Page 11&12
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Cikin abinda bai wuce kiftar ido ba sai ga Yaya Sadiya ta bayyana a wurin, ta zube gaban Nadiya wacce ke kwance cikin jini babu alamar numfashi tattare da ita, cikin matsanancin firgici da ruɗun da take cikinsa ne yasa gaba ɗaya ta daina wani function. Komai nata daina aiki ya yi sai idon kawai da ta kafe Nadiya dake kwance jikin jinin, A cikin rai da tunaninta take raye wanne irin mummunan mafarki ne take yi haka? Nadiya? Nadiyanta dai itace ke kwance haka cikin jini babu alamun wani zai taimaka mata? Ido ta rumtse da ƙarfi tana fatan idan mafarki take to ta farka daga wannan mummunan mafarkin haka nan mai tsananin muni da tashin hankali. Daidai lokacin da ta fara jiyo maganar Babansu sama sama yana cewa a kai shi inda Nadiya din take, a kai shi ya ganta, kunnuwanta basu kai ga gushewa a jin kalaman Mahaifin nasu ba ta sake jin maganar Shitu yana kunduma Ihu da zage zagen yau sai anyi kaza kaza, sai anyi yakin karshen duniya ko a shi ko a fulanin, wani irin mugun bacin rai da tukukin bakin ciki ne taji ya kome zuciyarta take. A kuma dai wannan lokacin ne ta sake jiyo karar jinyar motar ƴan sanda ta karade wurin. Idonta tana da tabbacin sun sama matsala ita ma don kuwa babu abinda take iya gani sai duhu kawai, ji tayi ana ture ta da fadin 'let go' din daya sakata saurin mirza idon ta a hanzarce tana buɗe su cike da hope din cewa zata gani zata ga komai tarwa ,ta kuma ga ta farka taga komai mafarki ne, kan Nadiya din dai ta sake bude idon nata tarwar daidai lokacin da wasu yan sanda biyu suka dauketa suna zirawa a mota da sauran wanda aka ma rauni zuwa cikin garin Bauchi babban asibiti. Salati da sallallamin Baba ta fara ji yana cewa "Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un" wanda take itama ta kama daram kaman an rada ta cikin bakinta....
Ɗaya daga cikin Ƴan Sanda din ne ya nufo Baba da har zuwa lokacin kalmar “Innalillahi wa Inna’ilaihi raji’un…yake furtawa cikin wata murya mai nauyin dake sake ratsawa wurin. “Baba!” Ta kira sunan Mahaifin nasu cikin wata muryan da ta kasa tantanceta,shi dai Baba har lokacin yana nan yana ta addu’o'insa motar da suka shiga daga ita har Baban naci gaba da gudu suna barin ƙauyen nasu suna daukar hanyar da zata kaisu har zuwa cikin garin Bauchi, yayin da motocin ƴan sandan ke ci gaba da bin su a baya tare suna bama wanda suka samu rauni tsaro sosai. Ita kuwa Sadiya gani tayi yau wannan hanyar ta yi mata tsawo fiye da yadda take a kullum a idonta, kowanne daƙiƙa ke wanne motsi tana kallon Nadiya ne, wani lokacin kuma tana ɗaga kanta tana kallon jami’an da ke gabansu, sake kamo hannun Nadiya tayi cikin nata ta furta “Nadiya… don Allah ki buɗe idonki…” Amma still shiru babu amsar nan dai har yanzu shiru. A cikin ƙasa da mintuna kadan sai gashi suna shirin daukan hanyar Bauchi motocin ƴan sanda kuma naci gaba da rufa musu baya. Kowane daga cikin jami’an yana cikin taka-tsantsan, saboda har yanzu babu wanda ya tabbatar da cewa harin ya ƙare. Sadiya kuwa har zuwa lokacin babu abin da take yi sai kallon Nadiya. ALLAH sarki dan uwa mai dadi aka ce wani lokacin ta kai hannunta daya ta taɓa goshinta, wani lokacin kuma ta kama hannunta ta rike cikin nata, ko ta sunkuyar da kanta tana addu’a.
“Ya ALLAH ka raya min ita… Ya ALLAH kada ka karɓi ranta ita kaɗai ke gare ni kaf duniyar…” ta kama hannun Nadiya kam ta rike da ƙarfi kamar tana fatan hakan kaɗai zai iya riƙe ranta a jikinta. Daga can gaba kuwa Baba ya kasa yin komai sai addu’a shima, fadi yake ya ALLAH ka rufa mana asiri ALLAH ka tashi kafadun Nadiya! ALLAH ka karbi nawa ran ka barta ta rayu domin cikar burinta, domin ta inganta mafarkinta taci gaba da karfafa kanta da ƴar uwar ta. Kusan cikin rabin awa suka fara hango fitilun garin Bauchi daga nesa, har zuwa lokacin da suka iso cikin wani babban asibitin Bauchi, ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro har sun riga sun fito suna jiran su . Kai tsaye aka buɗe ƙofar motar, aka fara sauke waɗanda suka samu raunuka. Sadiya ce ta yi saurin saukowa tana bin masu ɗaukar gadon NADIYA tana cewa. “Ku taimaka mana don ALLAH kar mu rasata, ita kaɗai ke gareni duniya da lahira bayan Mahaifina ku taimake mu don ALLAH!”
