Page 3&4
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Sosai Gwaggo Talatu ta sake tsaiwa daga bakin ƙofar ɗakin tana huci, dan guntun tsumman da aka yi labule dashi ɗage a hannunta, tana wani sake huhhura hanci sama ta kuma ki sakin labulen. Idanuwanta cike da wani irin gajiya da takaicin irin halin matar Baban nata ta dago, saboda darajar Mahaifinta kawai take ci in banda haka da tuni an jima da wuce wajen. Baban tane ya sake rike hannunta dake cikin nashi, cikin son ya kwantar mata da hankali ya ɗan sake matse hannunta dake cikin nasa yace.
"Kici gaba da haƙuri Nadiya! Domin hakuri shi ne mabuɗin nasara a koda yaushe, kamar yadda nake yawan gaya miki cewar kada ki taɓa gaggauta yanke ƙauna daga rahamar ubangiji, kar ki yi duba da cewar addu'ar da kika jima yi shekara da shekaru kamar ba ta amsuwa ne nan take, a ahh saboda ALLAH baya taɓa mantawa da bayinsa, saboda a koda yaushe yana ba da mafi alkhairi ne a duk lokacin da ya san ya fi dacewa da bayinsa, abu guda da zan ci gaba da baki kwarin gwiwwa a kansa, kici gaba da addu'a da kyakkyawan zato ga ALLAH. Ki tuna cewar duk abin da kake nema a duniya wata rana zai ƙare, amma kyakkyawan aikin da ka yi saboda ALLAH da kuma hakuri to ki sani ba zasu taɓa lalacewa ba. IN SHA ALLAHU rayuwarki zata yi kyau! Zata zata sha ban ban da irin tamu rayuwar da muka taso cikinta, zaki zama mace ta farkon da zata taɓa kafa tarihinta a cikin Kauyen Kurman Rafi....
"Nadiya!ke Nadiya Iyyeee kice har lokacin fira kika samu da nakashashen uban naki bayan shanya ɗin da kikayi kenan?" Haka Nadiya taji saukar muryar Gwaggo Talatu cikin kaushi da faɗa fada kamar kullum kamar yadda ta santa tun farko, Uban ihun kiran da gwaggo Talatu ta sake zabga mata ne ya sanyata ɗauke guntuwar kwallar data tarum mata tana cewa.
"...Yi haƙuri Gwaggo gani nan fitowa yanzu...."
"Kardai ki fito har yan gidan Madaka su rigaki ɗin kamar kullum ki dawo min da kwantai ta zamewa ubanki asara."
Sunkuyar da kanta kawai Nadiya tayi tare da mikewa tsaye wanda ya saka Baba Auwal ya ɗan yi wani gun tun murmushi, murmushin da ya fi kuka ciwo. "Ita rayuwar duniya da kike gani Nadiya ba ta tambayar ko kana da zabi tana zuwar mana ne kawai a duk yanayin da taso kuma dole mu karɓeta har ma mu durƙusa mata... Amma jajircewa da karfin adda'a kan sa ka tsallake wasu tarin ajujuwan da baka san dasu ba..."
