BEST LOVE
🤍🔥✅ ★★★★
2 months ago
Haka dai al'amurra suka ci gaba da wakana. Tuni baffa ya kashe waccen maganar haka kwanaki suka ci gaba da juyewa zuwa satikai satikai sukaci gaba da juyewa zuwa watanni. Cikin iko na Ubangiji meerah ta koma bakin aikin da ko a mafarki ba tayi tunanin komawa ba, Bisa matsawar MD da kuma wasu manyan anguwanni ta koma bakin aikin ta. Haka kuma maganar aurensu da Salman yake neman kan kama, Wannan abu shi yafi komai ɗaya hankalin meerah matuƙa saidai tana danne hakan a ranta. Kusan kullum yanzu shike zuwa har ƙofar gida ya ɗauke ta zuwa wurin aikinta saidai ta dakatar dashi first. A tacen ɓangaren su Salman kuwa wasu irin abubuwa suke ma shirye shirye shida mahaifinsa Isa Manu.
*******
Yamma ci ne mai daɗi haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma'a, ranan da yake ɗauke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala. Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin daɗi da kuma sanya shauƙi ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan jaridar zamani TV Kowa ka kalla harkar gabansa yake cikin tarin nutsuwa, amma banda meerah da tayi zurfi a cikin duniyar tunanin data jima ta faɗawa.
*"MEERAH!"* *"MEERAH!!"*
Disha dake tsaye kanta ta shiga ambata tana me ƙoƙarin rataya handbag ɗin dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta ɗan ranƙwafowa da kanta, tana me kallon Meerah.
"MEERAH wake up kodai bacci kikeyi ne?."
Disha ta faɗi tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta zunguri meerah ɗin.
Ahankali ta ɗago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago. Sam ba bacci takeyi ba hasalima duk abunda ƙawar nata ke faɗa tana jinta.
Numfashi ta ɗan sauke Ahankali tare da ɗago manya manyan eyes nata me kama dana mashaya masu matukar kyau, Wanda hakan ya sake bayyana tsananin kyawun dake kwance akan fuskarta, Idanunta da suka ɗanyi blue ta lumshe tare kuma da buɗe su aloƙaci guda.
Cikin unique voice ɗin ta mai daɗin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.
"What happen DISHA? ba bacci fa na keyi ba, just I'm tired." Ta ƙare maganan tana ɗan kwantar da wuyanta gefe.
"What happening kike tambaya? time ɗin tashi a aiki yayi, kalla ki gani babu kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman wurin ne bai isheki ba?." Disha ta faɗi tana ɗan hararanta tare da yin gaba.
Fuska meerah ta ɗan kwaɓe kana cikin yanayin gajiya da kuma tsananin damuwar dake cinkushe a cikin ranta ta miƙe itama. cikin sauri ta rufa mata baya tana me ƙoƙarin rataya jakanta bisa shoulder nata.
Atare suka fito compound ɗin, tafe suke suna fira sama sama abinsu. "Disha a raina inajin ina gab da ajje wannan aikin nake ga" Meerah ta furta cikin cushewar yanayi. Dafa kafaɗarta disha tayi cikin sanyin jiki ta furta. ”Haba meerah komai yayi zafi maganinsa Allah, ki barwa Allah komai Insha Allah shine maganin komai” "Hmmmmmm!" Ta sauƙe ijiyar zuciya me ɗan ƙarfi haka suka ci gaba da tafiya har suka fito gefen titin. Napep suka tara suka hau suna mai kwatancen anguwar da zai kai su. Ko a cikin napep ɗin ma wata sabuwar duniyar tunanin ta ƙara faɗawa. Na irin daskararriyar K'addarar dake kwance acikin jininta wacce ta fara motsawa kanta. Haƙiƙa akoda yaushe rayuwa tana tafiya ne tare da tarin ƙalubale.Haka kuma kowa da salon nashi Kalon ƙaddarar amma nata ƙaddarar gani take yafi na kowa, domin daga ta fita daga wannan sai kuma wannan ya kutso kai.
Kamar kuma yanda yake a bayan kowani baƙin ciki akwai farin ciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci. rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka mummunan ƙaddara ko akasin haka, wayewar garin yau sun waye shine da maganar kawo kuɗin aurenta da iyayen Salman sukai har Naira miliyan ɗaya. Wanda ya tashi hankalin jama'ar gidansu, suka wuni zazzaga ruwan bala'i da masifu kala daban daban. Ita kuwa wacce ake yi ɗin dan ita sammm ba abinda ke gabanta kenan ba. Wani abu ne daban ke damun rayuwarta wanda da tayi ƙoƙarin zurfafa kanta yake neman juyewa zuwa wani ɓigiren na daban...... Cikin nisan da tayi a duniyar tunani har suka isa ƙofar gidansu bata ma san sunzo ba, Saida disha ta mata magana da ɗan ƙarfi kana tayi firgigit ta dawo hayyacinta Cikin duniyar mutane bata tunani.
