DUHU na DUKAN duhu

Page 1&2

by @103453610185262939894

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, godiya ga ALLAH subhanahu wata ala maɗaukakin sarki mai kowa mai komai da ya bani aron rai da lafiyar daya sake kawo mu wannan lokacin da rai da lafiya. ALHAMDULILLAH Ina yima ALLAH dukkan godiya daya sake bani aron rai da lafiya har na sake dawo muku a cikin wata sabuwar tafiyar da zata Nishaɗantarwa ta kuma wa'azantar IN SHA ALLAHU. Ina rokon ALLAH yadda ya bani ikon fara rubutu wannan littafin lafiya da aminci ya na gama lafiya cikin annushuwa da kwanciyar hankali ba tare da gundurar juna ba. ALLAH ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al’umma baki ɗaya, ya ALLAH kar ya bani ikon rubutu ɓarna ko abinda ya saɓa addinin Musulunci da ruguza al'umma... Ameen ya nabiyyun rahamati ya Rabbal alamin...🤲🏻_

_Wannan labari mai suna GUDUN DA BABU TSIRA ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, in ya yi kama da labarinki ko labarinka ayi haƙuri a rashi ne a samin albarka🙏🏻..._

*Gargadi Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga ta daban ba, ban kuma amince a juya min shi zuwa wata fuska ba tare da izini ba!.*

ꨄ A ranar ranar 12 ga watan Yuni na kowacce shekara al'ummar Najeriya kan yi bikin Ranar Dimokraɗiyya, wata rana da aka keɓe domin tunawa da gwagwarmayar da aka yi wajen tabbatar da mulkin Dimokraɗiyya da kuma kare haƙƙin zaɓen ƴan ƙasa. An zaɓi wannan ranar ne saboda muhimmancinta na zaɓen shugaban ƙasan da aka gudanar a ranar 12 ga Yuni, 1993, wanda masana tarihi da masu sharhi kan siyasa ke kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi sahi hanci, lumana da adalci a tarihin kasar Najeriya. Don haka ranar Dimokraɗiyya ta kasancewa kamar wata muhimmiyar ranar da tunatarwa wace ta irin ƙarfin Dimokraɗiyyar, wanda ke nuni da cewar yana hannun al'umma, kuma ci gabanta na dogara ne da yadda ƴan ƙasa ke amfani da haƙƙoƙinsu tare da sauke nauyin da ke kansu wajen gina Ƙasa mai adalci da ci gaba....

MAFARI....

Cike ɗakin taron yake ya yi irin tsit ɗin nan da ke nuna rashin zaman lafiya ne ya tara duka jama'ar ɗakin... Tsit ne irin mai ɗauke da nauyin tsoro, damuwa da tambayoyin da babu wanda yake da amsar su. Manyan dattawan ƙasar kuwa da masu fada aji katafaninsu a wurin babu wanda baya zaune cikin babban dakin taron fadar gwamnatin. Gaba ɗaya fuskokinsu cike suke da tunani mai nauyi. Wasu sun jingina a kujerunsu suna kallon takardun bayanan da ke gabansu, wasu kuma suna kallon babban allon da ke jikin bango ne wanda a zahiri bawai allon suke kalla ba. Babban jami'in tsaron da ke tsaye a gaban taron ne ya sauke wani ɗan numfashi kafin ya fara magana.

"Tabbas wannan abun ba ƙaramin lamari ba ne, domin kuwa mun shafe watanni muna neman wannan mutum. Mun tura rundunoni daban-daban, mun kafa hanyoyin bincike da dama a kansa amma har yanzu yana gaba da mu, wanda tazarar da a koda yaushe damar shan iska muke basu, shine babban kuskuren da mukeyi kawai, a koda yaushe tazarar itace zarrarsu a garemu mu kuma jami'an tsaro" Wani dattijo ne daga cikin waɗanda ke zaunen ya ɗaga kansa a hankali yana kallar wannan jami'an tsaro tare da furta.

"To amma ta yaya za'a ce mutum ɗaya shi zai iya zama irin wannan babbar barazanar wamu da kuma ƙasar?"

