Page 7&8
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ A natse motocin convoy ɗin nata suka lula saman kwalta daya bayan daya cikin tsari, ita kuma tana zaune a bayan motar tana kallon window amma hankalinta gaba daya yana can kan abubuwan da take son ganin ta tattara. A kowanne wuri da ta je an bata amsa da cikakken tabbaci ne kusan iri daya, Sameer ya daina zuwa wuraren da yake yawan zuwa tun kusan makonni uku da suka wuce, wanda hakan ke kara mata wani irin tunani mara dadi a zuciya. Wayarta dake hannunta ta sake dubawa tana kallon notes din da ta cika da sunayen wuraren da kuma dates din zuwansa, kafin ta sauke ajiyar zuciya tana mai lumshe idanunta.
A daidai lokacin da motocin nata ke barin harabar gidan Vice President, wayar dake kusa da gadon Vice President ta fara ringing wanda komawarsa dakin kenan bayan yaga fitar Babyboo. Zaune yakai tare da kin kallar waya din, sai ma wata takardar dake hannunsa da yaci gaba da kalla yana dubawa kamar bai ji shigowar kirar ba,har sai da wayan ta sake daukan wani sabon ringing din a karo na biyu. Kafin ya juyo kansa a hankali ya kalla screen din wayar, dan Sak yayi da ransa don ganin a special phone nashi kirar ke shigowa, kenan koma waye yana daga cikin family nashi ne makusanta sosai na jini, don duk girman matsayin da kake da shi a wurin sa baya taba ajje number na kowa inba family nashi ba, gashi kuma ai bai san number ɗin ba, kamar ba zai daga ba amma kome ya tuna sai ya miƙa hannu yana ɗaukan wayar tare amsa call din ya kare a kunne tare da faɗin.
"Hello?" ya fadi amma yaji shiru ya sake cewa "Hello? Who is this? Ya kuma furta tambayar furtawa wanda kai tsaye wata murya ta katse masa tunaninsa da tambayar da yayi, murya ce mai cike da izza da cikakken ikon da babu alamun tsoro ko gaggawa a cikinta aka furta.
"Mr. Vice President."
Cak haka ya tsaya yana dakatawa tamkar wanda akayi preezing nashi, kafin cikin wani irin karfin hali da jarumta ya sake jefa tambayar.
"Who are you?" Dan gajeren murmushi ne ya fito dagata bangaren mai kiran kafin wannan muryan ta no nonsense ta sake kashe shi hadi da dakarsa ta hanyar sake furta "I believe you know who I am." tsaye ya mike yana furzar da wata zufa tare da kai hannunsa saman goshinsa ya sake furta. "What do you want?" Ya sake tambaya yana kawai zaune saman bed.
"Your son."
Haka yaji muryan nan ta sake bugar zuciyarsa daya saka gabansa faduwa jikinsa na wata irin rawa kamar a tsawace yace. "Where is Sameer?"
"Alive." Kalmar dayar da aka bashi amsa da ita kenan wacce yaji kamar ana tafasa jinin sane ya fesar da wani numfashi "Let me speak to him."
"Not yet." aka bashi amsa da hakan da wannan dakakkiyar muryan."Who are you?" "Someone who has your son." Vice President ya runtse idanunsa na dan lokaci, hannunsa daya yana rike da wayar sosai dayan kuma yana shafo saman kansa zuwa goshi. "How much?" shi ne kawai abinda ya tambaya yanajin kamar yayi fiffike ya ganshi gaban yaron nasa.Wata dariya mara sauti akayi daga cikin wayar kafin a furta. "You are asking the right question." wani dan shiru kadan ya ratsa wayar kafin zuwa can muryan ta sake cewa.
"Five hundred million dollars."
Cikin rashin yarda da abinda yaji ya saka shi bude idanunsa da ambatar. "What?"
"Five hundred million US dollars."
Aka sake furtawa kamar ana son bashi cikakken tabbacin kenan tabbas. "Are you out of your mind?" Ya faɗa cike da zafi wanda ya saka wanda ke kan wayar wani ɗan janyeta daga gefen kunnensa yana bashi amsa da "No!" wanda idan har beyi karya ba har bugun zuciyar na cikin wayar sai da yaji, kafin kamar daga sama ya sake jin ya furta. "Not my mind, ban rasa kwakwalwana ba..." sai ya ɗan dakata tare da sake fesar da wani zazzafan numfashin "I am the man keeping your son alive." Vice President ya sauke numfashi yana kallon kasa.
