Page 23&24
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Wani irin shiru ne ya mamaye duka ilahirin parlourn gaba ɗaya tun bayan damkar da Rayyern yama wuyan Mark. Da wani irin ƙarfi yake rike da wuyan Mark ɗin , wanda tsananin tsoro da wani irin firgici ne yazo ya mamaye duka yaransa dake parlourn. Tiger kuwa cak ya tsaya yana kallon Boss ɗinsu wanda zuwa wannan lokacin idanunsa suka sake sauyawa gaba ɗaya, sun yi wani irin ja sakamakon abinda ya jima yana binne shi a cikin zuciyarsa ne ya fito masa a lokaci guda. A wahalce Mark ya buɗe baki yana ƙoƙarin ganin ko iska ce ya samu ya shaka ko ta baki ne, yana saka hannayensa da nufin rike na Rayyern da ke riƙe da wuyansa, amma Rayyern bai ko motsa ba. Idanunsa kuma har lokacin suna kan hoton dake saman screen ɗin ne kawai. Matar da ke cikin hoton tana tsaye ne fuskarta ɗauke da wani amintaccen murmushin da har yau bai taɓa sake ganin mai irin wannan murmushin ba, murmushi ne irin na masu tsananin hakuri, biyayya da fawwala ALLAH dukka lamura, a tsaye aka mata hoton wanda shi da kansa shi ne yayi sa, wannan tsayuwar, wannan kayan… yadda ta rufe gefen fuskarta da nufin ita fa bata son hoton, ga matashin yaron cikin ta nan a jikinta daya mata kyau, so yake ya janye kansa daga kallon hoton amma yana gazawa komai na shirin dawo masa da wani sashe na rayuwarsa da ya yi shekaru yana ƙoƙarin binnewa. “Boss…” Mark ya furta cikin wahaltuwa da son ya dawo ainihin nutsuwa da hayyacinsa sai dai sun san hakan abune mai matukar hawaltuwa. Ɗan lumshe idonsa hoton komai na dawo masa daram kamar ana yaki, da ido Mark yama tiger wata alamar da tiger ya wani karyar da wuyansa gefe kamar kiftar ido ya ɓace ɓat a wurin. Babu jimawa sai gashi ya dawo hannunsa rike da allurai guda biyu. Kuma har zuwa lokacin Rayyern na rike da Mark jikinsa na tsananta rawa jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada, sauran yaran kuwa na ganin allurar da Tiger ya dawo da ita har guda biyu ne ya saka su kallonsa sosai suna shirin magana amma ya dakatar dasu, yana salallaɓowa ta baya ya samu gefen wuya da wuyan Rayyern duka biyun ya soka masa alluran tare da juye ruwan a jikinsa. Wanda jin an soka masa allurar ne ya saka Rayyern wani juyowa a fusace yana jifa da Mark ya damko Tiger ya cira ya buga da ƙasa. A wahalce Mark ya taso yana layi yana komai sake nufar sa da kama damatsen Rayyern din duka biyun ya matse, sosai suka shiga kokuwa dai nan allurar ya fara dibarsa ya wani fara lullumshe idanu yana shafar wuyansa. Kafin yaja wani numfashi yana yin baya idanunsa daya fara gani bibbiyu naci gaba da bin hoton da ido. Hannunsa ya miƙa daidai lokacin da yake zubewa suna saurin nufar shi da nufin tarosa ya watsar dasu duk da yadda allurar Penta din da suka masa ta fara dibarsa, gashi har biyu suka masa. A hankali idonsa ya tsaya cak akan hoton dake saman system ɗin, tare da miƙa hannunsa da ya zama kamar dutsi dan nauyi ya taɓa gefen screen ɗin da yatsa ɗaya kawai, kafin cikin wata muryar da ko sautin komai babu ya ambaci kalmar “MAIRAH!…” Idanunsa kuma daga nan suka rufe ruf allurar ta soma gudanar da aikinta a jikinsa, da wannan sunan da wani irin raɗaɗin da yake jin kamar zai tsaga kirjinsa ya fito ya dena gane komai. Sunan ya fito daga bakinsa kamar kalmar da ta daɗe tana jiran wani ya sake furta ta. Tiger ne ya kalli Mark dake shafar wuyansa shi kuma idonsa na kan Boss ɗin nasu, janye system ɗin yayi yana sake ma kansa kallon hoton sau ɗaya shima, saboda da hoton dake da wata irin nutsuwa a fuskar matar, kyakkyawa ce cikin ajin farko cikin yanayin dole zai saka mutum tsayawa ya kalleta na dogon lokaci ba tare daya gajiya ba. A natse ya sake adana hoton ya bashi tsaro na musamman.....