Jami'in tsaron ne ya kalli dattijon tare da cewa. "Yawwa an zo wurin..." jami'in ya fadi yana sake daidaita tsaiwar sa kafin ya ɗora da cewan. "Tabbas wannan ita ne tambayar da ya kamaci ace kun yi min tun daga farko, KIND DADA! KIND DADA!!... dole duk inda wannan KIND DADA ɗin yake to la shakka ya san yadda tsarinmu yake aiki ciki da waje. Ya kuma san irin karfin da muke da... kuma ya san inda muke da rauni da wannan yake wasa da hankalinmu yallabai.... "

Wani daga cikin dattawan ne ya ɗan matse hannuwansa tare da furta.

"Ka fahimtar damu! Ka bamu haske dan gane da wannan shegen ɗan ta'addar wanda mu dai babu shi a cikin jerin tantiran da muke marawa bay....."

"Shut your mouth! Say one more word... just one more, and you'll live to regret opening your mouth." wata kakkausar murya ta katse shi tare da yanka masa jerin uban waɗan nan sharrudan daya saka shi dawowa nutsuwa da taytayinsa yana kama kansa, saboda tunowa da irin girman ɓaran ɓaramar da yake shirin aikatawa.

Kusan gaba ɗaya jami'an tsaron dake zagaye a room din kuwa tsaye suke sun yi cirko-cirko a ɗakin, cikin matuƙar taraddadi da ƙaulanin fargabar ɗan gidan mataimakin shugaban kasar da aka nema aka rasa tun jiya karfe ɗaya da rabi na dare, duk da kasancewar yana tare da jami'an tsaro amma hakan bai hana ɗan ta'addar kwamushesa ba. Wani guntun numfashi daya daga cikin jami'an yayi tare da ɗan fesar da wata iska daga cikin bakinsa yace.

“Yallabai tabbas koma waye wannan mutumi yana da matuƙar wayo..." yay maganar yana dan dafe kansa cikin matuƙar dagulewar tunani da yanayi, kafin ya ɗora da fadin. “Idan har muka bari nan da 24 hours ta cika bamu amso Sameer daga hannun koma su waye waɗan nan kidnappers din ba to kuwa tabbas akwai matsala. Domin zai sake amfani ne da wannan damar wajen ganin ya sake cimma burinsa a karo na biyu, amma kafin nan dole muma mu canja salon namu wasan, wanda muke da bukatar lokaci. Don haka duk yacce za'a yi to ayi kada a taɓa barin maganar ya fita nan da 3 day's... " A matukar mugun fusace Vice president da tun da aka fara maganar bai ce komai ya mike tsaye cikin muryan tsawa yace...

"Maganar Ɗana fa ake! Ɗan da shi ka dai ALLAH ya mallaka min a matsayi namiji magaji, ta yaya har kuke tunanin sai an baku lokaci? To ku sani nan da rufawar magrib na baku duk dajin da yarona yake to a tabbatar an dawo min da shi a raye, don wannan karon koma waye wannan KIND DADA ɗin dole ne ya san ya tabo masu ƙasar ne, dole ne ku jami'an mu ku nunama wannan tsageran ɗan ta'addan yaron cewan bawai ƙarfin hukumar mu yafi ba, dole ina buƙatan yarona, dole a dawo min dashi". Yanda yay maganar da bugar desk ɗin dake gabansa zaka san cewar a matukar fusace yace. Shugaban jami'an tsaron ne ya mike yana kallar vice president tare da dafe hannuwansa saman desk ɗin ya furta. "Calm down... I need you to calm down! Anan ina son muyi duba da tunanin mune zuwa ga waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace Sameer da aka yi. Kamar yanda muka sani tun a daren jiyan wasu daga cikin mayan jami'anmu ke wajen domin binciko ainahin abinda ya faru a inda aka dauke shi, so a yanzu haka wannan itace hanya mafi sauƙin da zamu fara bi don sanin mataki na gaban da zamu ɗauka akan lamarin, so kuwa kaga dole ana bukatan dan lokacin tabbas, dan yanzu dai ga agogo ya nuna mana ƙarfe 6:00am, wanda nake da tabbacin duk inda 10 zuwa sha daya tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami'ai na farkon da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama'ar gari zuwa ƴan jarida dama duniyar baki ɗaya don ganin irin reaction namu..... "

Shiru ne ya sake mamaye ɗakin bayan jawaban da shugaban ya kawo, wanda bai kara cewa komai ba sai ma cikin tunanin kalaman da shugaban jami'an tsaron da ya fadi suke ta tunani a ransu.

