Page 5&6
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Baba Gaji kuwa dake cin gudu har lokacin bata bata tsaya ba, har sai data isa gida ta shiga can lungon dakin Nadiya sai faman raba idanu take cike da tsananin tsoro, bayan ta firgita yan gidan musamman ma gwaggo talatu da a daidai lokacin take tsaye kan Baban Nadiya tana surfa masa bala'in da babu gaira babu dalili. Aikuwa a sukwane ta aune ɗakinta zani a hannu, inda daidai nan Nadiya ke kara sowa gidan itama cike da tsananin alamun tsoro da duk ya gama bayyana tattare da ita ta kara so. Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya jikin Baba Gaji ya gama yin laushi sai hawaye da rawar dari a bayyane tana mai furta. "Wayyo duniya! Kayya ke duniya, wayyo duniya ina zaki damu Innalillah wa'inna ilaihi raji'un yau ni Gaji naga mala'ikun ɗaukar rai ido da ido shikenan kuma kwanana ya kare..." Shi kuwa Baba Auwalu in ban da hawaye babu abinda yake yi cike da tausayin rayuwarsu su dukansu. A natse ya kai yatsunsa yana danne idanunsa gwanin tausayi, daidai lokacin da take karasowa cikin dakin, fara kwantar masa da hankali tayi tana ce da shi ai sojojin gaske ne, da yan ta'adda ne ai da tuni wani labarin ake ba wannan ba. Da wannan ta samu ya ɗan kwantar da hankalinsa. Hawayen idon sa ya sake sharewa tare da cewa. "In sha Allahu komai zai wuce kamar ba'a taɓa yin saba, da ƙarfin ikon ALLAH sai gagarumin sauyi yazo mana a cikin kauyenmu domin kuwa ALLAH yana sane damu kuma shi zai kawo mana mafita a lokacin da bamu zata ba..."
Da ameen ta amsa masa tana mikewa ta masa sai da safe ta fita, a tsakar gidan suka hadu da gwaggo Talatu wacce taji shiru shirun ya tsaya ba'a fara sakin bama bamai da bindigu ba. Gajeran tsuka taja da butar ta a hannu tana wuce ban gida saboda cikinta daya dan rude. ALLAH Sarki Baba Gaji kam tana can karshen gadon ƙarfen dake ɗakin Nadiya. Koda ta shiga itama sake kwantar mata da hankalin tayi tana cewa ta tashi ta rakata gidan, wani kallo ta wurga mata tana furta. "Jar uba ashe bakya ƙaunata haka Nadiya? To ai wllh yanzu ko da kuɗi da mota maka duk sati aka hadani ko nan da ƙofar gida ba zan fita ba..." Tayi maganar tana sake gyara kwanciyarta da juya mata baya. Dan murmushi kawai Nadiya tayi tana karasa shigowa ta cire Hijjabinta ta rataye kan kyaure, alwala ta fita ta dauro tayi Sallah Nafila raka a biyu kana ta kwanta...
Washegari....
A fusace Audu ya faɗa ɗakin Sadiya har yana kusa cin karo da butarta da take ƙofar ɗakin, cikin mugun fusatuwa yake furta. "Wai me aka dauke ni ne a gidan nan? Uyumm to wllh bara kiji Sadiya daga rana mai irin ta yau na rantse da ALLAH a bakin aurenki kenan idan kika kara fita yaji. Dama na gaji da zama dake wllh haƙuri kawai nake sa'arki ma ɗaya da kikaci jiyan saboda wannan sojajin da suka shigo gari ne, amma wllh kin ji na faɗa miki da kin koma inda kika fito.. " Yaja mugun tsaki yana kada rigarsa ya bar mata ɗakin, wanda ta bishi da kallo idonta cike taf da ruwan hawaye. Shewa da maganganun kishiyarta Indo da kuma Uwar Mijinta ta soma ji suna jifarta da habaice hahaicen da suka saba kamar koda yaushe. Suna jifan ta da muggwan kalaman gidansu babu abinci iyayenta sun gaji da ita shi yasa suka korota ta dawo. Uffan bata ce musu ba ta koma gefen gadonta tana rokon Allah ya kawo mata mafita ya sassauta mata wannan halin da take ciki.
Nadiya.
