DUHU na DUKAN duhu

Page 15&16

by @103453610185262939894

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.

ꨄ Kwanaki uku kenan tun bayan da aka shigar da Nadiya emargency room ɗin nan har yanzun bata farfado ba, kwanaki ukun da suka kasance kamar shekaru uku ne a idon Sadiya da Baba Gaje, domin duk tsawon wannan lokacin babu wanda ya iya cewa komai ya dawo daidai. Duk lokacin da aka yi ƙoƙarin tambayar likitoci game da yanayinta sai su ce har yanzu tana ƙarƙashin kulawansu, kwanaki ukun da suka shude kenan da Nadiya take kwance a gadon asibitin nan. Kwanaki uku da babu wani daga cikin mutanen da suke ƙaunarta da ya samu cikakken barcin tsayin kwanakin, kwanaki ukun da Sadiya take rayuwa tsakanin fatan jin kalma guda daga bakin likita da kuma tsoron jin wacce ba za ta so ta ji ba. Domin a tsayin kwana kin daga Sadiya har Baba Gaje suna cike ne da wani irin tsoro da addu'a ce kawai ke rage musu kaifinsa, kwana ukun da kowane motsin da na'urar dake gefen gadon ta yi yake saka zuciyarsu ta buga da wani irin ƙarfi. A cikin waɗannan kwanaki ukun, sau da yawa likitoci suna shiga suna fita, wasu lokuta suna cewa yanayin nata ya daidaita kaɗan, wasu lokuta kuma su sake jaddada musu cewa har yanzu ba a fita daga hatsarin ba. Inda Alhamdulillahi a safiyar wannan rana wani irin sauyi ne ya fara bayyana a jikinta. Duk da cewan ba wani babban sauyi bane da zai sa mutum ya gane nan take, sai dai ga wanda ya jima yana kallon marar lafiya, ƙaramar motsin da Nadiya ta yi da hannunta a hankali ya saka nurse ɗin dake duba na'urar dake gefenta ta tsaya cak. Kai tsaye idanunta na sauka kan Nadiya, ta sake duba na'urar domin tabbatar tare da ambatar sunan.

"Doctor..."

Haka kallmar ta kwace daga bakinta kamar cikin gaggawa.

"Doctor!"

Ta sake kiran sunan Dr din da karfi wannan karon kam da babu jimawa ga babban likitan dake kulawa da ita, kafin sauran likitocin su fara rige rigen shigowa ɗaya bayan ɗaya, Sadiya wacce take zaune a wajen glass ɗin kuma ba ta san ainihin abin da ke faruwa ba sai ganin mutane tayi na wucewa ɗaya bayan ɗaya, miƙewa tayi da sauri tana dan zungurar Baba Gaje dake lazimi tana kuma dan gyangyadi.

"Baba Gaje..."

Ta sake zungurarta daya saka Baba Gaje miƙewa tana kallon cikin Sadiyan da faɗin. "Me ke faruwa?" Kasa amsawa Sadiya tayi sai idanunta dake makale kawai a kan ɗakin da Nadiya take.

A can dakin kuwa Likitan ne ya ƙaraso kusa da gadon da take kwance yana magana da nurse ɗin cikin nutsuwa, kafin ya sunkuya ya duba idanun Nadiya da dan saka hannunsa gefen fuskarta da ambatar.

"Miss Nadiya..."

Amma shiru ya sake kiran "Nadiya..." A wannan karon ƙaramar motsin gashin idanunta ne ya bayyana. Gaba daya hankalin likitocin ya tattare ne a kanta saboda ALIYU dake tsaye akan jinyar nata, komai shi yake tsaye a kai idan ya taso, kullum yana kan zaryan dubata da ci gaba da dawainiya dasu Baba Gaje, shi yasa yanzu kowa a cikin likitocin kulawarsa ta dawo kan Nadiya din, saboda yanzun kam patient din asibitin kusan tafi kowa gata, wannan hantarar da ake ma su Sadiya tuni an dena. Ko a yanzun ma Sadiyan tana nan tsaye daga bakin ƙofar glass din kamar wacce aka shuka a wajen, don ko da fitar numfashinta da ace zai tambayi izininta da bata bashi umarnin fita da sauri da saurin da yake mata ba. A can cikin room ɗin kuwa sannu a hankali Idanun Nadiya suka fara motsawa ta ƙarƙashin gashin idanunta. Ɗaya daga cikin Likitan ne ya ɗan ɗago kansa yana kallon nurse ɗin data kirasa da faɗin. "She's responding." Kalmar data nemi tarwatsa duk wani tunanin da Sadiya take yi nan take. A natse ya kai bayan hannunsa daya saman bakinta yana sauƙe ijiyan zuciya mai kyau. Wanda ya saka hawayen tsakanin farin ciki ciko idon Yaya Sadiya tana furta "ALHAMDULILLAH"

Baba Gaje kuma na ambatar "ALLAHU AKBAR..." hannunta saman kirjinta ta fadi hakan daidai lokacin da idanun Nadiya suka buɗewa, kokarin daga hannunta ɗaya tayi wajen kare fuskanta alaman haske ya mata yawa ne, sai dai hakan ta faskara domin ta gaza koda motsa hannun nema. Don haka ta ɗan runtse su kafin ta sake buɗewa, tana kallon sama ba tare da ta gane komai ba, kanta ta dan fara jujjuya tana ta son ganin tayi magana sai dai jin wani abu ya tokare kirjinta daya haifar mata da zazzafan ciwon azaba ya sakata tsaiwa cak tana daina mutsu mutsun, so take a karo na biyu ta sake furta koda kalma ɗaya ce amma ta gaza. Likitan ne ya ci gaba da mata magana cikin nutsuwa.

"Ki kwantar da hankalinki... kina asibiti ne miss Nadiya."

Ƙoƙarin motsa lips nata tayi a karo na kusan uku kenan, sai dai babu sautin da ya fito din ma a wannan karon ma. Sadiya wacce ke tsaye ta kasa jurewace ta kira sunanta da ɗan karfin daya saka Nadiya karasa dawowa daidai da kuma hayyacinta, jin ta ƙirata da hasalin sunan da Mahaifiyarsu take kiranta. "AUTAN DADA!..."