Daya daga cikin jami'an rundunar sirrin ne ya ɗan gyara zaman gilashin idon sa kafin ya mike cikin nutsuwa yace.

"Yallabai... akwai abu guda da nake son kowa ya fahimta anan wannan fa ba kidnapping ba ne irin wanda muka saba gani. Wannan ɗin alamar wani saƙo ne da aiko mana shi da gangan."

Nan take kuwa kawunan wasu daga cikin ministocin suka kawo wuta suna kallar juna kafin ministan gida Alh tukur Baba ya mike yana dan gyara farin gilas dinsa ya furta.

"...Saƙo! Sako dai?"

"Eh...domin da manufarsu don da don kuɗi suka ɗauke Sameer da tuni zuwa yanzu an tuntube mu. Amma tun bayan sace Sameer babu wata kira, babu wata buƙata, babu wata barazana. Wannan shi ke nufin wanda ya aikata hakan yana son mu shiga cikin ruɗani ne kawai."

Vice president Aminu Dakata ne ya ɗan bugi tebur ɗin dake gabansa a fusace.

"To me yake jira? Ko kuwa suna son su ballo yaƙi ne?"

Ɗan jingina kansa wannan jami'an yayi yana ce dashi.

"A ahh...yana son mu yi kuskure ne kawai, ku sani cewan mafi kuskuren hatsarin maƙiyi ba wanda ya fi ƙarfinmu ba ne. A ahhh sai dan mafi girman hatsarin shi ne wanda ya san yadda zai sa mu hallaka kanmu da hannunmu ne kawai."

Duk ɗakin kuwa ya sake ɗaukan shiru mai kalmar alamar tafiyar tunani a kusan karo na biyu.

"Mintuna goma kafin a sace Sameer... dukkan CCTV na yankin sun mutu lokaci guda har na daƙiƙa casa'in. Bayan sun dawo aikin kuma abin mamakin shi ne babu wanda ya shiga ko ya fita a cikin tarin hotunan da muka samu"

"Impossible..." Tukur Baba ya faɗi yana mikewa tsaye, Jami'in ne ya ɗan girgiza masa kai yana bashi amsa da cewan. "Da farko nima sai da nayi tunanin hakan... amma ƙungiyar fasaha ta tabbatar min da cewa ba a goge hotunan aka yi ba,haka kuma ba hacking a ka yi ba kamar dai wanda ya ɗauki Sameer yana son wasa da tunanin mune kawai..."

"...To idan haka ne wa muke nema ke nan tun da bamu da hujjar komai?"

Shugaban jami'an tsaro ya ɗan runtse ido na ɗan lokaci kafin ya buɗe su a hankali.

"Ba wai wa muke nema ba ne amsar tambayar namu, abin tambayar anan ita ce... wa yake zaune tare da mu a wannan ɗakin?"

Nan take idanun kowa suka fara yawo kan junansu, yayin da shakkar koma waye maci amanar cikinsu ta fara shiga zukatansu. Tsit haka shiru ya sake mamaye ɗakin taron kafin KHABEER K MASHI wanda ya kasance shi ne Director-General na baki daya Department of State Services (DSS) ɗin ya kalla Tukur Baba bayan ya kalli agogon dake manne da bangon ɗakin taron yace. "6:05am yanzun kaga kenan muna da sa'o'i 18, don haka hanyoyi biyu ne ke gare mu wanda sune suka rage mana, na farko mu yi abinda ya dace da doka mu yi sanarwa, mu yi taro kana mu jira.Na biyun kuma mu yi abinda ya dace da ɗanka wato mu shiga duhu mu karya wasu ƙa'idojin wanda shi ne abinda ba zai taɓa faruwa ba, kana daga nan zuwa nan da 24 hour bamu buƙatar media tasan halin da muke ciki, dole mu yanke sadarwa mu kuma rufe ko'ina hakan shi ne salon wasar da zamu buga masa, don na san zuwa yanzun ko wanne motsi namu yana iya gani, and.... Ai tun kafin ya karasa abinda zai ce din Vice President katse shi...