Tun sassafe ta tashi da jidon ruwa anan bohul din dake ɗan nesa da gidansu sosai, saboda kaf garin bohul uku kawai garesu, kuma ma a hakan wani mai kuɗi ne ya aiko aka musu daga cikin garin Bauchi. Kuma dama can rijiyarsu huduce a garin a takaice dai suna fama da matsalar ruwa wacce har yanzu bawai ta gama zuwa karshe bane, kawai dai an dan samu ci gaba ne. Kwatsam tana tafe sai ga tawagar yaran Shitu saurayinta marasa jin garin sun tare ta, su huɗu ne cif shi da baya wurin shi ne cikon na biyar din. Wuka Kallah ya saka mata a makoshi yana zazzara mata jajayen idanunsa yana huci yace. "Ke Ƴar uban waye a garin nan? Ubanki waye inba fakiri talaka ba, ke in banda ƙaddara ma uban me Oga Shitu zai yi dake shi da yake dan mai gari ke kuwa fa? Ubanki Makaho Uwarki Kurma amma a hakan har dan kin samu arzikin ance ana son ki ki tsaya kina raina mana hankali da ja mana aji, to yau shi wanda yake kare ki din baya nan, Wllh daga yau in baki amsa kina son sh..... Cak maganar nasa ya makale a makoshinsa sakamakon idonsa daya sarke a cikin na Shitu dake tsaye ya kafe Kallamu dasu wanda suke kira da Kallah. A ɗan tsorace ya janye wukar daga wuyan Nadiya da itama ta dago taga abinda ya saka shi janyewa haka da wuri. Sak tayi da ranta itama don ganin Shitun wato shi ne ya turo su dama kenan? Abinda ta fara sakawa a ranta kenan. Cikin hucin bacin rai ya iso garesu yana tsaiwa a gaban Nadiya din tare da tambayar "Wai me ke faruwa haka ne?" yay maganar yana gyara tsaiwarsa a gabanta. Wani zazzafar iska ta fesar daga bakinta tace. "To mai zan ce maka wanda idanunka basu gani ba, wuƙa fa yaranka suka saita a wuya na wanda nake da cikakken tabbacin kai ka aiko shi ya kasheni..." Wani zaro ido yayi alamar mamakin wai shi ya turosu su kasheta, wani ihu yayi yana girgiza dan iskan kansa da aka masa wani irin aski irin na ƴan iska a kan nasa wanda ya koma kamar wani tsohon mahauci shi a lallai uban daba kuma kauran garinsu, bayan idan yan dabar gasken suka zo baki daya ma rasa inda maboyarsa take a keyi a garin shi da yaran nasa, amma a hakan yake karyar shi ba wanda ya isa dashi shi ne uban kansa. "Zaka iya bani hanya in wuce saboda kuna sake ɓata min lokacine..." tayi maganar saboda Baba ta fito nemawa Kosai da Koko kar ya ƙare, sakamakon yau Gwaggo Talatu bata yi ba ta tashi da rudewar ciki kuma dama daren jiya ta kan kayan sana'ar nata ta bi don zuwa maboya. Sake tare mata hanyar yayi yana cewa ba zai matsa ba har sai ta amsa zata so shi... Yay maganar ne yana busa mata hayaƙin cigarettes din da yake zuka yana fesa mata hayaƙin saman fuska. Da hannunta ta shiga nuna shi cike da zallan bacin rai tace. "Idan na zabeka a matsayin miji uban yarana in nunaka wa jama'a da Mahaifina in ce ina son ka a matsayin wa? Bayan kuma naci buri akan Mahaifi da Mahaifiyata waɗan da sukaci buri a kai na nai karatu yau su wayi gari su ganni tare da wanda yayi ƙaurin suna a garin dama kowayensa duk da Dada bata raye? A ganinka innai musu haka na musu adalci kenan?... " Sai kuma ta hade hannuwanta duka biyun tace. "Ka tallafi rayuwata ka fita a cikinta, nasan ko ban faɗa ba kai kanka kasan cewar kai hatsarine acikin rayuwata" A wani mugun sabule ya ɗago idanunsa da sukayi wani irin ja saboda wutar da maganganunta suka ruru masa a cikin zuciyarsa, tsabar jan da sukai kuwa jijiyar kan har ta mimmiƙe, kafin ya kalleta dasu wanda tayi saurin janye nata daga kallonsa da saurinta. "Bazan iya rabuwa dake ba Nadiya kinfi kowa sanin hakan, domin har gaban abada bakin daya furta so baya taɓa iya furta ƙi har ƙarshen abada, su kuma waɗanda kike maganar a kansu hakannan zasu haƙura su barmu kuma da ransu za'ayi komai, zan dena komai sai abin da kika zaɓa min hakan zai miki? zaki soni?, zaki aureni? Na miki alkawarin zan koma kalar yadda kike so na koma Babynah"