Yana sake mayar da dubansa ga Boss din nasu. Wanda har zuwa lokacin babu wani abu dake motsi daga jikinsa, sai iyaka idonsa dake bude kafe a wuri guda, ahankali kaɗan can kasa sosai numfashinsa ke fita bayan tsananin kokawar da jikinsa ya yi da tasirintuwar allurar. Wanda in bama cikakken mai nazarta bane tsaf ma za kayi tunanin cewa a sume yake. Mark ne ya kalla tiger da cewa. “Ya suma ko?” Yay zan cen yana sake kallon Rayyern dake zube. Kai tsaye tiger ya matsa kusa da shi yana duban fuskarsa da kyau. Sai ya ɗan sunkuyar da kansa yana saurarar numfashinsa da bugun zuciyarsa kafin ya miƙe. “Mu ɗauke shi.” kawai ya furta ba tare daya bashi wancen amsar ba. Biyu daga cikin yaran sane suka ƙara so ɗaya ya kama kafafunsa, ɗayan kuma ya sunkuya da nufin ɗago kafaɗunsa. Sai dai kafin su samu damar ɗaga shi sosai yay wani irin motsi mai ƙarfi ya taso daga gangar jikinsa. Wanda ya saka Mark tsaiwa cak yana kallonshi na wasu ƴan daƙiƙu, kafin ya sauke numfashi a hankali. Domin ko shi kansa bai yi tsammanin abin da yake gani ba. Saboda allurar farko kaɗai ita yaci ace ta fara kwantar da shi zuwa wannan lokacin, amma ga shi har yanzu jikinsa yana ƙoƙarin yaƙar tasirin maganin.
Hannunsa ne ya sake motsawa kaɗan, tare da ƙoƙarin kamo ƙasan teburin da ke kusa da shi, yana ƙoƙarin samun abin da zai riƙe ya mike, amma babu damar hakan sai ma numfashinsa daya ƙara nauyi, jijiyoyin wuyansa suka sake bayyana rudu rudu, yayin da idanunsa suka sake yin ja fiye da farko. “Boss...” Tiger ya kira sunan yana kokarin sake nufar sa amma Mark ya daga masa hannu da faɗin.
“Kar ka kusance shi.”
Saboda ganin duk yadda maganin yake yaƙar jikinsa, amma dan bala'in yaki barin hakan ya faru cikin sauƙi, duk da sun san cewa Rayyern har yanzu ba ya cikin cikakken hayyacinsa, ta baya tiger yama daya daga cikin yaran inkiya daya zaga, aikuwa ya zaga din yana shirin kama shi babu zato kawai sai ganin sukayi ya damƙi hannun yaron da ke ƙoƙarin kama shi, ya wani irin murɗe shi da wani irin ƙarfi wanda ya sa yaron ya saki wani ƙara yana kokarin ja da baya. Kafin kowa ya fahimci abin da ke faruwa, Rayyern ya buɗe idanunsa da yake jin sun masa wata wani irin nauyi, jajayen jijiyoyi kwance a cikin idanun amma a cikinsu akwai wata irin tsananin fushi da taurin ran da ba wanda ya yi tsammanin har yanzu zai iya nunawa, sam kuma ko kaɗan basuyi mamakin ganin allurar bata gama daukar saba. Wani irin yunƙuri Rayyern yayi duk da cewa jikinsa bai gama bashi hadin kai ba wajen tashi, cikin dabara yaron ya samu ya janye hannunsa yana ja da baya cikin gaggawa. A matukar jigace Rayyern ya ɗago fuskarsa idonsa na sauka kan screen na system nashi da nufin sake kallon hoton, sai dai wayam babu ma system ɗin a inda ya barta. Baki da sautin muryansa na dagulewa da wata irin nauyi ya sake furta sunan.
