Page 17&18
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Ajmaal kuwa ko a washe garin ranar ma a kan aikinsa ya tashi, yana zaune yana ci gaba da harhada rohotonni game da case din a natse, gabansa ga glsa cup nan dake dauke da zazzafan coffee, baki ɗaya bangare guda na dakin pisc na Rayyern ne zagaye da wurin da duk wani wuri daya taɓa ziyarta cikin ƙasar dama kewayenta. Duk a bi anyi wasu jajayen layuka da yellow, daga cikin system nashi kuwa photo Rayyern ne tare da bibiyar Agency Sofehouses nashi zuwa agentlog. Amma No records found kawai yake samu. Glas cup nashi ya dauka tare da kai wa baki yayi sipping coffee din ahankali , tare da ajje cup din daidai da lokacin da wayarsa ke daukar kara alamar shigowan kira ta cikin telephone na computer room ɗin da yake ciki. Wani jahilin murmushi irin na gefen bakin nan Ajmaal yayi, tare da wani shafo sumar kansa da ambatar sunan "RAYYERN KHALID...." A bayyane don ya tsammaci hakan dama tun da har ya iya kutse a cikin computer nashi. Daga nashi bangaren shima lalataccen murmushin ya saki, don take ya gano yana kokarin bibiyar kiran sane. Wani ɗan mele baki Rayyern yayi da komawa jingine daga jikin kujerar da yake kai ya ce... "Kana kokarin bibiyar nan ne? Common Ajmaal ka manta da wa kake magana ne?..." Yay maganar da wani mikar da ƙafarsa ɗaya ya tallafo kansa da hannunsa ɗaya yana ɗorawa da faɗin. "Ka sani bibiyar zatayi ta zagaye daga wannan ƙasa ne zuwa waccan, idan kuma ka shirya zagayen duniyar to Bismillahi...." Wani dan marairaice fuskarsa Ajmaal yayi da faɗin "Yallabai...." Haka Ajmaal ya kira sunan daya saka Rayyern wani dan murmusawa da faɗin, " Ni ne kuma yallabai din wai? Kuma ni...." Yay mganar cikin wani irin salubabben yanayin da baka isa gane inda ya dosa ko ya nufa ba. Daga inda yake zaune Ajmaal ya mike tare da faɗin. "Abin mamaki yake bani taya akai na fahimce ka ba daidai ba yallabai?......." Wani kalan gyara zamansa Rayyern yayi yana jan pcarp din dake gefensa ya rufe fuskansa da shi yace. "No ko kadan ba haka bane Ajmaal baka fahimceni ba daidai ba, tabbas ni ne na ɗauke Sameer saboda shi ne farko a lissafina..." A ɗan kamar zafe Ajmaal ya bugi teburin dake gabansa da ihu yace. "Kuma na ƙarshe ba... Don kafin ka sake yunkurin taɓa wani nayi maka alkawarin zan dawo da Sameer kuma na kamaka...." Sautin wannan mayen murmushin da Ajmaal ke mayen ƙauna daga RAYYERN din a da ya ji fitar sa, kafin ya ce komai Rayyern din yace. "Sannan ka da ka manta na koyama cewa kayi shika idan ka samu dama kada ka ɓata lokaci nima ba zan ɓata nawaba... Yay maganar tare da daukan cigarettes ɗin dake jere gabansa ya ɗauka ɗaya a zuciye da sauri Mark dake tsaye daga gefensa yazo gaban sa tare da kunna masa lighter ya fara zuƙarta a haukace, cikin ƙankanin loƙaci ya hargitsa parlourn da hayaƙin cigarette din. Ata bangaren Ajmaal kuwa kai tsaye ya gane cewan halin ne ya motsa kenan, don haka ya bashi lokaci kafin muryan Ajmaal din ta sake dirar masa tana dawo dashi daga cikin duniyar gajimaren daya fara lulawa. "Ka kuma kara koyamin wani abu ɗaya, ƙasarka tazo a farko sannan ta kara zuwa ata biyu sannan tazo a ƙarshe, bazan manta da wannan ba..." "To ai ba zaka samu lokacin mantawar ba, sannan karka manta na ce ma idan ka shigo tsakiyar abin hari to wasa ya kare...." Yay maganar yana sakin wannan shegen lalataccen murmushin da Jin sautin fitar sa ke saka sanyaya jikin Ajmaal. Dauke baki daya maganar Ajmaal yayi kamar na 5 minutes tare da mayar da sound ɗin, amma still sautin fitar murmushin ya kuma ji daga Rayyern ɗin. dip dip dip yaji sautin katse ƙiran da akayi ba tare da an sake furta masa komi ba. Shima murmushin ya saki domin wannan loƙacin yaci alwashi akan Malamin nasa sosai, shi kaɗai yasan shirin daya danajama hakan ciki kuwa harda durkusar dashi akan gwiwwowinsa....