Daga haka ya janye yana bata hanya idanunsa sun sake rinewa sun yi jajir, yana jin kamar ya ɗauketa ya bar garin da ita, yaje ya bata sabuwar rayuwar da yasan zata dace da ita, domin ita ba kalar wahala bace kawai ALLAH mantuwa yayine wajen halittota a cikin talakawa ƴar makaho, ƴar gidan kurma wacce ta taso cikin kunci da wahalar rayuwa. Gwiwwarsa daya ya dira a kasa bayan yayi cilli da guntun cigarettes din dake hannunsa yace. "Na tafi abar ƙauna kiyimin adda'a zan shiga daji, zan tafi inyi barna, zan lalata tarkon makiya zan ruguza tarkon mahassadan da basu son ganin ci gaban garinmu..." Ya faɗi maganar da azababban sauti mai cike da shauƙi, ya manna mata kiss ta iskar bakinshi ya watso mata shi da hannunshi yana barinta sankame a wuri guda idonta runtse jikinta na rawa ƙafafunta suna kokarin gaza ɗaukarta, kenan yau ma ya tafi sake taro musu faɗa tsakanin Fulanin yankin nasu da kuma Hausawan garin, wanda ko cikakken sati uku ba'a yi ba da kafta wani mugun fada tsakanin Fulani makiyayan da sukan yada zango a dazukan garuruwan. Wani sake lumshe idonta tayi tana tunano komai kamar a yanzun abun ke faruwa...
*Sati hudu da suka wuce baya*
Daya daga cikin Dattijan garin ne ya shigo yana kawoma Mai garin garin cewa wasu sabbin makiyaya sun bayyana a dazukansu, wanda kuma da dukkan alamu ba masu mutumci bane, domin waɗan nan su da kansu suke sanya dabbobinsu gaba su shiga gonakin mutane suna musu barna, saboda fari farin shukokine, sai mai garin shima ya kai ma hakimin dake tsallakensu maganar wanda yake kamar shi ne sugabansu. Sai bai wani dauki maganar da muhimmanci ba, cikin kankanin lokaci suka yi barna da yawa a jejikansu. Ranar da suka cika sati guda cif cif da zuwa suka shiga gonar wannan dattijan daya fara kai korafin a zauna ayi zaman sulhu da makiyayan saboda sun fara musu barna, gidan mutumin da gidansu gida dayane kawai ya raba su, kuma irin daya ne daga cikin yan bangar garin nasu, yana da tsarin jiki, so ranar sai ya fita zuwa gewaya gonarsa da yamma wajen karfe biyun zuhr. Yayi sallama da iyalansa lafiya ya tafi gonar yaje ya tarar da wannan aika aikar da suka masa cikin gona, sai ya musu magana akan cewa ya zasu shigo masa gona suna gani tumakansu na masa barna? Daga haka babu dadi babu ragi sai kawai suka fidda makamansu suka haushi da Sara da duka, sai dai makayan nasu baya kamashi, nan fa suka fusata dama akwai adda daure a kugunsa cikin zafin nama suka zareta daga jikinsa suka sare masa kafofinsa daga yatsu zuwa saman yatsun duka biyun. Kana suka hau saran jikinsa tun yana ihu da naiman daukin jama'a har suka kai shi kasa kai tsaye kuma suna sare masa kai, wani makwafcin gonarsa ne ya fado gonar don bashi dauki shima suka hau saransa wanda da kyar ya gudu ya auna cikin gari. Nan ya shiga garin jikinsa na zubar da jini yake sanar dasu abinda ke faruwa. Nan hankalin jama'ar garin ya tashi ALLAH Sarki matasan garin masu jini a jiki sukayi ganganko zuwar su Shitu da sauran marasa jin garin suka nausu daji, nan fa aka ringa bata kashi tsakaninsu da Fulanin da sune sukafi musu muguwar illa, don haka suka ringa datsa mutane suna zubarwa, a lokacin mutum uku ne suka rasa ran su wajen mutum goma sha biyu kuma aka illata su, wasu an sare musu hannuwa, wasu kafafu, wasu kunne wasu jiki, har yamma faɗan ake wanda