“Madam, ku ja baya ku bar likitoci su yi aikinsu.” wata cikin likin ta fadi suna shiga da Nadiya cikin gaggawa. Cak haka Sadiya ta tsaya bakin ƙofar tana kallon yadda aka tafi da ita har sai da wata ƙofa ta rufe tsakaninsu. Hawayen da ta daɗe tana riƙewa suka fara gangaro mata. Da lalube Baba ya karaso kusa da ita. “Ki yi haƙuri Sadiya.” ya furta a tausase wanda ya sakata dagowa ta kalle shi da furta. “Baba… za ta rayu ko?” Shiru kawai Baba ya mata ba don bai san amsar ba, a ahhh sai don ba ya son ya faɗi abin da shi kansa bai da cikakken tabbaci akan shi. “Mu bar komai ga ALLAH.”Ahankali ta lumshe idanunta amma a zuciyarta tana jin wata irin ƙarar tsoro da ba ta taɓa ji ba.
Da sauri da sauri likitoci suka fara fitowa daga dakin da aka shigar da Nadiya, zuwa can kuma sai gashi an sake gangaro da gadon da Nadiya ke kai cikin gaggawa ba tare da sun daga kai sun kalla kowa ba. Wanda ya saka Hankali Sadiya sake tashi a matukar tsorace ta nufesu tana tambayar "Mai ya faru da ƴar uwata? Za ta rayu? Me yasa kuma fito da ita daga nan ɗin?..." kusan duk a susuce take cilla musu tambayar a kuma hargitse. “Madam, ku yi haƙuri. Za ta rayu IN SHA ALLAHU Muna iya abin da za mu iya..."Sadiya ta bi gadon da aka ɗora Nadiya akai har zuwa bakin ƙofar emergency room din da aka komar da ita, tana kokarin mara mata baya wata nurse ta tare ta da furta.
“Ki yi hakuri ki tsaya a nan.” daga haka ta wuce cikin emergency din ana rufo kofar daya saka Sadiya tsayawa cak kamar yadda ta yi a wurin harin ta kalli ƙofar. Tare da kallon hannunta da Jinin Nadiya ke makale a jikin tafin hannun. Ahankali ta rufa tafin hannun saman fuskarta cikin rawan furta ta furta.
“Innalillah wa'inna ilaihi raji'un! Ki yi haƙuri…” Hawaye suka sake gangarowa daga cikin idanunta taci gaba da faɗin. “Ki yi haƙuri Nadiya… kada ki bar mu kada ki tafi ki barmu don ALLAH....” Shi kuwa Baba ya kasa cewa komai sai addu’a. Addu’a kawai a cikin rai da ruhinsa da fatan ubangiji ya bama Nadiya lafiya. Awa uku cur likitocin nan suka dauka cikin ɗakin kafin su fito gaba ɗayansu suna sauke ajiyar zuciya duk sun hada uwar zu fa. Sadiya ce ta miƙe cike da matsanancin faɗuwar gaba tana jiran jin abinda likitocin zasu ce game da ƴar uwar ta. Daya daga cikin su ne ya shiga cire safar hannun sa da mask yace Baban ya biyo shi, Sadiyan tayi saurin mikewa tana cewa Baba baya gani, tayi maganar tana share kwalla, likitan ne ya kalle ta da kuma Baba da jikinsa ke rawa sosai shima, cike da matsanancin tausayinsu yace "Ina so ku kwantar da hankalin ku. Munyi iya bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun cece rayuwar ta, kuma alhamdulillah IN SHA ALLAHU zata mike taci gaba da rayuwarta, abinda ma ya saka sumewar ba komai bane face kwakwalwarta ce dake mata processing abinda ya faru. Shi yake sake triggering nata da har take neman rasa numfashin ta! abinda zakuci gaba da mata kawai shine adda'a. "Numfashi daga ita har Baban suka sauke mai karfi kafin tayi shiru don in dai tace zata sake bude baki maimakon tayi magana kukan da aka hanata ne zai sake ɓarke mata, saboda she felt her heart broke into pieces, a hankali ta zame hannunta daga fuskarta ta juya tana kallon Baba dake tsaye fuskarsa cikin wani irin yanayi mara misalta. Take wani abu ya nemi daya sake cunkushe zuciyarta da yayi mugun karaya a wannan gaɓar da ƴar uwarta da Mahaifinta ke ciki, all of a sudden taji duniyar tayi mata zafi a ɗan kankanin lokaci irin haka, kafin wasu hawaye taji sun kawo idonta, da sauri ta saka bayan hannunta tana gogewa sanin kuka ba mafita bace. Tana marawa likitan baya tana tura ƙofar da taga ya shiga jiki