Ta furta daga bayan glass ɗin, ko kafin ta sake wani yunkurin maganan ɗaya daga cikin likitocin ya ɗaga mata hannu da alamar ta yi shiru kawai. A natse Nadiya ta sake lumshe idanunta.

Hannu Sadiya ta kai saman bakinta tana toshe shi saboda wani irin kuka na farin cikin da ya taso mata kwatsam, Baba Gaje kuwa hannayenta ta ɗaga itama sama tana cewa, "Alhamdulillah! Alhamdulillah ya ALLAH!" Hawayen godiya ga ALLAH na gangaro mata. Ko da aka bama Sadiya damar shiga ta ganta, ta shiga cikin ɗakin a hankali tana jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa da kowanne takun da take tunkarar gafon. Nadiya tana kwance tana kallon rufin ɗakin da idanunta masu nauyi fuskarta tayi fa yau na jinya, idanunta kafe a kan Yaya Sadiya dake tunkaro ta fuskarta dauke da muradin son ganin ƴar uwar ta. ta ɗan motsa leɓenta kamar tana son magana, Sadiya ta ƙaraso ta kama hannunta tana cewa, "Shhhh... kar ki yi magana." Hawaye suka cika mata ido. "Ki huta kawai mun gode wa ALLAH da ya baki lafiya." Ɗan lumshe idanu Nadiya tayi kafin ta buɗe su ta kalli Yayar nata, sai kuma wani ɗan murmushi mai rauni ya bayyana a fuskarta. Sadiya ta sunkuyar da kanta tana sumbatar hannunta, tana jin wani irin sauƙi da ba ta san ta yaya za ta iya bayyana shi ba. "Kin tsoratar damu AUTAN DADA...." Ta furta cikin raunin murya ta dan kamo kumatunta da faɗin "Irin sosai ɗin nan fa." Kaɗan ta iya mata murmushin gefen baki tare da ƙoƙarin motsa leɓenta, "Baba..." ita ce kalmar da ta iya furta wa kawai. Sadiya ta yi saurin cewa, "Yana gida, da Baba Gaje tazo shi ne ya tafi" a natse Nadiya ta sake dan rufe idanunta cikin nutsuwa. hannayensu cikin na juna, zuciyarsu cike da godiya ga ALLAH. Bayan ɗan lokaci ne likita ya fito yana cewa yanayin Nadiya ya fara daidaituwa amma har yanzu tana buƙatar hutu, kulawa da kuma rashin wani nau'in tashin hankali, domin jikinta bai gama farfaɗowa daga abin da ya faru ba da haka suka fice.

A can gidan Vice President kuwa tun bayan abin da ya faru gidan ya koma tamkar kurkuku a wurinsu. Ga Jami'an tsaro sai shige da fice suke tun da abin ya faru, Vp kuwa tun da ya zube aka kwaso shi yake kebantaccen wuri a killace. Daya rufe ido abinda ya faru ne ke dawo masa, sunan RAYYERN din kuwa kamar naima yake ya zame masa wata masifar rayuwar shi ne, don suna ne da ya makale a cikin kansa yaki fita. Sannan kalma daya ce kawai ke dawo masa bayan wani zaman sirrin da yayi da wasu daga cikin kusoshin ƙasar, wanda abu daya suka yi ta nanatawa shi ne cewar. "Ka sani cewar idan har muka yi saken da aka tono ainihin gaskiyar abinda ya faru! To akwai yiwuwar rugujewar ababuwa da yawa don wannan abin girgizar ƙasa sunan shi..." sune kawai kalaman da yake iya tunawa wanda yake jin su tamkar saukar guduma ne.

ꨄ Ata bangaren Kind Dada kuwa bayan da mutumin ya gama furta masa kalamansa ne ya saka Rayyern komawa yana sake jingina bayansa sosai da kujerar da yake zaune, idanunsa na komawa kan ruwan swimming pool din dake gabansa wanda hasken fitilun da aka jera gefensa ke karya duhun daren yana mai ba ruwan wani irin haske mai nutsuwa. Tabar dake tsakanin yatsunsa yaci gaba da Zuka yana fesar da hayaƙin iska na kwashe shi zuwa sama.... .Shi kuwa wannan mutumin dake tsaye gabansa kuwa bai sake cewa komai ba, saboda ya san irin wannan shiru na Rayyern ba shiru ba ne na rashin abin faɗa ba, A ahh shiru ne irin wanda yake yi idan ya riga ya gama yanke shawara a cikin kansa, kuma duk wanda ya san shi ya san cewa babu wani abu da zai iya sauya abin da ya riga ya yanke a karan kansa...A hankali ya ɗaga hannunsa ya kalli agogon dake ɗaure a damtsensa, kafin wani ɗan murmushi ya sake bayyana a fuskarsa. Shiru kawai wannan mutumin yayi kafin ya ɗan kusanto da jakar dake gabansa yana cewa, "Amma Boss, akwai wani abu da muka gano." Rayyern ya ɗaga gira kaɗan, yana mai nuna masa ya ci gaba. "Mutumin da ya kamata mu kula da shi ba AJMAAL kaɗai bane." Rayyern ya yi murmushi kaɗan. "Na sani." "Akwai K Mashi." Wannan karon murmushin da ke fuskarsa ya ɗan tsaya na ƴan daƙiƙu kafin ya koma irin yadda yake. "Ina son ku barsu suyi duk iya ka yin su mu gani in zasu iya..." Daga haka komai bai sake cewa ba, sai ma ɗaukan glass cup ɗinsa da yayi ya kurɓa kaɗan, kafin idanunsa suka sake komawa kan ruwan dake gabansa. "Aikin da nake so su yi musu ba farautar mutum bane." Ya ɗan dakata. "Ina son su da kansu su fara binciko abin da aka jima da binne wa me." Mutumin ya tsaya cak yana kallonsa, domin kalmar ta fi masa nauyi fiye da yadda ya nuna. "Boss Kana ganin duk cikin su akwai kwaron daya isa gano ainihin gaskiy...." Rayyern ya ɗaga hannu yana katse shi ba tare daya bari ya kai ƙarshen maganar nashi ba. Wani ɗan lalataccen murmushi yayi tare da rufe idonsa ruf da faɗin. "Idan har sun cancanci su gano shi, to kuwa lallai za su gano din. Idan kuma ba su cancanta ba din... to su ci gaba da farautar inuwata."