har sai da yakai ga wannan Hakimin yankin nasu yazo ya shiga har cikin daji kan, wanda ganin irin muguwar barnar da Fulanin ke musu ya saka mazaje suka ringa gudu suna nemar maboya. Koda hakimin yazo shima yi suka ringa yi kamar sa sare shi, ga kibiyoyin da suka ringa harboya. Wanda zunzurutun matasa sukayi garkuwa suna bama Hakimin kariya, har zuwa lokacin da folisawa suka iso da aka turo musu daga Bauchi. Sune suka fita da masu rauni ka zuwa asibiti matattun kuma akayi gidajen su dasu, a lokacin da ake shimfidarma da iyalan Malam Hudu gawar sa kuka suka sanya suna mayar da yanda abin faru, tun daga kiran daya samu akan yazo yaga barnar da fulanin suke masa, har zuwa gardamar da machine din sa ya masa wajen tashi, uwar gidansa ta tambayeshi mai zata dafa musu? Yace tayi Dambu shi yake marmari shi yasa tun daren jiya ya shigo musu da zogale, tace kudin cefane yace In sha ALLAHU sai ya dawo zai bayar ta ara masa tayi. A wannan lokacin gaba daya garin sun shiga cikin wani mummunan tashin hankali. Kuma abu mafi kona rai ko bayan da lafawan komai sai Yan Sanda suka ce ai fulanin basa da laifin komai, haka shari'a taki tayi aikinta da kyau kuma gasunan aka ci gaba da barin su a dajin suna ci gaba da rayuwa dasu, sai daga baya aka ringa jin jita jitar cewa shi kansa hakimin da kuma mai gari tun farkon zuwansu makudan kudade fulanin suka basu, shi yasa suka samu daurin kugu daga ta ko ina. Ga hare haren ta'addancin da suke yawan fuskanta gaba daya kowa ka kalla a garin ba'a cikin cikakken hayyaci da nutsuwarsa yake ba har zuwa daren jiya da aka kawo musu sojojin...
Wani dogon numfashi taja a ranta tana adda'ar ubangiji ya kawo musu dauki da mafita bayan dawowa daga tunanin...
*****
Ɗakin ya yi shiru tsit babu komai haka babu motsin komai sai ɗan ƙaramin sautin iskan dake fita daga cikin na'urar sanyaya ɗaki da kuma motsin ƙarar wasu kayan tarkacen ƙarfen da ke jere saman table ɗin dake ɗakin, wanda wani mutum ke zaune a kan kujerar katako mai faɗin baya. Ya ɗan jingina jikinsa baya, kamar wanda ya gaji da dogon tunani. Idanunsa a lumshe suke ba tare da wani motsin komai tattare dashi ba. Hannunsa ɗaya yayi folding chest nashi ɗayan kuma ya ɗan tallafi kansa yayin da kafafunsa suke harde. A kunnensa na hagu wata ƙaramar na'urar sadarwace ta Bluetooth, wanda ya saka tane domin haka tsarinsa yake a haka yake, baya taɓa rike waya domin sauraron magana ko sadarwa ba. Hannunsa daya na hagu yana daure da rolex na fata baki. A gabansa kuwa saman table ɗin da yake mai faɗi, kayayyaki ne zube na aiki iri-iri wanda suke shirye cikin tsari. kowanne yana zaune a inda ya dace kamar wanda ya shirya su da gangan domin ya samu abin da yake buƙata cikin sauri. A gefensa na hagu na teburin akwai wata black toolbox, tare da ƙaramin akwatin da ake ajiye kayan gyara a cikinta. Tana rufe amma girmansa da yadda aka sanya shi kusa da hannunsa shi ke nuni da cewar kayan da ke cikinsa suna da matukar muhimmanci game ita.
Kusa da shi akwai electric drill, na'urar bibiyar duk abinda yaso a kowacce cikin duniya mai launin ja da baƙi. Wanda kai tsaye wannan na'urar ba'a ko ina ake samu ko iya amfani da ita ba sai inda aka shahara aka kuma san muhimmancin aiki da ita, kai tsaye ana iya amfani da ita ne kawai a irin wajen huda ko gyara abubuwa masu tsauri. musamman idan ana buƙatar ƙarfi da sauri fiye da abin da hannu zai iya aiwatarwa. A ƙasan drill ɗin kuma battery pack ne, wato batirin da ke ba na'urar ƙarfin aiki fiye da kima, an ajiye shi kusa da na'urar domin a iya sauyawa ko cajinsa idan ya ƙare.
