DUHU na DUKAN duhu

Page 21&22

by @103453610185262939894

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.

ꨄ Kamar yadda aka saba cewa duk wani sirri da ya daɗe ana binne shi, wata rana dole ne shi da kansa ya fara neman hanyar da zai fito da kansa, hakan cewa kuwa ta kasance dangane da lamarin Kind Dada wanda ya fara sauya salo daga abin da jama'a suka ɗauka a matsayin wani babban aikin ta'addanci zuwa wani abu na daban din da babu wanda ya isa sanin ya farkonsa yake bare ya san inda ƙarshensa zai tsaya. A lokacin da kafafen yaɗa labarai suke ci gaba da ɗaukar zafi, ta inda ya zama kusan gaba ɗaya duniyar ma zance da ake ta mayarwa kenan, kasancewar abu ne na media don haka lamarin ya zama kamar gobarar da aka cinna a cikin daji haka lamarin ya kasance. Baki ɗaya hankulan jama'a duk kusan a rarrabe yake wurare daban ko ina da kalar nasa labarin dake fita. A daidai lokacin da Abuja dama duniyar bakinɗaya suke ta sake jujjuya maganar KIND DADA, ita kuma a daidai lokacin ne Babyboo ta fara nata aikin cikin sirri ba tare da sanin kowa ba, domin kuwa tun da ta riga ta gama fahimtar cewa wasan ya sanja salo itama ta koma gefe tayi kamar bata cikin lamarin, sai tayi kafta kutse cikin duk wanda take hasashen RAYYERN KHALID ka iya kai masa farmaki a koda yaushe sai kuma akayi gamo da katar ya fara da da babban yaronsa kuma na hannun damarsa wato Ajmaal. Kuma dama shi ta fara bibiyar duk inda ya taka, don tasan dole ne ya bar wata alama ko da kuwa ace ƙaramar alama ce wadda ba kowa zai iya ganewa ba. Domin Ajmaal ba irin jami'an da suke yawo da takardu ne ba kawai, shi mutum ne wanda baya taɓa barin tunaninsa a cikin aikin da yake yi, ya iya rikitarwa amma duk da haka sai data sama dama da hanyar. Ba tare da tambayi wani inda yake ko me yake bincika ba. Ta bi sawun abin da ya bari ne kawai, ta haɗa ɗaya da ɗaya, ta bar tsarin kwamfuta ya yi mata magana a maimakon ta jira wani ya gaya mata gaskiya. Wannan shi ne dalilin da ya sa lokacin da ta fara bibiyar hanyar da Ajmaal ya yi amfani da ita wajen neman Rayyern, ba ta shiga cikin tsarin Kind Dada da karfin tsiya ba, sai dai ta bi hanyar da Ajmaal ya bari a baya ne cikin nata salon wasar, domin itama Boss ceee.... Tana zaune gaban system nata Idanunta suna tsaye cak kan wani ƙaramin shafin da babu wani suna a kansa, sai wata alamar dake tattare da hoton sai wasu lambobi da alamomi da suka bayyana kamar rubutun da wanda ya ƙirƙire shi yake son ya ɓoye shi daga duk wanda ba shi da masaniya akan tsarin nada, hannunta kuwa na kan mouse ɗin na wasu daƙiƙu, sannan ta janye shi kamar tana tunanin ko abin da take shirin aikatawa ba daidai bane ko bai dace ba. Saboda tun farkon fara wasan a duk lokacin da zata ji an ambaci sunan RAYYERN KHALID wani irin tashin hankali take ji, ko a yanzun ma hannunta gaza ci gaba da abinda take yi yayi, ba wai don tana tsoro ko wani abu ba ne, A ahh domin da ace tsoro ne da ta rufe computer ta tafi, da kuma bata soma buga nata hasalin wasar ba tun farkon fari, duk da kasancewar abin da take ji ya fi haka najin cewar kamar akwai wani abu da aka taɓa haɗa shi da ita, aka cire shi daga ƙwaƙwalwarta, amma yanzu wani ɓangare na daga cikin wannan abin yana ƙoƙarin dawowa gareta. A natse ta sake kallar lambobin da ke gabanta, kafin a hankali hannunta ya ci gaba da zirga-zirga a kan keyboard din idanunta naci gaba dabin screen ɗin cike da taka tsantsan. Kafin ta dan dakaga na ƴan daƙiƙu tana kallon wani code, don haka hankalinta yake yin kamar zai tashi ga uban bayanan dake gabanta masu yawa, duk da hakan bata jin cewar zata sare domin kwakwalwa da tunanin ta wuri ɗaya kawai suke son gano mata. Inda Kind Dada yake zaune! Inda ya ɓoye har ya keɓanta kansa daga cikin duniyar mutane, ta san cewa idan har ta gano wurin da yake to kuwa komai zai fara samun ma'ana kenan. Wani dan lumshe idonta tayi tare da yin baya, kafin kamar a bazata kuma ta buɗe idon da dukkan karfinta. Kai tsaye ta shiga cikin tsoffin routing ɗin kiran da aka yi Ajmaal ta haɗa lokutan da saƙonnin suka shigo, sannan ta sake dawo da wani bayanin da aka goge daga wani sashe na system din. A hankali wasu lambobi suka fara yin ma'ana a cikin kanta, sake ɗan lumshe idonta tayi tare da tura kujerar da take kai baya, ta na mai sake kallar screen ɗin na wasu daƙiƙu, wani ɗan murmushi mai kyau na bayyanuwa a gefen bakinta kafin ta sake komawa kan aikin. Ba ta yi hakan ne don ta taimaka wa Kind Dada ba, kuma ba don ta yi wa Ajmaal kutse ba. Abin da take so shi ne ta gano wanda yake bayan wannan suna, ta gano inda yake, sannan ta miƙa abin da ta gano ga waɗanda aikinsu ne su ɗauki matakin da ya dace. Bayan kusan wasu mintuna masu yawa na aikin, wani sabon bayanin ya sake bayyanar mata. Babyboo ta ɗan karkatar da kanta, idanunta suka tsaya wuri guda. Ba cikakken address ba ne, amma ya isa ya ba mutum hanyar zuwa wani yanki na musamman. Ta sake haɗa bayanin da wasu bayanan da ta samo daga tsarin Ajmaal, sannan ta buɗe wani taswira. Wannan karon abin da ya bayyana ya fi kusa da abin da take nema. Ta sake yin wasu ƙananan gyare-gyare, ta tabbatar da bayanin sau biyu, sannan ta tsaya tana kallon screen ɗin. “Na same ka…” ta furta wani kalan shegen murmushi ɗauke a fuskanta. “Kind Dada?.” ta furta tare da ɗan lumshe ido kafin ta sake furta, “Ko Rayyern Khalid?.”