*AK*
Msalin ƙarfe biyar na yamma manyan motocin Ak dake cikin garin Abuja suka ma airport ɗin tsinke. Wasu irin zafafan motocin kusan goma sha biyar irin su Range Rover, Bugatti Veyron, Toyota Highlander, Toyota Tacoma, Ferrari California,gefe ga wasu mahaukatan manyan jifa jifai har guda biyar da aka ware su baƙaƙe wulik dasu. motocine a wurin babu colourn da babu shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman. Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen. Su kuma samudawan sa na aikin su na take mai baya, cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi. Don kuwa kallo ɗaya zaka masa ka kasa ɗauke idonka a kanshi. Sanye yake cikin Wani arnen cashmere valley wanda kallo ɗaya zaka ma yadin ka tabbatar da ba karamin kuɗi aka narka wurin siyen shiba... Ahankali yake taka Fararen sawayensa da tamkar wanda bai taɓa takasu ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai. Wata kafurar Black blue ɗin Mota ƙirar Mercedez Benz aka buɗe masa Armstrong kuma ya faɗa cikin wata narkakkiyar bakar jeep Wrangler . Suka ɗauki hanyar wannan haɗaɗɗen Hotel ɗin na da sukayi booking tun a daren jiya. Dake babu wata tazara tsakanin support ɗin da kuma Hotel ɗin babu nisa cikin 25 minute suka isa ƙaryataccen hotel ɗin. A room me lamba 105 AK ya ɗauka su kuma duk suka rarrabu daban daban.
Kwance yake acikin bathtub dayake cike da ruwa masu tashin qamshi na musamman, Iyaka kanshi ne a waje ya lumshe idanuwan sa ya faɗa duniyar tunani me zurfi, wanda nake da tabbacin ya mantar dashi a duniyar dayake yanzu haka. ya jima sosai acikin ruwan wankan daga bisani ya wanke jikinsa ya fito towel blue ɗaure a jikinsa.ga kuma wani mini qarami a hannunsa shi kuma kalar light blue yana tsane gashin kansa dake cike sosai baqa wuluk! lotion ya shiga shafe jikinsa dashi tsadadde ya gyara tulin gashinsa da mayuka masu kyau da tsada. Kayan da aka rigada aka ciro masa ya ɗan kalla a takaice dogon wandon jeans ne blue da shirt fara qal me asalin kyau an mata zanen Lion ajiki da blue din colours, sanya kayansa yayi kafin ya fito zuwa balcony na room ɗin. Hannuwansa zube jikin wandon jeans ɗin. Wurin ba hayani sai sassanyar iskan dake kaɗawa mai cike da tarin ni'ima sakamakon hadarin da yayima sararin samaniya ƙawanya.Hakan yasa garin ya yi luf ga dukkan alamu akoda yaushe a ko wanne loƙaci ruwan sama kan iya sauƙa. Yana zaune kan Chiar silinder caution ɗin dake cikin balconyn Wata ƙatuwar Toyota land cruiser Prado ta shigo harabar wurin fara ce kal sai faman kyalli da ɗaukar ido take yi.Wurin da aka tanada dan adana motoci motar ta parker,cikin slow mamallakin motar ya yi parking. Kasancewar glass ɗin motar tinted ne yasa ba'a iya hangen mai mamallakin motar har saida ya fito.An ɗauki tsawon 10 minutes kafin matashin dake draving motar ya fito. Back sit ɗin motar ya buɗe nan kuwa sai da aka kusan 20 kafin wani siririn matashin saurayi ya fito izza. Ƙafa ɗaya ya fara zirowa ƙasa sanye da halp cover shoe white color mai adon Stone a jiki irin na sarakuna.Cikin loƙaci ƙalilan ya fito da gangar jikinsa,Dogo ne sosai amma yana da ɗan kauri jikin shi a murje yake alamu na yana cikin hutu da jin daɗi,yana da hasken fata amma ba sosai ba.Farin yadin boyal ne a jikin shi mai ɗauke da ƙananun zane,wanda ya sha ɗinki irin na samarin zamani,sai Black agogo daya ɗaure a tsintsiyar hannun shi na dama dashi,a jikin siraran fararan yatsun shi kuwa ya saka white ring mai kyau a karamar