A gefen dama kuwa akwai ƙananan kayan aikin ƙarfe, waɗanda suka haɗa da screwdrivers da wasu kayan gyare gyaren hannu. Kowannensu yana da aikin kansa wajen ɗaurewa, sassautawa ko gyara ƙananan sassa. Daga cikin kayan akwai wani kayan aiki mai jan handle, wanda aka ajiye shi a kwance. Handle ɗin ya fito fili saboda launinsa, yayin da ƙarfen da ke jikinsa ya kama hasken fitilar dake sama. A bayan waɗannan kayan akwai spray can, wata kwalbar fesawa da aka ajiye tsaye. An sanya ta nesa kaɗan da sauran kayan domin kada ta zube ta gurɓata teburin saboda tsabar irin hadarin da take da. A kusa da gefen teburin akwai ƙananan kwantena da kwalabe, wasu ɗauke da abubuwan amfani wajen gyara ko tsaftace kayan aiki, yayin da wasu kuma suka kasance mafi hadari fiye da kima. An jera su ne ba tare da hayaniya ba kowanne zaune a mahallinsa. Yayinda a gefen dama kuma akwai gilashin ruwa, wanda aka zuba kusan rabinsa, ruwa ne kawai wanda ta cikin wannan dakin mai duhu, hasken fitilar ya ɗan haska wani gefen gilashi daban wanda ya sa ya ɗan yi kalli. Daga ta can baya kuma kusa da bangon bottle din ruwan sha ne na Mr. V kan dispenser. Ba ta cikin tsarin aikin da ke gabansa, amma tana cikin ɗakin kamar wani abu ne muhimmi ko al'adar da aka saba wajen amfani da shi kullum. A saman teburin kuma akwai fitilar rataye, wadda haskenta ya fi karkata kan wurin aikin nasa ne kawai. Wannan ne ya sa sauran sassan ɗakin suka kasance cikin duhu, yayin da teburin da mutumin ke zaune a gabansa ya fi bayyana. Ya juya bayansa ne kuma yana bama windows na ɗakin baya, yayinda cottons din suka rufe yawancin hasken da ka iya ketowa ya shigo daga waje. Bangon ɗakin yana da duhun launi wanda shi ne ya kara ma dakin yanayin sirri. Tsakanin mutumin da wasu daga cikin kayan akwai babban gilashi, wanda yake kama da madubi daga yadda yake nuna hasken ɗakin. Wanda kai tsaye idan ya ɗaga kansa zai iya ganin kansa ta cikin glasses din.
Sai dai bai ɗaga kan nasa ba yaci gaba da zama ne a hakan, idanunsa a lumshe, jikinsa jingine da jikin kujerar katakon har zuwa lokacin hannunsa daya sarke a saman kirjinsa ɗayan kuma tallafe da kansa. Kamar koma waye a wajen yana tattara tunaninsa ne wuri guda kafin ya fara gudanar da koma miye mai muhimmanci. Karar wayar sadarwar shi ne ta dauki wani ƙaramin sauti alamar lokacin da jira kenan ya cika. A wani kalan kasaitaccen ya wani wani buɗe idonsa ɗaya kai tsaye yana kai dubansa kan agogon dake daure a hannunsa.
2:00 na dare.
A natse ya karasa bude idanun nasa tare da ɗaga kansa a hankali ya kalli teburin. Ya kalli kayan da ke gabansa ɗaya bayan ɗaya, kafin ya miƙa hannunsa zuwa electric drill.
★....
PRESIDENTIAL RESIDENCE ABUJA
Yau kimanin kwana biyar cif kenan da dawowar Babyboo daga ƙasar America, baki ɗaya gidan yayi shiru da alamun ba yanzu masu gidan suke tashi ba, baka jin sautin komai sai na ruwan dake zuba daga fountain ɗin da ke tsakiyar garden din dake tafe da ƙamshin furannin da aka shuka a gefe da gefenta. Daga can zuwa compound na gidan kuwa Jami'an tsaro ne tako ta ina iyaka ganinka suna tsaye a wuraren da aka ware musu, yayin da ma'aikatan gidan ke gudanar da ayyukansu cikin tsari sanin cewar wacce ta dawo din ba kamar sauran mutanen gidan take ba, ita takan iya tashin tsakar dare ma ta fara gudanar da ayyukanta matsayinta na jami'ar dake ɗaya daga cikin jami'an da ake ji dasu amma ta karkashin kasa. Don a bayyane banda iya shege da sheke ayarta da shuka shika shikan rashin mutumcinta babu abinda ta iya.
Tana zaune a cikin wani katafaren parlour da aka kawata shi cikin tsari mai nutsuwa. Idonta na lumshe ta jingina bayanta da jikin kujerar tsararren parlourn da babu wani abu daya nuna yayi yawa ko nuna rashin nutsuwar karikicen da zai iya bama wurin rashin natsuwa. Sai gabanta dake dauke da wata doguwar glass table, wacce a kanta ke dauke da plate mai ɗauke da fruits da aka yayyanka mata ƙananu cikin tsari, na apples, grapes, watermelon, pineapple da strawberries, gefen plate din kuma wata ƙaramar bowl ce wacce take dauke da madara mai sanyi da aka zuba powdered milk a saman, tare da wani glass na fresh juice. Har zuwa lokacin bata bude idon taba bare kuma saurarar abinda ke gaban nata, tana sanye cikin wata doguwar riga mai laushi mai kyau, gashinta dake gyare yana daure daga keyarta da babu cap saman kan nata. babu yawan kayan ado a jikinta sai wata ƙaramar sarka da agogon dake hannunta kawai sirara wanda da dukkan alamu diamond ne.