Tun bayan rabuwar taron, AJMAAL bai koma gida ba. cikin dakin daya kasance kamar ɗakin binciken su ne dake ɗauke da manyan screens guda uku ya nufa, kai tsaye files din da aka basa akan Rayyern ya baje a gabansa, duk wasu ababuwan da suka danganci Rayyern din ne a wurin, har zuwa wani sashe da yafi ko ina tsaya masa a rai. MISSING IN ACTION. AJMAAL ya kafe idanunsa a kan kalmar na dogon lokaci kafin ya miƙa hannu ya buɗe wani folder dake gefe. Wani tsohon hoton Rayyern ne ya fito. A wannan hoton Rayyern yana sanye ne da kayan aikin DSS, fuskarsa ba ta da wannan tsananin duhun da take da shi a yanzun, amma idanun sun kasance iri ɗaya ne dana yanzun koma ace a yanzu sun fi alamar firgitarwa. idanun da kai tsaye suke iya kallon abin da ba kowa ke iya gani ba. AJMAAL ya yi wani dan murmushi mai ɗaci. "Har kwanan gobe wannan salon naka na kallo baya taɓa sanjawa..." ya furta shi kaɗai. Kafin ya ɗauki hoton ya juyo da shi zuwa gare shi. "Idan mutum yana so ya ɓoye wata gaskiya, ba zai ɓoye ta gaba ɗaya ba. Zai bar maka abin da zai sa ka ci gaba da nema ko bibiyar sane. Anan ina son sanin dalilin da yasa ka kai ka bar shi?" Daga haka ya mike tare da car key nashi yana fitowa zuwa compound, motarsa ya shige yana bata wuta ya nufi gidansa. A madaicin parking space na gidan yay parking car nashi, gidan yayi shiru kasancewar sha biyu ma tuni ta jima da bada baya wajajen karfe ɗayan dare lokacin, ajiye makullan motarsa yayi a kan wani ƙaramin teburin dake kusa da ƙofar shigowan, sannan ya cire agogon hannunsa yana kallonsa na ƴan daƙiƙu kamar yana ƙoƙarin tunawa da lokacin da ya fara rasa kansa ne a cikin wannan aikin. A yau jikinsa ya gaji, amma abin da ya fi gajiyar da shi ba aikin da ya yi ba ne, kalaman da suka yi ta dawowa a cikin tsakar kansa ne tun bayan da ya bar ofishin. “Ba za mu gano Kind Dada ba sai mun fara gano abin da ya faru da RAYYERN KHALID.” Wannan kalmar da ya faɗa da bakinsa a gaban K Mashi ita ce ta fi komai nauyi a zuciyarsa, domin ya san cewa da zarar ya fara tono tsohon tarihin Rayyern, ba wai kawai zai buɗe wani tsohon case ba ne; yana iya buɗe wata ƙofa ne da aka rufe shekaru da dama da suka wuce, ƙofar da wataƙila ita ce ta raba Rayyern ɗin da ya sani da mutumin da duniya take kallo a matsayin KIND DADA.

Ɗakinsa ya nufa ba tare da ya kunna manyan fitilun gidan ba. Ɗakin nasa ya kasance mai tsari, ba irin barkatai karikicen nan sai wasu littattafai da fayiloli sune a jere cikin nutsuwa, yayin da wani ƙaramin shelf dake gefen bangon yake ɗauke da wasu abubuwan da ba su da alaƙa da aikin DSS kai tsaye. Wasu tsoffin medals ne, wasu hotuna, wasu ƙananan abubuwa daga ayyukan da ya taɓa gudanarwa, da kuma wasu abubuwan tunawa da mutanen da suka kasance wani ɓangare na rayuwarsa kafin aikin ya koya masa cewa ba duk wanda mutum ya kira aboki ne yake da damar zama abokin har ƙarshen abada ba. Ƙaramin fitilar dake gefen gadonsa ya kunna haskenta na gauraye ɗakin, inda kuma kai tsaye idanunsa suka sauƙa a kan wani tsohon hoto dake kayace cikin frame. Wanda kai tsaye hoton dake jiki nashi ne da RAYYERN KHALID. Suna sanye da kayan aiki ne fuskokinsu cike da irin wannan tsantsar nutsuwar jami'an da suka saba shiga wuraren da kuskure ɗaya zai iya zama na ƙarshe. Amma duk da haka wannan hoton akwai wani abu daban, Rayyern yana tsaye a gefensa yana kallon camera da wani ɗan murmushi, yayin da AJMAAL yake kallon shi ma kamar mutumin da ya manta cewa camera na gabansu ne ko na ɗaukarsu. A natse AJMAAL ya matso kusa da hoton fuskarsa dauke da wani murmushin da ya ɗan bayyana a fuskarsa ba tare da ya shirya ba. "Kamar baka taɓa zama haka ba?" ya furta a hankali, kamar yana magana da mutumin dake cikin hoton. Kai tsaye wani dan lumshe idonsa yayi wani tsohon tunani na dawo masa.