Jinjina masa kanta Nadiya ta yi tana fitowa tsakar gidan, a gurguje ta watsa ruwa tayi sallan karfe daya kana ta fito, kwaryan furar ta dauka bayan ta nannaɗa ɗan kwalinta tayi gammo dashi, Gwaggo Talatu kuwa tin da Nadiya ta fito take kallonta tana son ganin wata gazawa ko rauni tattare da ita amma babu kamar koda yaushe, babu wannan tsoron da take son gani a tattare da ita sammm. Haka Nadiya ta dauki furarta ta nufi inda fulani ke zama, amma kafin nan sai data biya shagon da take amsar sugar wanda idan an sakata damu ba sai ta saya a wurin kowa ba idan ya kare ta kai ma mai shagon kudinsa ta ɗauke ribar, a natse take takunta jikinta sanye da riga da zani na atamfa sai bakin shijjabi da silifas a kafarta da ya ɗan ji jiki. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba ta isa inda take zama, dake babu wani nisa sosai daga gidan su zuwa wurin. Tun kan ta isa Jebu mai nono ke dago mata hannu saboda ita Nadiya ce tata, duk wanda ya sai nono a wurinta a gurin Nadiya ake sayen furar, da wasa da dariya suka tarbeta kamar kullum bayan ta gaida su, tana zama babu jimawa masu damun da su ke yi a wurinta suka soma isowa, daga masu dari biyar sai masu dari bakwai har dama masu dubu daya, idan kuɗin ka dari biyar ne zata saka maka Nonon dari uku furar dari sugar na dari, idan dari bakwai ne nonon dari hudu, furar dari da hamsin sugan dari da hamsin haka ake hawan hawa. Sai gashi la'asar din fari har ta sayar kai tsaye ta kai ma mai shagon nan kudin sugansa, ta sayi awarar dari biyu da ruwa mai sanyi ta zauna ta ci ta sha ruwanta ta kara gaba ko gwaggo Talatu bata bata abinci ba bata da damuwa. Sai dai me? Tana shiga gidan taja turus ta tsaya don ganin Yayarta Yaya Sadiya da ita kadai ALLAH ya mallaka mata zaune daga bakin ƙofar dakin ɗan dakinta tana kamar sheshshekar kuka, a sanyaye jiki a mace ta iso tsakiyar gidan tana daukar yaron ta dake rarrafe jikin nan yayi dumu dumu dashi ya haɗa uwar alnakiyar dauɗa bana wasa ba. Ita kuwa gwaggo Talatu sai faman kaiwa da komo take tana zagba fadan ita fa bata ga amfanin wannan yawan yaje yajen da Sadiyan ta tsira ba, don kawai mijinta ya mata kishiya ai ba'a akanta farau ba haka kuma ba a kanta denau ba. In banda rashin hankali da hauka tayaya ana irin wannan hali na kani kayi taka yawon yaji gida tazo kara jibga musu wani nauyin, wanda suma nasun bawai gama dannuwa yake ba kawai ana ɗan hadawa da karma karma ne, in da badon ALLAH yaso ma yarta kuma autarta Tsahare tana cikin garin Bauchi aikatau ba a da basu san ma inda zasu yi da ransu da rayuwarsu ba, ita kuwa Yaya sadiyan da har lokacin take tsugunne kuka kawai take tana sharewa da majina, idon nan yayi jajir alamar kukan bana iyaka lokacin bane. Baba Auwalu kuwa dake zaune daga bakin ƙofar dakin babu abinda yake cewa sai tufkarsa da yake yi yana tufkawa da sauri alamar ransa ya kai ƙololuwa wajen baci kenan. Kai tsaye tiken dabbobin da gwaggo Talatun ke tsaye Nadiya ta bita tana miƙa mata kudin furar da tayi dari tara da hamsin. Wartar kudin daga hannun Nadiya ɗin tayi tana jan tsuka tare da furta "Irin tsiya" a bayyane. Wani kallo Nadiyan ta jefa mata daya sakata hadiye sauran maganar da taso sake yabo musu, don tasan ma'anar irin wannan kallon idan Nadiya ɗin ta mata na ki iya baki da shiga taytayinkin nan ne. Aikuwa kitsim haka taja bakin tana rufe shi tare da since haɓar zaninta ta daure kudinta tana ci gaba da bama yan dabbobinta ruwan tsami da dusar awarar data saya musu.
Kai tsaye dago Yayar tata tayi bayan tama Baba sannu da gida suka nufi ɗakinta, yaron nata rigima da yunkurin son kwacewa daga jikinta zuwa gurin uwarsa. ALLAH ma yaso yau dan nonon da take yawan tahoma da Baban da dan yawansa, don haka silbar Dadansu ta dauko mai kyau sai walkiya take ta juye nonon ta dama musu har zuwa lokacin bata cema Yayar tata komai ba, sai dai akai akai takan ja kwafa. Furar ta tura mata tana fita da wacce ta dibarwa Baba ta kai masa tana zama ta amshi tufkar da yake ta fara da sauri da sauri don har ta fishi saurin ma.
