Page 25&26
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.
ꨄ Mark dake tsaye daga bayansa tun bayan shigar da yayi yaga yana Sallah yake tsaye daga bakin ƙofar, nufar sa yayi da kokarin taro shi amma yana watsar da shi, idanunsa da jijiyar kansa gaba ɗaya sun gama tashi. Yana dago kansa a wahalce da mayar da idonsa saman hannunsa, yana kallon yadda jijiyoyin jikinsa da suka kwanta ɗoɗar a ƙarƙashin fatarsa, suka yi wani irin ruɗu-ruɗu suna zana masa layuka manya da ƙanana. Kamar kububuwa haka yabar wurin inda kai tsaye ɗakinsa ya koma ko gani sosai ba yayi. Zuwa lokacin kuma babu abinda ke ci gaba da masa amsa kuwa in banda munanan munanan kalaman na God Father nashi, wanda kaf duniyar idan aka ɗauke uwa da ubansa bashi da abin koyi sama dashi. Wannan yasa ya zama God Father nashi ba tare da sanin muguwar irin aika aikar da yake aikatawa a ban ƙasa ba. A jigace ya kai kansa wani wurin da duk masifan kokkofinka baka isa cewa daki ko wurin ajiya na musamman ne a ciki ba.... "Ki min uziri, yau rana ɗaya kawai! rana daya ki bar ni in ɗanɗani zumarki MAIRAH, zan ba ki kuɗi na wadataki da duk wani jin dadin duniyar nan, zan miki gata da duk abin da Ƴa mace take da buƙata. Idan tsoron dodon mijinki Rayyern kike ina son ki sani yayi tafiyar da ba zai taɓa dawowa ba, domin babu tab..... " daidai nan, daidai wurin da ƙwaƙwalwarsa ta cake kenan ya gaza gaba ya gaza baya a cikin duniyar daya faɗa, wacce ya gammaci gwamma mutuwarsa shi akan dai zuciyarsa taci gaba da tunaso masa ire iren jerrin waɗan nan kalaman. Wani irin kakkarwa gaf gaf jikinsa ya shiga, wanda ya saka shi dukan cover ɗin daya gama budewa wasu ababuwan suka yo kasa suna tarwatsewa, saurin biyo kayayyakin nasa yayi yana dadumar wata allurar da take nan kamar ta glas kamar silver, jikinsa har wata hujin zafi yake bayarwa ya nemi daidai jijiyarsa ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara ɗurama kansa ruwan allurar sannu a hankali. Sai da ya juye ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, yana sake fasa wata ya sake yi ma kansa, kafin ya koma ya zube akan abinda bai gama tabbatar da ko menene ba, yana bin ko ina da kafin kuma ya sunkuyar da kansa ƙasa yana jiran sakamakon hukuncin da ya ɗaukarma kansa. Tun da dama sama da shekaru hudu kenan da aka dauka ana azabtar dashi da irin ta, tun da haka mutanen cikin duniyar suka zaɓa daya rayu kenan. Don haka ne ma yake kan shige da ficen ganin an dakatar da kowa amfani da ita sai iyaka shi kaɗai, tun da ita ce ta zabe shi ba shi ne ya zabe taba.... Sai da ya dau kusan mintuna goma sha biyar koma fiye da hakan, bai fara jin abin da yake son ji ba, sai ma wani irin nauyin da kansa ya sake ɗauka fiye da farko, kafin sannu a hankali idonsa ya soma masa yaji, wanda yay saurin rintse idanunsa yana soma jin kamar ana fara bikin mahaukatan aljannu ne a cikin kansa. Don sai wata kuwwa ake masa da gyada, ga kuma kansa dake ci gaba da sara masa, ƙirjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da duka hannunsa bibbiyu yana soma jujjuyawa tare da rufe idanunsa kirif. Kafin ya soma jin kamar ana wata gango da hajijiya da shi wanda ya saka sa sakin wani ihun da Yay daidai da danno ƙofar da Mark yay, don kullewa yayi da pin sabo ba irin na gidan ba, a zube ya tarar dashi yana ihu iya ƙarfin sa yana taƙarƙrewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga ya fashe koya tarwatse. A guje Mark yayi kansa yana ƙoƙarin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da shi, sai ga wasu daga