Wani lumshe idonsa yayi yana tuno da wani operation ne da suka fita, wanda suka shafe kusan kwana biyu suna bin sawun wasu mutane a wani yanki da ke bayan garin, ba su samu damar hutawa sosai ba. A lokacin ne suka samu ɗan lokacin zama a gefe suna duba taswirar wurin, Rayyern yana ta yi masa bayanin wani abu da irin wannan nutsuwar nasa, amma AJMAAL bai saurare shi sosai ba. Daga baya ne ya gane cewa ranar ce ranar haihuwar Rayyern. Sai ya haɗa kai da sauran jami'an da ke tare da su suka shirya masa abin da bai yi tsammani ba wato surprise. Ba wani babban birthday bane, domin suna wurin aiki ne, amma sun samu ƙaramin cake suka kunna masa candle ɗaya kawai, suka masa wish. A cikin hoton da ke kusa da wancan, AJMAAL ne yake riƙe da cake ɗin da hannu ɗaya, yana dariya sosai, dayan hannunsa kuma ya miƙa cake ɗin zuwa fuskar Rayyern ne kamar yana son shafa masa a fuska. Rayyern kuwa yana ta ƙoƙarin kaucewa yana kallonsa da wani irin kallo na "Idan ka yi kuskure ka shafa min wannan, baka da wani maceci sai ALLAH." Amma daga ƙarshe ya kasa hana dariyarsa fita. AJMAAL ya tsaya yana kallon hoton na dogon lokaci. Wani murmushi mara ɗanɗano na kubce masa na tsohuwar ƙauna da abotar daya tuna, kafin ya ɗan girgiza kansa. "Ka yi ta cewa ba ka son birthday din nan amma ranar nan kai ne ka fi kowa dariya daga ƙarshe Boo..." yay maganar yana sake kallon hoton, wannan karon murmushinsa ya fi rauni. Domin a yau, abin da ya fi masa zafi shi ne tunanin cewa mutumin da yake dariya tare da shi a wannan hoton yanzu shi ne mutumin da aka umarce shi ya kama, kuma idan ya yi jayayya a harbe shi. Kamar a ɗan zafe ya sauke idonsa kasa, yana tuna wannan maganar ta Rayyern da yake yawan furta masa cewar _Wasu lokuta mutum ba ya sanin darajar wasu kwanaki sai bayan sun zama tarihi a gare shi... _ Zaratan yatsun hannunsa ya miƙa yana ɗaukar hoton daga cikin frame ɗin, ya zauna a gefen gadonsa, yana riƙe da shi a hannunsa. Yatsarsa ta bi gefen hoton a hankali, sannan wani hoton dake bayansa ya jawo hankalinsa. Ya juya shi. A wannan karon Rayyern ne shi kaɗai. Amma Rayyern ɗin da ke cikin hoton ba shi ne wanda ya saba gani ba. Ya sa wata irin shiga da za ta sa mutum ya ɗauka cewar mahaukaci ne idan bai san shi ba. Gashinsa ya watse a duka fuska da bayansa, tufafinsa sak na mahaukata, a cikin mahaukatan ma na wanda ya kwashe kwanaki yana yawo a cikin datti, hatta da fuskarsa sai data zama kamar ba tashi ba, idonsa kuma yana ɗauke da irin wannan kallon da ba za ka iya gane ko yana wasa ne ko kuwa ya manta da kansa ba. AJMAAL ya ɗan lumshe idanunsa yana tuna cewar. Har sati biyu ya kwashe cikin wannan yanayin, kai tsaye tunaninsa ya sake komawa kan wani tsohon aiki.

A lokacin wasu ɗaliban makaranta ne aka kwashe bi ma'ana akayi kidnapping nasu, kuma jami'an tsaro sun shafe kwanaki suna neman wanda ke da hannu a lamarin. Sun samu wani ɗan ƙaramin bayani cewa mutumin da ake zargi yana zaune a wata unguwa inda baƙo zai iya jawo hankali cikin sauƙi. Rayyern ne ya shiga aikin, amma ba kamar yadda kowa yake tsammani ba. Ya canza kansa gaba ɗaya, ya shiga unguwar a matsayin wani mahaukacin da ba shi da wani abin yi sai yawo da magana shi kaɗai. AJMAAL ya tuna yadda ya yi masa dariya a ranar farkon da ya gan shi.

"Rayyern, wallahi kai ƙarshe ne wajen iya acting." baya mantawa a lokacin Rayyern din dago kansa yayi ya kalle shi cikin shigar mahaukatansa ya ce, "Sawa a rai ne ya sa falke baya jin wahalar tafiya.... Karka manta jami'ai ne mu tamkar mafarauta,sunan kura muke amsawa kyaci da gashi..." Murmushi yayi a lokacin a ransa yana jin cewa lallai tabbas Boss din sa ba zai iya buga wannan role din ba. Saboda a lokacin bai san cewa Rayyern zai iya ɗaukar wannan wasan har tsawon makonni biyu ba tare da ya gaji ba. Sanin cewa yafi kowa sanin irin halin sa na kenkeni, ya san ba zai iya kwana a bola ko bakin titit ba, ba zai iya cin abincin da mutanen unguwar suka ci su rage masa ba, ba zai iya jure raini, zagi da kuma kallon tausayi ko kaskantacce ba. A sai Rayyern din ya bashi mamaki na farkon da shi ne karon farkon daya fara bashi, sai gashi har yayi nasarar aikin ba tare da mutumin ya taɓa fuskanta ko zargin komai ba, illa kallon mahaukacin da kawai yake masa. A ranar da aka samu nasarar aikin kuwa, AJMAAL ya kasance daga cikin mutanen da suke a kusa kusa suna kallon Rayyern yana aiwatar da matakin ƙarshe na aikin nasa cikin nutsuwa. Bayan komai ya ƙare ne, Rayyern ya dawo yana wani dakune wannan kyakkyawar fuskar nashi, mai cike da ban tsoro da saka abokan gaba firgita, AJMAAL ya ce masa, "Kai wallahi idan ba aikinmu bane, da na ce ka cancanci award Sir." Rayyern ya amsa masa da cewa, "Ni award ɗin nan ka bani abinci kawai shi ne babban award dine daga gare ka Firstly." AJMAAL ya yi ɗan murmushi guntu bayan dawowa daga wannan tunanin, a natse ya ajje hoton tare da miƙewa idanunsa suka sake komawa kan shelf nasa. Kai tsaye kuma a wannan karon din ma idonsa na fadawa kan wani ƙaramin hoto na mutane da dama bayan wani operation. Wasu suna murmushi, wasu suna a yanayi na gajiya ne, wasu kuma suna kallon camera. AJMAAL ya ɗauke shi, ya dube shi na ɗan lokaci, sai tunanin wani dare ya dawo masa; wani operation da suka yi a lokacin damina, inda ruwa ya hana motocinsu wucewa, suka yi tafiyar kusan awa shida a kafa kafin su isa wurin da suke son kai wa. A lokacin Rayyern ne ya lura da wani abu da babu wanda ya lura da shi, ya ce musu su tsaya kafin su shiga wurin. Bayan mintuna kaɗan ya gano cewa wurin tarko ne. Wani numfashi Ajmaal ya sauke "Kai din na musamman ne, daban a cikin daban, domin ka kasance kana ganin abin da ba kowa ke iya gani kai tsaye daga kallon farko ba..."