ꨄ Wani ɗan lumshe idonsa yayi yana fadawa duniyar tunanin lokacin da ƙasa da mutanen dake cikinta sukaci amanarsa, lokacin daya faɗa cikin wani haɗari saboda ƙasar da kuma al'ummar cikinta, a daidai wannan lokacin ne ya sake fahimtar cewa tabbas akwai lokacin da maƙiyi baya zuwa da bindiga ko tanki… sai dai da murmushi da kuma aminci na ƙarya. A daidai lokacin da ƙasa ke kokarin shiga wani hali na tashin hankali, kashe-kashe, satar bayanai da cin amanar da ta fara rusa komai a hankali. Yayin da mutane suka fara rayuwa cikin tsoro, yayi iyaka bakin yin sa, yayi iyaka bakin ƙoƙarinsa amma duk wata hanya da ya bi bame karewa bace, tana karewa ne da masu juya gidan ranar da sune kamar suke juya duniyar a duk lokacin da suka so. Duk wanda ya kuskura ya nemi gaskiya baya daɗe wa a duniya kamar yadda ya gani a karan kansa, bai damu da barazanar mutuwar da ake masa ba, haka kuma bai damu da waɗan da suka juya masa baya ba. A wannan lokacin kawai babban burinsa ɗaya ne kawai… kawo ƙarshen waɗanda suke kokarin sayar da ƙasa domin son zuciya da kuɗi. Wacce ya gane cewar wannan tafiyar ba tafiya bace ta sauƙi. Domin duk inda ya juya, cin amana ce ke bibiyarsa. Wanda yake tsammanin amini ne… shi ne yake rikidewa ya koma maƙiyi. Wanda yake gani tamkar mafaka… shi ne ƙarshen rayuwa. Yayin da yake ƙoƙarin tona asirin wasu daga cikin kusoshin ƙasar da kamar sune ke mamaye komai cikin gwamnati da ƙasar ma baki ɗaya, sai abubuwa suka fara sauyawa daga yaƙi zuwa gudun tsira da rayuwa. An fara nemansa kamar dabba, an kuma fara farautarsa kamar bai taɓa yiwa ƙasarsa aiki ba.Sunansa ya koma abin tsoro. Yayinda da rayuwarsa ta koma cikin duhu, a duk inda ya dosa, mutuwa ce kawai ke binsa a baya. A duk inda ya fake, akwai wanda ya rigaya ya sayar da shi. Yayin da harsasai ke ratsa iska…Yayin da jini ke zuba saboda cin amanar da bata da iyaka… Yayin da gaskiya ke neman mutuwa kafin ta bayyana… Saboda zuciyarsa dake gudun gaskiyar da zata iya rusa rayuwar mutane da dama. An koyar dashi kare ƙasa… amma ba’a taɓa gaya masa cewa wata rana ƙasar kanta zata juya masa baya har taci amanar nasa. Yayi yaƙi domin mutane…amma mutanen suka kira shi maƙiyi maci amanar ƙasar da itace taci amanar shi. Yayi sadaukarwa domin ƙasa amma aka saka farautarsa kamar dabba. Saboda duk wanda ya kusanci gaskiya yana ɓacewa ne tamkar ba'a taɓa halittarsa ba, haka kuma duk wanda ya san sirrin yana mutuwa.Sai dai shi bai tsaya ba, saboda a zuciyarsa akwai abu guda ɗaya da ya fi tsoron mutuwa, ƙasar da yake gani tana rushewa a hannun masu cin amanar cikinta. Amma idan duniya baki ɗaya ta zama maƙiyinka…Lokacin da duhu ya mamaye komai sai gaskiya ɗaya data rage, aka kama shi aka garƙame a gidan kaso, an azabtar dashi azabtarwar da babu iyaka ko adadinta. An kashe masa mahaifinsa. Don haka ya ja da baya ya rikide zuwa wani irin kasurgumin dan ta'addar da duniyar ke neman sa ruwa a jallo, ya tashi hankulan kowa dake cikin kasar har dama wajen ta..... Wani numfashi a zafe ya kawo yana fesarwa, tare da rike kansa yana fasa wani mahaukacin ihun daya saka Mark runtse idonsa, shi da yake yana masa shan giya ko cigarettes amma yau da kansa ya zube masa cigarette kara biyar, tare da tura masa bottle na Red wine. Tamkar zararre haka ya yaja karan cigarettes din ya kunna masa lighter ya wani zuketa ita din ma a zafe. Kafin ya mike yana nufar bedroom