babu wani kuzari tattare da ita ya. A natse likitan ya mata nuni da wurin zama tana kaiwa zaune a darare, shi kuma likitan yana ci gaba da aikin da yake yi cikin nutsuwa. Kafin daga baya ya ɗaga kansa ya kalle ta yana cewa, “Kada ki cika damuwa da yawa Hajiya saboda halin da kike ciki kema, mun yi iya abin da za mu iya a yanzu, kuma abin da ya rage na ALLAH ne.” Sadiya ta gyada masa kai kawai, domin har yanzu kalaman likitan da ya ce Nadiya zata rayu IN SHA ALLAHU suna ta yawo a cikin kunnuwanta kamar ita kaɗai ce kalmar da ke riƙe ta daga sake rushewa, ta sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta, jinin Nadiya har yanzu bai gama fita daga jikin tafin hannunta ba saboda bushewar da yayi, wani irin yanayi ne da ya sa take ji kamar dukkan abubuwan da suka faru yau sun faru ne a jikinta ita kanta, tun daga ihun mutanen ƙauyen, gudun da aka dinga yi, har zuwa ganin ƴar uwarta kwance cikin jinin da tayi. A hankali ta ɗaga kanta ta kalli likitan tana cewa, “Zan iya ganinta?” Likitan ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Ba yanzu ba, tana ƙarƙashin kulawa sosai, idan yanayinta ya ɗan daidaita za mu sanar da ku IN SHA ALLAHU.” Da “Toh” kawai ta amsa masa, sannan ta sake komawa cikin tunaninta, Baba kuwa yana can wajen ƙofar emergency yana zaune a kujerar da aka kawo masa, hannayensa biyu cikin na juna yana ɗaga su sama lokaci zuwa lokaci yana roƙon UBANGIJI da ya tashi masa ƴarsa lafiya, shi kansa bai san me zai ce ba, addu'a ce kawai ta rage masa.
*ABUJA*
Tun lokacin da aka fara wannan tafiyar, muryar da suke ji ta ci gaba da bama Vp president umarni, “Juya dama ci gaba da tafiya.” haka ya sake juyawa yana ci gaba da tafiya din. Daga ta can baya kuwa haka suma jami’an suka ci gaba da bin umarnin kamar yadda aka ce bama Vp president din, wanda duk wani jami'in dake wurin suna sane da cewar ko waye wannan mutumin yana kallonsu daga duk inda suke, kai tsaye motar Vp hanyar babbar gadar sama ya nufa, wanda ya saka jami'an nan a ɗan rudu saboda shegen go slow din dake hanyar, wanda da dukkan alamu ma an hada shi ne da gangan da ganganci. Ko kafin su ankare ma sai gashi kwasam connection nasu ya yanke. Shiru haka suke dena jin komai daga Vp president din wanda ya saka dukkan jami'an yin shiru. K Mashi ne ya sake kai hannunsa zuwa ga na’urar dake kunnensa tare da furta, “Repeat.” sai dai babu amsa ya sake maimaita kalmar “Repeat!” amma har yanzun shiru. Wanda ya saka Babyboo ta dago kai tana kallon K Mashi din tare da furta. “Ya katse.” ta furta suna sake bin bayar motar Vp data fara nisa. “Sir, motar VP!” daya daga cikin jami'an ya fadi wanda ya saka K Mashi juyowa yana furta. "Me?" "Kwarai Sir. Motar na nemar bace mana ne..." jami'in ya fadi wanda yasa K Mashi furta. “Follow it!” Jami’an sukaci gaba da bin motar cikin gaggawa, sai dai duk da kokarin da suka yi haka cunkuson ababen hawa ya yana musu gane motar, wanda zuwa yanzun kusan duka motocin wurin iri daya ne dana Vp din. Wanda hakan Yay sanadiyyar da suka rasa Motar. “Where did it go?” Amma babu wanda ya iya amsawa “Search!” ya sake fada....
Daga ta can bangaren Vp president kuwa, daidai kamar za'a sauka daga kan gadar aka dakatar dashi cak a wurin, ka ƙarar ruwa nan yana ji wanne ke gudana ta ƙarƙashin babbar gadar. A wani irin hankali da taka tsantsan Vp ya fito a motan da aka bashi umarnin ya fito din, tare da kallon gabansa sai dai babu kowa ya juya dama nan ma babu kowa, a birkice ya juya ko ina yana kallo tare da furta “Me ya faru?” nan ma babu amsar dai. Kafin wata muryan da sam bata yi kama da tantanceta aka yiba aka furta "Successful Vp...."