A daidai lokacin da Babyboo take nan zaune don tabbatar da bayanin ta, a ɗayan ɓangaren kuwa Rayyern ne zaune cikin nutsuwarsa kamar koda yaushe. Bai san cewa macece mai bin sawunsa ba, don duk abin ke faruwa tun farkon lokacin da aka fara shiga cikin tsarin nasa shi ne irin hanyar da Ajmaal yake amfani da ita. Tsarin da aka yi amfani da shi, yadda aka haɗa bayanan, irin tambayar da aka yi wa wasu files, da kuma hanyar da aka bi wajen kusantar wata ƙofa da ya ɗauka ita ce hanyar Ajmaal din sa. Saboda haka bai samu wata damuwa ba, don a nasa tunanin da ganinsa Ajmaal ne kaɗai keda irin wannan zarrar. Kuma wannan ma ba abin mamaki ba ne a gare shi, domin dama ya daɗe yana jiran Ajmaal ya fara bin sawun da ya bar masa. A natse Rayyern ya kalli screen ɗin nasa yana ganin motsin bayanan yana gudana a hankali, sannan ya ɗauki glass cup ɗin sa dake dauke da Red Wine ya kurɓa kaɗan. Mark yana daga ta gefensa ya rankofo kaɗan daga tsayen da yake ata bayan Boss din nasa. Ɗaya daga cikin yaransa ne ya shigo yana cewa, “Boss, someone is inside the system" Rayyern bai ko ɗago kansa ba bare yasa ran zai kalle shi ya ce. “Na sani.” Mutumin ya ɗan tsaya kafin ya ce, “We should cut the connection.” Rayyern ya ɗan ɗage girar sa ɗaya, sannan ya ce, “A'a.” “Amma Boss…” “Na ce a bar shi.” Ya faɗa a zafe yana sake komawa kan screen ɗin. Wata iska ya furzar daga bakinsa kafin kamar wanda aka fisga yace “Ajmaal yana yin abin da nake son ya yi ne kawai! Wannan ɗin tsarinane” Yaran suka kalli juna, domin ba su fahimci yadda Boss ɗinsu yake magana da irin wannan nutsuwa ba. Shi kuwa Rayyern ya ci gaba da kallon bayanan da wani kafirin murmushi kaɗan dauke saman fuskarsa, domin a tunaninsa wasan da ya shirya yana tafiya daidai yadda ya tsara shi ne.