"Taki cewa komai sai kukan da kawai take yi, na tambaye ta bata bani amsa ba, kije kiji abinda yau kuma ya faru da ita..." Baban ya fadi a tausashe wanda ya sakata mikewa tsam ta isa ɗakin daidai Yayar nata na kokarin fitowa, ƙasa tayi da kanta da sauri tana sake dauke hawayen idanunta, wanda suka kumbura sukayi sumtum ɗayan kuwa harda taruwan jini a cikinsa, wanda kai tsaye Nadiya ɗin tasan Mijin Yayar nata ya dake tane, ga tsohon ciki a jikinta amma bayyi duba da hakan ba ya da keta. Haba rashin tausayin ai kamar har yaso yayi yawa ma, shi kuwa Audu ina yake son Sadiya takai ranta ne wai? Shekara daya da aure an maka kishiya ka jure, kuma anzo zaman yaki dadi saboda tsabar son kan da yafi yawa a zaman nasu, sai yayiwa jimma kishiyar Yayar tata abu sai biyar bai ma sadiyan ba, amma ta dauke kai, idan aka samu akasin rana daya tayi magana ya kama ya linka kamar bai san zafin taba, kamar ba soyayya su kayi suka auri juna ba. Ita ire iren waɗan nan ababuwan suna ɗaya daga cikin abinda yasa ta ke cire son aure kwata kwata a rayuwarta, shi yasa har yanzu Shitu yake nan yana fama a kanta amma sam taki amincewa da bashi fuska kwata kwata, duba da kallon yadda zamanin ya gama lalacewa, sam ba'a wani bima yaya hakkunansu a gidajen auren su, shi yasa su kuma mazan suke sake samun damar lasisin ci gaba da shuka duk abinda suka ga dama. Wasu ruwan hawaye ne suka ciko idon Nadiya duk da ba komai ke sakata saurin hawaye ba, kai tsaye hannun Yayar nata ta kama tana yin dakin Mahaifinsu. Tana ta zaunar da ita gabansa a zafafe tace.
"Amman Baba kana ganin haka zamuci gaba da zuba ido Audu yana neman nakasa Yaya Sadiya? Dubi yanda ya tara mata jini a jiki?..."
Ya bude baki kenan da niyar magana shigowar Baba Gaji Yayar Baban nasu ta katse shi da wannan balbalin bala'in nata. Sai dai kuma mukut maganar nata ya katse ne lokacin da idonta ya sauka akan Sadiyan da tayi wani kwajaja da jiki. Tayi zuru zuru kamar beran da aka jijjiga a buta. "Sadiya yanzu kece kika fige kika lalace haka?, kalle ki kamar wacce ake gutsuran namanki danye, kai Innalillah wa'inna ilaihi raji'un wannan duniya ina zaki damu haka?" Baba Gajin ta faɗa tana tafa hannayenta, kafin ta ɗora da fadin. "Shi ne kuma tsabar cin amana da rashin darajar da ake bamu aka je aka fa domin kin yi yaji? Kai ALLAH mun tu ba ALLAH ka yafe mana kurakuranmu, wato yau ga masifaffiyar da bata san kanta ba sai abinda aka ɗora ta akai, aka je aka ce gaki can kin tafi gida, saboda kawai an saka rayuwarmu a kwandon shara. Wanda da wannan tunanin mazan suke buɗe idanu suga ana wulakantamu shi yasa suke buɗar idanu bamu da daraja ko ta gayan koko a wurin su, saboda sun ga iyayensu mata ai basu da wata daraja ko kima a idanun iyayensu maza. Amfaninmu shine kawai musu girki, haihuwa, kashe musu ƙishi shikenan. Iyakar darajarmu Kenan. In banda sanin rashin darajar aure ai ko bakici albarkacin komai ba kyaci darajar tsohon cikin dake jikinki..." Habawa nan fa ta shiga surfa fada ta inda ta shiga bata nan take fita ba.