"Kuyi duk abinda zai yiyu walau media ta sani ko kada ta sani ni dai abinda kawai na sani shi ne ku dawo min da Ɗana! Ko da hakan na nufin za'a rasa rayuka..."

"Dole akwai bukatar dawo da AJMAAL kenan bakin aiki, domin shi kadai ne zai iya da wannan yakin..." Gaba daya kowa da kowa dake ɗakin taron ne ya juyo yana kallar *Assistant director I (ADII) Jameel Baita* ko kafin kowa yace komai *Chief security Intalligence office (CSIO) Abba Aminu ya riga su da furta."Ba dole bane, duk mu nan aikin me muke yi kenan? Karku manta cewar a yanzu baya tare damu, kuma irin hadarin aikinsa ɗaya ne da tsohon jami'inmu _RAYYERN KHALID_" Wani kalan ƙara murtuke fuska Jameel Baita yayi ya ce "Ba laifi bane don munyi amfani da damisa don firgita sauran namun dawa ba, duk da kasancewar ƙarfe a wuta wuyar ɗauke ke gare shi to mu a wannan taƙin da muke ciki ba ƙarfe a wuta ba ko gobarar data kama daga cikin kogi ce zamu iya tunkara muddin zamu samu abinda muke so daga gare shi.."

A tsawace Khabeer k Mashi ya mike yana dakatar dasu dukansu yana ɗorawa da fadin." Idan har muka zartar da hukuncin akan koma waye ya riga ya zartu kenan, duk da gudanar da cikakken bincikenmu tun daga kama kan jawabansu, alaƙarsu da wasu ƙungiyoyin da ake zargi duk da sun sha dakile harin ƴan ta'adda amma hakan ba shi ke nufin zamu dawo dasu bakin aiki ba! Kaiiii.... " ya kai karshen maganar da nuna Jameel baita." mun ɗora alhakin binciken kacokam akan ka a karkashin rundunar tawagar ZURU..."

Wani numfashi Jameel Baita ɗin ya fesar tare da risinar da kansa yana fita daga dakin taron don soma gudanar da aikin da aka bashi..... Daga nan su kuma suka ci gaba da tattaunawa da rarraba yadda tsare tsaren ayyukan nasu zasu gudana, cikin taka tsantsan da sanin makamar aiki.

*3 day's*

A ranar Alhamis din data kasance sha huɗu ga watan Mayu gidan jaridar Monday break ta fitar da wata jaridar da ta kawo cece kuce a garin Kaduna dama kasar baki daya. Mai ya sa ta kawo cece kucen? Ta kawo wannan cece kucen ne akan abinta ta fitar ya danganci UWA NAJERIYA ne, domin kuwa ta bayyana yadda jami'an sojojin suka dakile wani harin yan ta'adda ne a karkashin atisayen Operation na Fansan Yamma , sun dakile harin ne a wani yunkurinsu na kwato Ɗan vice president daga wannan gwawurtaccen ɗan ta'addar da duniya ke nema ruwa a jallo KIND DADA. Inda suka kwace makamai tare da babura, da sauran kayan yaki daga hannun miyagun, duk da basu samu nasarar kwato ɗan vice president ɗin ba, dakarun basu tsaya anan ba sun gano bomb din IED mai amfani da waya (command-wire IED) da aka binne a gefen hanya a dajin da suka isa dake kusa da wani yankin ƙauyen dake makwaftaka da dajin, inda gano bamb ɗin akan lokaci ya taimaka wajen dakile yiwuwar wani hari da zai iya jawo hasarar rayuka da dukiyoyi masu dinbin yawa. Yayin da dakarun ke ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da tabbatar da tsaro a yankin baki daya karkashin kulawarsu. Duk da cewar dakarun soji goma sha biyar sun samu karaya, biyu sun mutu, huɗu sun ji rauni. Amma a gefen maƙiyan anci nasarar kashe ƴan ta'addar har mutum ashirin da biyar, an kama kimanin mutane ashirin. Wanda wannan harin yan ta'adda da aka dakile ba ƙaramin farin ciki ya sanya kasa da yankunan garin ba, domin kuwa kasa ta kiyasce cewan kimanin mutane dubu ashirin ne ke mutuwa duk shekara a Nigeria sakamakon ta'addancin, wanda a bayyane a kuma zahirin gaskiya kowa yasan cewar gwamnati nada hannu dumu dumu akan rashin tsaron da kasar ke fama. Banda mutane kimanin miliyan biyun dake rasa muhallansu duk shekara sakamakon harin ta'addancin da kullum sake ta'azzara yake maimakon yayi baya a kasar. Bayan haka kimanin mutane dubu 25 ne yunwa take kashewa sakamakon ba'abarsu sun noma gonakin su ba, Haka za kuma kimanin mutum dubu shida ne ke mutuwa a duk shekara saboda ƙarancin magani a asbitoci, inda rahotannin gidan jaridar ta rufe da cewar, da yawan ma'aikata wannan aikin nasu shi ne zai kaisu wuta, sabo da babu gaskiya, ba tsoron ALLAH, babu adalci a cikin aikinsu sai tsantsan zalumci da ha'inci duk da cewa da yawansu ana zalumtar sune ta hanyar yanke musu albashi ko karanta musu duba da cewar a wannan takin da ake ciki kowa mafita yake nemawa kansa ido rufe amma hakan ba shi ke nufin kayi zalumci wa kasar data raineka ba.....