Ata bangaren Babyboo kuwa ta ci gaba da bin bayanan har ta kai ga gano abinda take son ganowar, amma duk da haka bata yanke hukuncin kai tsaye ba har sai data sake yin nazari sosai, kuma ta sake tabbatar da coordinates ɗin, sannan ta ɗauki wayarta. Kai tsaye tana saka kira ba ta yi wata doguwar magana ba. Ta bayyana abin da ta gano tare da tura bayanan wurin, da bayyana musu cewar abinda suke nema yana ata can. Wanda hakan yasa wanda ake ma jawabin yin shiru na ƴan daƙiƙu kamar bai yarda da abin da ya ji ba, sannan ya tambaye ta, “Kin tabbatar?” Babyboo ta kalli screen ɗin, ta sake tabbatar da bayanan, kafin ta ce, “Na tabbatar, amma ku yi taka tsantsan kit daga haka ta datse ƙiran..... Rayyern kuwa da ya fara ganin wani abu daban a tsarin nasa ba, wanda ba shi yayi hasashe ba ne ya saka shi kokarin yin wani abu, don a da komai yana tafiya ne ta hanyar da ya sani. Amma sai wani sabon tsarin ya bayyana ba irin na Ajmaal ya saba masa ba. Rayyern ya ɗan matsa kusa da screen ɗin. Ya kalli wasu lambobi, ya kalli yadda aka shiga cikin wani sashe na daban daga cikin na'urarsa sannan ya sake kallon tsarin motsin bayanan. A hankali fuskar Rayyern ta sauya daga wannan nutsuwar da take kanta zuwa wata irin mamaki, kafin a mamakance ya ɗaga hannunsa ya rage sautin screen, sannan ya buɗe wani sashe da zai nuna masa duk wanda ya shiga cikin tsarinsa. Da farko babu suna, sai alamar UNKNOWN USER, don haka ya ci gaba da bin hanyar. A karo na farko tun bayan da wannan kutse ya fara, Rayyern ya zauna sosai ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan abin da yake gani. Ya sake buɗe hanyar da aka bi, ya kwatanta ta da irin tsarin da yasan Ajmaal dashi, sannan ya sake kallon wasu ƙananan alamomin da ya gani, kafin ya yi murmushi mara sautu ko kadan domin kai tsaye har ya gano ba Ajmaal ba ne. Ya ci gaba da bin sawun bayanan ya duba yadda mai kutsen yake shiga, ya duba yadda yake guje wa wasu security layers nashi, ya duba inda yake taɓawa, kafin wani ɗan murmushi ya sake bayyana a fuskarsa.

“Da farko na ɗauka Ajmaal ne…” Ya fadi a bayyane wanda ya saka Mark saurin kallonshi da fadin, “Ba Ajmaal bane to waye?” Wani shiru yayi tare da komawa yana jingina jikinsa da jikin kujerar da yake zaune wanda ya saka Mark saurin janyewa daga rankofon da yayi a saman sa, yana mai nazartan system ɗin, wanda ya saka shi ɗan saurin dago kai yana kallon Rayyern din. Don ganin koma waye makutsin kai tsaye ya gano inda suke zaune yanzu haka.... "Boss!" Mark ya ambata sunan Boss din nasu amma yana saurin daga masa hannu da alamar gimtsewa alamar baya son jin komai, wanda ta saka Mark sake kallon Rayyern din da ya wani lumshe kyawawan fararen idanunsa.

“Boss!”

Ya sake furta sunan amma Rayyern ko motsi bai yi ba bare ya saka ran zai bude idon.