Anan gidan ta zauna har dare a cewarta taga dan mara kunyar da zai biyo bayan Sadiyan da sunan biko. Da kuwa ta yanka masa daya daga cikin shika shikar haukar data iya, ita kuwa Sadiya Islamiyyar bayan gidansu ta wuce wacce dama duk a lokacin da kaga dama za ka iya zuwa. A can gidan kuwa in banda habaice habaice babu abinda Gwaggo Talatu keyi, ganin bama iyaka Sadiya din ba yanzu harda karin Baba Gajin, aikuwa taki ɗora abinci a cewarta dama ai ita ke fafutukarta ba uban kowa ba. Oho dai su sun barta da aiki sun kule daki Baba Gajin nata sake dannar Sadiya din. Koda Nadiya ta dawo ta tarar da halin da gidan yake ciki sosai taji ranta ya so su, ta rasa gwaggo Talatu wacce kalar mata ce mai shegen bakin hali, muddin zata ga gimlawar bako gidan ta ringa cika tana batsewa kenan ita kadai. Gyadarta tun ta kalen bara ta fiddo taje ta aunar da kwano biyu ta sawo rogo ta jefa musu dan wake. Shi kuwa Baba yana can waje tare da abokanansa ana ta sake mai da yadda daren jiya ya kasance.
Bayan ya dawo gida lokacin Baba gaji ta tafi gwaggo Talatun kuma ta fita anguwa ya kira Sadiyan ya mata nasiha sosai mai ratsa jiki da zuciya, sosai ya taushi zuciyarta da cewar tabbas yasan ana zalumtar ta amma ya mata nasihar cikin hikima , inda daga karshe ya rufe da cewa. "Sadiya daga karshe ina mai shawartanki da ki koma ɗakin mijinki, ki sani aljannarki tana ƙarƙashin tafin ƙafar MIJIN kine, kici gaba da mishi biyayya. Duk wata macen duniya da zaki ga tayi lib a dakin mijin ta, to tabbas haƙuri take yi dashi, kuma tana duba makomar rayuwar yaran ta ne, shi kuma dama aure dan haka ne ya gaji haka, amma idan kika yi duba da hakuri da halayen mahaifiyarku ba zaki fara yawon yaji ba, duk tsahon zamana da Hidaya ba ta taba min yaji ba, duk da irin gallawa da bakar wahalar da Talatu bata bata ba. Amma haka take dannewa tayi hakuri baka taɓa jin ta tanka ballantana harta kaita ga yin yaji."
Tun da ya fara mata maganar take gyada masa kanta tana sake share hawayenta, shigowar Gwaggo ne ya saka ta mikewa tana wucewa ɗakin Nadiya wacce take can tana bitar karatunta. Shigowarta ɗakin ne ya sakata rufe alqur'anin nata tana gyara mata gidan sauron data daura musu ita da yaronta, a ɗan guntun gadon ƙarfen Dadansu, ita kuma ta kwanta a tabarmar kaba a tsakar ɗakin, shiru su dukka suka yi bayan ta shige net ɗin. Kafin ta fara magana a sanyaye.
"Ban san haka auren yake ba Nadiya da ban yi ba, dama ashe haka auren yake? ashe haka mazan suke amma a hakan har wasu ke tururuwar yin auren, ba tare da sun san irin bakar wahala da ƙalubalen dake cikinsa ba, ba su san irin ƙunci da tashin hankali dake cikin saba? Tun muna tun bamu da wayo muke yawan ganin Dada na kuka, sai dai ita nata ƙalubalen ba irin nawa bane, gashi a yau nima na faɗa irin taskun da mahaifiyarmu ta faɗa. Sai dai nawa yasha ban ban da nata, saboda ita Baba yana sonta, baya dukanta irin yadda Audu ke dukana,ita sai dai ma ya lallasheta ya tausheta akan taci gaba da hakuri da gwaggo talatu,ni kuwa fa?ya kama ya daka, amaryarsa tamin duk rashin mutumcin data ga dama. kuma nasan a haka zanta zaman haƙuri har ranar da ALLAH zai karfi raina.... Nadiya da ace zan iya fasa miki irin zaman haƙurin da nake yi a gidan aure na da sai kin zubar min da hawaye, gaba ɗaya Audu bashi da imani, da wannan uban tsohon cikin haka ya daure ni a jikin ƙarfen gado ya rinƙa tabkata kamar ALLAH ya aiko shi...."