A wani irin natse cike da isa da kasaita ta bude idonta tare da dago kanta dake jingine kai tsaye tana sauƙe idonta akan wayanta dake gefenta. Tsaye ta mike tana yin yar miƙa tare da kwalla kiran Victoria... Kai tsaye matashiyar matar mai kula da gidan ta bayyana daga bakin ƙofar parlourn tana amsawa da.
“Yes, ma.”
“Take these outside.” ta yi maganar tana mata nuni da fruits ɗin da ke gabanta. Karasowa wacce aka kira da Victoria din tayi tana cewa. "Ma, the fruits" tayi maganar tana mata nuni wai ko bata lura da abinda ke gaban nata bane, kasancewar ta kusa kowa fin sanin duk wani motsin Babyboo din. “Ban jin yunwa ne. I said take them outside.” ta furta da murya mara ƙarfi ko hayani tare da kyarar da take dibarta da duk wani ma'aikatan dake gidan, walau tsoho ko matashi kamarta. Kai tsaye Victor din ta dauke plate da bowl na fruits din kasancewar tasan tafi kowa sanin cewa Babyboo din ba ta taɓa maimaita umarni sau biyu.
“Yes, ma.” ta furta lokacin da take ɗaukan tray ɗin ta fice ita kuma tana yin sama. Tana isa lafiyayyen sashen dake a matsayin mallakinta kayan shan iskar dake jikinta kawai ta shiga zarewa har zata faɗa bathroom sai kuma tayi kiran waya ta landline din dake ɗakin tace a shirya mata hutawa a garden tare da breakfast nata. Da yes aka amsa mata daga haka ta yanke kirar tana fadawa bathroom din.
Few minutes...
Babyboo ta fito daga cikin babban corridor ɗin gidan cikin nutsuwa, babu woni ado mai hayaniya tattare da ita. Amma duk da sauƙin kayan dake jikinta hakan bai hana izzah da kuma kwarjinin da take tattare dasu bayyanuwa ba, tana sanye ne cikin wasu navy blue Armanis ɗin da suka mata wani azababben kyau. Sai dai a yanzun ma babu komai saman kanta da dukkan alamu scarf baya samun wurin zama ne bisa kanta, sai dai Ma sha ALLAH tanada gashi harda na hauka ma gashi baki sidik kaman na yar buzuwa dan ma wai a hakan parking nashi tayi donut din daya saka gashinta gammo sosai a kanta, yana gyare tsaf sai sheki yake abunsa. Wani dan bata fuska tayi tana tsayawa daga bakin balcony tana kallon garden din da aka gama kawata mata shi. Yau bata son magana da kowa ciki kuwa harda mahaifanta don haka kai tsaye ta wuce zuwa garden din. Ahankali iskar safiyar da rana data dan fara dagawa na bugan fuskanta daya saka dan lumshe ido. Kai tsaye kujerar da aka shirya mata domin zama ta nufa wacce ke gaban ƙaramin table ɗin da aka jere mata komai. Zaune takai su kuma jami'an da tun farkon fitowanta suka yi read suna tsaiwa nesa kadan da inda take. Hankali kwance ta fara soma cin abincinta tana latsa phone nata har wani lumlumshe ido take alama tana amsar sakon girkin yanda ya kamata.
Wayanta dake saman table ta duba taga lokacin da take son fita bai yi ba. A natse ta tonkoshe hannuwanta duka biyun tana kaiwa saman habarta, kafin ta wani lumshe ido tana kokarin taga tayi tunani, taga tayi zeroing mind nata dangane da abinda take kokarin tunkara dangane da batar Sameer da har zuwa lokacin babu shi babu lamari. Five days, kwana biyar kenan kwana biyar da dawowanta wanda yayi daidai da sati guda cif kenan da sace sameer din. Amma har ya zuwa wannan lokacin babu wani sabon labari, lumshe idanunta tayi tana furta....