*****

*KAUYEN KURMAN RAFI....*

Masu iya magana sukan ce akwai wasu wuraren da idan mutum ya taka ƙafarsa iskar wajen kaɗai ta isheka fahimtar cewa farin ciki ya daɗe da yin kaura a irin wannan wurin, kamar yadda ya kasance Kauyen Kurmin Rafi na ɗaya daga cikin jerin wannan littafin na masu hasashe da hangen nesa. Dokar daji ce da ta ɗanyi nesa da gari, wadda wata tsohuwar bishiyar Kanya wacce kowa a garin tashi da budar ido yayi ya ganta a idda take ɗin, wanda tsoffin garin sukance tana da shekaru da yawa fiye da yawancin mazaunan ƙauyen garin, a karkashin bishiyar kuwa wata matashiyar budurwa ce ke zaune ita kaɗai. Hannunta ɗaya na riƙe da ɗan ƙaramin kwando na saka, ɗayan kuma na tallabe da kumatunta. Idanunta a buɗe suke kamar tana kallon wani abu sai dai a zahiri ba kallon komai take ba, kawai ta tsaya ne kawai ta zubama wuri guda ido tana auna yadda ababuwa ke faruwa da shudewa tamkar basu wanzu a doron kasar ba, sai dai data rufe ido babu abinda ke mata amsa kuwa cikin kunnuwanta illa ihu da kururuwar mutanen dake zagaye da kauyen, tana jin ihunsu ne tamkar suna bibiyar rayuwarta tun daga jiya har zuwa gobenta ne. Sunanta Nadiya Auwal Habu! Wacce a kiyastin shekaru ba zata zarta shekara ashirin da ɗaya ba, amma ita rayuwa ta koya mata manyan darussan da wasu sukan shafe tsayin shekaru kafin su fahimta. Ta koyi cewa ba kowanne hawaye ne ke kawo tausayi ko mafita ba, ta koyi cewar yunwa na iya sa mutum ya manta da mutuncin sa, ta kuma koyi cewar wassu lokutan ba harsashin bindiga ne ke kashe mutum ba...illa tsoro ne da fargaba. Duk da wannan tsananin, duk da wannan fafutukar akwai abu ɗayan da rayuwa ta kasa ƙwace mata shi ne jarumtaka!.

Duk da talauci, duk da rashin gata, duk da yawan tashe tashen hankulan da suke fuskanta wanda suka mamaye Kurmin Rafi, ba ta taɓa durƙusawa gaban ƙaddara ba. Ta yi imani cewa mutum ba ya zaɓar inda aka haife shi, amma yana iya zaɓar yadda zai rayu ya tsira da rayuwarsa...