Sai kuma ya yi shiru yana sake cira kansa kamar alamar tunani, a cikin shekaru da yawa na aiki, ya san mutane da dama. Wasu sun zo sun tafi, wasu sun zama abokan aiki, wasu sun zama abokan gaba, amma Rayyern ya kasance wani abu daban. Ba wai kawai malami bane ko mai horas da aiki, kuma ba wai kawai abokin aikin bane. Rayyern ya kasance mutumin da ya koya masa cewa aikin jami'in sirri ba ya ta'allaka ne kawai da bindiga, gudu ko ƙarfi ba. Ya koya masa yadda ake kallon mutum kafin mutum ya yi magana, yadda ake karanta wuri kafin a shiga, da kuma yadda ake yin shiru lokacin da magana za ta iya lalata komai. AJMAAL ya yi murmushi a hankali. "Ka koya min komai..." ya furta, sannan idanunsa suka sauka kan hoton da ke hannunsa. "Amma ban taɓa tunanin wata rana zan yi amfani da duk abin da ka koya min wajen nema ko farautar ka ba." ya yi maganar murmushin na bacewa daga fuskarsa, wani irin ciwo na bayyana har ta cikin idanuns. A hankali ya koma yana jingina da jikin ginin dakin ya rufe idanunsa na ƴan daƙiƙu, kuma kamar yadda ya saba yi duk lokacin da yake son haɗa abubuwa, sai ya fara dawo da kowane abu a cikin kansa. Rayyern da aka ce ya mutu. Babu gawarsa. Fayil da aka rufe. Wasu bayanai da suka ɓace. Wasu shafuka da aka sanya CLASSIFIED. Sai kuma dawowar mutumin bayan shekaru, ba tare da wani bayani ba, a matsayin KIND DADA. Tabbas wannan al'amari akwai ɗaure kai. Kuma bayan duk wannan akwai wani irin shakku a bayan hakan na cewa mai yasa Rayyern zai koma haka? Mai kuma yasa ya bayyana kansa bayan yasan cewa zai iya ɓacewa idan ya so. Zai iya ɓoye kansa wurin da ko sauro bai isa gano shi. Zai iya rayuwa tsawon shekaru ba tare da ya bar alama ko wacce irin alama ba ce. Amma shi ne ya zaɓi ya fito. Shi ne ya bar a san sunansa. Shi ne ya bar a gano cewa KIND DADA shi ne RAYYERN KHALID.

"Me kake so in gano?"

Ya furta a zafafe cikin muryan tsawa.

"Me kake son in gano?"

Ya sake furta wa da ihu yana kallon hoton da ke hannunsa kamar yana tsammanin Rayyern ɗin cikin hoton ne zai ba shi amsar tambayoyin nasa. Wayarsa dake saman teburi ce tayi kara ya ɗauka, daga ofis ne an sanar dashi cewa an samu wani tsohon bayanin operation ɗin Rayyern ne da za a iya buɗewa da safe, amma sai da izinin babban jami'i. Ya karanta saƙon sau biyu, sannan ya ajiye wayar kawai ba tare daya bama hakan muhimmancin komai ba. A zuciye ya koma kan hotunan ya ɗauki hoton Rayyern na ranar birthday ɗin, ya mayar da shi a hankali inda yake. Kafin ya kashe fitilar da furta. "Idan da gaske ne kana son in gano wani abu ne!? ... Tabbas zan gano shi." Ya kashe hasken ɗakin tare da kwanciya hadi da tunano wata maganar Rayyern, a lokacin da yake horar da shi, cewa, "Aikinmu ba wai gano abin da mutum yake ɓoyewa bane kawai AJMAAL. Wani lokacin aikinmu shi ne gano dalilin da ya sa mutum ya zaɓi ya ɓoye shi"

*ASIBITI*

Kwanan Nadiya uku bayan ta farfaɗo yanayinta ya ci gaba da sauyawa a hankali. Har yanzu jikinta yana ɗauke da raunin abin da ya same ta don ko wanka sai dai a rufe wurin raunin da Leda kana take yi, sosai yanka ya shiga jikinta over ga kuma yanka a kirji sai a hankali, wanda ko wankan sai Yaya Sadiya ta taimaka mata take iya yi, amma tana iya zama na ɗan lokaci ba tare da taimakon wani ba, tana iya magana fiye da yadda take a farkon farfaɗowarta,wannan tsoron da ya mamaye zukatan su Baba Gaje da Sadiya ya fara raguwa sosai. Duk da haka, duk lokacin da likita ya shigo ɗakin sai sun kalli fuskarsa kafin su saurari abin da zai ce dasu, domin sun riga sun fahimci cewa a irin wannan lokaci kalma ɗaya daga bakin likita na iya ɗaga mutum zuwa sama ko kuma ta mayar da shi cikin duhun da ya fito. A kuma washe garin data farfado Baba yazo ya ganta. A safiyar ranar Sadiya tana zaune kusa da Nadiya tana gyara mata gashin kanta, yayin da Baba Gaje ke daga bakin taga tana kallon harabar asibitin. Nadiya ta ɗan ɗago kanta ta kalle su, sannan ta ce cikin murya mara sauti, "Baba fa?" Sadiya ce ta tsaya tana kallonta kafin tace. "Baba yana gida Nadiya mune muka ce ya koma ai tun jiya da yamma."

"Gida kuma?"

"Eh. Ya tafi jiya tun da ya koma bashi da aikin yi sai tambayar ko kin ci abinci, ko kin sha magani, ko likita ya shigo shi ne aikinsa kawai, yaya jikinki? Kin ji sauƙi? Kina samun kulawa?."