Su kuwa daga ta can bangaren jami'an DSS din nan, cike da tsananin tashin hankali K Mashi da sauran jami’ansa suke tsaye, game da bacewar da motar Vice President ta musu, kuma abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne yadda komai ya faru cikin ɗan lokaci kaɗan ba tare da sun samu damar fahimtar daga inda ainihin matsalar ta fara ba. Wasu daga cikin jami’an sun rabu gida biyu suna binciken wurare daban daban, wasu kuma suna duba na’urorin sadarwa, yayin da K. Mashi yake tsaye yana kallon yadda duhun magrib ke sake kusantowa, cike da wani irin nutsuwa mai ɗauke da fushi. Gashi baki daya an katse musu alamar bibiya da sadarwar dake tsakaninsu da Vp president din. Daga ta can gefe suka jiyo muryar wani jami'i yana faɗin“Sir!” K. Mashi ya juya, “What happien?” Jami’in ya yi saurin zuwa gare shi yana miƙa masa wata ƙaramar na'ura, “Mun samu wani abu.” K. Mashi ya karɓa ya kalle ta, “Menene?” “Na'urar sadarwa ce da muka gano a kusa da wurin da connection namu ya yanke.” K. Mashi ya ɗan juya ta hannunsa yana dubanta, kafin ya tambaya, “Ta yaya kuka tabbatar da cewa anyi amfani da ita?” “Mun gano ta bayan mun bi frequency ɗin da aka samu daga motar.” K. Mashi ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ya kalli AJMAAL wanda yake can gefe yana nazarin wasu bayanai a cikin na'urar tasa. “Ajmaal.” Ya kira shi. AJMAAL ya ɗaga kai ya nufo su. K. Mashi ya miƙa masa na'urar. Ya karɓa ba tare da wata magana ba, ya fara kallonta, ya duba gefe guda, ya juya ta, sannan ya saka ta cikin wata na'urar da ke hannunsa. Bayan ɗan lokaci kaɗan ya yi wani ɗan numfashi mai nauyi, “Wannan ba na'urar da ake amfani da ita wajen sadarwa kawai ba ce.” K. Mashi ya kalle shi. “Me kake nufi?” AJMAAL ya ɗaga idanunsa. “An yi amfani da ita ne domin ta ɗauki attention ɗinmu zuwa wani wurin daban.” “Meaning?” “Meaning wanda ya tsara wannan ya san yadda muke aiki.” Ya ɗan yi shiru. “Ya san za mu bi signal nashi dole, Saboda haka?” sai kuma ya kalla na'urar ya sake furta. “Saboda haka wannan ba kuskure bane. An shirya shi” Wani irin shiru ne ya mamaye wurin. Kafin K Mashi ya kalli sauran jami’an, sannan ya kalli AJMAAL. “Toh ina motar?” AJMAAL ya ɗan lumshe ido. “Idan abin da nake tunani gaskiya ne, motar ba ta yi nisa ba, tana nan a boye a wurin da ba za mu fara nema ba.” K. Mashi ya ɗan yi murmushi mara sauti tare da furta. “Ka yi magana.” AJMAAL ya ɗaga na'urar. “An katse mana connection ɗin ne da gangan, sannan aka bar wani signal na ƙarya domin mu bi shi. A lokacin da muke binsa ne aka fitar da motar daga wani ɓangare daban.” K. Mashi ya kalli inda yake nunawa. “Saboda haka mun bi abin da suke so mu bi.” AJMAAL ya gyada kai. “Exactly.”
VP A lokacin da wannan muryan ta dake shi kai tsaye badan ace a kamar rude yake ba da ace ya fahimci wani abu a cikinta, kafin ya daga kansa a hankali. Kuma a daidai wannan lokacin ne jami'ai suka yi nasarar isowa kan gadar a kafa. bayan sun yi ta zagayawa suna neman motar Vice President ɗin da ta ɓace musu kamar ƙasa ta haɗiye ta, sai daga can gefe ɗaya cikin duhun wurin suka fara jiyo ƙarar wata mota tana kamar kusantowa zuwa wurin, cikin taka tsantsan din da ba gudun da za ta sa a gane tana gudu ba, ba kuma tafiyar da za a ce mai motar yana tsoron wani abu ba ya faru da shi ba. Kai tsaye K Mashi ya ɗaga hannu yana bada alamar kowa ya tsaya, haka jami’an suka yi shiru ɗaya bayan ɗaya, wasu suka fara zagaye ata wurin, wasu kuma suka ɗauki matsayi a bayan wasu motocin, kowa hannunsa yana kan makamin da ke tare da shi. Shiru ya sake mamaye wurin, sai ƙarar injin motar da take ƙara kusantowa, kafin daga ƙarshe ta tsaya can nesa kaɗan. Ƙofar motar ta buɗe, amma babu wanda ya fito nan take. Wani jami’i ya ɗan matsa gaba kamar wanda ke ƙoƙarin gane wanda ke ciki amma cike da iya taku da taka tsantsan, A wani irin mayen slow aka fara ziro da kafa daya, kafin ɗayar ta biyo baya kai tsaye wani ingarman gangar jiki ya biyo baya yana fitowa baki daya, bakinsa dauke da cigarettes din da yama wata yar banzar zuka yana busho hayaƙin cikin wani irin salon jan magana, tare da sanya ƙafarsa daya ya rufe ƙofar motar da nutsuwa kamar wanda bai damu da tarin jami’an da suka kewaye da wurin ba. Mutumin yana