“MAIRAH...”
Ya sake furta sunan a karo na biyun da babu ƙarfi ko kaɗan, muryan cike da wani irin raɗaɗi da ɗacin da yake jen kamar wuta ce aka cinna daga cikin tsakiyar kirjinsa. Su duka kansu suka sake risinarwa suna sauƙe idonsu ƙasa. Daidai lokacin da Rayyern ke sake ƙoƙarin tashi a kan gwiwwowinsa, amma gangar jikinsa ta kasa ɗaukar nauyinsa, ya sake komawa baya yana shirin faɗuwa. Kamar kiftar ido haka Mark ya sake nufar sa yana talleshi a jikinsa don gudun kada kansa ya bugu da rose flowers ɗin dake bayan nasa. Wani irin kallo Rayyern yama Mark din da idanunsa da suka sake haurewa ssaboda maganin da yaci gana da ƙoƙarin kashe hayyacinsa, amma har yanzu akwai wani abu mai ƙarfi a cikin idanunsa. Sannu a hankali jikinsa ya sake saki yana shikawa amma bai dena kananun motsi ba “Har yanzu yana yaƙar maganin.” Mark ya furta Rayyern din rike a jikinsa, wata yawu Tiger ya hadiye shima yana kallar yadda Penta ɗin ke sake yakarsa. Cike da kamar duban mamaki tiger ya sake kallar Rayyern da faɗin “Penta har biyu fa! Amma ta kasa ɗaukarsa lokaci guda...”
Domin ko a yanzu da yake ganin yadda jikin Boss ɗin nasu ke karkarwa, ya san wannan ba irin ƙarfin da ake gani a wajensa ba ne. Sun san Rayyern. Sun san irin abin da jikinsa yake yi idan aka yi ƙoƙarin kwantar da shi da ƙarfin tuwo, amma har yanzu abin da suke gani a wannan lokacin ya wuce abin da suka saba gani. Tiger ne da kirar jikinsa ba ɗaya da Mark ba ya sunkuya kawai ya ɗauki Rayyern din ya saba a kafaɗar sa yana yin saman shi da shi....
A ɗayan ɓangaren kam Babyboo har yanzu tana tsaye a gaban madubi, wayarta a hannunta bayan ta datse kiran. Murmushin da ke saman fuskarta bai ɓace ba, amma idanunta sun sauya. A natse ta sake duba wayarta, sannan ta buɗe wani ƙaramin file da ta adana tun kafin ta aika da coordinates ɗin wurin. Sake kallon bayanan da ke ciki tayi da furta... "RAGAYAR DUTSE KENAN...." tay maganar da wani murmushi mai kyau ɗauke saman fuskarta da sake faɗin "Yanzu za'a fara sabon wasan..." tana mai sake kallon kanta a madubin tare da ɗan yin tsam a ranta ita kaɗai a cikin zuciyarta take ayyana. 'Yanzu idan abin da ta gano game da Rayyern ya kasance tarko ne ya zanyi?.....' Tayi maganar daidai tana karasa fita daga bedroom nata baki daya zuwa bangaren Mahaifinta....
NADIYA...