Nadiya ta yi ɗan murmushi tana komar da kanta ta kwanta da fadin"Shi kenan." Baba Gaje ce ta juyo tana yar dariya a hankali. "Kina ganin wannan Baban naki zai iya zama a gida kuwa anya ya manta da ke?" Nadiya ta yi shiru na ɗan lokaci kawai tare da sake sakin dan murmushin sanin cewar. Tabbas a irin waɗannan lokuta ne mutum yake gane cewar duk abin da yake faruwa a cikin wannan duniyar, akwai wasu mutanen da suke nan kasancewarsu kaɗai a cikin rayuwarmu kan sa zuciya ta samu mafaka da samun nutsuwa su ne iyaye....

Kafin ta sake cewa komai aka turo ƙofar ɗakin Aliyu ya bayyana. Wannan sojan, wannan sojan dai daya dauki duk wani nauyin kula dasu ba tare da gajiyawa ba yaci gaba da dawainiya dasu tamkar ahalinsa. Ba tare da hayaniyr komai ba kamar yadda ya saba. A nats ya sama wuri yana zama hannunsa dauke da babbar leda, Baba Gaje data zama kamar Kakarsa ya fara gaidawa kafin Yaya Sadiya itama ta gai da shi, Kafin ya kalla Nadiya da tun da ya shigo tayi makus tana lafewa kamar mai yin bacci.

"Ya ya jikin?" kai tsaye furta daya saka Nadiya ta amsa da "Alhamdulillah." kai ya gyada da faɗin . "Da sauƙi kenan."

"Eh."

Ta sake bashi amsa a gajarce shi kuma yana ajiye abin da ya kawo din a gefe, ya tambayi Sadiya ko akwai wani abu da suke buƙata, sannan ya fita bayan ƴan mintuna. Ba ya da wata magana mai yawa, amma abin mamaki shi ne, duk lokacin da yake zuwa, akwai wani abu da ya rage wa Sadiya da Baba Gaje nauyi. Wani lokaci magani ne da ya kamata a samo, wani lokaci abinci, wani lokaci takardar da ake buƙatar a kai wani sashe, wani lokaci kuma kawai ya zo ne ya tabbatar komai yana tafiya yadda ya kamata kafin ya tafi. Wani numfashi mara sauti Nadiya ta fesar tana, tana auna yadda Aliyu ya zama wani fuska da idanunta suka saba nema a cikin harabar asibitin ba tare da ta shirya hakan ba idan har zata wuni bata ga ko gilmawarsa ba, duk da ba budar baki take ta tambaya ba amma tana yaki da zuciyarta kwarai game da hakan.

Ba wai yana yawan zama a ɗakinta bane. A'a. Sau da yawa ma sai ya zo ya tsaya na ƴan mintuna kawai. Amma irin yadda yake tambayar halinta, yadda yake kula da ƙananan abubuwan da wasu ba sa lura da su ba, da yadda yake kallon fuskarta idan ta yi shiru ya sa Sadiya ta fara kallon su da wani irin murmushin da take ɓoyewa. Haka suka kusan kwashe makonni biyu a cikin asibitin garin Bauchi, kuma duk wannan uban zaman ko da wasa Gwaggo Talatu bata taɓa karar zuwa duba ta ba, amma mutanen kauyen sun yi musu kara sosai haka su ka yi ta zuwa duniyar. Yayinda Shitu ya zo amma Aliyu ya saka akayi ram dashi, bama tare da sani kowa ba, ciki kuwa har dasu Nadiya din, ranar da suka cika sati na biyun kuwa arabar ne likita ya shigo musu da labarin da suka jima suna jira. "Za mu iya sallamarta, amma dole ta ci gaba da shan magun gunanta, ta samu isasshen hutu, kuma kada a bar ta ɗaukar wani abu mai nauyi. Don har yanzun ba ta gama samun ƙarfi sosai ba ne, idan ma so samu ne kamar su kai ruwan wanka duk za'a iya mata."

Sadiya ta ɗaga hannayenta tana cewa, "Alhamdulillah." Baba Gaje aka lumshe idanu na ɗan lokaci, kamar tana ƙoƙarin gode wa ALLAH da dukkan abin da ya faru ya ƙare lafiya. Nadiya kuwa da kai tsaye fuskarsu Baba Gaje ta kalla, sai taji wani irin farin ciki ya bayyana a idanunta. Ta gaji da ɗakin asibitin dama dan babu yacce zata yi ne. Ta gaji da warin magunguna, da sautin injuna, da farkawa da dare saboda nurse ta zo ta duba jini ko wani abu. Abin da take so kawai shi ne ta koma gida, ta ga Baba, ta zauna a inda ta saba, ta ji muryoyin mutanen da ta saba ji. Ko da aka gama shirye-shiryen sallamar, sai Aliyu ya bayyana da motarsa. Bai yi wata magana mai yawa ba, sai dai ya tabbatar an saka dukkan magungunan Nadiya a cikin wata jaka, sannan ya ɗauki wasu kayan da Baba Gaje take ƙoƙarin ɗagawa. "Bar shi," ya ce. "Ni zan ɗauka." Baba Gaje ta yi murmushi. "Kai dai baka gajiya da aiki ne haka?." ɗan murmushin gefen baki kawai ya mata ba tare da yace komai suka shige cikin lafiyayyar motarsa. A hanya Nadiya tana zaune a bayan mota tare da Sadiya, yayin da Baba Gaje ke gaba kusa da Aliyu dake tuƙi cikin nutsuwa, ba ya gudu ko garajen duki, cikin taka tsantsan yake driving nashi, duk lokacin da ya taka birki sai ya yi shi a hankali sanin cewa akwai mara lafiya mai danyen rauni bayansa. Wanda kai tsaye Nadiya ta lura da hakan, babu zata motar ta ɗan taka wani rami, Aliyu yayi saurin kallon madubin motar nan take seti da inda take yana mai tambayar.

"Komai lafiya?"