sanye ne da wata riga mai guntun hannu wacce ba ta da wani abu na musamman a jikinta, amma yadda ya saka ta da yadda komai yake a jikinsa ya sa ta yi masa wani irin salo na daban. Wani irin dan iskan aski ne a kansa, wanda aka seseya gefe da gefen kan amma ba irin wanda za a ce an zauna an gyara shi tsaf ba; like dai kawai irin na manyan tantiran nan na duniya lamba ɗayar dake nuni da kamar mai shi ba ya ɗaukar lokaci yana damuwa da abin da mutane za su ce game da shi. Idanunsa kuwa sanye cikin wani black shades mai duhu sosai, yayinda fuskarsa kuma ke rufe da face mask sai nose mask din da sune sukayi taron dangi wajen rufe mafi yawan abin da zai iya bayyana ko wanene shi. Safar hannu ce a hannuwansa duka biyun black suma, har ma da tufafin da yake sanye da su babu abin da zai ba mutum damar gane ko wanene shi cikin sauƙi ta ruwan sanyi. Kafin ya tsaya kamar mai nazartan wani abu yana kallon irin shige da ficen kusan duk mutanen wurin, amma ba irin kallon nan na wanda ya firgita ganin jami'an bane, sai irin kallon nan na mutumin daya gama sanin kansa wanda da kuma son sanin iyaka adadin mutanen da ke kewaye da wurin, ya san abin da suke iya yi, kuma duk da haka bai ga dalilin da zai sa ya ji tsoron ba domin dama can ba matsoraci bane ko da ace yana a tsakiyar filin yaki rundunar yakin duniyace. Kai tsaye daga inda yake tsaye din yake iya kallon jami'in dake kewaye da wurin ta bayan eye glasses nashi, kafin ya wani ɗaga hannayensa sama a hankali ba don ya miƙa wuya ba, sai kamar yana yi ne kawai saboda ya ga dama yana soma tafiya zuwa ga Vp dake rike da jakar kudin, wanda kai tsaye Vp din ya furta “Who are you?” daidai da lokacin da yake wata yar iskar tsaiwa a gabansa. “Na tambaye ka, waye kai?” Vp ya sake fada wanda ya saka mutumin wani irin ɗan karkatar da kansa gefe guda, kamar yana nazarin Vp ɗin ne irin tun daga sama har ƙasan nan. Wanda ya saka Vp ƙara tsananta kallon mutumin, domin kuwa tun farkon fitowar mutumin daga motar yake kallonsa, wanda kai tsaye da da farko kamar bai fahimci abin da yake gani ba, sai ya ƙara kai dubansa ga mutumin daya saka wani abu motsawa a cikin zuciyarsa, wani irin tunanin da jima yi shekara da shekarun da yayi yana ƙoƙarin binne shi na fara nemar dawo masa cikin ka, kai tsaye ya ci gaba da kallon mutumin wanda shima shi yake kalla. Wani irin shiru na mamaye wirun, kafin a wani irin hankali mutumin yakai hannunsa baya tare da ture pcarp din dake kansa and glasses, Wani irin harbawa zuciyar Vp tayi domin kamar Gizon da yaga idanunsa sun masa da mutumin da sam bai kamaci ace ya kasance a gabansa ba. “RAYYERN…” zuciyarsa ta furta sunan da kai tsaye ta taho masa da wata irin faduwar gaban da har sai daya saka shi saurin dafe zuciyarsa yana karfafa kansa a cewar baya wannan duniyar....
Shi kuwa wannan mutumin kamar wanda ke son bama Vp din tabbaci ya wani janye face mask and nose mask din dake fuskarsa amma ba duka ba, wanda ya saka Vp sakin jakar wannan karon kam a bayyana da kuma karfi ya furta... “RAYYERN KHALID???…” wanda ya saka mutumin da ya kira da sunan wani irin ɗan murmushin da kai tsaye baka isa gane masa ba, saboda face mask ɗin da yake rufe fuskarsa don har ya mayar sai iyaka idanunsa da yake bin Vp din dashi. Shi kuwa Vp President cikin wani irin matsanancin tashin hankali ya ja da baya da ƙarfi yana furta. “Ba zai yiwu ba…” Cikin muryan dake ɗauke da mamaki kafin yaci gaba da faɗin. “An ce ka mutu… an ce ka ɓace…” Wani irin jan ƙafarsa baya Wanda aka kira da RAYYERN KHALID din yayi tare da ɗage ma Vp din girarsa ɗaya kaɗan. “An ce ba ka…” Vice President ya sake bude baki da nufin sake faɗin wani abu yana kasa ƙarasa maganar kwatsam wata tsohuwar magana na faɗo masa a rai.Wata murya wani mutumi wani sunan da aka taɓa furtawa a cikin rahotanni, sannan aka binne shi a cikin fayilolin da babu wanda yake son sake buɗewa su. Kafin Vice President ya sake juyowa ya kalli mutumin sosai, cikin wata murya mai cike da tsoro da rashin yarda ya furta. “KIND DADA?…” A wannan karon kam mutumin wani irin murmushin gefen baki ne ya kufce masa, kamar wanda ya daɗe yana jiran wannan rana da kuma lokacin dama can. Kafin cikin muryan da bata tare da irin ko wacce hayaniya ya furta.
