BEYOND HER WORDS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY SEVEN:97*
*BEYOND HER WORDS*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Suhaila ta fita daga part ɗin Raihana, kai tsaye ta nufi sashin Seeyama domin isar da saƙon Hajiya Hauwa, ta tura ƙofar falon ta shiga, nan ta hango Seeyama zaune a tsakiyar doguwar sofa tana ta faman danna wayarta cikin nutsuwa, kamar ba ita ce ta je ta gama zazzaga wulaƙanci a ɗazu ba, ta yi kamar tana cikin her own little world, hankalinta gabaɗaya a kan wayar hannunta, Suhaila ta tsaya a gabanta, tana kallon wajen, kafin ta ce da ita, “Ki zo, inji Mommy, tana part ɗin Anty Rayy,” bayan ta gama faɗar haka, Suhaila ba ta tsaya ta jira wata amsa daga gare ta ba, ta juya ta fice abinta, leaving Seeyama staring after her.
Seeyama ta zaro idanunta waje da mamaki, gaba ɗaya ta tsaya cak da danna wayar hannunta, maganar ta shiga kunnuwanta kamar wata guba, ta bi bayan Suhaila da wani shegen kallo mai cike da baƙin ciki da takaici, ta saki wani uban tsaki mai ƙara, “Kamar ya na je part ɗin ta?” ta faɗa a zafafe, tana ɗaga gira cikin disbelief, ta sake buga wani uban tsakin kafin ta miƙe tsaye, fuskar nan a bala’in haɗe, zuciyarta ta fara tafasa da wani irin mugun takaici, meye abin da zai kai Mommy sashen Raihana? Tun yaushe Mommy ta zo gidan da za ta wuce can, salon ta ja mata raini haka har ta je mata har ɗaki? Tunani iri-iri ya dinga ratsa kanta, she couldn’t understand what was going on, kuma ba ta son ta zauna tana guessing, sai ta miƙe ta nufi hanyar fita domin ta je ta ga abin da ke faruwa da idanunta, don kamar ma ba ta yarda ba.
Suhaila ta dawo falon inda Hajiya Hauwa take, ta ƙaraso ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon tana ɗan sauke numfashi, yayin da Raihana ke nan a zaune a kusa da Hajiya Hauwa, kanta a ɗan sunkuye, still, tana wasa da fingers ɗinta, domin she wasn’t comfortable sitting there at all, Suhaila ta kalli Hajiya Hauwa, “Na faɗa mata,” ta faɗa a taƙaice, “Toh,” Hajiya Hauwa ta amsa, hankalinta ba a kan Suhailan yake ba, Suhaila ta juya ta dubi Raihana, wacce idanunta ke nan a ƙasa, “Anty Rayy, ga breakfast ɗinki nan an kawo miki… don na san da ƙyar idan kin ci wani abu tun ɗazu, ko na zubo miki ne?” Raihana ta ɗan ɗago kanta, amma kafin ta ba Suhaila amsa, ba zato ba tsammani aka banko ƙofar falon da wani irin mugun ƙarfi!
Seeyama ce ta shigo, fuskarta a haɗe tamauuuu, tana watsa wa mutanen cikin falon wani kallon rashin albarka kamar ba uwarta a wajen, takunta cike da fushi, idanunta na yawo a falon, as if tana neman wanda zai fara yi mata bayanin abin da ke faruwa, amma da idanunta suka sauka kai tsaye kan Raihana, wacce ke zaune gefen Hajiya Hauwa, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa, “Kutmar ubancan!” Kalmar ce kaɗai ta faɗo daga bakinta ba tare da ta shirya ba, tana mai zaro idanu tana kallon Raihana, sannan ta sauke su kan Hajiya Hauwa cike da uban mamaki da tarin ruɗani.
Hajiya Hauwa ko kaɗan ba ta ɗago ta kalli Seeyama ba, hankalinta na kan Suhaila, tana kallonta da ɗan mamaki a fuskarta, “You mean har yanzu ba ta yi breakfast ba? Why?” Ta juya da kallonta kan Raihana, wacce a daidai wannan lokacin mamaki ya kusan kashe ta, ta kasa cewa uffan, kawai haɗiyar yawu take yi, tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa a gaban Hajiya Hauwa, Hajiya Hauwa ta dawo da kallonta ga Suhaila, “Je ki zuba mata abincin ki kawo maza,” Suhaila ta miƙe ba tare da ɓata lokaci ba, ta ɗauki basket ɗin abincin, ta wuce ta gaban Seeyama, wacce ke tsaye kamar ice, tana kallon ikon Allah kamar wata ‘yar tsana, ko kallon arziƙi Suhaila ba ta yi mata ba, ta wuce ta nufi hanyar kitchen a hanzarce, Seeyama ta bi ta da kallo na ɗan lokaci, sannan ta juya ta ƙaraso gaban Hajiya Hauwa da sauri, fuskarta na fitar da wani uban huci, tana ta falan hira hanci saboda tsananin zafi da baƙin ciki, “Mommy, gani na zo! Me ne za ki kirani wannan wajen? Me zan yi a nan, kuma… ke ma me kike yi a nan a sashin, for God’s sake?!” Ta faɗa, muryarta na rawa, kuma tana cike da wani irin zafi mai ɗaci da za ka iya ji daga zurfin zuciyarta.