"Eh babu komai ta bashi amsa kai tsaye" Yaya Sadiya kam a ɗan sace ta kalli Nadiya, sannan ta kalli Aliyu ta yi murmushi a ɓoye kawai, wanda kai tsaye Nadiya ta hango ta da tambayar. "Me kike murmushi?" wanda ya saka Aliyu dan kallonta a fakaice yayinda Sadiya ke bata amsa da "Babu komai." Ko da suka isa gida shi da kansa ya taimaka musu wajen sauke kayan, da kwasarsu zuwa har tsakar gidansu, babbar damar da ya sai musu a zaman jinyar suka shimfida yana bude ledar magungunan ya fara nuna musu, duk da cewar sun sani amma sai da ya sake maimaita musu. "Za ku rika ba ta wannan da safe, wannan da rana, wannan kuma da dare," ya ce yana nuna su ɗaya bayan ɗaya Baba Gaje sai aikin gyada kai tame, Sadiya kuma na furta. "ALLAH ya saka da alkhairi Yaya Aliyu..." Aliyu ya kalle ta da amsa da "Ameen." Nadiyan kuwa tana zaune jikinta yane da kyalle don banda saka riga, kuma ko da a kuskure Aliyu bai taɓa kuskuren kallon taba. Ko raunin dake saman kirjinta sai da ya kalla a fisge amma bai taɓa tsayawa ya ma wurin kallon kurilla ba. Tana zaune jingine da bishiyar mango ɗin dake tsakar gidansu, ta zuba masa idanunta a ranta tana tambayar.

Me ya sa wannan mutum yake kula dani har haka?.... Dab da magrib ya bar gidan bayan ya gama yankama Gwaggo Talatu mugun gargaɗi game da Nadiya, don lokacin da suka dawo bata gidan, kuma sam bata lura da motar data kawo su ba, yarane suke je suna bata labarin ga su Nadiya can sun dawo, shi ne ta shigo da balbalin bala'in da ya saka Nadiyan bata mutu ba, aikuwa tun da taki mutuwa yanzu babu gudu babu ja da baya walaha da aiki yanzu ta fara. Yarda Indo a bayanta da duememen cikinta, da ɗan yagwalgwalin ɗan ta Bahari gayau tana jan hannunsa. Sai dai ganin Soja ya saka ta jan birki da saurin kai ƙafafunta kasa tana kwneeldwon tun kafin ya ce mata komai. Nan fa ya gindaya mata sharadi yace duk abinda ya samu jikin Nadiya sai ya harbeta, jiki na rawa tace wllh babu ita babi cutar na Nadiya don ko guda inda hali ma ba zata bari ya taɓa ta ba. Da wannan ya fice bayan Baba Auwalu ya masa godiya sosai da adda'an gamawa da duniya lafiya....

MEDIA

Tuni media ta ɗauki hazo dangane da maganar Kind Dada. Duk da cewa lokaci ya fara ja amma har lokacin wasu tashoshin basu daina saka labaran na suna ci gaba da kawo sabon bayani kan sacewar Sameer, sunan Kind Dada ya fara ɗaukar hankalin jama'a, amma abin da ya fi tayar da kura shi ne sabon bayanin da aka fara samu cewa mutumin da ake kira Kind Dada na iya kasancewa tsohon jami'in DSS mai suna RAYYERN KHALID.

Hotuna na tsohon Rayyern suka fara bayyana, wasu daga cikin tsoffin rahotannin hukumar suka sake fitowa, wasu mutane suna tambayar dalilin da ya sa aka ce ya mutu alhalin ba a taɓa samun gawarsa ba. Wasu suna cewa tabbas akwai wani abu da aka ɓoye, wasu kuma suna cewa ko da zaluntar sa aka yi, hakan ba shi ne zai bashi damar zama dan ta'adda ba. Wasu tsoffin jami'ai da suka taɓa jin labarin aikin Rayyern suna cewa mutumin ya taɓa ceton rayukan jami'ai da dama, wasu kuma suna cewa sunan sa shi kaɗai ya isa ya sa wasu su ji tsoro saboda irin ayyukan da ya taɓa gudanarwa. Inda a ka samu wani ɗan a mutun ɗan jarida ya ce, _Tambayar da mutane suke yi yanzu ita ce, idan Rayyern Khalid da gaske ne Kind Dada, me ya faru da shi tsakanin lokacin da aka ce ya mutu da kuma lokacin da ya sake bayyana?_

_Duk yadda aka yi, akwai wani abu a ƙasa. Mutum ba ya bacewa haka tsawon lokaci sannan ya dawo da irin wannan salo ba tare da akwai abin da ya faru ba dole_yayin da wasu ke cewa. _amma kada mu manta, yanzu ana magana ne akan mutum da ake zargi da aikata laifuka masu tsanani, amma tambayar ita ce... shin abin da ya zama Kind Dada ya fara ne bayan an zalunce Rayyern, ko kuwa Kind Dada ne ya kasance a cikinsa tun farko?_ Tambayar data bazu a social media kenan kamar wutar daji.

Rayyern Khalid + Hero ko Villain? Me ya faru da tsohon jami'in DSS? Why was Rayyern Khalid declared dead?, Who is Kind Dada?

Wasu suna rubuta sunan Rayyern cikin yabo, suna tunawa da tsoffin ayyukansa, suna cewa "Rayyern Khalid ba irin jami'in da ake mantawa dasu bane cikin sauƙi." Wasu kuma suna cike da haushi suna cewa "Ko ya kasance jami'i a baya, yanzu Kind Dada ne." Wasu kuwa ba su goyi bayan ɗaya bangaren ba, sai dai suna cewa kafin a yanke hukunci, dole a gano abin da ya faru da shi.