Kukan da yaronta Ƙasimu yayi ne ya sakata yin shiru tana jan ijiyar zuciya, tare da cewa Nadiya ta biko mata ruwa shi ya farka nema. Komai bata ce mata ba, ruwan kawai ta bata ta koma tana juyar da kanta wani bangaren daban, zuciyarta na wani irin tafasa da tukunzuma... Ta jima tana dannar zuciyarta akan kalaman da suke shirin fita daga bakinta wanda ba masu kyau bane, dake ita din macece mai irin zuciyar jarumta da kuma zafi, amma duk da haka tayi kokarin kawar da koma miye ta mike tsaye tana kamo hannuwan Yayar nata cikin sanyi da raunin da ba kowa ke iya gani kai tsaye daga gare ta ba ta shiga fadin. "A cikin kowacce rayuwa! a cikin kowacce tafiyar dole akwai kalan ƙalubalen da ake fuskanta, sau da dama a wasu lokutan shaydan da son zuciya na iya sanyawa ka ji kamar hanyar gaskiya tana da tsawo ko wahala. Za ka ga wasu suna samun ci gaba ta hanyar cuta ko makirci, sai ka ji kamar kai da kake nufin kowa da alkhairi kana ta ci baya ne. To a cikin dan wannan ɗakin ne in ji ALLAH madaukakin sarki shi ne lokacin da ake gwada imaninka da hakurinka. Amma idan muka fuskanci ALLAH maɗaukakin sarki, muka koma gareshi da duk wasu bukatunmu,to kuwa tabbas haƙiƙa ALLAH zai saurare mu, zai kuma yaye mana dukkanin damuwar da take damun mu ko ba-daɗe ko ba-jima, musamman idan munyi haƙurin mun kuma tsaya akan biyayya ga ALLAH subhanahu wata'ala. Akoda yaushe zuciya itace take sarrafa gangan jikin kowanne dan adam tare da tunaninsa. Yadda mutum yake kasancewa to haka aikinsa yake kasancewa. Shi yasa masu iya magana suke cewa zai fi kyau ko wanne mutum ya cika zuciyarshi da tunani mai kyau kuma mai amfani, hakan shi zaisa mutum ya samu ribar rayuwar tare da amfanar da al'amuran rayuwarsa yadda yakamata, kici gaba da rokon ALLAH yaci gaba da baki ƙarfin zuciya da hakuri In sha Allahu wata rana zai canja rayuwar aurenki baki daya... " Hannunta dake cikin na da Nadiyan ta sake kankamewa tare da furta." A wasu lokutan mukanyi kuka ne da hawaye, sai dai kukan zuci shi ne mafi ciwo da ɗacin da yafi kassara rayuwarmu da nasarorinmu a ɓoye ko a zahirancen da bama iya mantawa dasu cikin sauƙi irin haka Nadiya. Saboda idan aka baka wani tabo ko tambarin ciwo a cikin zukatanmu, su ne bamu iya mantawa dasu har gaban abada domin kuwa suna bar mana tambarin tabon da ba zamu iya taba mantawa ba, zamu ringa tunasu a lokaci bayan lokacin duk kuwa irin sauyin da rayuwar zata bamu. Amma In sha Allahu zan jure, zan ci gaba da yin hakurin, zan ci gaba da yin biyayyar.... " gaba daya tausayin Yayar nata ne ya sake rufe ta don haka a hankali ta zare hannuwanta daga cikin nata tana komawa saman tabarmarta ta kwanta...