"Where do you want the money?" ya furta yana fara zirga zirga a cikin bedroom din, "You will be told." wata iska ya fesar daga bakinsa "How?" ya sake furtawa yanajin kamar kansa zai fashe. "Someone will contact you." aka fada daga bangaren mai kiran. "Who?" ya sake jefa tambayar don ganin yacce ake ta son yawo da hankalinsa. Kafin tamkar daga sama tamkar saukar aradu yaji an furta.
"Khabeer K. Mashi."
Wanda ya saka Vice President ya dago kansa da sauri cikin wata muryan dake nuni da kamar tsoro yace. "What?... The head of your DSS operation." Kamar ba za'a ce komai ba zuwa can kuma akace. "He will take the money." cikin rasa yanda zayyi da rai da rayuwarsa yace. "Why him?" duk a kidime yake don ya gama kidimewa da rudewa baki daya "Because I want him." muryan ta sake bugansa, "Listen to me, you cannot just"
"I can."
Ya katse shi nan take cikin wata dakakkiya kuma dakilalliyar muryan no nonsense din nan nashi. "Because I already have what you care about." gaba ɗaya ji Vice President yayi jikinsa yayi sanyi kafafunsa sun sage ya kasa cewa komai har muryan ta sake katse shi cikin a karon da babu adadi.
"And I have one more condition." cikin rawan murya da son ya tseratar da Ɗansa yace. "Which is?" Sai da aka ja wani guntun tsuka kafin a furta.
"No government." Wanda ya saka Vice President wani daure fuska yana shirin cewa wani abu amma aka sake katse masa lissafi da hanzari ta hanyar furta. "No DSS team! No Army, No Police, No intelligence operation, No tracking device, No media! Nothing....."
"How am I supposed to trust you?"
"You don't. But you will." Vice President ya matsa kusa da gadon dake fuskantar sa yana kallon kofar bedroom nashi idonsa ya kada yayi ja sosai. "And if I refuse?" Kafin muryan ta canza cikin wani yayi mai kamar ban tsoro "Then you will never see Sameer again." Daga haka ya saka hannu da nufin datse kirar amma sai wata wata murya ta fito daga nesa wacce tayi zurfi sosai kamar kuma a wahalce aka ambaci kalmar.. "Da..." Din daya saka Vice President tsayawa cak cikin wani irin mummunan tashin hankali murya cike da in inar da yasan baya da a rarrabe ya furta.
"S... Sa... mee..r?"
"Da..." Muryan ta sake bayyana cike da yanke tsammani a wahalce, kafin kamar a wahalce ya samu ya sake fusgo kalmar "Dad..." completely wanda ya saka Vice President wani kalan sake rike wayar da karfin da tsaf zata iya cin screen. Yana zubewa kan kafafunsa numfashinsa na fusga ya shiga furta. "S.. S.. Sameer! So... Son, where.. are you?" amma shiru alamun an rufe bakin ne kodai wani abu da zai saka bakin rufuwa, "Sameer!" ya sake faɗa hankali tashe.
"Enough." Aka daka masa tsawa ana yanke kiran kai tsaye, wanda ya saka Vice President ya tsaya yana kallon wayansa dake kokarin zamewa daga hannunsa. Kafin sautin fadowar message ya biyo baya,cike da zallan tashin hankali ya rarumo wayan kai tsaye yana shiga cikin sakon da aka turo masa guntu.
_72 HOURS._
Shi ne kawai abinda aka rubuta, wanda ya karanta shi ya kusa sau goma koma fiye, kafin ALLAH ya bashi damar lalumar number ɗin wacce ke a private ba tare daya tsaya dubawa ba yana karata a kunnensa. Amma bata shiga, ya sake kokarin kiran Still nothing. Wayar ya ajje a hankali yana kaiwa zaune daga gefen gadon yana dafe kansa da yaji ya dirar masa da ciwon kan lokaci guda.