Alhmdulillah sosai jikin Nadiya yayi sauki fiye da duk tunanin mai tunanin saboda bata da ƙan jiki ko kadan. Shi yasa ma cikin abinda bai wuce sati biyu ba ciwon dake ƙirjinta ya kame, yanzu ita ke yin komai da kanta sai dai fita ne kawai da har yanzu bata fara ba, amma alhamdulillah komai ita ke yi wa kanta don har Yaya Sadiya ta koma gidan ta wacce ta haihu kwana biyar da suka wuce. Kuma washe garin data haihu sai da taje, tun daga ranar da Ya Aliyu ya tafi bai sake dawowa ba gashi babu waya a hannunta babu kuma number nashi a gurin ta. Indo kuwa masifa tayi masifa tsanani yayi tsananin da sai data gudo daga kauyen da take aure ta bar musu yaron ta. Yayin da ita Yaya Sadiya bayan komarta abin yazo mata da sauƙi kasancewar a yan kudaden da Aliyu ke basu ta samu ta tsira dana yar sana'ar data fara na saida fara da kuma aya mai shuga. Gashi ita dama surukuwarsu in dai kana da kuɗi to babu ruwan ta da takura maka inda zaka ringa bata na koko da kosai to an wuce wurin.
Zaune suke a farfajiyar cikin gidan nasu daga wajen karkashin bishiyar mango ɗin dake tsakar gidansu. Cike da nishadi da kwanciyar hankali suke labarinsu ita da Mahaifinta cikin kulawa, ƙauna da kuma soyayyar juna, wanda kana gani kasan ba sai an faɗa maka uba da ƴar na ƙaunar junansu kwarai da gaske. Sallamar ɗan uwan Mahaifinta Baffa Isiye ce ta saka firan nasu dakatawa cak, yana bambami ya shigo gidan. "To wllh ni dai da rai na da lafiya na ba za'a daura min ciwon zuciya da hawan jini ba, wato ma Auwalu kai har damar zaman fira da dariya ka samu da wannan tambadaddiyar yarinyar kenan? Bayan ƙasan irin masifa da jafa'in dake gabammu na me gari?. To wllh gashi can ya haɗa gangami yace tun da bazaku faɗi inda ɗan sa yake ba wllh ya a cinnawa gidan ku wuta. To nidai wllh zuwa zan yi nace masa babu hannuna a ɓatan Shitu ɗan sa ni na gaji da masifa da bala'in da Nadiya ke janwo mana a cikin wannan gari.... " tun da ya fara maganar ya bari numfashi ya shaka amma bai bari hakan ya faru ba sai da yakai har ƙarshen maganar nashi babu aya bare waƙafi. Tun kuma daya fara maganar Baba Auwalu yayi ɗif komai ya dena shiga da fita a cikin kunnuwansa. Gwaggo Talatu kuwa da tun farkon fara zance ita da Indo da suke can uwar ɗaka suna raba hali sukayi bukut suka fito, hannu Gwaggo Talatu aka take faɗin. "Na shiga uku ni Talatu wannan wacce irin masifa ce? Nadiya don girman Kur'ani ki faɗa masa in da ɗan sa yake tun kafin yasa a cinna mana wutar nan, kun dai san Mai Gari ba mutumci gare shi..." A hankali Baba Auwalu ya mike yana laluben hanya Nadiya ta mike tana kokarin nufarsa ya dakatar da ita. "Ki bari zanje nayi magana da Hallirun Nadiya...." Saurin kallon Baban nata tayi, kafin ta ce. "Amma Baba tayaya kake tunanin zan barka kaje inda Mai Gari yake kai kaɗai?..." Indo ce ta kalleta a tsiyace da ture hannunta daga na Baban tace. "Ke dalla Malama sakar masa hannu yaje, duk ba kece kika janyo masifar ba?" Kallo ɗaya Nadiya tama Indo din ta ɗauke kanta tana sake nufar Baban daidai da lokacin da hayaniyar mutane ta kaure ƙofar gidan nasu. Kafin kowa yayi wani motsi sai gashi sun faɗo gidan, wanda tuni Baba Isiye ya kama yar guntuwar katangar ya dira ta baya ya gudu. Fetur suka soma zuzzubawa a tsakar gidan ɗaya daga cikin mutane ya fidda ashana sai cilla, ɗaya daga cikin mutanen ne yayi caraf ya dakatar dashi yana nufar Mai Gari yace. "Ni a nawa tunanin mu canza shawara mana! Saboda in an kone gidan waye zai gano mana inda Shitu yake? Ka tafi da uban Nadiyan ka ɓoye, hakan shi zai saka Nadiyan ta faɗi inda Shitu yake cikin sauƙi..." Wata dariyar data saka jajayen hakoransa bayyana a fili Mai Gari yayi da faɗin. " Tabbas ka kawo shawara mai kyau Sule! Tanimu a fasa kunna wutar a tafi da uban bayan an debo duk wani dan jarin daya masa saura bisa asarar da aka saka mukayi ta feturin da muka sayo lita biyu..."