"RAYUWA!..." ta furta a bayyane tana kallon yadda iska ke kaɗa ciyayi irin na farkon damunar nan da suka fara fitowa, a bayyane tana mai sake furta. "...kin kasance kamar ruwa amma mai yasa duk lokacin da na ce na fahimce ki, sai ki canja min ajin hanyarki?."

Wani murmusawa ta yi ba murmushi irin na farin ciki ba, a ahh sai dai murmushi ne irin na wanda ya saba da ciwo tun yana mamaki har ya daina mamakin sa. A daren jiya, ƴan ta'adda sun sake kai hari garin nasu, har suka ƙone wani inda matar gidan da ɗanta suka ƙone, wani yaro kuma ya rasa mahaifinsa. Wanda kamar koda yaushe, kamar duk sanda ake kawo musu farmakin a daren na jiya babu gidan daya runtsa, amma sai gashi gari ya waye rana ta sake fitowa kamar babu abin da ya faru, a nan ne Nadiya ta fahimci wata babbar hikima. Tabbas rayuwa ba ta taɓa tsayawa saboda baƙin cikin mutum ɗaya, kai ne kawai za ka yanke shawarar ko za ka tsaya tare da baƙin cikin ka ne?... ko kuwa zaka ci gaba da tafiya a tare da shi ne da duk abinda ka zabar ma kanka?, domin ita rayuwa mai wucewa ce. Tsamm ta miƙe tsaye ta ɗauki kwandonta, sannan ta karkaɗe ƙurar da ke jikinta ta soma tafiya zuwa gidansu, gidansu dai wannan gidan nasu mai cike da tarin ƙalubale da baƙin ciki, bata da mahaifiya sai mahaifi wanda ya kasance makaho ne baya baya gani mahaifiyarta kuma Dada kurma ce, shekaru biyu baya da suka wuce ALLAH ya mata rasuwa. Kaf garin babu mai jin kanta, babu mai tallafawa rayuwarta saboda Mahaifinta bashi da karfi ko kaɗan, igiyar daure dabbobi yake saidawa da tuka irin ta daurin gero, ita kuma Gwaggo Talatu matar baban nata fura take daka mata ta kai wurin Fulani ta sayar, se dai hakan ba shi ke saka in ta gadama ta hana mata abinci ba, ta taso cikin wani irin kunci da kadaicin rayuwa, saboda babu wanda yake shiga sabgarta a duk Kurmin Rafi...

A wani irin natse da rangaji irin na wanda yake jin matukar yunwa take tafiya, tana tafiyar ne kuma tana sake auna rayuwa da mizanin hankali, ita kadai a ranta take ayyana cewar.

'Wato ita fa hakikanin rayuwar kanta wata abace mai dauke da nau'in darasi da tarin Ilimin da da ace za'a bashi muhimmanci fiye da komai da kowa bai shiga halin da yake ciki ba, hatta daga sautin bugun Numfashi ma yana daga cikin tasirin Rayuwar ko wanne bawa sa'ilin da kyakkyawar ma'amala da zaman take wa suke kasancewa sune jigon sanin abinda ita kanta rayuwar ta Kunsa. Tabbas Acikin Rayuwa akwai dumbin darasi ma'abota ilimi da kowace halitta yana da kyau ta samu damar nazarin hakan domin yin hakan shi ne zai bama kowa damar aiwatar da rayuwarsa cikin sauƙi da sauƙaƙawa.

Rayuwa cikin nau'in kaddara shima wani abune da kan iya zama wani Sashen koyon ilimi tare da fahimtar abinda Ubangiji ya tsara ga kowanne bawa.Yayinda kyakkyawan aikin kowanne bawa shi ne zai bashi damar yin kyakkyawar Rayuwar da da zarar an rasa aiki mai kyau toh an rasa dukkan farin cikin ne. Da ace yadda Mahaifiyarta Dada take da kawaici da Alkunya haka kowanne mutum yake da rayuwar mutane da yawa tayi karko domin ita kunya tana daga cikin sashen yaduwar IMANI neee. Kamar yadda furuci na alkhairi yana kara wanke zukata ne, yayinda su kuma zukatan sune matattarar Sirrikan kowanne Ɗan Adam...