*DSS HEADQUARTERS ABUJA 12:10pm*
Tsit haka babban dakin da suke zagaye da na'urorin kwamfuta din yayi, babu motsin komai baka jin sautin komai a dakin in ba sautin danna keyboard ba, wasu Jami'an kuma ba wai danna computer ɗin suke ba suna tsaitsayene hannuwansu rike da file. Jameel Baita na tsaye a gaban babban allon dakin, wanda kai tsaye hotunan CCTV yake kalla da taswirar Kaduna ta gama bayyana, sai hoton Sameer dake gefe.
"Sa'o'i Sha ɗaya da rabi suka rage mana domin kai farmaki a inda muka fi tsammani cimma nasara." Yay maganar yana juyowa gaba dayansa zuwa fuskantar duka mutanen dake dakin.
"Tawagar ZURU fatar kuna nadar umarni?" "Yes Sir!" muryoyinsu suka amsa a kusan tare. Dan bugar table ɗin dake gefensa yayi yana rankwafawa, yana mai furta. "Dole mu iya takunmu kamar koda yaushe saboda tabbas dole wanda ya sace Sameer ya san tsarinmu. Don haka daga yanzu lokacin mu ya fara! Babu waya iyaka ta PTT kawai zamu dinga sanar da junanmu duk abinda ke faruwa a kafta...."
Ya ƙarasa maganar yana kallon kowa da ƙwayar idonsa ɗaya bayan ɗaya. Sai ya miƙe, ya ɗauki file ɗin da ke gabansa ya rufe shi yana mai sake fuskantarsu da fadin. “Ku shirya muna da sa’o’i goma sha ɗaya da rabi kacal.” Tsit haka ɗakin yayi don kowa yasan irin aikin da ke gabansu mai girma ne, kasancewar kowa yasan dajin da zasu shiga mafi hadari ne sosai a yankin kaduna, wanda yake kamar maɓoyar yan ta'adda ne.
KADUNA Kambari forest.
Sosai zuwa lokacin duhun daren ya sake mamaye dajin, baka jin komai a dajin sai wani irin shiru yayi irin mai bada tsoron nan, sai gudun motocin DSS din nan wanda biyu ne kawai suka kutsa kansu zuwa cikin dajin, biyun kuma ana barinsu daga bakin Ƙauyen. Jameel Baita ne ya fara saukowa a natse sanye da baƙar riga da wando, bindigarsa rataye a kafaɗarsa nan sauran suka fara fitowa suma, hannunsa ya ɗaga musu aikuwa sauran jami'an suka tsaya, ɗan ƙaramin PTT ɗin da ke makale jikin kunnensa ya taɓa yana mai furta.
“Zuru One, status.” manyan yatsun hannayensu suka daga masa suna amsawa da, “Zuru One, ready.” sake danna PTT ɗin ya kuma yi tare da sake furta. “Zuru Two?”
“Ready, sir.” suma daga can ɗayan bangaren suka bashi amsa, wanda ya saka Jameel ya ɗan lumshe ido.
“Good. Daga nan babu wanda zai yi magana sai da izini, muna tafiya a hankali, kada wani ya kunna haske ko yunkurin aikata wani abun da ba'a bashi umarni ba, domin kowa yasan hukuncin bijirema umarni.” sake hade baki sukayi suna sake bashi amsa da yes sir. Tawagarsu ce ta fara kutsawa cikin dajin Kambari forest. Wanda yake da wani irin zurfi fiye da duk tsammanin mai hasashe. Wani irin hatsabibin daji ne dake kewaye da manyan dogayen bishiyoyin da suka rufe sararin sama, har wata ba ta iya haskaka hanyar da suke bi. Ƙasan kuwa cike take da busassun ganyayyakin da idan har wani cikinsu yayi kuskuren taku zai iya bayyana motsinsu. Sai dai cak ya dakata yana daga musu hannu sakamakon kamar gittawar abu daya gani, sake kashe kunnuwansa yayi tare da zuke numfashinsa yana janyewa, sai dai bai sake jin motsin komai ba, don haka suka ci gaba da tafiya har suka isa wani babban fili a tsakiyar dajin. Wacce take dauke da wata tsohuwar rumfa a tsakiyarta, amma ƙofar rumfar a buɗe take, dan dakatawa duk suka yi saboda basu san ko wanne irin tarko bane aka dana musu, Jameel ya ɗaga musu hannu tare da furta.