“Who takes someone and doesn't ask for anything?” Tayi maganar tare da ɗan buɗe idanunta. “Why him?” ta sake fadi kamar kuma wacce aka harbo mata wani sabon tunani ta dauki wayanta kai tsaye ta saka kira. Ana amsa kiran kai tsaye ta jefa tambayar. “Where was Sameer last seen?” “His office? house? Club?.... " Kai tsaye ta datse kirar bayan an bata cikakkiyar amsar da take son ji din tare da runtse idanunta, sai data ɗan fesar da wani numfashi kafin ta sake saka kira. “Get me the list of every place Sameer visited in the last seven days. Not the official list.” sai kuma tayi shiru tamkar ba zata sake cewa komai ba sai zuwa can ta sake furta. “I want everything. Restaurants. Hotels. Clubs. Private residences. Gyms. Golf course. Anywhere he went.” Tana kaiwa nan ta datse kirar daidai da isowar mace ɗaya daga cikin security officers nata.
“Ma.” kai tsaye ta furta sunan saman lips nata cike da ladabi a ladabce.
“Ma. is in a meeting with the security chiefs.”
“I know.” ta bata amsa da hakan tare da miƙewa tsaye, “I want the vehicle.” “Where are you going, ma?” jami'ar ta jefa mata tambayar duk da tasan ba lallai ta sama amsar da take son samar ba kuwa. A natse ta ɗauki handbag nata tana bata amsa da. “To the Vice President's residence.” Wanda amsar ya bama Jami'ar damar yin shiru kafin Babyboo din ta kalle ta tana mai furta.
“I'm not going there to wait.” Ta fadi hakan tana dago ƙaramin vail din dake hannunta tare da sake ce da ita. “I'm going there to ask questions.” kai tsaye tana bar mata wajen zuwa compound na gidan. Amma duk da haka wannan jami'ar bata hakura ba sai data rufa mata baya daidai sanda take isa compound din da tambayar.
“Where is the convoy?” suka bata amsa da “Ready, ma.” hannu ta jinjina musu da faɗin. “Good.” ta juya ta fara tafiya kafin ba tare data juyo ba ta ce. “Tell the security team I want the convoy ready in twenty minutes.” suna sake amsawa da “Yes, ma.” saurin shan gabanta wannan jami'ar tayi mai suna Sophie tana fada mata irin muhimmancin da meeting din ke da. A wani irin matukar fusace ta juyo tana sauƙe mata idanunta da suka fara sirka jan bacin rai cike da ihu tace. “Cancel the press schedule for today.” cike da taurin kai ta sake dan risinar da kanta tace. “Ma, the meeting with” “Cancel it.” ta sake fadi a tsawace wanda ya saka cikin girmama duk abinda ta tsarama kanta Sophie gyada mata kai da cewa. “Yes, ma.” ta juya tana barin mata hanyar baki daya.
A babban parlourn data soma zama da farko ta tarar da mahaifiyarta first lady Fareederh zaune. A natse ta ƙaraso ta zauna kusa da ita tare da jingina kanta jikin mahaifiyar nata, tana furta mata "Good morning" , da "Mornings how are you feeling today?" mahaifiyar nata ta bata amsa da tambayar yadda ta kwana, da fine ta bata amsa lady Fareederh din na sake jefa mata tambayar taci abinci? Kai Babyboo ta gyada mata alamar ehhh taci. “Mom...” ta kira sunan mahaifiyarta data amsa da “Hmm?” gyara zamanta Baby tayi kafin tace "Ina son fita zuwa President's residence. Dan shafa kanta dake kafadarta Mom din tayi tace “Babyboo, ki yi haƙuri. Jami'an tsaro suna kan aiki a kansa.” a hankali ta janye jikinta daga na uwar ta ɗaga idanunta ta kalle ta kafin tace.
“Ni ma zan yi aiki a karan kaina Mom.” Wani daure fuska mahaifiyar nata tayi tana mai furta. “Mai kike nufi?” "Ina nufin zan yi iyaka kokarina wurin gano case din inda yake nufi ne Mom...
“Soumayyerh”
Mom din ta kira cikakken sunanta a daken daya sakata tsayawa cak ba tare data juyo ba tace. “Mom, idan ba zan iya taimako wajen nemo shi ba, aƙalla zan iya gano inda ya fi yawan zuwa.” ta juya tana ficewarta domin wannan ɗin kowa dake gidan yasan idan har ta riga da tayi niyar abu ruwa iska babu abinda ke iya sanja mata ra'ayi wurin dakatar da ita. Tana fita convay nata sun gama zama ready motar da aka bude mata kawai ta fada suna tada motocin tare dayin reverse suka bar gidan baki daya.