“Finally.”
Din data sake saka Vice President sake matsawa baya cikin wani zallar tsoro, kafin cikin karfin hali da aro jarumta ya furta. “Me kake so daga gare mu?” Wanda ya saka Kind Dada wani cillo masa ɗan iskan kallo tare da furta. “Abin da nake so?” sai kuma ya saki wani guntun murmushi mara tabbas da furta. “Da ace kun san abin da nake so din, dana tabbata ku dukan ku da ba ku kawo kanku nan ba.”Vice President ne ya yi yunkurin matsawa gare shi yana ambatar. “Where is My Sameer?” Wata iskar dariyan daya manta rabon da yayi ta yayi yana mai furta. “Har yanzu kana tunanin komai yana game da Sameer ne kenan?” sai kuma Vice President ya yi shiru kawai. “Kun yi kuskure.” “Then what is this about?” Kind Dada ya ɗan juya kansa ya kalla Vp din “Ka fi kowa sanin cewa wannan abun ba game bane.” Vice President ya yi wani yunkuri na bazata kamar zai kama shi. Saidai tun kan yayi yunkurin komai Kind Dada ya kama hannun Vice President ɗin kafin shi ya kai gare shi, ya juya shi gefe guda sannan ya ɗaure kama dayan hannunsa yana makalewa da handcuffs da jikim karfen Gadar da suke wurin, Vice President ya yi ƙoƙarin janye hannunsa, amma Kind Dada ya riƙe shi na ɗan lokaci, ya sunkuyar da kansa kusa da shi sannan ya yi masa wata alamar shiru da yatsansa.
“Shhh…”
Ya ya ja sautin tare da sake kallon shi yana kuma jijjiga masa kai da fadin...
“Ba yanzu.”
Ya sake sakin hannun ya fara ja baya da baya don yana lure da cewan wannan jami'an na daf dashi, bye bye ya shiga ma Vp da hannu da masa alamar kanselin na aikin su hadu wani lokacin banda wannan.... Fuskarsa cike da wata irin mugun firgicin da har yanzu ba ta bar fuskarsa ba. Daidai lokacin da Jami'an nan ke isowa suna zagaye shi kafin wani daga cikin jami'an yay hanzarin saka makulli ya buɗe handcuffs din ɗaya rufe shi dashi. Wani mayen jan numfashi yayi idanunsa suna kafe wuri guda da kallo l kamar har yanzu abin da ya faru ɗin yana nan ne daram a cikin kansa, K Mashi ne ya nufo shi cikin gaggawa yana cewa, “Sir!” amma Vice President bai amsa ba, ya ci gaba da kallon duhun bayansa, har sai da K Mashi ya sake tambayar, “Sir, are you alright kuwa?” Sai a sannan Vp ya juyo da kansa ya kalli K Mashi, amma babu amsar da ya bashi, sai kawai ya ɗaga hannunsa yana kallon ta yadda ya rataye shi da shi, sannan ya furta wata kalma guda cikin wata murya da ta fito kamar wacce aka cire ta daga cikin tsananin mamaki. “Rayyern…” Wanda ya saka wutar K Mashi daukewa cak tare da ambatar “What?” Vice President ya ɗago idanunsa ya kalle shi, ya sake furta sunan wannan karon a kausashe ya sake furta, “RAYYERN KHALID...” Wani irin shiru ne ya ratse wurin kamar wacce mutuwa ta ratsa wurin saboda kawai iyaka ambatar sunan da kai tsaye ya saka AJMAAL wani irin rumtse idanunsa. Kafin yaji jikinsa yayi wani irin laushi kamar wanda aka zarema wani abu daga ƙarƙashin ransa haka AJMAAL ya tsaya cak. Hannun da yake riƙe da na'urar da ke gabansa ya yi sanyi na ɗan lokaci guda shima yana kamewa. Kafin da kyar ya iya bude idanunsa kai tsaye yana sauke su akan Vice President ba tare da ya iya cewa komai ba, haka yaci gaba da kallon Vp din da wani irin kallo mai zurfi, kamar yana son tabbatar da cewa kunnuwansa ba su yaudare shi ba. “Me ka ce?” Kalmar ta fito daga bakinsa a hankali, amma tana ɗauke da wani irin nauyin da ya sa K Mashi ya juya ya kalle shi. Vice President ya sake maimaitawa, “RAYYERN KHALID.” AJMAAL ya yi wani ɗan motsi da kansa sannan ya yi wata gajeriyar dariyan da bata da zurfi, wacce ba ta ɗauke da annashuwa ko kaɗan a cikinta tare da faɗin “A’ahh…” Ya furta yana dan wani jujjuya kansa, “Ba zai yiwu ba ba zai taɓa iyuwa.” ya furta hakan yana sauje kansa ƙasa, kamar wani tsohon tarihi ne da aka buɗe masa ƙofa kwatsam, ya fara kokarin dawo masa ka daki-daki, wani sake lumshe idonsa yayi yana tuno da wasu ababuwan na baya.