Wani irin tsuma da rawa jikin Nadiya ya soma yayinda Gwaggo Talatu suka sauƙe wata ajiyar zuciyar ganin sun tsira, su sam basa ma ta yadda akace za'a tafi da Baban bare hankalinsu ya tashi kamar yadda na Nadiya ya tashi. Wanda aka kira da sule ne ya isa ga Baba Auwalu babu tausayi bare imani ya kama hannuwansa duka biyun ya murde ya hade ta baya ya daure, a sukwane Nadiya tayi kansa tana kiran sunan Mahaifinta sai dai kafɗiya daya wannan mutumin ya mata ta kife suka ja Baba Auwalu suna barin gidan dashi. Anan Nadiya ta zube tana kuka har ALLAH ya kawo Baba Gaje tazo ta tafi da ita gidanta bayan ta tsigalle su gwaggo Talatun.
RAYYERN
Tun da suka kwantar dashi bai sake sanin ainihin inda kansa yake sai can wajajen sha biyun dare, kansa na masa wani mugun ciwo ya farka kai tsaye ya fara dayin wanka da dauro alwala ya fito. Sallah ya fara gabatarwa kana ya fita ta wani corridor mai tsawo na gidan, a kasalance yake taka kafafunsa wanda hakan ma don yana da karfin zuciya ne, don wasu allurar takan yi masu har kwanaki ukku ne bata sake su ba. Hannunsa ɗaya yana cikin aljihun wandonsa, ɗayan kuma ya ɗauki cigarette wacce bai kai ga kunna taba. Ya tsaya gaban wata babbar taga yana kallon duhun daren dake kewaye da daren don wata yayi nisa sosai, har zuwa lokacin babu abinda yake iya ganewa yana jin sane a sama kamar kan gajimare. Cikin kansa kuwa babu komai illa hoton Mairah dake sake bayyana a cikin kansa da kwakwalwar sa, abinda ke iya biyu bayan hoton kuma wasu memories ne masu dadi da rashin dadi. A bayan hakan ma abu biyu ne kawai suka fi makale masa a cikin kansa wanda kwakwalwarsa ta gaza mancewa. Mairah tana murmushi, Muryarta, Idanun nan masu kyau da ɗaukar hankali, da kuma wata ranar da ya daɗe yana ƙoƙarin yaga manta amma tunaninsa baya taɓa barinsa aikata hakan. "Ke kaɗai! Ke kawai nake buƙata MAIRAH, dududu mintunan ba za su wuce goma sha biyar anyi an gama an wuce wurin. So nake in ji ya naki ɗanɗano da ni'imar yake? Don nasan zakifi yayarki Mahira daɗi da ni'm.... Wani ihun ihu ya saki yana toshe kunnuwansa, duk yadda yaso ya manta, ya bisne, ya dena tado da hakan ba zai taɓa bisnuwa da boy uwar ba kuwa. Saboda wannan ɗin wani tsohon hoto ne na ƙwaƙwalwarsa da kamar da karfin tsiya aka cilasta shigar sa harma da wurin daya samu yayi babakere a cikin kansa. Da karfi Rayyern ya sake lumshe idanunsa. Yana son cilastama kansa mantawa da Mutuwar Mairah, duk da yasan ba abu ba ne da yaci ace ya manta cikon sauki haka ba, domin dama can ba abinda zai zo ya yi wuce bane kamar yin ruwa da ɗaukewarsa. Akwai wani abu da ya rage a bayan hakan, koma yace ababuwa, wasu ababuwan da suka taɓa shi fiye da yadda kowa yake zato a kafin hakan. Ahankali ya danne setin kirjinsa tare da sake lumshe idanunsa. Ahankali ya samu kansa da karanta adda'ar da take masa a duk lokacin da zai tsinci kansa cikin hali na bacin rai.... "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Rabbi inni magalubun fantasir³! Wa la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³....."