nashi da ya daketa da kafa kuwa zaune ya kai saman lafiyayyan gadonsa yana dafe kansa, daga yanda ya zauna yay shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane Abubuwane kawai suke masa kai-komo a rai hoton ababuwan da suka wuce ne kawai ke ta famar dawo masa, da ta yanda aka yi Ajmaal ya iya bibiyar tsohuwar na'urarsa duk da cewa ya bar mata matakan tsaro sosai fiye da kima. Kenan hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata ba tare da tangarɗar komai ba. Goran ruwan Mr. V din dake a Centre table ɗin dake gaban gadonsa ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na ba adadi yana sake nutsar da kansa. Sosai abubuwa masu yawan gaske suka shiga ƙoƙarin zeroying Brain nashi. Tamkar kuma wanda aka zabura ya miƙe aɗan zafafe yana yin gaban ƙofan Glass ɗin dake a shafe da Pics manya na emeji me hoton lion, babbar yatsar hannunsa ya sanya a take wurin dake a shafe yayi On tamprint na yatsansa, zuuuuuuu wata haɗaɗɗiyar ultra door ta baiyana. Wasu manyan Computers ne a ɗakin da suke a jojjone ta ko wacce kusurwa dake ɓangaren, akan wani ƙayatacce dogon table sai kuma macbook akan wani dogon l kujera. Zama yayi cikin hanzari tare da ɗaukar MacBook ɗin dake kan kujerar, buɗewa yayi ya fara aiki cikin ƙwarewarsa da kuma baiwar iya sarrafa ko wanne irin abu, yakai kusan 30 minute yana danne danne, kafin ya saki wata iriyar ajiyan zuciyan daya sauƙe kafin ya tashi yana barin ɗakin da yafi kama dana bincike.
*Kurman Rafi*
Ko da aka idar da Sallar Magariba har Baba ya dawo duk suna zaune suna debema Nadiya kewa, Yaya Sadiya ce ta shiga ɗakin Nadiya tare da fito da wata babbar farar roba mai fadi wadda take ɗauke da mixed fruit salad, a ciki akwai ayaba da aka yanka kanana, kankana, dabino, kwakwa, aka gauraya komai da madara, hatta 'ya'yan kankana suna ciki sai in ka so ka hade ka taune dasu in baka so ba kuma ka hurzar, sai ta ajiye robar a tsakiyar tabarmar da suke zaune a kai, Nadiya wadda take zaune kusa da bango ta dube ta, sai murmushi ya subuce mata ba tare da ta shirya ba, domin kuwa tun daga lokacin da Ya Aliyu ya fara sawo musu shikenan ya shiga ranta take ƙaunar sa, ko yanzun ma da yake a hannun Yaya Sadiya wanda ta kawo ne da yamar kuma akayi sallama, gashi basa da fridge bare su ajje shi zuwa safe, don suna ajje shi kuma shikenan ya lallace, don haka ta fito musu dashi wajen roba biyar ne ma. Nadiya ce ta dan matsa kusa da robar tana kallon yadda madarar ta lullube 'ya'yan itatuwan, ta ce, “Ni ai tun kafin ki bude robar na san zan ci, wallahi.” Sadiya ta yi dariya, tare da ɗaukar cokali ta fara rabawa wadanda suke kusa da ita da suka shigo dubiya,yayin da Gwaggo Talatu wadda take zaune gefe guda tana kallon su tun da farko ta wani tabe baki ta ce, “Wannan kuma wacce kazantarce haka?” Sadiya ta juyo ta kalle ta fadin, “Mixed fruit salad ne Gwaggo.” Gwaggo Talatu ta sake kallon robar daga sama har kasa tana yamutse baki, ta dan karkatar da kai kamar wadda ake kokarin nuna mata wani abu da ba ta taba gani ba, sannan ta ce, “Salak kuma?” Sadiya ta ce, “Ah ahh Gwaggo fruits salad.” Gwaggo ta yi shiru na dan lokaci, sai ta ce, “To me ya sa aka yanka ayaba aka jefa da kankana, aka sake jefa dabino da kwakwa, sannan aka zuba madara a kai? Kowanne bai san inda yake zama bane?” Nan take dariya ta barke a tsakanin mutanen gidan, Nadiya ma ta dafe bakinta tana dariya