“Stay.”
Jami'ai biyu ne suka zagaye gefen dama, wasu biyun kuma suka koma bangaren hagu, Jameel ya yi gaba shi kaɗai tare da tura ƙofar. Sai dai wayam babu komai sai wata kujera da igiya a jikinta, wanda da dukkan alamu wani abu aka daure. Cak haka a wannan karon ma Jameel ya sake dakatawa tare da fesar da wata numfashi mai ɗumi yana kaima iska naushi da ambatar....
“Sameer?”
Daga haka ya karasa kutsa kansa ciki ya shiga duba ko'ina amma babu kowa babu kuma wata alamar da zasu iya bibiya. Har ya juya zai fita kenan kyal haka idon sa da yake sak na mage hango masa wata farar dakardar da aka rubuta.
*SAƁA LAMBA!*
Da manyan baki dara dara, wani irin runtse idonsa yayi jikinsa ya shiga tsumar bacin rai ya kai durkushe tare da kaima jikin kujerar naushin da sai da ya fasa hannu, PTT ɗinsa ya danna tare da furta. “All units, fall back! fall back !” Sai dai tun kan ya karasa maganar da yake shirin fadi din wani abu mai kama da karar fashewar Boom ya karade dajin baki ɗaya. Babbar fashewar da ta girgiza ilahirin dajin, Jami'an mafi kusa da wurin iska da fashewar boom din na daukar su ta maka da jikin bishiyoyin dajin, kafin wani mugun hayaki ya biyo bayan hakan ya turnike wurin tare da mamaye dajin. Kafin karar harbi ta ko ina ta fara ratso musu babu kakkautawa Jameel ya jefa kansa bayan wata babbar bishiya, yana neman ganin ta inda harbin ke fitowa tare da danna PTT ɗin dake makale a kunnensa da ƙarfi yace.
“Zuru One to Headquarters! We've been compromised! Repeat, we've been compromised!” Amma shiru bai hakura ba ya sake dannawa “Headquarters, respond!” nan ma shirun ne babu amsar dai da gasken gaske, kai tsaye ya gane baya aiki kenan ko wani abu ya katse communication ɗinsu ko dai an katse musu ne da gangan, take ya fahimci cewar tabbas koma waye wannan makwamishin shi da kansa ya jawo su cikin dajin ne domin kafa musu tarko... Sake jarraba danna ƙaramin PTT ɗin yayi yana sake furta. “Zuru Team, ku amsa me ke faruwa ne...?”. ★....
Manya kuma zaratan sojoji aka turo tun daga garin Bauchi zuwa Kurman Rafi, wanda a cikin daji kan garin suka yada zango sai zuwa dare kana suka shigo cikin garin, su kuwa jama'ar garin ganin sojojin nan ya saka su gudu kowa na kokarin cetar rayuwarsa, kasancewar suma masu shuka tsiyar da kayan sojawan suke zuwa, saboda ko na daren shekaranjiyan ai da kayan sojawan suka zo. Ganin yadda ake tika uban gudu ne ya saka hankalin fiye da rabin jama'ar garin tashi, sai ihu da iface ifacen jama'a kawai kake ji, wanda a daidai wannan lokacin Baba Gaji da Nadiya ke dawowa daga raka Sadiya ɗakin mijinta, "Innalillah wa'inna ilaihi raji'un!.... Mun shiga uku yauma da wannan masifar muka sake tashi kenan, wayyo Malam wayyo Alawuyata shikenan mu a haka rayuwarmu zata kare kenan... Tsit haka ta dinke bakinta ya dinke don ganin wani badakaren soja tsaye a gabansa, wuyansa rataye da bindiga daya ratayo ta kafafarsa. Wani uban ihu ta buga tana daka wani tsalle sai gata tana tsallen kwaɗo tun ba'a sata ba. Ita kuwa Nadiya tsaye kawai tayi cak itama ba wai don bata tsorata ba a ahh sai dan irin karfin halin da shi ne ya hana ta nuna shi a fili.