A yayin da sunan KIND DADA yake ƙara yawo a cikin bakunan mutane, wani abu daban ne yake faruwa a bayan labaran da kafafen yaɗa labarai suke kawowa. Domin duk wanda ya ji sunan Kind Dada a yau, yana jin labarin wani mutum ne mai hatsari, mai tsananin taurin kai, wanda ba ya barin sawunsa a bayyane kuma ba ya bari a karanta tunaninsa cikin sauƙi. Amma duk da haka, duk lokacin da aka yi ƙoƙarin binciken asalin wannan mutum, sai a dawo kan suna ɗaya wato *RAYYERN KHALID*. Kamar dai Kind Dada bai zo duniya da wannan sunan ba. Kamar wani abu ne da ya faru da shi a hanya, har ya tilasta masa ya binne tsohon sunansa sannan ya gina wa kansa wani sabon sunan da a yanzun duniya tafi sanin sa dashi wanda kuma take matukar tsoratarwa. Rayyern bai kasance irin mutumin da yake buƙatar hayaniya domin a lura da shi ba. Akwai wani irin nutsuwa a tare da shi da take sa kasancewarsa a wuri ta fi kowace magana ɗaukar hankali. Ba ya yawan magana, amma idan ya yi magana, kalmominsa sukan zo ne kamar waɗanda ya riga ya auna nauyinsu kafin ya furta su. Ba ya saurin fushi, amma wannan shi ne abin da ya fi sanya shi zama mai ban tsoro; domin mutumin da ya saba da ihu da fushi ana iya karanta shi, amma wanda ya kalli abin da ke gabansa cikin shiru, ya yi murmushi kaɗan, sannan ya ɗauki mataki ba tare da ya ɗaga murya ba, shi ne mutumin da ba a san inda iyakar ko alkiblarsu take ba, irin wadannan mutanen kuma dama can sun fi hadari ko a lissafin mutanen da. Shi ya sa wasu suke kiransa dodo. Wasu kuma suke cewa babu wani abu da ya rage a cikin zuciyar Rayyern Khalid bayan abubuwan da ya shiga. Babu wanda ya taɓa samun cikakkiyar amsar sa. Domin akwai bambanci tsakanin mutum mai mugunta da mutumin da aka tilasta masa ya koyi rayuwa cikin mugunyar duniya. Yayinda wannan bambancin shi ne abin da tarihin Rayyern yake ɓoyewa. A lokacin da yake jami'in DSS, Rayyern ya kasance mutum ne da ba a tura shi aiki saboda ƙarfin jikinsa kawai ba. Ana tura shi ne saboda kwakwalwarsa. Ya kasance daga cikin mutanen da za su iya shiga wuri su fahimci abin da yake faruwa kafin wanda ya shirya shirin ya gane cewa an gano shi. Yana iya kallon mutum sau ɗaya ya lura da abin da wasu suka kasa lura da shi cikin sa'o'i. Yana iya shiga matsayin wanda ba shi da ko wanne irin muhimmanci, ya shafe kwanaki yana sauraro da kallon mutane, har sai ranar da ya tattara dukkan abubuwan da yake buƙata sannan ya kammala aikin cikin nutsuwa. AJMAAL shi yafi kowa sanin wannan fiye da kowa, domin shi ne ɗalibinsa.

Rayyern bai koya masa yadda ake amfani da makami kawai ba. Ya koya masa yadda ake amfani da hankali kafin ƙarfi. Ya koya masa cewa mafi girman sirrin aikin ba wai yadda za ka rinjayi abokin gaba bane, sai dai yadda za ka sa abokin gaban ya yarda cewa shi ne yake sarrafa komai alhali kai ne ka riga ka san inda matakin na gaba zai kasance.Wannan shi ne Rayyern da AJMAAL ya sani, wanda duniya ba ta san wannan Rayyern din ba. Mutumin da ya bayyana bayan shekaru kamar inuwa daga wani kabari da aka rufe ba tare da an san abin da yake cikinsa ba. Kuma duk lokacin da hotonsa ya bayyana a kafafen sada zumunta, mutane sukan tsaya suna kallonsa na ɗan lokaci fiye da yadda suke kallon hoton wani da ake nema. Ba wai saboda sun san shi bane, sai saboda fuskar tasa tana ɗauke da wani abu mai wuyar fassara. Ba fuskar mutumin da yake roƙon a fahimce shi ba ce, kuma ba fuskar mutumin da ya damu da abin da duniya take tunani a kansa ba ce. Fuskar mutum ce da ya riga ya yanke shawarar cewa idan duniya ba ta fahimce shi ba, ba zai tsaya ya tilasta mata ta fahimce shi ba din ba.

A lokacin daya gama fahimtar cewa idan mutum zai iya ba da rayuwarsa ga ƙasa, ya yi mata hidima da zuciya ɗaya, amma idan wasu suka yanke shawarar binne sunansa, za su iya yin hakan cikin sauƙi ya tuna da mahaifinsa, jinin da ya gani a jikinsa, kurkukun da aka garkameshi. Ya tuna darare da yawan daya sha yi ma kansa tambayar cewa.

"Shin dama idan ni ma ba zan iya amincewa da mutanen da nake aiki domin su ba, to wa zan amince da shi?" Tambayar da ta kasance ba tare da amsa ba har zuwa yau daya dena neman amsa daga mutane ya fara nemo ta da kansa. Wannan shi ya sa dawowarsa ba ta kasance ta mutum mai neman ɗaukar fansa kawai ba. Akwai wani abu mafi zurfi, abun da yake so ya nuna, abinda yake so wasu mutane su tuna. Wani abu da ya san idan ya fito fili, zai iya girgiza tarihin mutanen da suka yi imanin cewa an riga an binne shi. Shi ya sa ya bar AJMAAL ya bi sawunsa. Shi ya sa bai hana shi ci gaba da buɗe tsoffin fayiloli ba. Shi ya sa duk lokacin da AJMAAL ya gano wani ƙaramin abu, Rayyern baya firgita. Domin Kind Dada baya gudun gaskiyar da yake son a gano. Abin da yake yi shi ne yana jagorantar wanda zai gano ta. Ba wai ya ɓoye kansa bane, yana iya sa ka yi tunanin cewa kai ne kake neman sa, alhali tun kafin ka fara nema, shi ne ya zaɓi inda zai kai ka. Amma Rayyern ya san cewa akwai tambaya guda ɗaya da har yanzu babu wanda ya yi ta yadda ya kamata.

"Me aka yi wa Rayyern Khalid?"

Domin wannan ita ce tambayar da yake jiran su fara yi, wanda yayi ma kansa alkawarin cewa idan idan har wannan ranar ta zo...ba KIND DADA ba ne zai amsa musu. RAYYERN KHALID ne zai dawo ya ba su ainihin ita wannan amsa din....

BY AMMEY LAYLERH ✍🏻

***

༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺

Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️