ƙasa kasa saboda raunin dake kirjinta, Sadiya ta ce, “Gwaggo, ai haka ake yi ne.” Gwaggo ta gyada kai, “Ku kuka sani ni dai na san ayaba ita ce ayaba, kankana ita ce kankana, dabino kuma dabino ne, amma yau na ga an yi musu taron hadin kai.” Sai Nadiya ta ce cikin dariya, “Gwaggo ki dandana mana kawai.” Gwaggo ta girgiza kai da sauri, “Ni? Me zan yi da shi rufamin asiri wannan jagwalgwalo in nasha ai sai cikina ya ruguje in tafi masai...?” Sadiya ta ce, “Ki dai sha din mana sai kiji.” Gwaggo ta kalli robar sannan ta kalli Sadiya, “Kuma masu shan ubangiji ya rufa muku bargon asiri wllh.” Sadiya ta yi murmushi, “To ki dandana kawai, idan ba ki so sai ki bar shi.” Gwaggo ta sake cewa, “A'a, ku sha abinku amma banda talatuwa... "Ta yi maganar ne tana juyar da kai gefe amma duk da haka idonta ya ci gaba da komawa kan robar lokaci zuwa lokaci, musamman duk lokacin da ta ga wani ya debo cokali ya saka a baki sannan ya gyada kai yana cewa “wayyo , dadi.” Daga karshe Sadiya ta dauko wani cokali ta debo kadan daga cikin hadin ayaba, kankana da dabinon, ta mika mata, Gwaggo ta kalli cokalin, ta kalli Sadiya, sannan ta ce, “Ai na ce me zan iya sha ba?” Sadiya ta ce, “Ki karba kawai Gwaggo.” Wasu daga cikin matan suka ce, “Don Allah Gwaggo ki karba mana ki taɓa,” sai Gwaggo ta yi kamar an takura mata sosai, ta ce, “To shikenan.” Ta karba da kanta, ta dube shi na dan lokaci kamar wadda take son tantance wani abu, kafin daga bisani ta saka a baki, ta tauna a hankali, sannan ta tsaya cak. Ba ta yi magana ba. Sadiya ta kalle ta tana murmushi, Nadiya ma ta kasa dauke ido daga fuskarta, domin ta ga yadda Gwaggo ta sake lumshe ido kadan, ta sake taunawa, sannan ta hadiye. Bayan wasu dakiku ta ce, “Hmm.” Sadiya ta ce, “Yaya kika ji Gwaggo?” Gwaggo ba ta bata amsa ba, sai ta mika hannu ta dauki cokalin da ke kusa da robar, ta debo da kanta, wannan karon kuma ta dauko ayaba da dabino da kwakwa, ta saka a baki, ta sake taunasu, sannan ta ce, “Karkwai wannan ai shi ne YI WA KAI ƊIN....!” Nadiya ce ta fara fashewa da dariya da fadin, “Gwaggo meye hakan kuma?” Gwaggo ta kalle ta, ta ce, “Ni dai ba zan yi karya ba, wannan abin ya fi yadda na dauka.” Sadiya ta ce, “Na ce miki.” Gwaggo ta gyada kai tana kara debo wani cokalin, “Ai na dauka kun kawo wani abu ne na zamani wanda mutum zai ci ya yi nadama, ban san cewa abin yana da dadi har irin haka ba.” Ta sake sha sannan kamar an bude mata kofar surutu, sai ta fara cewa, “Wallahi yanzu na gane wani abu, masu kudi suke da duniya!” Nan take dariya ta cika gidan, Nadiya ta ce, “Gwaggo Gwaggonmu?” Gwaggo ta daga cokalin da ke hannunta tana magana cikin cikakken kwarin gwiwa, “Me kuma? Ba gaskiya nake fada ba? Mu talakawa muna ganin ayaba sai mu ci ayaba, kankana sai mu ci kankana, dabino sai mu ci dabino, su kuma masu kudi suka ce a'a, me zai hana mu hada komai wuri daya, mu zuba madara, mu zauna cikin sanyi muna ci? Wallahi masu kudi suna da dabarar jin dadi!” Sadiya ta fashe da dariya, “Gwaggo ai ba sai mai kudi ba.” Gwaggo ta juyo ta kalle ta, “Ke ki bar ni, kar ki lalata min jawabin nan, yau na gano sirrin duniya.” Ta sake debo wani cokalin mai yawa, ta ce, “Ga shi nan, idan talaka ya samu ayaba zai ci ya wanke baki ya tafi, amma mai kudi zai ce, ‘A'a, kawo min kankana, kawo min dabino, kawo min kwakwa, kawo madara,’ sannan ya hade su ya ce rayuwa tana da dadi. To