!.......... Ta faɗa da wani irin gursheshen kuka irin wadan yake fitowa daga cikin tsakiyar ƙirjin nan "ALHAMDULILLAH Allah abin godiya Allah mun gode maka" Sune kalaman da Hajiya umma tayi ta maimaita wa kafin ta shiga nanata kalmar _INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN²_ Hakan ya sanya Anne kamawa itama suka hau maimaitawa a tare harda ma Raiha.....
By AMMEY LAYLERH ✍️~ *🦅 MIKIYA 🦅* _Mai hangen nesa 👀_ *~We want an end to oppression💪~* *** ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*