A lokacin da AJMAAL yake sabon shiga aikin DSS, lokacin da yake da saurin fushi da taurin kai irin wanda ba ya sauraron kowa, sai dai duk wannan ababuwan nashi akwai wani mutum gudan da ya iya ɗaukar wannan taurin kan nasa ya mai da shi makami. Mutum guda din da bai taɓa jin tsoron faɗa masa gaskiya a fuska ba. Mutum dayan da duk lokacin da AJMAAL ya yi tunanin ya kai kololuwar sanin makamar aiki, sai ya nuna masa wani sabon matakin da bai san akwai shi ba. RAYYERN KHALID kenan. Wanda ya zamana har sai da ya koma babban yaronsa. Shi ne wanda ya koya masa yadda ake kallon wuri ba tare da ido ya nuna abin da kake tunani ba, yadda ake karantan mutum kafin ya furta kalma, yadda ake sanin tarkon da aka shimfiɗa tun kafin akai ga taka shi, yadda ake amfani da shiru fiye da magana, da kuma yadda jami’i zai iya shiga tsakiyar hatsari ba tare da tsoro ya mallake shi ba. Duk wasu dabarun da AJMAAL yake amfani da su a yau, mafi yawansu ya fara koya ne daga hannun DEPUTY DIRECTOR GENERAL (DDG)) Sir RAYYERN KHALID. Kuma idan akwai abu guda da suka yi kama da shi sosai, to shi ne taurin rai. Rayyern bai taɓa jure masa idan AJMAAL ya yi ganganci ba, AJMAAL kuma bai taɓa jin daɗin yadda Rayyern yake tilasta masa ya yi tunani kafin ya motsa ba. Sau da yawa suna saɓa wa juna, har wasu daga cikin jami’an suka kan yi mamakin yadda malami da ɗalibinsa suke iya yin gardama ba, gashi kusan tsarar shekarunsu ɗaya. Amma a ƙarƙashin duk wannan akwai girmamawa da aminci irin wanda ba a iya gina shi cikin kwana ɗaya. AJMAAL ya san Rayyern fiye da yadda yake sanin kansa a lokacin, shi yasa a lokacin da aka ambaci sunan “Rayyern Khalid.” din zuciyar AJMAAL ta motsa tare da bugawa da ƙarfin gaske. Bai dawo daga tsakiyar tunanin daya rufka ba ya sake jiwowa muryan Vp president ta sake dakar kansa. "Shi ne KIND DADA.” babu shiri AJMAAL ya buɗe idanunsa...
“Ka ce…?”
“Kind Dada.” Vp din ya sake bashi tabbacin daya saka AJMAAL ya yi wani irin shiru wanda ya fi magana nauyi, kafin yayi wani ɗan guntun murmushi, amma murmushin ba na farin ciki bane.
“Shi ne wanda ya ɗauke min Sameer.” Vp president ya sake fadi wanda ya saka Ajmaal juyowa baki dayansa har yana fidda wani huci ya furta.
“Ka tabbatar?”
Kansa ya gyada masa da sake bashi cikakken tabbacin da cewa.
“Na tabbata! Shi ne mutumin dana gani! Shi ne kuma wanda ya ɗauke min SAMEER .” Shiru AJMAAL ya yi kafin ya sauke idanunsa kan na'urar da ke hannunsa, tare da furzar da wani dogon numfashi,
“Yanzu na gane inda salon wasar yake..... " Domin kai tsaye AJMAAL ya gane cewar tabbas wannan salon nasa ne, saboda haka ya saba haka yake aikinsa, shi da kansa idan yaso yake jan mutum inda yake, domin isar da duk sakon da yake son isarwa. Ko ta yadda aka jawo hankalinsu daga wuri zuwa wuri, yadda suka yi ta bin umarninsa suna tunanin su ne suke sarrafa akalar wasan… komai ya fara haɗuwa a cikin kansa kamar wani babban hoton da aka daɗe ana warware ɓangarorinsa. Ya lumshe ido, sannan ya buɗe su da wata irin kaifin da ya sa K Mashi ya san wannan ba AJMAAL ɗin da yake gani a mintin da ya wuce bane.
“Shi ne…tun farkon wasan shi ne.” K Mashi shi ne ya sake kallar sa a baybay tare da furta "Kamar Yaya?" AJMAAL ya ɗan yi wani murmushi da faɗin.
“Saboda wannan shi ne salon wasan daya koya min.” Vice President ya kalli AJMAAL yana cewa, “Wllh sak komai da komai RAYYERN KHALID ne na gani da ido na . Na tabbatar shi ne.” ba tare da ajmaal ya kalle shi ba yace.
