KWARTON SARKI

5-6

by @oumhairan1

Ja baya tayi da sauri ta jingina da bango tace “Kuyanga kuma ranka ya daɗe dama har yanzu ana yin kuyanga?" Tsayawa yayi cik ba tare da ya juyo ba yace “Ko baayi ƙarfin iko yanasa mallakin wani ya zama na wani ba tare da wani sharraɗi ba kina ji na ina kwaɗayin abubuwa da yawa ne kuma banji ina jin zan iya sallama abubuwa a kowa ba Shiyasa na yanke shawarar zaɓar wasu cikin bayi na su zama kuyangi na so kuma sai akayi Sa'a ƙuria ta faɗa kanki so haka zaki karɓi tsarin ko ranki Bayaso" Tsayawa tayi ta zuba masa ido kanta na juyawa Jikinta na ɗaukar ɓari karon farko a rayuwarta da taji Maina Hameen yayi doguwar magana kenan" Hayewa gado taga yayi ya ja duvet ya juyawa Azeemah baya ta tsaya cike da tsoron wannan sabuwar rayuwa da ake faɗa mata ta shiga ciki, fita tayi daga ɗakin ta nufi ƙofa ficewa daga sashin mutumin da ke gadin ƙofar ya sanar da ita Mainah ya hana shiga ya hana fita a wannan daren, zsmewa tayi ta zauna a wajen tana faɗin “Aa wai meye hakan ne?"  daren baiyi nisa ba amma an kulleta an Hanata fita yanzu ta san Kaka Ajuzi tana can tana nemanta lungu da saƙo na gidan sarautar idan bata gano inda take ba kuma hankalinta tashi Zaiyi. Tashi tayi ta leƙa ta window A sassan babu kowa sai karnukan gadi da wani matashin zaki da Mainah Hameen yake kiwo wanda ake sakinsa duk dare da rana ake maidashi cikin shingensa, tsayawa tayi tana kallon yanda sakin yaketa zagaya gidan yakai ya kawo ya kuma kaiwa a ranta tana raya da ace za'a barta sai ta fita saidai ta san ajali da karar kwana ne zasu haɗata da wannan zakin domin duk gidan baya ɗaukar umarnin kowa sai na Mainah Hameen.
"Kije ki kwanta"  taji an faɗa a bayanta ta juyo da sauri ganin Hameen tsaye cikin shigar alfarma  tayi ƙasa da kanta ya kalli wata ƙofa yace “Akwai duk abinda zaki buƙata anan  ya nuna mata wani guri me kama da ɗaki ya fice da sauri, kallon bayansa tayi har ya ɓacewa ganinta tana kallon yanda wannan zakin ya bi bayansa ya dakatar dashi ya fice ta wata kofa da zata sadashi da sashin mahaifinsa, a tsaye ya tarar da sarki Fadalu yana kaiwa da komowa a parlourn gashin bakinsa ya miƙe da alama ɓacin rai ne yasashi kiransa a wannan lokacin.
Sadda kansa yayi irin gaisuwarsu ta al'ada sarki Fadalu ya nemi guri ya zauna tare da nuna masa wajen zama shima ya zauna ya kalli tsegumi ya sadda kai tare da barin wajen, ya jima yana kallon Hameen kafin yace masa “Wanne kaya ne a hannunka?" sarai yasan me mahaifin nasa yake nufi amma sai yace “Kayan da Aka aiko daga Masarautar Haizur" tsawa Ya daka masa yace “Ba wannan ruɓaɓɓen kayan nake maka magana akai ba ina maka magana ne akan kayan da muka ƙinƙisa a cikin wannan masarauta wannan kayan ba naka bane yafi ƙarfinka kayi gaggawar miƙoshi gareni yau dashi nakeson shashe baki"............