Farkon inda suka fara nufa shi ne wani luxury resort da Sameer yake yawan zuwa idan yana son samun nutsuwa, wanda tasha zuwa har nan ita da kanta ta same shi. Tana isa managern wurin dake yasan da zuwan nata ya gaida ta cike da girmamawa, kai tsaye abu guda kawai ta tambaye shi shi ne. “Yaushe ne karo na ƙarshe da yazo?” records lises din dake hannunsa ya bude wanda ya saka Babyboo ta tsaya tana kallonsa.“Na ƙarshe... kusan makonni uku da suka wuce kenan yanzun haka! " ya bata amsar daya sakata ɗan lumshe ido tare da juyawa ta fada motar ta suka bar wurin bayan ta sallameshi. Daga resort ɗin kai tsaye wani private golf club suka sake nufa. Amma amsar kusan iri daya ce suma ya jima rabon shi da zuwa wurin, daga nan wani exclusive restaurant, sannan wani luxury yacht club, daga ƙarshe wani wuri na shakatawa da Sameer yake son zuwa lokacin da yake son zama shi kaɗai. A kowanne wuri tambayarta ɗaya ce yaushe ne zuwansa na ƙarshe? Haka kuma duk lokacin da ta samu wata sabuwar alama, sai ta rubuta ta a wayarta a ranta tana jin cewa IN SHA ALLAHU zata same shi...
★....
Directly daga nan motocin su basu nufi ko ina ba sai President's residence house. Manyan motocin ne suka soma danna horn a ƙaton get na gidan, kai tsaye na'ura ce daga cikin gidan ta gama tantance su kafin a bama motocin umarnin shiga ganin ko na inane, wani irin uban securities ne jibge a gidan tun daga farkon get har zuwa ƙarshensa. Kai tsaye zugar convay na motocin nasu ne suka danna hancinan motocin nasu zuwa cikin harabar compound din. Ɗaya daga cikin masu tsaron tane yayi saurin fitowa ya bude mata motar tana fitowa bayan ta maka katoton glass nata saman face nata. A natse mata biyu suka rufa mata baya zuwa cikin gidan bayan wata daga ainihin na gidan ta wuce gaba. Tsit haka babban parlourn gidan yake tamkar su garin su bai gama wayewa ba, daga wannan parlourn na farko duk jami'anta suka dakata daga ita sai wannan macen ta gidan ce suka ratsa zuwa sama. A zaune ta tarar da Lady Sakinat Mahaifiya ga Sameer kenan, sai kanwar Sameer din mai biye masa Laylerh wacce ta ɗaura kanta saman cinyarta! daga gefe kuma Amaryar vice president din ce Madame Solina data kasance Baturiya. Ita da autar Babynta Aseemah. Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙara so cikin parlourn saman tana cire hills shoe din dake kafanta. Gaba ɗaya haka suka zuba mata ido, domin tun tun washegarin da aka dauke Sameer bata sake dawo musu ba. Da sauri Laylerh kanwa ga Sameer din ta mike daga jikin Hajiyar nata tana tafiya da gudu suka rungumi juna ita da Babyboo din. Cike da farin cikin ganin juna suka koma saman daya daga cikin kujerun parlourn suna zama, kafin a natse ta gaida su tare da sake jajanta lamarin da take jin In sha Allahu zata yi iyaka bakin ƙoƙarinta na son ganin ta gano wannan cukurku ɗaɗɗan al'amarin. Ta jima sosai kafin su rankaya zuwa ga fadar Mahaifinsa, wanda tun da abin ya faru bayan fitowar su a zaman meeting din nan bai sake fita ko ina ba yana nan kwance yana jinyar yaronsa ɗaya tal da shi kawai ne babba magajinsa, dududu dama yaransa uku ne, daga Sameer din sai ita laylerh sai kuma dan Amaryarsa Solina wanda shi yaro ne dan baifi 4 years zuwa 5 years ba.
Suna isa Baby ta tafi wurin sa tana masa kiss a goshi da gaida sa, da masa ya jiki, ya amsa da lafiya yana sakar mata murmushi mai kyau da shafa kanta da Daddynta duk da suna tare kusan koda yaushe a waya. parlourn dake kusa da bedroom nashi suka fito, inda su sai a lokacin ne ma zasu yi break nasu. Kowa yana sanye cikin guntayen kaya irin na shan iska na yayan hutun da babu ruwan su. Anan suka gudanar da breakfast nasu wajajen sha biyu saura. Karfe ɗaya cif Babyboo ta bar President's residence, wanda kamar jiran ta tafi ake kira ya shigo cikin wayar vice president wanda number ɗin iyaka ta family nashi ce kawai...
BY AMMEY LAYLERH ✍️
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️