lallai duniya tana inda take in dai haka ne abun!” Nadiya ta rike cikinta saboda dariya, har tana mancewa da ciwon dake kirjinta, Gwaggo kuwa ba ta damu da dariyar da suke yi ba, sai ta ci gaba da shan nata tana yin magana a tsakanin cokali da cokali, “Kuma ga abin da na kara gane wa yau, mutum kada ya yi gaggawar cewa baya son wani abu saboda bai san shi ba, domin da farko na ga wannan abin na ce me zan yi da shi, amma da na saka a baki sai na ce ashe duniya tana boye mana dadi ne saboda jahilcinmu.” Ta yi shiru na dan lokaci, sannan ta gyada kai, “Rayuwa ma haka take, wani lokacin mutum yana kallon wani mutum ya ce ba zai taba zama kusa da shi ba, amma sai lokaci ya nuna masa cewa wannan mutumin ne ALLAH ya aiko domin ya zama masa dalilin farin ciki.” Maganar ta sauya yanayin dariyar na dan lokaci, Sadiya ta kalle ta cikin nutsuwa, Nadiya ma ta yi shiru tana kallonta, amma kafin su gama dawowa daga cikin duniyar tunaninsu Gwaggo ta sake daga cokalin tana kaiwa baki ta ce, “Amma duk da wannan hikimar da na fada, gaskiyar magana daya ce…” Ta saka cokalin a baki, ta tauna, sannan ta ce, “Masu kudi suke da duniya!” Sai aka sake fashewa da dariya gaba daya. Sadiya ta ce, “Gwaggo kin dawo seti kenan?.” Ta ce, “Me zan yi? Hikima ma tana bukatar a fada gaskiya.” Ta sake debo wani, “Wallahi da ALLAH ya bani arziki, ba zan sake cin ayaba ita kadai ba.” Nadiya ta ce, “To me za ki yi?” Gwaggo ta mike kamar wadda aka tambaye ta tambaya mai muhimmanci, ta ce, “Zan sayi babbar roba irin wannan, in cika ta har ta kai nan…” Ta nuna kirjinta, “Sai na zauna ina ci har sai cikina yaki amsar wannan abin dadi.” Sadiya ce tayi murmushi da fadin, “Amma fa kin ce ba kya son shi da.” Gwaggo ta tsaya, ta kalleta, sannan ta ce, “Ai tun da farko ban san haka yake bane, yanzu na san shi.” Ta sake zama, ta ce, “Wannan shi ne babban darasin da na koya yau, kada mutum ya raina abin da bai sani ba, domin wata kila abin da yake gani karami shi ne zai zama dalilin da zai sa ya manta da babban damuwarsa.” Nadiya ta yi murmushi a hankali, tana kallon Gwaggo Talatu wadda a yau ta zama kamar ba ta san akwai damuwa a gidan ba, tana cin mixed fruit salad din tana surutu tana dariya, kuma ko da yake kalamanta suna zuwa ne cikin barkwanci, a cikin kowanne barkwancin nata kuwa akwai wata maganar da ke dauke da gaskiyar rayuwa. Sai ta sake daga cokalin, ta ce “Hmm… masu kudi suke da duniya wallahi.” Shigowar wasu mata ƴan dubiya shi ya saka maganar Gwaggo Talatun mutuwa, tana saurin surar robarta tayi ɗakinta gudunma kar wani ya gani ta biya ransa, ita kuwa dama kowa ya san halin ta ba kyauta gareta ba, can babu jimawa sai gata ta fito a guje ta zura zuwa ban daki wai cikinta ya rugwage mixed fruits salad din ya sakar mata da ciki. Nan sukayi ta mata dariya, har wajajen goman dare ƴan dubiya basu dena lekowa gidan ba. A haka kwanaki suka ci gaba da ja a hankali, kamar yadda lokaci yake da dabi’ar yi ba tare da ya damu da irin abubuwan da mutum yake ciki ba. Yaya Sadiya ita ke ci gaba da kulawa da Nadiya duk lokacin da ta mike daga inda take zaune, Sadiya kan daga kai ta kalle ta, kamar tana son tabbatar da cewa ba wani abu ne ya same ta ba. Idan ta yi shiru na tsawon lokaci, Baba Auwalu kan tambaya, “Ina Nadiya?” ba don yana ganin inda take ba, duk da kasancewar ba ganinta yake ba, sai don ya saba da jin motsinta, so idan