cikin yaransa har su uku suka shigo domin sun san yau allurar mahaukatan ce ta motsa kenan, wani uban juyi da ihu yayi yana watsar dasu ya kuma ci gaba da ihu da kururuwar da yake yi tun karfi. Ga wani irin uban gurnanin daya soma fitarwa tamkar wani mahaukacin zaki. Da ƙyar da sudin goshi suka haɗu suka kai shi ƙasa daka tsayen daya mike, suka daddane shi yana cigaba da ƙoƙarin watsar da su ya tashi. A hankali Mark ya shiga soma ɗan dukan bayansa cikin sigar rarrashi yake faɗin "Easy maza, easy! mun san ka na cikin damuwa da raɗaɗi, amma hakan ba mafita bane ba, ka yi haƙuri muna tare da kai ɗari bisa ɗari iya wuya sai munga ƙarshen yakin, sai mun kawar da kowa in dai da hannunsa cikin wannan ehh yane din ka sani, ko uban waye sai mun ci gyatuma nai, koda kuwa matsayinsa ya zarce na God Father " duk da yadda allurar ta gama ɗaukarsa amma jin an ambaci sunan God Father sai da yayi wata girgiza kamar namijin zaki kafin a hankali jikinsa ya saki, ya daina wannan uban gurnanin da yake yi, da fisge fisgen yana lumshe idanunsa, ya rufe su ruff tamkar mai yim bacci. Wanda yake fata da rokon ya wuce daga nan kawai directly zuwa ga MAIRAH din sa... Su kuwa sai da suka gama tabattar da cewa ya yi relaxing, ya gama sumewa kana suka ɗaga shi suna nufar lafiyayyen gadonsa da kusan koda yaushe yake a harmutse....
ꨄ Nadiya kuwa tun daga lokacin da Baba Gaje ta tafi da ita gidanta take zaune kamar wacce aka zare wa ruhinta daga gangar jikinta, don hatta kukan ya gagare ta ma saboda abin da ya faru ya fi ƙarfin a ce zuciyarta ta iya ɗauka, duk kuma lokacin da ta lumshe idanunta sai hoton yadda aka murɗe hannun Baba ya dawo mata, yadda aka ja shi daga gidansu ba tare da ya samu damar kare kansa ba, sannan muryarsa da ya ce mata ta bari zai je ya yi magana da Halliru na sake ratsa wa ta cikin kanta da kunnuwanta suna mata amsa kuwwa. Gwaggo Talatu kuwa ta kasa samun nutsuwa ita ma, ta kasa zaune ta kasa tsaye domin duk da tsoron da take yi wa kanta, ta san abin da aka yi wa Baba Auwalu ba ƙaramin abu ba ne, kuma yanzu Nadiya ce kaɗai za ta iya sa mutanen nan su dakatar da abin da suke shirin yi idan har ta san inda Shitu yake, amma ita kanta Nadiya bata san komai ba. Baba Gaje ta zauna kusa da ita daga safa da marwar da take tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, tana gaya mata kada ta bari tsoro ya rinjaye ta, amma kalamanta suna shiga cikin kunnenta ne kawai ba tare da sun samu wurin zama a cikin zuciyarta ba. Kafin ta ɗago da fuskarta da hawaye suka gama cika idanunta ta kalli Baba Gajen cikin wata irin damuwa kafin ta ce, “Baba… me zan yi yanzu? Sun tafi da Babanmu… ni ban san inda Shitu yake ba, wallahi ban san inda yake ba!, ta yaya zan samo shi kafin su cutar da Mahaifina saboda nasan mai gari bashi da imani ko kaɗan?” Baba Gaje ta ɗan yi shiru tana kallonta, domin itama ta san cewa wannan ba irin matsalar da za a warware ta da kalmar haƙuri ba ce kawai, tun kafin ta iya samu abin da zata ce sai suka ji hayaniyar mutane daga can nesa tana sake tasowa, Nadiya ta fara yin firgigit ta miƙe da sauri tana kallon ƙofar tana jin kamar sune za su sake dawowa, Baba Gaje ta miƙe tana hana ta fita da hannu tana faɗin, “Ki zauna Nadiya, kada ki fita, ba za ki iya taimaka wa Baban naki da wannan yanayin ba, sai dai ki fara tunani ki nemi hanyar da za ki ceci shi.” Nadiya ta sunkuyar da kanta tana share hawaye, domin a wannan lokacin tsoron da take ji ya fara haɗuwa da wata irin jarumtar da ita kanta bata san tana da ita ba.