“Na san shi ne dama saboda babu wani mutumin da zai iya yi mana irin wannan wasan…” sai ya ɗan shiru kafin ya hurzar da wata iska daga cikin bakinsa yace.
“…Sai shi.” Saboda yasan yadda Rayyern yaje, yasan yadda taurin kansa yake, ya kuma san yadda zurfin tunani da kaifin basirar yake, ya san irin yadda yake iya juya wasa daga inda aka san shi zuwa wani mataki na daban. Ya kuma san irin yadda yake iya sa mutum ya gaskata cewa yana da iko alhalin tuni ya jima da kwace masa ikon daga hannunsa, wani dan dakar kansa yayi yana tunanin ta yaya Mutumin da yake binsa yanzun kuma ya rikide ya koma abokin gaba? Alhalin shi ne mutumin da ya koya masa yadda ake bin abokin gaba... Sauƙe kansa kasa yayi ahankali kafin ya furta. “Rayyern…” Ya ɗan yi wani murmushi mai ciwo saboda sanin cewar Mutum ya fi jin zafin faɗa da malamin da ya horar dashi yadda ake faɗa fiye da wanda bai taɓa sani ba....
Jiniyar motocin sune ya saka shi bude idonsa ya kalla motocin nasu. A natse ya koma tashi motar shi ma suna barin wurin baki daya zuwa headquarters din su...
*Around 12: 00Am*
Da misalin ƙarfe sha biyun dare ya miƙe daga kan gadon da yake zauna a kai tun farkon zaman sa, a natse ya nufi tankamememen Railer nashi cup na Wine rike a hannunsa ɗaya, ɗayan kuma yaja curtains na dakin ababuwa da yawa na nefar fasa kansa, kafafunsa sanye cikin burberry slippers mai laushi Sosai, jikinsa na ɗan tashin ƙamshin turaren Versace bright crystal. Wani ɗan lumshe idonsa ya yi saboda iskan data daki fuskarsa yaja dogon numfashi kafin ya buɗe su ya ɗaga kai yana kallon sararin samaniya da hadari ya fara haduwa sai walkiya a ke, iska mai dadi tana ta kadawa wanda ya hade da ƙamshin turarensa sai hakan ya bama yanayin dadɗan yanayi na musamman, tare da cakuɗuwa da iskar wajen da kuma ƙamshinsa yana sanja yanayin iskar wajen. Hannunsa ya zira cikin aljihun dogon wandon baccin dake jikinsa fari tas ,inda ya bar madauran loose bai ɗaure wandon so sai ba a jikin kugun sa. Hakan ya bama wandon damar ɗan zamowa kaɗan har kana iya hango V-line nashi dake nan kaman an zana shi saboda perfection. Wandon ne kaɗai a jikinsa babu riga. Murdadden Jikinsa sai wani irin shinning na kyau da kyau yake, wani irin lumshe manyan fararen idonsa yayi yana fesar da wata numfashin data fita da zafi, yana komawa ya jingina da JIKI ya ƙara mannewa da jikin Railer ɗin yana jin shin a wanne mataki ne ma ya kamaci ace ya saka wannan sabon salon lissafin?. Ji yayi komai na shirin son dawo masa tun da ga lokacin da su da kansu suka fara lalata komai... ♡Wani kalan Runtse rinannun idonsa yayi sakamon kansa da yaji ya wani kalan sara masa. Dan jujjaya kansa ya shiga yi alamun zurfin da yay a tunani nason haifar masa da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ya fesar yana hana bama kansa kowacce damar tunani. Domin kuwa shi din mutum ne mai tsananin taurin kai da kuma ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu yake bama dama yay crossing mind nasa ba, ƙin bama ko wacce ƙofa dama yayi na zurfi a cikin tunanin dake son bijiro masa, duk yadda yaso da karfafa kansa har sai da hakan yaso fin karfinsa. Wanda knocking doorhandle ɗin da akai ne ya katse masa tunani, zuwa loƙacin jikinsa har rawa yake a mugun wahalce ya nufi doorhandle ɗin yana buɗewa. Mark ne dama kuma ya sani yasan shi din ne, yana ganin yanayinsa yasan ba ƙalau ba, juyawa yayi tare da komawa inda yake fuska a mugun tamke. Dining kai tsaye ya wuce domin yasan dama hakan zata faru. Kai tsaye fruits salad din da yaji strawberry and condense milk da ƙanƙara, sai chocolate cake daya ji chocolate cream yana kawo masa. Yana zama kusa da shi yana jin da ace wani na ɗauke damuwar wani daya jima da ɗauke damuwar uban gidan nasa. And that was my greatest regret ever, tabbas da ace bawa yana da iko da zai maida hannun a gogo baya, yana kuma da ikon da zai iya goge his greatest mistake, daya jima da goge tashi rayuwar ta baya tun tuni....
BY AMMEY LAYLERH ✍🏻
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️