Bai fi mintuna biyar ba sai ga shigowan sabon wani kiran ta wayarsa da yake using da iyaka abinda ya danganci harkan tsaro, sunan Khabeer K Mashi ne ya bayyana dake suna bi diddigin duk wani shiga da fitan wayansa kamo daga lokacin kwamushen zuwa yanzun da ya amsa waya daga tantirin. Kai tsaye tun kafin K Mashi din yace komai ya riga shi don dama a matukar bukace yake da kiran nashi. "Get me Khabeer K. Mashi." Sai kuma ya furzan da wata iska bayan am amsa masa "Immediately." daga haka ya gimtse wayar yana yasarta gefe daidai da shigowan matan sa dakin duka su biyun.
A wannan lokacin da K Mashi din ya kira shi daidai lokacin yana tare da duk wasu manyan jami'an tsaron kasar. Don haka cikin kasa da mintuna talatin bayan haka, sai gasu har sun iso ta wata ɓoyayyan hanya suna kutsa kansu cikin babban security briefing room na gidan. Khabeer K. Mashi ne ya fara shigowa cikin nutsuwa, kafin manyan jami'an tsaron da suka riga suka zauna a dakin suka dago kansu suka kalla Vice president dake Jan wata kujera yana kaiwa zaune don safa da marwa suka shigo suka tadda yana yi. Wani dan shiru ne ya ratsa tsakaninsu kafin Vice President ya mike ya nufi screen dake gabansu inda ya nadi sautin muryan ta hanyar yin recording yana kunna musu. A natse duk jami'an dake wurin suka saurara, har zuwa inda recording din ya kare.
"Five hundred million dollars?" K Mashi ya furta a sigar tambayar daya saka ɗaya daga cikin jami'in sauke ajiyar zuciya. Kafin a natse K Mashi ya daga kansa ya kalli Vice President."They asked for me?" jinjina masa kai Vice president din yayi yana bashi amsa da "Yes." "To deliver the money?" ya sake t tambaya nan ma ya jinjina masa kai da sake bashi amsa da "Yes." Sai kuma wani dan shiru ya ratsa wurin kafin zuwa can kuma ya juyo yana furta. "Did they say why?"Vice President ya girgiza kai da fafin "No." K Mashi ya sake kallon screen din "Then the money is not the main reason." ya furta yana wani lumshe idonsa da dafe goshi. Daya daga cikin jami'an ne ya kalleshi da furta. "How can you say that?" A natse K Mashi ya juya ga jami'in yana bashi amsa da.
"Because if money was their only target, they wouldn't have waited this long."
Ya dakata yana fesar da wata numfashi kafin ya dora da fadin. "They took the Vice President's son, stayed silent for days, watched our response, and now they are asking for five hundred million dollars while giving us instructions on who should carry it." sai kuma ya juya ga Vice President yana kallonsa tare da furta. "They are testing the government." Wani daga cikin jami'an ne yay saurin furta. "Then what do you suggest?" Khabeer ya jingina bayansa da jikin kujerar dake gefensa yana bashi amsa da. "We don't rush." "His son is in their hands." "I know." jami'in ya sake furta. "Then we have seventy-two hours." Khabeer ya daga idanunsa ya kalleshi da cewa "And that's exactly why we shouldn't make a mistake. An ina son ku sani cewar wannan din ba kamar sauran kwamushen da aka saba yi bane get ready kawai guy's mu buga wasan tun da har dani ya zabi buga wasan,da dukkan alamu koma waye wannan makwamishin ya sanni farin sani tabbas " daga haka ya fice a dakin yana dan karkada yatsarsa manuniya alamar wasar za tayi zafi kenan.
***** Babyboo
Tana lafe a bayan motar ta tana kallon sakonnin dake shigowa wayarta, har yanzu tana kokarin hada dukkan bayanan da ta samu daga wuraren da Sameer yake zuwa,sai wayanta ya fara ringing. A natse ta dago wayan tana duba screen din, ganin sunan laylerh ne ya sakata daga wayan tana kaiwa kunne da furta.
"Yes?"
Cikin sauri muryan Laylerh ta amsata da. "Beb you need to know something." ta furta wanda ya saka Babyboo saurin bude ido daga lumshen da suka tace. "What kamar ya kenan?" "The vice president received a ransom call." Babu shiri Babyboo ta mike daga jikin kujerar da take jingine da tambayar. "How much?" ta bata amsa da "Five hundred million dollars." ɗan shiru tayi domin ta iya bin komai yadda ya kamata yadda ya dace a natsenta ta furta. "Who called?" "The kidnappers." ta bata amsa, tana sake jefa mata wata "Did they ask for anything else?" Dan shiru Laylerh tayi kafin ta ce "Yes." Ɗan daure fuskarta Babyboo tayi. "What?" Sai da laylerh ta dan janye wayan daga kunnenta kafin ta iya bata amsa da "They specifically asked that K Mashi should deliver the money."