“Idan sun ce ni ce na san inda Shitu yake… Baba Gaje ki barni naje naga Babanmu, Wllh ni ban san inda Shitu yake ba ko kaɗan... "
Kama hannunta Baba Gaje ta sake yi tana komar da ita saman tabarmar kabar da suka tashi, tare da tura mata ruwan dake gabanta tace.
"Ki yi haƙuri, ki bar komai ga ALLAH, IN SHA ALLAHU babu abinda za su masa."
Kai kawai Nadiya ta iya gyadawa kafin ta samu damar sake magana wannan zancen zasu kwashe kudin Baba ya faɗo mata a zuciya. “Baba…” ta kira cikin sautin da ya bayyanar da tsoronta muraratan.
“Me ya sa suka ce za su debe duk wani ɗan jarin da Baba ya ke da?”
Baba Gaje ce ta ɗan kalleta domin ita ma ta fahimci cewa mutanen nan ba wai kawai suna son samun Shitu ba ne, suna son su azabtar da gidan ne gaba ɗaya. “Saboda suna neman hanyar da za su karya zuciyarki,” Ta bama Nadiya amsa tana ɗorawa da faɗin. “Amma kada ki bari su samu wannan damar.” Nadiya ta sake zama a kasa tana sake ƙanƙame kanta a cikin gwiwowinta, idanunta suka kafe a ƙasa yayin da hawaye suka sake gangarowa a hankali.
Tun da Ajmaal yabar room meeting din nan nasu bai sake waiwar kowansu ba, yana can ya zuba musu ido don shi ma ya kasa samun nutsuwa tun bayan abin da ya faru a cikin ɗakin meeting ɗin. Don haka ne ma yasa tun da ya samu kansa shi kaɗai, kansa ya fara ɗaukar zafi mai tsanani, kamar ana matse masa kwakwalwar kansa a ɓangarori guda. A matukar gajiye yakai zaune a gefen teburinsa yana shafa goshinsa, saboda tsabar rashin baccin dake damunsa, idanunsa kuwa ji yake sun yi masa wani irin nauyi saboda rashin barcin da baya iya samun damar yi da yawan tunani, amma duk yadda ya yi ƙoƙarin dakatar da kansa daga tunanin Rayyern sai wani sabon abu ya dawo masa. File ɗin dake gabansa ya ɗauka yana dan jujjuyawa, yana kallon file din da rinannun idanuwan da suka sake bushewa sosai. “To me ya sa aka ɓoye wannan file din? Mai yasa komai babu gaskiya a cikin sa?” Ya tambayi kansa da kansa amma a cikin zuciyarsa. Kafin ya ɗan haɗiye wani yawu, sannan ya miƙa hannu da nufin buɗe shi, sai kuma cak ya dakata yana sakin wani ɗan iskan munafikin murmushin takaici mara daɗi, duk da zafin kansa yana ƙara tsananta masa. “ Gani nan tafe gareka Sir Rayyern…” Yay maganar tare da miƙewa yana jin a karon farko ya yarda zai yaƙi Malaminsa. Sai shiga cikin sahun masu farautarsa tamkar dabba, zai yi masa kamun karen mahaukaciya ta hanyar wajiga rayuwarsa kamar yadda ya azabtar da duka jami'ansu. A wani irin natse ya sake jingina jikinsa da kujerarsa, ya shiga ɗan jujjuya idon sa tare da yin baya da kansa yana tura table ɗin dake gabansa da ƙafarsa ɗaya.