kuma bai ji motsin ba ya dinga tambayar tana ina?, kuma duk lokacin da ya daina jin muryarta sai zuciyarsa ta fara neman ta. Gwaggo Talatu kuwa, duk da irin abin da ya faru a tsakaninta da Nadiya, ta fara rage yawan kalamanta, musamman bayan gargadin da Aliyu ya yi mata. Ba wai komai ya zama cikakke tsakaninsu nan take ba ne, amma akwai wani irin sauyi da aka fara samu daga cikin takurar da tama Nadiya din, A cikin satin da suka dawo kusan sau uku Ya Aliyu yana zuwa wanda zuwansa na ƙarshen da yayi har yazo da wani abokinsa zaffar, wanda yake sunan Muzaffar ne amma suke kiransa zaffar din a wurin aikinsu na soldier sunce ko dan sabo da zafin namansa. Kusan kullum a tsakar gida suke hutawarsu ita dasu Yaya Sadiya da Indo wanda a irin wannan lokacin ne Nadiya kan ji kamar duniya tana ci gaba da tafiya ne kamar babu abin da ya faru da ita, sai da tana jin kamar akwai wani sashe na daga cikin rayuwarta ne da ya tsaya a ranar da aka ɗauke ta zuwa asibitin nan. Yau kam basu fito ba dake anyi ruwa da asuba suna ɗaki, don haka duk Nadiya take jinta kamar a takure a matse kuma. Tana kwance daga ɗan saman gadon ƙarfen ta Yaya Sadiya ta shigo hannunta dauke da silba mai murfi data sayo mata wainar hatsi sai ruwan shayi da biredin data sayo mata suma. Kasancewar ko a nan din ma sosai Aliyu ya saki kudi yace aci gaba da kulawa da Nadiya din.
“Nadiya ki tashi kici abinci sai ki sha maganin?” Nadiya dake kwance ta kalleta da gyada mata kai ta taimaka mata ta tashi zaune. Baba ne ya shigo dakin yana zama tare da yima Nadiya yaya jiki ta amsa masa tana sake gaida shi duk da sun gaisa da asuba. A natse Baba ya soma mata ƴan nasihun da kan ɗan taɓa mata lokaci bayan lokaci, wanda ya saka Nadiya yin shiru idanunta na cikowa da ruwan hawaye. Baba ne ya dafa kanta da furta. “Kada ki yi kuka duk abinda ya faru dama can tabbataccene tun daga rabbi izzati, kuma ai abinda ya riga da ya wuce ya wuce kenan IN SHA ALLAHU baya sake dawowa sai dai mu godewa ALLAH... " Nadiya ta amsa da Ameen tana ƙoƙarin tashi da kanta da ƙaramin kofi rike a hannunta Yaya Sadiya tayi saurin rikota tana fadin. “Ki bar shi zan ɗauke koma ki zauna...” Wani ɓata fuska Nadiyan tayi ta kalli Yayar nata da faɗin. "Ke me yasa kin fiye matsalane? Shikenan ko komai sai dai kice zaki min wanke hannu ma shikenan ba zan yiba, kofin sai kace wani abu..." karasa amshe kofin tayi da faɗin “Ko da ƙaramin cokali ne. Likita ya ce a barki ki huta sosai.”Nadiya ta yi yar dariya kadan da faɗin. “Ƙarfi da yaji so kike sai kin mai dani kamar wata jaririya, dan ko tsarki da da dama na tabbata ke zaki min.” Murmushin itama Yaya Sadiyan tayi da faɗin. “Eh koma mi zaki ce ki ce na ɗan lokaci ne.” Dole komawa tayi ta zauna tana wanke mata hannun a ɗan kwano ta fita dashi, shi dai Baba murmushi ne kawai nasa daci gaba da bin yaran nasa da fatan alkhairi da dacewa da duniyarsu dama lahira. Sai zuwa can yamma Baba Gaje ta shigo gidan kasancewar tun washe garin da suka dawo ta koma gidanta. Kuma har dare tana nan, Gwaggo Talatu kam sai rokon ALLAH take ubangiji ya kawo Aliyu, saboda zuwansa na ƙarshe ta bashi sakon idan zai dawo ya taho mata da kankanar robar nan me dadi. Duk data sakar mata da ciki amma tace dan wuya ba'ar dadi ba. Su dukansu suna zaune kan tabarma bayan idar da sallar magriba, aikuwa adda'ar Gwaggo Talatu ta amsu saiga sallamar Ya Aliyu nan.