Wani furzan da iska tayi mai zafi daga cikin bakinta a zafafe kafin ta wani runtse idonta tana fara tunanin kalaman mutumin dake neman kudin. Five hundred million? K Mashi kana ya bada umarnin kada duk wata harkan jami'ai ya shiga. Da sauri ta bude ionta tace "Send it."
"Yes, Bhu!." Laylerh ta faɗa daga ta bangaren nata dake sau tari takan kira Babyboo din da Bhu kawai tana katse wayar. A natse ta dan lumshe idonta tare da buɗewa tana maida idon nata gun window din motar, wasu ababuwa na fara dawowa cikin kanta, a hankali ta ja wani dogon numfashi daidai nan motocinsu na kutsawa zuwa ainihin cikin gidan nasu. Kai tsaye samanta ta wuce tayi ruf da ciki saman bajajjen hadadden gadonta. Ta jima sosai a hakan kafin ta faɗa toilet babu jimawa ta fito kai tsaye wata guntuwar riga ta saka tana sake fadawa saman bed din, bacci sosai tasha kafin karfe dayan nan zuwa karfe ukun yamma. Wanka ta sake ta sauka ƙasa kai tsaye bangaren Mom nata ta nufa, a zaune ta tarar da ita tana karanta newspaper da gilas fari a idonta, wani dan bata fuska tayi saboda sallaman da tayi amma Mom din taki amsata. A shagwabe ta karaso tana jingina kanta da jikin mum din...
A shagwabe ta karaso tana jingina kanta da jikin Mom ɗin, hannunta ɗaya ta sa saman cinyarta tana ƙoƙarin samun nutsuwa, amma Mom ɗin kamar ba ta san da zuwanta ba. Idanunta na kan jaridar dake hannunta, ko kallon Babyboo ɗin ma bata yi ba.
“Mom…”
Babyboo ɗin ta sake fada da matsayawa gaban Mom din da har zuwa lokacin taki kallonta.
“Mom, me ya faru hala na ɓata ranki ba?” Juyo da fuskanta baki daya Mom din tayi tana kallon Babyn, kallon dake bata cikakken tabbacin tabbas akwai wani abu kenan. Tana tsaka da wannan tunanin taji muryan Mom din ya katse ta da faɗin. “Me ya faru? An kinsan ban son kira irin haka zaki iya tafiya ina duba Muhimmin Abu ne” A hankali Babyn ta cire kanta daga jikin Mahaifiyar nata ta miƙe cikin rashin jin daɗi. Kallo ɗaya Mom din ta sake mata tana dauke kai kafin kafin ta furta. “Kin san me yake ɓata min rai game da ke?” dan girgiza kanta Babyboo tayi alamar a ah bata sani ba. "Taurin kai! Rashin daukan maganana da muhimmanci... And ke sai abinda kika tsarama ranki zakiyi kawai kike yi woni bai isa tankwaraki ta sauki ba..." Jikinta a ɗan sanyaye ta kalla Mom din da ambatar sunanta.
“Mom…”
“Ki min shiru ban son jin komai Soumayyerh.... Muryar Mom ɗin ta faɗa a ɗan kamar tsawace cike da fushi taci gaba da faɗin. “Duk lokacin da kika sa wani abu a ranki, sai ki ɗauka cewar kamar ke kaɗai ce za ki iya warware shi wannan abun, why? Why Baby da ba zaki bi umarni na ba sai na Mahaifinki kawai? Don ya fini son ki? Ko kuwa don ya fi baki kulawa fiye dani uymmm? Shin ashe ko ban cancanci komai daga gare ki ba ba zaki iya jin kai na da tausayina a matsayina na Mahaifiyar data dauki nauyin ciki da rainonki fiye da shekaru uku ba uymmm?" Mom ta yi shiru na ɗan lokaci idonta na fara sanja launi kafin ta ɗora da faɗin. “Ni uwarki ce, shin idan ban isa dake ba waye kike son in nuna isa da iko na a kansa matsayina na Mahaifiya?... " wani dan numfashi mai dumi ta fesar tana sake daidaita zaman glas na idonta kana taci gaba da faɗin. “Kin girma na sani. Kina da hankalin ki na sani, haka kuma ban taɓa son na hana ki yin abin da kika san ya dace ba Baby. Amma girma ba yana nufin mutum ya daina buƙatar wanda zai riƙe shi ba ne ahhh dole dolen dole yana buƙatan mai bashi shawar wani time to time haka .” Tunda Mom din ta fara magana jikin Baby yayi weak ta kasa cewa komai. A natse Mom ta janye farin gilashin dake idonta kafin ta numfasa kai tsaye tana bata hannunta daya da faɗin.