A daidai lokacin kuma tuni har waɗan da aka bama bayanan sun iso inda aka faɗa musu, wasu jiga jigan jami'ai aka turo fiye da mota biyar. Wanda a kuma daidai lokacin ne Mark tare da Tiger da bai jima da dawowa ƙasar ba suke sake kutso kansu cikin lafiyayyen control room ɗin da Rayyern ke zaune. Suna sanar masa da cewar lallai suyi gaggawar barin gidan nan don jami'an nan suna daf da cimmusu. Wani irin lalataccen murmushin daya kan jima baiyi irin saba Rayyern ya saki tare da kallon agogon hannunsa. Daidai lokacin da Tiger tare da Mark ke cewa “Muyi gaggawar fita Boss?” Wani miƙa Rayyern yayi tare da ɗaga kansa sama yana busa hayaƙin cigarette nashi daya kunna a natse. “Mun riga mun fita.” ya furta cikin wani irin deeply voice. Ya miƙe tsaye tare da daukan glass cup ɗin dake gabansa, sannan ya fara tafiya cikin nutsuwa kamar babu abin da ke faruwa. Kai tsaye yana nufar parlourn kasa, “Gidan da suka gano ba shi ne inda nake ba.” ya faɗi a dake lokacin da yake daf da karasa ficewa daga room ɗin, wanda ya saka su Mark tsayawa cak. “Amma Boss, duk bayanan sun nuna anan ne!”

“Na sani.”

Ya furta yana juyawa ya kalle su da cewa “Na san nan din suka nuna” Ya ɗan yi murmushi “Saboda na bar su su gano shi din ne dama” yaci gaba da tafiya yana sake faɗin. “Wani lokacin idan kana son ka ɓoye gindayar da wani, ba ka ɓoye shi ne a inda ba za a same shi ba. Kana sa su same ka ne a inda kake so su fara neman.” Daga haka ya fita yana barin su a kame....

A lokacin da jami'an tsaro suka isa wurin da Babyboo ta ba su, sun tarar ne babu kowa a ciki sai dai akwai wasu kayan aikin da aka bari a wurin, files, na'urori da kuma wasu ƙananan alamomin da suka tabbatar musu cewa tabbas inda aka basu tabbacin suka iso. Ɗaya daga cikin jami'an ne ya yi saurin kiran shugaban tawagarsu yana cewa, “Sir, the place is empty.” A ɗayan ɓangaren mai ƙiran kuwa wanda yake zaune yana sauraron rahoton, ya ɗan rufe idanunsa na ƴan daƙiƙu kafin a furta. “Empty?” “Yes sir.” Jami'in ya fadi wanda ya saka wanda ke kan layin datse ƙiran nasa...

*KIND DADA*

Ɗaure da sky blue bathrobe yafi to sanye a jikinsa daga bathroom nasa, bayan ruwan daya sakarma kansa kai tsaye yana nufar Inda Red wine nashi dake zube a glas cup, farar fatarsa da wannan murɗadden jikin na cikakken ƙarfaffan namiji da hutu ya gama ratsa sai kyalli take... Tsayawa gaban mirror yayi yana goge gashin kansa da ƙaramin towel ɗin dake rike a hannu sa. Kafin ya ɗan ja idanunsa ya lumshe daidai da lokacin da yake cilli da mini towel din dake rike a hannun nasa da fesar da wani numfashi mai zafi yace.

"Sai dai jikina ya bani haka something is wrong. Amma sai ban ɗauki abin da wani muhimmanci ba, bisa tunanin cewa waya isa yaja dani? Sai dai irin wanda na kawo a raina sam ba mace bace.... " KIND DADA ya faɗi a wani irin zafe tare da kai ma iska naushi... Domin tun a lokacin daya fara fahimtar cewa wasan da yake tunanin Ajmaal ne kaɗai ke buga masa, ya samu wani sabon ɗan wasan da bai shirya zuwansa ba. Kuma abin da ya fi ba shi mamaki ba wai yadda Babyboo ta kutsa kanta cikin tsarinsa ba ne. Abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda ta gano inda yake cikin lokaci kaɗan, sannan ta miƙa bayanin wurin ga jami'an tsaro ba tare da jin tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo ba, kai tsaye wayansa dake ring ya nufa yana amsa call din, Mark ne mai ƙiran don haka ya kara wayan da kunnensa yana faɗin "Yes!" Sai da Mark yayi wani ɗan shiru kafin ya iya budar baki yace. "Sunanta Sumayyah amma anfi sanin ta da Babyboo, diya ce ɗaya tal ga Mr president Ibrahim Hashim. Kuma ita ce wace Sameer zai aura nan bada jimawa, and tana aiki a ɓoye tare da kungiyar DSS 1 years kenan da fara aikin nata, kuma tayi amfani ne da bididdigin data sanyawa Ajmaal har ta gano kiran da kuka yi da wannan tayi amfani wajen haƙo inda muke, a takaice dai Babyboo ta bi sawun Ajmaal ne har ta same inda muke, Boss mai ya sa kabar musu wannan hanyar tun farko? Boss a wasu lokutan fa dole idan ana gudu a ringa ƙoƙarin ɓoye sawaye...." Mark ya kai ƙarshen maganar nasa da sauƙe ajiyan zuciya, sai dai shiru dif din daya ji ne ya saka shi saurin kallon wayar da kuma duba wurin kiran, sai dai abinda idanunsa suka nuna masa ne ya saka shi tsaiwa kawai yana bin wayar da ido, ganin 5 second kenan da datse ƙiran da Rayyern ya masa. Wata numfashi ya sauƙe saurin yaransa dake parlourn na binsa da kallo, don duk sun ji komai sun kuma fahimta ya jima da yanke masa wayar.