yatsa.kanshi bai saka hula ba sai baƙar sumar shi data sha gyara gwanin sha'awa kamar ɗan India. kyakkyawar face na mai ɗauke da manyan dara-daran eyes balls ɗin da suke kamar madara. A hankali ya rufe manya eyes ɗin shi yana sauke ajiyar zuciya.Tare da furzar da iskar bakin shi.Manyan wayoyin shi dake riƙe a hannu ya kalla ga dukkan alamu ƙira ne ya shigo. Ɗan siririn tsaki ya ja wanda idan ba kana gaf da shi ba ba lallai ka ji ba. A kunne ya manna woyar cikin fusata murya a daƙile ya furta. "Zanci ubanka Wllh Najeeb akan takura min da kayi!, Wllh idan ka tunzirani zan fasa maka visa'n naga uban da zakay ok” Datse woyar yayi Cike da taku irin na zaratan maza ya fara taku yana nufar cikin hotels ɗin.da sauri driver'n ya mara masa biya da system nashi da dayar woyarsa. A room na daban shima ya sauƙa tare da kayayyakinsa suka zube akan lafiyayyan gado. ZAYD SURAJ kenan ɗa ga Sarkin kano mai martaba SURAJ SUNUSU SHUREIM.
*AK*
Cikin bacci yaji ya soma jin vebration na woyarsa, da ƙyar ya iya buɗe lumsassun idonsa. Idanu ya tsurawa screen ɗin wayar dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu haka ya tsira wa woyar kaifafan idon shi. Duk da cewar yasan ZAID bazai ƙirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu haka nan ya tsinci kansa da faɗuwar gaba. Hannunsa ya miƙa da niyar ɗaukar wayar saidai kafin yakai ga ɗauka ƙiran ya katse. Ɗin Jim yayi yana me tunanin bin ƙiran saidai sanin da yayi cewar mai ƙiran nasa zai sake ƙira ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya tare da fesar da numfashi. Anutse ya tashi zaune yana me tunani acikin zuciyarsa, haka nan Idanunsa da suka dan ɗan tara ruwa ya lumshe saboda tunowa da PAAH tare da Momma'n shi da yayi. ”ZAID EMAAR KUWAIT”
Ya furta a saman laɓɓansa woyar ya jawo tare da mannata da kunnensa. Daga cennnnn Zaid cikin yanayin sanyin jiki ya furta. ” ABDOUL-MALEEK PAPA?” Zaune ya tashi da sauri amma a zahiri ba saurin yayi ba shine a ganinsa yayi saurin. Cikin fitar sautin da yayi low sosae ya furta. ”Why? Where is my PAAH”
Shiru daga cennn Zaid yayi, Ak kuma jin shirun Zaid shine ya sanya shi furta. ”Ina PAAH yake you will die ko? ka buɗe baki kamin magana Zaid” Ya ƙarashe cikin sautin tsawa
“Ko ɗaya bai mutu ba anyi poisoning nashi ne agant!, wannan tafi ko wacce iriyar gubar da aka saba poisoning nashi da ita. Domin wannan da wuri zata iya zama sanadiyar rasa shi acikin loƙaci kaɗan, matuƙar akayi wasa to tabbas zamu iya rasa rayuwar PAPA gaba ɗaya”
Wani irin sakur zuciyarsa maganan da Zaid ya faɗa mishi yayi, yana jin daidai yake da bugun zuciyarsa acikin kunnuwansa, haka yake jin maganganun na yankar zuciyarsa. Saurin fusgo numfashinsa dake ƙoƙarin kwacewa zuciyarsa yayi ta hanyar furta kalman. “Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju’un!!!” da sauri saurin dake tafiya da gudun bugun zuciyarsa ya furta. ”what? My papa his under incapable survive in the world at this condition? oh god tell me the Truth I'm very dangerous twin!”
Jin yadda lokaci daya yanayin dan uwansa twins dinsa jininsa ABDOU-LMALEEK AK KUWAIT ya sanja ne ya sanya. Ya shiga kontar masa da hankali, ganin kamar hankalinsan na kwanciya zai yi bane ya sanya ya shiga fada masa kalma daya takkk. Wadda bansan ko wacce kalma bace itane ta nutsar da AK da kuma lurar dashi......
*BY AMMEY LAYLERH*
*🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* *** ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*