.... Su Tiger kuwa sai da suka gama tabbatar da cewa ya yi relaxing, ya gama sumewa, kana suka ɗaga shi suna nufar lafiyayyen gadonsa da kusan ko da yaushe yake a harmutse. Mark ne ya fara tafiya a gaba yana buɗe musu hanya, yayin da Tiger da wani daga cikin yaran suka ɗauki nauyin jikinsa. Duk da cewa idanun Rayyern a rufe suke, amma hakan bai hana wannan ɗan banzan kwarjinin nasa babbyanu qa, duk da kasancewar ba cikakkiyar kamala ko nutsuwa take bayyanawa amma kuma tana nan tsam a kamenta kamar koda yaushe, goshinsa har yanzu cike yake da ɗigon zufar daya dinga fitarwa, numfashinsa kuwa yana fita da nauyi kamar wanda yake cikin wani irin yaƙi da kansa. A hankali suka kwantar da shi saman gadon, Tiger ya gyara masa kai da matashin kai kafin ya ja bargon da ke gefe ya rufe masa ƙasan jikinsa. Mark kuwa ya tsaya kusa da gadon yana kallonsa, idonsa cike da damuwa da wani irin ciwon dake taso masa. Ya san Rayyern fiye da yadda sauran yaran suka san shi, ya kuma san cewa duk lokacin da ya kai kansa ga irin wannan matakin ba wai maganin kawai yake yaƙa ba ne, akwai wani abu a cikin zuciyarsa da yake ƙoƙarin tserewa daga gare shi. Ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarsa kafin ya sauke wata ajiyar zuciya. “MAIRAH...” ya furta cikin wata irin raɗaɗi wanda ya saka Tiger kallonsa da kyau. "Wacece MAIRAH? an miye alakarta da Boss saboda karo na uku kenan da gani ko ambatar sunanta ke jefa Boss cikin wannan halin, ban san ko miye asalin dangar takar dake tsakaninsu ba..." Tsaye kawai Mark ya miƙe yana shafa wuyansa, inda Rayyern ya damƙe shi ɗazu har yanzu yana jin ɗan radadin wurin. "Komai da komai nashi ce, idan nace komai ta kuwa komai din nake nufi, ita ce mace ta farkon data fara samun damar shiga cikin zuciyar Boss, sun rayu irin rayuwar da ban taɓa gani ko jin kwatankwacin irin taba... Amma daga ƙarshe itama basu bar masa ita ba! Sai da suka rabasu.... " Mark Yay maganar yana sake kallon Boss ɗinsu, yana kallon yadda numfashinsa ke tafiya a hankali. Mark ya yi wani ɗan murmushi mai ciwo. “Tabbas wasu ababuwan basu taɓa iya goguwa ta cikin sauƙi" Wani irin shiru ne ya sake mamaye ɗakin. Kowa ya yi kamar yana sauraron numfashin Rayyern ne kawai, kafin Tiger ya juya ya kalli sauran yaran ya yi musu alama su fita. “Ku bar shi ya huta.” Suka fara fita ɗaya bayan ɗaya, Mark kuma ya ɗan tsaya a ƙofar kafin ya sake waiwayawa. A daidai lokacin da zai fita sai ya ji kamar motsin Rayyern wanda ya saka shi tsaiwa cak, yatsun hannunsa ya motsa amma bai iya buɗe idonsa ba. Sai kawai leɓensa da suka yi alamar motsawa cikin wata irin raɗaɗin da yake jin kamar zai iya tarwatsa zuciya da kirjinsa ya sake furta sunan....
“...Mairah...”
A kusan karo na babu adadin daya saka Mark ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya rufe ƙofar a hankali ya bar ɗakin. A wannan lokacin Rayyern yana can cikin wani yanayi da shi kansa bai san mafarki ne ko gaskiya ba. Yana ganin wani haske mai laushi, yana jin wata murya daga nesa tana kiransa, amma duk lokacin da yake ƙoƙarin kusantowa sai hoton ya yi nesa dashi “Ya Rayern!...” Haka yahi wannan kamilalla kuma daddadan muryan nata ta kira sunan da kaf duniya ita kaɗai ce ke kiransa da RAYERN, ba tare da tayi dobble R ba, ƙoƙarin buɗe idanunsa yayi amma ya kasa. Wani kalan riƙe kansa yayi da ihu ya sake ambatar sunan “Mairah...” ya furta a cikin yanayin da yake jin kansa kamar mafarki kamar kuma zahiri, kafin wani irin tsananin raɗaɗi ya biyo bayan hakan ya ratsa tsakiyar kirjinsa...