A ta bangaren Rayyern kuwa tun da ya datse ƙiran ya nufa clothes nashi domin shiryawa. Kai tsaye ya fito sanye cikin guntayen fararen riga da wando mai kirar kamfanin Dior. A natse ya sawo kansa cikin parlorn da har lokacin su yaransa ke tsai tsaye, a wani irin ƙasaitance ya kai zaune zama irin na sarauta saman daya daga cikin Royal chair ɗin dake jere a parlourn, binsa da ido wannan samudawan suka ci gaba dayi har sanda ya fara sarrafa system nashi dake ajje a parlourn. Cikin wani irin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin A/cn na ratsa ko ina na parlourn, duk yadda suke ta faɗin "Boss good morning, Boss good morning" Amma ko kallo basu ishe shi ba. Su kuwa ganin komai bai ce game da batu akan Babyboo din bane yasa suke masa wannan kallon, saboda ba tun yau suke tunanin cewa anya Boss din nasu cikakken mutum ne kamar kowa kowa? duba da cewar shi murɗaɗɗen mutun ne da baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa. Kullum cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, shin wacce iriyar zuciyace gare shi sammm baya tsoron kowanne kalar hadari?. Saboda yayin da kowa ke gudun faɗawa wani hadari ko to shi tunkararsa yake shi yasa ake masa laƙabi da mutum mafi haɗari, barin ma yanzun daya juye ya zama makiyin ƙasar baki ɗaya. MARK daya fi kowa tafiya da yin zurfi a tunanin Boss ɗin nasu ne yay saurin kallonsa, ganin Boss In nasu ya daga masa hannunsa ɗaya, da wata shegiyar alama tare da sakin wani irin killet murmushin gefen baki tare da faɗin...

"A barta taci gaba da buga wasan da dukkan alama zai yi armashi, zai kuma kawo nishaɗi, domin mu nazari muke da ƙwaƙwalwa karku manta!, sadaukai ne mu tamkar mafarauta!, ba'a taɓa nasarar yaƙi sai in da mayaƙa, don haka ina son a buga wannan game ɗin tare dani" Wani mugun waro idanu suka sake yi suna bin boss in nasu da kallo. Lallai yanzun suke sake tabbatar da cewar Boss din nasu rigimarsa yawa gare ta da ɗaukar abu me muhimmanci da rashin sa, sam baya tsayawa tuna abinda zai iya zuwa ya dawo,in banda taryan Aradu da ka taya ma zakace a bar yarinya taci gama da buga game da kai? buga wasa akan mutanen dake farautar rayuwarka fa ake magana?. Sune kalaman da da Gimba ya shiga nanatasu cikin zuciyarsa.... Sai dai kalaman uban gidan nasu ya sake dawo dasu ne daidai lokacin da yake gyara zamansa a ƙasaitance ya ɗora da faɗin.

"Idan abokin karawa ya fimu kaifin basira iya iwarka ka nuna masa baka da wayo, to anan ne abokin karawarwar zai baje duk wata kaifin basirarsa don gwabzawa da kai...." Wata iska mai zafi ya hurzar daga cikin bakinsa kafin ya ɗora da faɗin.