“Zo nan.”
Wannan karon muryarta ta sauya gaba ɗaya babu fushi ko kaushi sai na zallan tausayi irin na uwa da ƴar ta, sai da baby ta tsaya na ɗan lokaci kafin ta sake matsowa kusa da ita. Mom ta kama hannunta, ta ja ta zuwa gareta tana kwanto da kanta a jikinta kamar yadda ta saba mata tun tana ƙarama, kafin gaba ɗaya Mom din ta rungume ta. Hannunta ɗaya ya shiga shafa mata kai a hankali, ɗayan kuma tana shafa bayanta, a tausashe Baby tace “Ki yi haƙuri Mom ko nayi kuka!.” Lumshe ido Mom din tayi tana sake shafa kanta tace. “Na yi Baby narh ba sai kin yi kuka ba, an ki saurare ni Baby ita rayuwar duniya da kike gani tana da abubuwan da mutum ba zai iya canza su ba. Akwai lokacin da za ki yi ƙoƙari, akwai lokacin da dole za ka yi jira. Amma kada ki bari abin da kike nema ya sa ki manta da kanki.... " Sake kwantar da kanta jikin Mom din tayi tana zagaye ta da hannunta. “Amma idan mutum yana kallon wani nashi na cikin matsala fa? Ko wasu ma da basu dangancemu ba?” Kai tsaye tambayar data cilla ma mahaifiyar nata kenan. “Ki taimaka masa.” “Idan taimakon yana da haɗari fa?” ta sake tambayar Mom din, wanda ya saka ta yin shiru kafin tace.
“Ki nemi hikima kafin ki nemi jarumta.” dago da kanta tayi kalli mahaifiyar nata wanda itama ta kalleta tana sake gyada mata kai alamar tabbaci kenan, kafin ta ɗora da faɗin. “Jarumta ba ta nufin mutum ya shiga wuta da kansa bane, Wani lokacin jarumta ita ce ka san lokacin da za ka tsaya, ka san lokacin da za ka jira, ka kuma san lokacin da za ka yi magana.” Sake kwantar da kanta jikin Mom tayi data ci gaba da shafa mata kai. "Nagode!nagode sosai da sosai best Mom..." A hankali Mom ta sumbaci goshinta da fadin. “Ki kwantar da hankalin ki, duk abin da yake faruwa, kada ki bari tsoro ya fara yanke miki hukunci kafin komai" A hankali ta sake lumshe idonta tare da sake furta.
“Na gode, Mom.” dan dungurin kanta Mom din tayi tace “Ba sai kin gode min ba.” Sosai ta jima jikin Mahaifiyar nata kafin ta koma samanta,ranta cike fal da tambayar da taki barin ranta na son sanin ko waye wannan makwamishin, an kuma ta ya za'a ce kidnappers sun san Khabeer K. Mashi? Ehhh ta yaya? Dole a kwai lauje cikin nadi tabbas. Da iPad nata tayi wasu ƴan ayyuka zuwa magrib, da Isha'a kuma Laylerh ta sake kiranta take sake sanar da ita cewan ai kidnappers din nan sun sake kiran Dad sun ce yanzun shi suke son ya kai kudin ba K Mashin ba, kuma ƙarfe biyar na yamman gobe. Sosai hankalinta ya sake tashi tana jin tabbas dole akwai abinda yake tafiya ba daidai ba, waya tayi mai ɗan tsayi sosai kafin tayi sallama da wanda take wayar wani shegen murmushi kwance saman fuskarta ta haye gado bayan tasha fruits with pancakes...