Amma Baba Gaji kam, ganin yadda mutanen ƙauyen keci gaba da sheƙa gudu ya riga ya gama kada yan hanjinta baki daya.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!”
Nadiya ta faɗa tana juyawa da sauri ta kalla inda Baba Gaji ke tsallen kwaɗon da ba'a aike taba, wata uwar tsawa wannan sojan ya buga musu su duka biyun. Wanda ya saka Baba Gaje ta tsaya cak har numfashinta na kokarin sarke ta, Idonta kai tsaye na sake fadawa kan sojan da ke gabansu, sannan ta sake kallar bindigar da ke rataye a wuyansa a fakaice. Babu zata Nadiya taji Baba Gajin ta suri hannunta da nufin su koma gidan Yaya Sadiyan, amma kafin ta kai ga kowanne motsi sukaji tsaiwar wannan sojan tsaye a kansu.
“Ku dakata, ku daga hannayenku sama.” sojan ya fada wanda ya saka su dole tsayawa cak, Baba Gaji kam hannunta daya ta ɗaga ɗayan kuma ta riƙe habar zaninta. "Baba hannaye sama aka ce..." “Na ɗaga fa!” Baba Gaji ta faɗa cikin rawan murya. “Duka biyun.” Baba Gaji ta ɗaga ɗayan hannun a hankali tana kallon sojan da wani irin tsoro.
“Rankadede…ai da ɗayan na ɗan tare zani ne saboda zamewa, kuma wallahi mu ba ƴan daba bane au ba ƴan leken asiri ba ne...” Wani kallo ya mata yana sake sabar bindigar nasa, sai ga ɗayan dake dan nesa dasu ya iso don ganin diramar taki ta kare, "Kin ga Baba ku sauƙe hannuwan naku kasa tukunna..."Kin amincewa Baba Gaji tayi sai data kalli Nadiya a hankali kamar wacce take neman tabbaci, kafin ta dawo da kallon nata kan sojan, wanda ya jinjina mata kai. Wani numfashi Baba Gaji ta saki a bayyane tana mai furta.
“ALHAMDULILLAH…”
Amma tun kafin ta gama dire kalmar nata wani daga cikin jami’an ya ce su zo nan, domin shi dirama ɗin nasu haka kawai yaji tana birgesa duk da babu fara'a ko kadan tattare da ita. "KUZO zamu bincike kune dan ban gama yarda daku ba...." "Innalillah Nadiya ki gaya musu ni tsohuwa ce mana ke tun da aka fara wannan abun kin yi wani gum kin rufe baki, muguwar nan..."
“Relax Mama babu wanda yake zargin ku da wani laifi, kawai zamu yi bincike ne... " Ƙafafun Baba Gaji ne suka fara rawa sai ga wani abu mai kama da ruwa na bin ƙafafunta wanda Nadiya take da tabbacin fitsari ne. Hannunta ta saka tana danne bakinta don gudun kar dariyar da take ta kokarin ganin ta danne ta kubce mata. Bakinta takai setin kunnen Nadiya ta rada mata. “Ni fa har yanzu ban yarda da waɗan nan mutanen ba, takai takai kawai nafsi nafsi.... " Ko kafin Nadiya ɗin tayi wani aune sai ganin Baba Gaji tayi ta ranta ana kare, wanda ya saka wannan sojan dan ja baya yana kife tafin hannunsa ɗaya saman fuskarsa. Cike da tsoro amma kuma a natse take a zahirinta tace. " Don ALLAH! don girman ALLAH kuyi hakuri ku kyale mu..."
Janye hannunsa yayi a natse jin yadda muryan ya bugi ƙofofin kunnuwansa, kai tsaye ya kafe ta da kaifafan idon sa. Kallon kusan 10 sacend ya mata a fakaice yana janye idon sa, kafin ya mata nunin taje, a sanyaye zuciyarta cike da zullumin ubangiji yasa ba harbeta zai yi ba.....
BY AMMEY LAYLERH ✍️
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️