"Ina son ku cinna mata wuta da ranta tunda taki bani hadin kai, ko kona min ita da ranta, tun da ban mori wannan ni'imar ba shi ma daga yau har zuwa numfashinsa na karshe ba zai sake ɗanɗanar wannan ni'imar ba... Koneta ku saka mata wuta...." Wani kalan jijjiga jikinsa ya shiga yi, yana son toshe kunnuwansa amma kuma babu hali saboda babu damar iya motsawa.
“Ko kun binne ta a duniya, ba za ku iya binne ta a cikin zuciyata ba... Sai na tagayyara rayuwar kowannenku sai na daidaita rayuwar kowa.... " Daga haka komai ya sake dusashewa a cikin kansa yana sake komawa halin daya fito.
Kwanaki uku kenan da kame Baba da Mai gari yayi amma komai ya kasa mantuwa a cikin kai da zuciyar Nadiya. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jikinta. Duniya ta mata ƙunci, irin kun cin nan da har ƙarshen numfashi da wahala ta manta. Yayinda farin cikinta ya zamana kamar fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na ƙasa da su. Da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai, da ta zama mace ta farkon da zata fara kafa tarihin da babu wanda ya taɓa ginawa, har zuwa yanzu kuma tana nan a gidan Baba Gaje. Ko yanzun ma zaune take a gefe guda ita kaɗai tana kallon ƙofar gidan kamar akwai wani abu da take jira ya bayyana daga cikinta. Tunda aka tafi da Baba Auwalu, babu wani abu da ya sake samun muhimmanci a idonta. Bare wani abincin da bata sake ko kallar inda yake ba, ko ruwa ba don kore kishi ba ji take yi da bata sha shi ba, kullum sai dai tayi jigum a wuri guda taki cewa komai, duk da kuwa yadda Indo ke yawan debe mata kewa ta hanyar zantukanta ita kadai. Ko a yanzun ma dai zaune take lokaci zuwa lokaci ta saka bayan hannunta ta share hawayen dake mata sintiri ko da gefen hijab ɗinta. Baba Gaje dake zaune daga gefen tana ta ɗan sake matsowa kusa da ita. “Nadiya.” Bata amsa ba. “Nadiya, ki samu kici wani abu ko ba yawa.” A hankali ta girgiza kanta,saboda ko karfin yin maganar ma bata da, shar wasu sabbin hawayen suka sake zubo mata wanda ya saka Baba Gaje furta “Kukan nan fa da kike yi ba shi ne zai dawo da Auwalu ba. Abin da zai taimaka masa shi ne ki kasance cikin hayyacin ki.” Nadiya ta ɗago idonta ta kalleta da rinannun idonta tace. “To me zan yi?” Baba Gaje ta sauke numfashi. “Za mu fara da abin da muka sani. Sun ce suna neman Shitu. Ke kin ce ba ki san inda yake ba. To dole mu gano dalilin da ya sa suke ganin ke kin san inda yake.” Nadiya ta ɗan lumshe idonta hadi da yamutsa fuska saboda a yanzu ko sunan bata son ji. Zumbir kuma ta mike tsaye tana rike kanta da dafe kirjinta, a fisge ta kamo kalmar data ambata... "Ya Aliyu!!!" Sai kuma hakki da yunwar da suka gama jigatar da ita suka saka ta kasa cewa komai, kafin cikin wannan karfin halin, wannan jarumta da dakewar nan nata da bama kai kwarin gwiwwa tace.
“Ya Aliyu naji yana waya a lokacin bana cikakken hayyacina sosai, amma tabbas naji yana waya da bada umarnin a kama shi..." wani dan ja da baya Baba Gaje tayi da zaro ido, kafin ta dafe kirji da faɗin. "Na shiga uku ni Sa'ade wannan basamuden kwaton sojan wai kike nufi? Cab ai kuma sai abinda hali yayi, shege ashe shi yasa tu daga wancan ranar bai sake dawowa ba, Kafirin banza da wofin nan zai dawo ya same ni ne ai wllh sai yaci uwatasa...." Tai maganar da sharce majina daci gaba da faɗin. "Ashe yasan tsiyar daya kulla mana kenan shi yasa bai sake dawowa ba dan kwal uba, ALLAH yasa yau ya m...." Sai dai maganar nata ya makale mata a makoshi ne sakamakon dagowar da tayi da nufin fa ce majina idonta ya faɗa cikin.....
BY AMMEY LAYLERH ✍🏻
***
༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺
Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️