Washe gari...
*IN THE EVENING*
Tun kafin lokacin da aka gama gindaya musu suka gama tsara komai cikin hikima, cike titunan ya ke wanda ke kewaye mutane kowa na sabgar gabansa, saboda nan ne inda aka sharɗanta musu zasu kai kuɗin, sosai mutane keta ci gaba da zirga zirgarsu kamar yadda suka saba, wasu suna sanye da kayan aiki, wasu da kayan gida, wasu suna riƙe da jakunkunan cefane, wasu kuma suna tsai tsaye daga gefen titi suna jiran abin hawa, inda suma wasu daga cikin jami'an tsaron sun riga sun gama bazuwa a wurare daban-daban cikin badda kama, cikin hikima kowanne yana da nasa matsayar da kuma hanyar fita idan wani abu ya sauya. Wasu suna cikin motocin da aka faka a wurare daban-daban, wasu kuma suna cikin jama'a suna kallon komai cikin nutsuwa, babu wanda ya yi kala da ma'aikaci ko wani motsin da zai jawo hankalin mutane kansu. Daga ta can nesa kuwa K Mashi ne zaune cikin wata motar da aka faka gefe guda irin marsandi din nan, yana zaune daga cikin motar kamar bai san abinda ake yi ba,amma a zahiri idanunsa na kan wani ƙaramin screen din dake gabansa ne. Yana zeroyind komai dake tafiya a kan tsari da umarninsa.
“Ku tabbatar babu wanda ya matsa kafin lokaci,” ya faɗa cikin natsuwa, hannunsa ɗaya yana kan abin magana dake kunnensa. “Duk wanda ya zo wurin karɓar jakar, kada ku taɓa shi sai na bada umarni.” “Copy that, sir.” suka amsa yana ɗan lumshe idanunsa da ci gaba da kallon screen ɗin da sake lumshe ido yace “Ku kuma ci gaba da kula da VP. Bana son wani abu ya faru da shi.” sake amsa shi sukai daidai nan wata mota ta shigo a hankali a kuma slow ta tsaya can gefe. Zuwa can kuma sai ga bayyanuwar Vice president daga cikinta Motar ya fito. Fuskarsa ta yi siyau alamar tashin hankalin da yake a ciji, ga yawan bugawan da zuciyarsa keyi akai akai fiye da yadda zai iya ɓoyewa, hannunsa na riƙe da jakar da ke ɗauke da uban makudan kuɗaden nan, idanunsa na yawo a hankali kamar wanda yake son gano wani abu da ba zai iya gani ba ko jiran umarni, daidai nan kuma wayarsa tayi ƙara yayi saurin dagawa.
“Ka iso daidai wurin da na umarce ka?” kai tsaye abinda aka ce masa kenan, cike da taka tsantsan Vice president wato Aminu Dakata ya amsa da. "Ehh! Ehhh na iso!"
Cikin kamewar muryan da kai tsaye baka isa tantance a yanayin da yake ciki ba aka furta. "Da kyau! To juya ta bangaren damanka yanzu sai kaci gaba da tafiyan..." Aka furta masa wanda ya saka Aminu Dakata ɗan saurin furta. "Ahhh minti daya don ALLAH nace ko zaka iya hadani da ɗana Sameer yanzu haka yana tare da kai don ALLAH zaka iya bani shi naji?...." Wata yar siriryar dariya akayi da faɗin "Tabbaci kenan?. Idan har kana son ɗan ka ya dawo gareka kayi komai bisa umarnin dana gindaya maka. Karka manta na ce ma kada ka naimi taimakon yan kowa shi ne sharadin? Ni kuwa idan har ka gimtse bakinka kayi hakan, kabi duk abinda zan fadama to salin alin zan dawo maka da danka, yanzu ka juya dama ka soma tafiya.... " aka sake fadi....
"Jeka..... "
Babyboo dake tsaye daga bayansa ta juya bayanta ta fadi kai tsaye tana juyowa baki dayanta, tana sanye cikin wasu bakaken kaya kunnenta sakale da abin magana tare da dan taɓawa da furta. "Soumayyerh ce kuna jina? Ina son ayi tracking wannan kiran kai tsaye ku turomin da wajen da tantirin yake...."