"Koda wasa kada ka yi gaggawar nuna masa cewa ka fahimci dabararsa bare inda ya dosa ,wani lokacin mafi girman hikima ita ce ka ɓoye irin ƙwarewa da basirarka, ka bar shi ya ɗauka cewa bai da wani abin tsoro a gabansa. Domin idan ya yi tunanin cewa ka fi shi wayo, zai yi taka-tsantsan ya ɓoye maka komai ne. Amma idan ka bar shi ya yarda cewa kana bayan sa ne da tunani, to a nan ne zai saki jiki, ya buɗe dukkanin ƙofofin dabarunsa, ya kuma fito da duk wata kaifin basirar da yake jin yana da ita domin ya gwabza ɗin tare da kai. Saboda a wasu lokutan ba lallai ne ka doke abokin karawarka da ƙarfi ba, abin da kawai kake buƙata shi ne ka bar shi ya yi tunanin cewa shi ne yake jagorantar wasan, alhali kai ne kake kallon kowace ƙafa da yake ɗorawa, kana jira ne kawai ya kai kansa inda kake son ya je. Wannan shi ne sirrin mutumin da ya san cewa nasara ba koyaushe take buƙatar ka nuna abin da ka sani cikin gaggawa ba, wani lokacin kana buƙatar ka yi shiru, har abokin karawarka ya yi amfani da dukkan basirarsa… har sai basirarsa ita kanta ta zama hanyar da za ta kai shi gare ka.... "

Daga haka tsam ya miƙe yana barin musu parlorn cikin tafiyar nan na ƙasaita da kuma izzar da yake da ita zuwa compound na gidan saboda fitan da yake son yi.... Tun kafin ya iso bodyguard nashi dake compound din suka mimmike tsaye da manyan bindugu rike a hannunsu, su Mark na maro masa baya. Cikin abinda bai zarce kiftar ido ba wani guard buɗe masa ƙofar motan, a natse ya kama marfin motar ya rike yana mai kare musu kallo kafin ya shige motar kuma cike da izza.... Tare da kallar Mark da bashi cikakken umarnin kai tsaye ta hanyar cewa. “Ba na son a bi ni da yawa.” Mark ya ɗan yi mamaki don haka ya bude baki da furta. “Boss…” Sai dai bai bashi ko wacce iriyar dama ba ya katse shi ta sake furta “Motoci biyu kawai, sauran su zauna.” Daga haka ya faɗa motar sukayi reverse suna barin compoun din. A lokacin da motocin suka yi reverse suka soma tafiya Rayyern ya jingina da jikin kujerar baya, idanunsa a kan titin dake gabansu. Mark ne ke tuƙi a natse kafin cike da taka tsantsan ya kalla madubin motar. “Boss, kana ganin Ajmaal ya fara fahimtar abin da yake faruwa kuwa zuwa yanzun?”A fisge Rayyern ya ɗan ɗaga idanunsa ya kalla Mark din kai tsaye. “Ajmaal ba mutum bane kamar sauran mutane. Idan ya tashi nasa aikin yana farawa ne da haɗa abubuwan da mutane suka yi shekaru suna ƙoƙarin haɗa su shi ya kan haɗa su ne a cikin kwana ɗaya kacal.” Wata numfashi Mark ya furzar kana yace. “To, hakan ba zai iya zama matsala ba?” Mark ya tambayar, wanda ya saka Rayyern yin ɗan wani murmushi. “Matsala ce idan ya gano abin da bai kamata ya sani ba kafin lokacin da ya kamata ya sani?.” Ya ɗan kalli mirrorn motan da ci gaba da faɗin “Amma idan ya gano shi a lokacin da nake so… to, zai iya zama amsar da nake jira ce.” Daga haka Mark yaja bakinsa ya kulle bai ƙara tambaya ba. Don ya san cewa idan Boss ɗinsu ya yi irin wannan maganar mai harshen damo akwai wani abu da ya riga ya shirya, ko da kuwa shi kansa bai san cikakken shirin ba. Daga haka kuwa ya koma yana lafewa cikin kujerar motar luf don ya san cewa Ajmaal ba irin mutanen da za su tsaya a wuri ɗaya ba ne. Idan ya fara neman amsa, zai ci gaba har sai ya sami wata ƙofa ne, ko da kuwa ƙofar tana bayan wani sirri ne mai haɗari saboda shi din malamin sa ne, wanda yasan kowanne irin motsin da dalibinsa zai iya yi ya kuma fahimta nan take. Kuma shi kansa Rayyern ya san cewa Ajmaal yana da wani abu da ya bambanta shi da sauran jami'an su a wancan lokacin.