Haka kalmomin suka fito daga cikin bakinsa a hankali, amma kowacce kalma kamar tana son dawo masa da wata tsohuwar murya ce... muryar MAIRAH. A duk lokacin da take ganinsa cikin irin wannan halin, sai ta rungume shi a jikinta, ta bar shi ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ta fara karanta masa addu'ar. Shi kuma a lokacin bai taɓa tunanin wata rana zai zauna shi kaɗai yana maimaita kalmomin nata ba, sai yau, kuma a yau din babu hannunta a kansa. Babu rungumar da ta saba rage masa zafi da nauyin zuciyarsa. Sai shi kaɗai... da kalmomin da ta bar masa a cikin zuciyarsa. Sake maimaita addu'ar a hankali yayi, amma wannan karon idanunsa a rufe suke tamkar yana son ƙoƙarin yakar kansa ne tare da sake kamo farkon adda'an.
“Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir...”
Addu'ar daya sake furtawa kenan yana komawa da jikin window din ya jingina cigarettes din hannunsa na faduwa ta windows din tayi kasa. Ahankali tunanin daya jima da kulle kofarsa dake kokarin buɗe tsohuwar ƙofar daya riga da ya shafe tarihinta ya kulle da kansa da hannuwansa suka soma guduwa. Wani cijje gefen lips nashi yayi wani irin ƙuduri na taso masa da wutar ɗaukar fansa na dawo masa.
"Ina son RAYYERN KHALID ya ɓace a cikin duniyar nan bama iyaka rayuwata nake son ya bari ba! Ayi masa allurar mahaukata! wacce zata ƙarasa zarar dashi, kana a miƙa shi gidan yari ya kare rayuwarsa acan life in prison har ya mutu har gaban abada ban son sake saka shi a cikin DUNIYATA....Ta yadda ko ya rayu bayan haukan zai mance komai, ciki kuwa har da uban sa BATUREN ZABE.... " Haka ya tuna da kalaman K Mashi na ƙarshe, hakan kuwa aka yi suka banka masa allurar mahaukatan, bayan ita dake dama kusan duk jami'an nasu haushin sa suke ji suka ƙara masa da allurar Penda. Aka kama shi aka garƙame akan ana tuhumarsa da laifin kisa....
Wani dukan kansa yayi domin baya son tunawa da komai a yanzu. Kafin ya wani cije baki yana kaima iska naushi da faɗin. "Zan addabi rayuwarku! Zan zame muku masifa da bala'in da ku da kanku sai kun gwammace mutuwarku akan rayuwar da zan jefa ku a ciki ta wahala....." Ya furta hakan yana yin baya saboda yadda jikinsa bai gama dawowa gaba ɗaya ba..
BY AMMEY LAYLERH ✍🏻
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️