"Ina Madame saboda kiran internet ne yake yi, sannan yana amfani da T. O. I ne wanda yake ɓoye adireshin inda yake, domin yana nuno mana ƙasashe da wurare da daban daban ne" Wani iska ta kaima naushi tana furta "Aikin banza" A bayyane ta fada tana sake furta. "Yawwa kuna jina?" ta furta tana sake danna abar dake makale jikin kunne ta, "Ehhhh Madame muna jinki muna kan layi..." "Ina son ku tsananta idanuwanku Ata ko ta Ina domin kewaye wannan makwamishin yana da matukar wayo sannan masanin net work ne, don haka kuci gaba da bibiyarsa da mutumin da zai ya shi kudaden a hannunsa, daga nan sai ku jira kuji miye zance...."
"Aha..." suka amsa, shi kuwa ata bangaren Aminu Dakata cikin wani sabon salon iska wanda bayan canza muryan da akayi har da wani iskanci iskanci ke a cikin muryan aka ci gaba da bashi umarnin. "Ci gaba da tafiya! Kaci gaba da tafiya! ci gaba mana ci gaba da tafiya..." Aka furta daidai lokacin da kamar karar wucewar mota ambulance ta gitta da kuma wata karar daban.
K Mashi dake zaune cikin motar sane ya sake latsa abinda ke kunnensa da faɗin." Tabbas koma waye wannan tantirin yana ata nan wajen kuma tabbas ina da cikakken tabbacin yana ganin komai..." Soumayyerh (Babyboo) ce ta dake tafiya tana bin sawun duk inda Vice president ya ɗauke ƙafarsa tace. "Ta yaya zaka ce haka amma sir?" dan gyaran murya K Mashi yayi da faɗin. "Lokacin da motar ambulance din nan ke wucewa naji karar abu biyu. Don haka nake tunanin yana amfani da abar canza murya ne kana sannan a cikin muryoyin da akwai ababuwa da yawa daban daban. Kowanne daga cikinsu photocopy ne sannan suna sauraren duk abinda muke muke fada....."
"Maza mujeeeee.....ci gaba da tafiya ci gaba mana ci gaba da tafiya ci gaba kaje...." wata murya daban ta sake fadi da aka sake canza ta. "Dakata!..." Wata murya din daban again ta sake faɗi kafin a ɗora da cewa. "Kaga wata farar mota doguwar mota ata hannun hagunka? Dan nesa kadan? Kaje ka bude ka ajje wannan jakar a ciki ci gaba da tafiya....." Ya fadi cikin wani dan iskan salon mai tafe da zafin kai kai tsaye. A natse vice president yaci gaba da tafiyan har ya isa ga motan bayan ya tsallake titin dake gefensa...
"Ina turrrr...." K Mashi da Babyboo suka hade baki wajen furtawa lokacin da suke bude motar suka ga baki dayan jami'an da suka zo dasu ne cikin badda kama a cikin motar bakunansu a rufe..." Wata mahaukaciyar dariya ce ta ratsa duka kunnuwansu kafin wani sauti mai tsananin kaushi ya biyo bayan dariyan. " Ohh! Ohh!! ohhh!! C. U. I? garin yaya akai kuka bari kukai saurin shiga hannu irin haka? Yanzu kuma ko miye abinda zasu iya vice president?...." Aka fadi wanda ya saka take jikin Vice president din soma rawa kafin ya sake tsinkayar muryan da faɗin."Na tabbata ba kai ne kace su zo ba, kuma kana matukar son dan ka ya dawo gareka, kuma kamar naga kana son ya dawo a raye ne ko? To kenan wanda ɗan ƙaniyar ne ya kawo su?..." Aka fadi a mugun fusace.
"Ehh ehhh Ni ne !ni ne wllh wanda nayi hakan ne badan su shiga cikin wannan lamarin ba...." Yay shiru kafin ya juya gabas da yamma kudu da arewa ya hade hannuwansa wuri guda da furta. "Yallabai Ɗana! Ɗana don ALLAH kada kai ma sameer wani abu! Kada ku cutarmin dashi..." Wata shegiyar dariya akayi wacce duk yadda akayi sai da aka shawu mankas aka yi maganar da ita yace. "Ka reneshi cike da soyayya ba? To shikenan bari mu gabatar da wani ɗan ƙaramin wasa mana?..."
BY AMMEY LAYLERH ✍️
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️