“Ka da ka manta sunana Ajmaal,”

Ya tuna da hakan Ajmaal ke yawan maimaita masa a duk lokacin da yaga zai iya ruftawa wani rami, sake dan lumshe idanunsa yayi, “Wani lokacin ja da baya ba gazawa ba ne ko gajiyawa. Wani lokaci ja da baya shi ne ka ba wa kanka damar ganin inda za ka taka.” ya sake tuna hakan idan ya dage sai yayi wani abu shi kuma ya hana mishi yin wannan abun, saurin kawar da tunanin hakan yayi yana bude idonsa dai dai lokacin da suke isowa inda suka nufa.

“Boss, akwai wani abu da ya kamata ka gani.” Tiger ya fadi daidai lokacin da suke karasa shigowa inda suka zo, Rayyern ya ɗan yi shiru cikin nutsuwar da kowa ya saba gani saman fuskarsa, kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa dashi. Hankalinsa gaba ɗaya ya tattare zuka kan kallon iPad din dake hannun tiger yana kallar abin da ke saman screen na iPad din, yatsunsa na motsi a hankali, kamar wani abu mai muhimmanci yake shiryawa. Sai dai a zahiri, dukkaninsu sun san cewa akwai wani batu dake damunsa, musamman da yake tun da suka dawo daga ɗakin da aka killace Sameer da Zayed, bai sake cewa komai ba. Mark ne ya fi kowa fahimtar irin shirun da Boss ɗinsu yake yi a irin wannan yanayin, shi ya sa ya ɗan kalli Gimba, wanda shi kuma ya ɗan ɗaga kafaɗarsa, like kawai mu bar shi. Saboda sam ba abin mamaki bane wannan ɗin daga cikin ire iren halayen Rayyern Khalid din. Mutumin nan yana da wata irin dabi'a da ke sa ka kasa tantance lokacin da yake cikin nishaɗi da lokacin da yake shirin aikata wani abu mai girma. Yana iya zama cikin tarin mutane, amma tunaninsa ya kasance a wani wuri dabam. Yana iya yin murmushi a lokacin da kowa ke tsammanin ya kamata ya fusata, ya kuma yi shiru a lokacin da kowa ke jiran jin muryarsa. Amma abin da ya fi ba su mamaki shi ne yadda yake kallon haɗari. A lokacin da sauran mutane suke neman hanyar tsira daga gare shi, shi kuwa sau da yawa yana neman hanyar da zai kusance shi ne. Wanda a zamaninsa na lokacin da yake matsayin jami'in DSS, ba kasafai yake son sanya kariyar da sauran jami'ai ke amfani da ita ba yayin da suke fuskantar hatsari. Ba wai don bai san muhimmancin san ya kariyar ba ne, sai dai yana da wata irin amincewa da kansa wadda wani lokacin take sa abokan aikinsa su ji tsoronsa fiye da abokan gabar dake gabansu. Yanzu kuma, bayan ya juya wa ƙasar da ya yi wa hidima baya, wannan dabi'a tasa ta zama ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa aka sanya shi cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo. Gimba ya ɗan sauke numfashi, yana kallon yadda Boss ɗinsu ya ɗauke kansa daga kallon bayanan da ace ya kamata ya tsaya ya nutsu ya kalla... Daga ƙarshe ka abinda ya kawo shi wurin yayi zuwa sha ɗayan safe har sun bar wurin, bayan sun sake biyawa ta wani wurin daban.

Safa da marwa kawai yake famanyi a karo na babu adadi ke nan sai yana dab da cimma burin sa, tun a wancan lokacin sai wannan dan jarabar yazo ya ruguje masa shi, yayi duk wata muna kisa, sunbi ta karkashin ƙasa ba tare da barin irin kowacce kofa ba sun ha'ince shi, sunci amanar sa a tunaninsu shikenan ƙarshensa yazo, ashe ba haka hasalin wasan take bai. Baki ɗaya ya gama jigata kansa gumi sai kwaranye masa jiki yake. Dama yasha ce masa shi jan zaki ne maganin abokan gaba, kuma shi daji ne wanda ba'a yi masa kyau re, haka yasha ce dashi shi hadarine malafa ga duniyar kenan, babu wanda ya isa ganin bayansa ko sanin inda ya dosa... Wani kalan ihu yayi tare da toshe kunnuwansa duka biyun da karfi yana mai furta. "Inaaaaaaa hakan ma bazai taba yiyuwa sammmm! Dole ni ne game over a wannan wasar kamar yadda na faro" Ya faɗa da ƙarfin masifa haɗi da dakar table ɗin dake gabansa.