“Assalamu alaikum.”
Gwaggo Talatu ce tayi saurin amsa masa tana leken hannunsa, wata ajjiyar zuciya ta sauƙe bayan data ga wata babbar leda a hannunsa. Sosai zuciyar Nadiya ta yi wani irin motsin da ba ta san dalilin sa ba, muryan na buganta sosai da faɗar mata da gaba haka kawai duk lokacin da zata jita, kafin a hankali ta ɗaga kai zuciyarta naci gaba da bugu muryan na sake ratsawa cikin kunnen ta. Kai tsaye idonta na fadawa kansa yana dag tsaye baƙin kofa sanye da kayan da ba na aiki ba yau, amma yanayinsa har yanzu yana ɗauke da irin tsari da nutsuwar da aka saba gani a tare da shi. Hannunsa dauke da ledar da indai zai zo sai ya zo musu da ita, baya taɓa gajiyawa, yana tsaye daga bakin ƙofar cikin ladabi yana jiran a ba shi izinin shiga. Baba Gaje ce ta bashi izinin shigowa da suka game jonewa tuni tun a asibiti yake kiranta da Goggo. A natse Aliyu ya shigo cikin gidan a hankali, idonsa kan Nadiya dake kishingide tayi mata shin kai da pillow. Sai da ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta kamar yana son ya tabbatar da cewa lallai tana lafiya kafin ya kara so a natse yana zama daga gefen tabarmar. Nadiya kuwa ta kasa hana kanta kallonsa. Ba wai saboda wani abu na musamman ba, sai don yadda zuwansa ya tunatar da ita kwanakin da ta kwashe tana cikin wani yanayi da ita kanta ba ta san ko za ta fita daga cikinsa ba a kansa, zama yayi kafin ya kalleta a wani kaikace da faɗin. “Yaya jiki?”
“Alhamdulillah.” ta amsa masa tana sunkuyar da kanta kasa. "Kina shan magungunanki akan lokaci dai?" Wani dan tura baki gaba tayi da faɗin. "Ina sha" Kamar a kule don ita ta fara gajiya da tambayar a koda yaushe sun fiye takura mata akan shan maganin nan. Ita har mamakin yadda yake iya faɗar magana cikin sauƙi take amma ta zama kamar ba ta da damar yin gardama akan duk abinda yace da ita, Yaya Sadiya ce ta mike tana yar dariya da fadin. “Wllh kamar kasan yau duk da gardamar kin shan maganin ta tashi bari in dauko na kawo maka...daga haka ta shige ciki ta bar sai Baba Gaje data amshe zancen itama suna hawa kan Nadiya da mitar kin son shan maganin ta. Shiru ne ya ratsa tsakani bayan mitar da suka ga na ƴan daƙiƙu. Kafin Nadiya ta ɗan matsa baya tana kokarin gyara zanin da ke jikinta, tare da satar kallon inda Aliyu yake zaune, wanda shi sam bama ita yake kallo ba, idanunsa na kan tsakar gidan ne suna yawo ne kamar mai son gano ko tantance wani abu. “Ya Aliyu.” Nadiya kira yi sunansa a hankali wanda ya saka shi dagowa da amsawa da “Na'am?” Wasa ta shiga yi da hannunta kafin ta shiga mamula bakin son yin cikakkiyar magana amma tana kasawa. “Na gode.” Wani kallo ya mata da cewa, "Game da?" Ya fadi alamar tabbacin yake nema kenan. "Komai da komai ina nufin for everything ma...tun a asibiti kake ta dawainiya damu har muka dawo baka dena dawainiyar damu ba..." Wani ɗan numfashi kawai ya iya sauƙewa a hankali da cewa. "Kada ki damu da ace ina da damar yin fiye da abin da na