A hankali taci gaba da taka ƙafafunta cikin ƙurar hanyar da ta saba bi tun yarinta, rana ta fara ɗagawa zuwa sama, haskenta ya soma dallarewa tana ratsawa ta cikin rassan bishiyoyin da suka yi wa hanyar inuwa, don haka ta dan kara hanzarinta tasan duk inda Gwaggo Talatu take ta na can ta gama daka mata fura. Tuni kuwa cikin dan kankanin lokaci sai gata a bakin garin, inda ta hango dandazon yara ƙananu suna ta gudu suna dariya a bakin rijiya. Na ɗan lokaci kawai ta kallesu da wani murmushn da yaso bayyana a saman fuskarta, amma tana shanye abinta domin dariya irin haka ta kasance abu mai matukar wahala a gare ta... Saboda rayuwa ta koya mata cewa ba kowace rana ake yi wa mutum alƙawarin cikar farin ciki ba, tare da ɗan jijjiga kanta tana ci gaba da tafiyarta.

Kai tsaye wani tsohon ginin kasa ta nufa, wanda gaba daya katangar gidan a gajiye take ko da yaushe tana iya zubewa domin ta ruɓe, a saman guntuwar katangar kuwa igiyoyi ne iri-iri da aka shimfida ana jiran su gama bushewa. Wasu sun yanke, wasu har sun soma warware ma alamn sun gama bushewa. Da sallama dauke a bakinta cikin muryanta mara hayaniya ta shiga gidan.

"Assalamu alaikum..."

Amma shiru alamar babu kowa a tsakar gidan kenan ko kuwa matar gidan bata kusa, a natse ta kara sa kutso kanta zuwa filin tsakar gidan nasu, daidai lokaci data dan soma jin tari mai zurfi daga cikin ɗaki, tari ne irin na dattijon da shekaru da wahala suka haɗu suka raunana masa jiki ta hanyar taron dangi.

Kwandon hannunta ta ajje a hankali tana nufar ƙaramin ɗakin, a kan wata guntuwar tsohuwar tabarmarsa ta tarar dashi ya she, hannunsa daya na riƙe da wata igiyar da bai gama saƙawa ba, alamar baccin ya ɗauke shi ne yana aikin neman abin da za su ci. Fuskar nan tasa mai cike da nutsuwa duk da makantar idanuwansa ta ƙara karya zuciyarta..

"Kin dawo Nadiya?"

Ya tambaya ba tare da ya buɗe idanunsa ba sai dan kokarin motsa su kawai da yake, ɗan murmushin da ita kanta ta san ba gaskiya ba ne tayi tace.

"Na dawo Baba Sannu da aiki."

Tun kafin kafin ya amsa ta wata kakkausar murya ta fito daga bayanta..

"Nadiya!ke Nadiya Iyyeee kice bayan shanya ɗin da kikayi har zaman fira kika samu da uban ki kenan? Furar dana daka tana nan tun ɗazu nake jiran ki zo ki ɗauka amma sai yanzu kike dawo kika dasa zaman gulma?"

Haka duk su biyun suka ji saukar muryar Gwaggo Talatun.. Dan lumshe ido Nadiya kawai tayi wani abu na zuwa ya tokare kirjinta....

_To fa masu karatu ya take ne? Aje ko ba'a je ba?_

_Yau kuma inda alkalamin ya cillo mu kenan, ina basu cewa AMMEY me yasa baki fiye rubutu akan rayuwar kuncin da kasa da mutanen cikinta ke ciki bane? To yau ga amsar tambayarku nan, yau ALLAH ya nufe ni da zaku lo wasu ababuwan dake kewaye damu na ɗora alkamina akai da sunan ALLAH da kuma izini da yardar sa_

_Tofa Fan's shi kuma wannan nashi salon kenan, da wannan muka fara yau kuma ta wannan salon labarin zai soma_ *Idan kun so muyi tafiyan tare Bismillahi kamar dai kullum kamar yadda aka saba a nuna min One love din mutanen Amanar AMMEY*

_Ya kuke tunanin wasan ze kaya? Ya kuma kukaji salon rubutun wannan karon? _

_Ni ban ze ce ma kowa komai ba kawai dai nasan zance mu haɗu a kashi na gaba ne domin jin yadda zata kaya_

#KIND DADA #AJMAAL #RAYYERN KHALI