"Dole na dakile duk wata hanyar da nasan wannan ɗan shegiyar yaron da nasan zai ganni, kafin na gama samun mafita" K Mashi ya faɗi wanda tun da Rayyern khalid ya bayyana a matsayin Kind Dada hankalinsa yake a wata irin tashe. Ya masa ababuwa da yawo a cikin rayuwa ciki kuwa harda kawar dashi ya maye gurbi da kuma matsayinsa....

*10:00 pm*

Tun da suka dawo ya shige room nasa babu wanda ya sake ganin ko gilmawarsa, wanda sai a wannan lokacin yake sakkowa inda kuma yake sakkowa rike da systems ya sakko har guda biyu, da kuma AirPods Pro ɗin dake makale a kunnensa. A natse ya ajje system ɗin kan table ɗin da dake gabansa, wanda indai zai fito nan ne kawai mazauninsa. Ta farkon ya soma buɗewa kafin ya kunnan ɗayar itama, yana dan karkata fuskan system ga Tiger dake tsaye daga bayansa shi da Mark. Cikin system ɗin hoto ne guda uku, dukan su kuma babu haske sosai a cikin su. Inda na farko hotan Macece tare da namiji sai dai shi namijin ya juya bayansa ba’a ganin fuskarsa sai kayan da ya saka da kuma bayansa. Na biyun kuma hotan building ne, shi ba full ba shi ba incompleted building ba. Mai ya tuna kuma ya wani taune gefin lips nashi kaɗan ba da yawa ba, yana wani hade girar sama da ƙasa kamar mutumin da yake cikin hoton ne aka ce masa tsaye a gabansa.

“Again and Again….” Sune kalaman da Tiger tare Mark suka fadi suna sake nazartan pisc in, wanda ya saka shi ajje waccen yana jayo ɗayar itama ya buɗe wani file yana nuna musu. Sai da suka gama karanta abinda yake ciki suka koma suna kallar sa, yaje da nufin kife system ɗin ne wani pisc mai ɗaukar hankali ya bayyana wanda ya saka su Tiger saurin dauke kansu daga pisc din, ban da shi daya wani kalan kurama pisc din ido sosai ko blinking ba yayi, kafin idanuwansa su wani kalan sanjawa take suna rinewa wanda cikin kankanin lokaci baki ɗaya halittar jikinsa ra fara sanjawa wanda Mark yay hanzarin saka hannu da nufin janye system ɗin, a wani irin zuciya kawai ya mike yana shakar wuyarsa idanunsa jajir.....

Babyboo

At the end take tsaye gaban madubi tana conferring idanuwanta da take kalla ta jikin mirron da take tsaye. Ta gana shirin ta tsaf cikin wata doguwar ash abaya wacce ta sirka brown sosai. Babu ko powder a fuskanta bare makeup, harta lipgloss na mata babu, sai dai skin nata dake daukan idon mai kallonta babu ko digob tabo. A natse ta nufi IPhone nata ta ɗauka daidai lokacin da kira ke shigo mata, dama tayi zatan hakan kuma bata sake gasgatawa ba har sai da ta ga mai ƙiran ko wanene shi. "Mai yasa zaki kutsa kan ki a cikin ramin daya kasance na zaki ne? Waya baki umarnin abinda kika aikata uymmm why Boo..." Kai tsaye abinda aka fadi kenan a cikin wayan wanda ya saka Babyboo sakin wani dan banzan murmushi tare da daidai tsaiwar ta tace.

"Yayinda Zaki ya kasance mayunwaci yunwarsa batasa yaci zakanya koda yunwa zata kashe shi. Don haka bari a tantance jarumtakar, ina son ka ringa tuna cewar wani lokacin ja da baya sam ba gazawa bane bada ƙafa neeeee..... BABYBOO I'm back...."

Kit daga haka ta datse ƙiran tana wani kalan juyi wata shegiyar murmushi ɗauke saman kyakkyawan fuskanta..

BY AMMEY LAYLERH ✍🏻

One Love Masoya AMMEY LAYLERH........🫶🏻❤️

***

༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺

Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️