yi, da na yi" Yay maganar daya saka Nadiya kallonsa amma ta gaza cewa komai. A kuma daidai lokacin ne Yaya Sadiya ke dawowa dauke da maganin. Ta kalli su, ta ɗan yi murmushi, amma ba ta ce komai ba. Ta miƙa wa Nadiya maganin da cewa Aliyu ya kula don tsaf zata faki idonsa ta zubar. Shi da kansa ya tsaya har sai da ya tabbatar da cewan tasha maganin kafin kwalawa Gwaggo Talatu kira da Baba Gaje wanda duk suka basu wuri a fakaice, ledan ya tura gabansu yana cewa gashinan yau harda Shawarma ma ya sayo musu da chocolates. Wayyoooo murna da farin ciki agun Gwaggo Talatu gata ga rabin ranta mixed fruits, daga nan ya tambayi Baba aka ce dashi ya baro shi cikin masallaci. Daga haka Yay sallama dasu bayan yace musu zai iya cinye satin nan bai leko ba, saboda wani aiki ne dashi sosai, da fatan alkhairi suka bishi harda Nadiya data sake jaddada godiyarsu gareshi. Aliyu ya ɗan kalleta na wasu daƙiƙu, sannan ya ce, “Ki kula da kanki.” ba tare da ya sake bi ta kan godiyar da take masa ba ya sa kai yana juyawa tare da barin gidan. Nadiya ta sauke idanunta kasa tana jin zuciyarta tana bugawa da wani irin yanayin da ita kanta ba ta fahimta ba. Sadiya ta zauna tana binta da kallon tuhuma, kafin tayi murmushi kawai don ta san koda ace ta mata magana ba komai zata ce da ita ba. Ita kuwa a nata bangaren lumshe idanunta kawai tayi domin tun ranar da ta buɗe idanuwanta a asibiti, cikin duhun tsoro da rashin sanin abin da zai faru da rayuwarta, shi ne mutan na farkon da ALLAH ya sanya a hanyar ceto rayuwarta ya zama sanadin da ba za ta taba mantawa da shi ba.
Acan waje kuwa a zaune Aliyu ya tarar da Baba Auwalu shi kadai yana lazimi. Wanda jin motsi ne ya sa shi tambayar waye? “Ni ne Baba.” Aliyu ya bashi amsawa yana tsugunnawa a gabansa, wanda take fuskar Baba Auwalu ta sauya da farin ciki. “Aliyu?” ya kira sunan yana masa nuni da kusa dashi da fadin “Zo ka zauna.” A kunyace Aliyu ya zauna kusa dashi yana gaida shi, shi kuwa Baban hannu kawai ya miƙa masa da fadinm “Yaro na ALLAH ya saka maka da alkhairi ya kareka daga sharrin duniya da abinda ke cikinta.” “Ameen Baba.” ya amsa murmushi bayyane a fuskarsa duk da cewan ba koda yaushe aka fiye ganin murmushin kwance saman taba. “Tun lokacin da muka shiga wannan jarabawar, ban san abin da zan ce maka ba. Kai ka san cewa ni ba na gani, amma na ga abubuwa da yawa ta hanyar yadda ka tsaya mana ubangi ya dafa maka,ya maka majingina yaci gaba da jiɓantar lamuranka tamkar yanda ka jiɓanci namu, domin kuwa a yau Nadiya tana nan saboda ikon ALLAH ne. Amma kai ne wanda ALLAH ya sa ka zama sanadin rayuwarta..." A kunyace Aliyu ya sunkuyar da kai da fadin."ALLAH ya ƙara muku lafiya baki ɗaya Baba" Haka Baba yaci gaba da masa addu'a yana amsawa da ameen har ya masa sallama shima ya tafi bayan ya basu kudi wanda sam Baban yaki amsa yana ta masa fadan mai yasa shi baya gajiya.....
BY AMMEY LAYLERH ✍🏻
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️