Hajiya Hauwa ta ɗago kanta a hankali, ta ɗora idanunta a kan Seeyama wacce har yanzu take tsaye a gabanta da fuskar nan a haɗe, “Common, sweetheart, zauna mana, magana zan yi da ku duka, da mijinku,” ta faɗa cikin nutsuwa, tana nuna mata kujerar da ke gefenta, Seeyama ta ɗan dage gira, sannan ta kalli kujerar da Hajiya Hauwa ta nuna mata kamar an ce ta zauna a kan garwashin wuta, “Mommy, seriously?” ta tambaya, tana ɗaga hannayenta kaɗan, “You called me all the way here just to sit down?” Hajiya Hauwa ta ɗan kalleta, amma ba ta ce komai ba, Seeyama ta dan kalli Raihana ta gefen ido, wacce har yanzu take zaune cikin nutsuwa, kanta a ɗan sunkuye, sai ta dawo da kallonta kan Hajiya Hauwa, tana tabe baki, “Wallahi, I don’t understand this at all, Mommy, ke kika zo gidan nan, amma instead of coming to my part first, sai kika wuce nan?” Ta faɗa tana nuna sashen Raihana da hannu, fuskarta cike da rashin jin daɗi, “Like, how does that even make sense? Ni ce ɗiyarki fa! Your own daughter! Kin shigo gidan nan, kin wuce direct nan, yanzu kuma sai a kira ni in zo nan kamar ni ce na yi wani laifi,” ta ja wani uban tsaki, sannan ta zuba wa Raihana wani kallo mai ɗauke da raini, “Honestly, Mommy, I don’t like this, ba wai saboda wata yar iska ba, but there should be some respect, you could have come to my part first before coming here,” Raihana ta ɗan ɗago kanta da mamaki, amma da ta lura da yadda Seeyama take kallonta, sai ta sake sunkuyar da kai, ba ta son shiga maganar da ba ta shafe ta ba, especially a gaban Hajiya Hauwa.
Hajiya Hauwa kuwa ta sauke ajiyar zuciya a hankali, “Seeyama,” “Me?” ta amsa da sauri, tana ɗaga gira, “I’m only saying the truth, Mommy, or am I not allowed to speak anymore?” Hajiya Hauwa ta kalleta na wasu seconds, tana ƙoƙarin danne haushin da ya fara taso mata, “Kin gama?” Seeyama ta ɗan buɗe baki, sannan ta haɗe shi, tana kallon mahaifiyarta da mamaki, Hajiya Hauwa ta gyara zamanta, “Toh, yanzu ki zauna ki saurare ni, ba na son mu fara magana da gardama tun kafin ma na faɗi abin da ya kawo ni, na ce zan yi magana da ku duka, ku da mijinku, so, please, sit down and listen,” Seeyama ta sake tabe baki, ta juya ta kalli Raihana ta gefe, sannan a hankali ta zauna a kujerar da ke can gefe, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa, “Fine,” ta faɗa a dan zafafe, “I’m listening,” amma daga yadda ta haɗe rai, a bayyane yake cewa zama kawai ta yi, ba wai ta haƙura da abin da ya ɓata mata rai ba.
Sautin takun Zayd ne ya sa kowa ɗan juyar da kansa, amma ban da Raihana, ita kuwa tun kafin ma ta ji takun nasa sosai, ƙamshinsa ya riga ya kai hancinta, numfashinta ya nemi ɗaukewa na ɗan lokaci, ta haɗiye yawu a hankali, tana ƙoƙarin acting normal kamar babu abin da ya same ta, Zayd ya canja kaya daga na ɗazu, yanzu yana sanye da wata fitted black trouser da polo black shirt mai gajeren hannu, wacce ta zauna a jikinsa daidai, ta bayyana faffaɗan kafaɗunsa da ƙarfin jikinsa, hannun rigar da ya kasance short sleeve, ya bayyana agogon hannunsa mai tsada, yayin da black leather shoes ɗinsa suka ƙara ba shi wani irin classy appearance, gashinsa a gyare yake, fuskarsa kuma yanzu da ɗan sauƙin haɗewar, not exactly a smile, amma kuma ba irin fuskar nan tasa da take nuna kamar duniya ta ɓata masa rai ba, ko dalilin ganin Hajiya Hauwa ne ya sassauta, Allah kaɗai ya sani, kai tsaye ya ƙarasa cikin falon, bai ce komai ba, ya zauna a kujerar da Suhaila ta tashi, wacce ke gefen inda Seeyama ta zauna, ya gyara zamansa a hankali, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sannan ya zaro wayarsa ya duba screen ɗin na seconds kaɗan kafin ya ajiye ta.
Seeyama kuwa ba ko kunyar idon uwarta, ta zuba masa idanu kamar tsohuwar mayya, idanunta na bin fuskarsa, tana jiran ya kalleta ko ya tambayi ya ya ganta a nan ko dai ya fadi wani abu, amma Zayd ko kallon arziƙi bai yi mata ba, ta ɗan tabe baki, sai ta sake gyara zamanta, tana ƙoƙarin jan hankalinsa, amma Zayd ya ɗauke kansa ya mayar da hankalinsa ga Hajiya Hauwa, Raihana kuwa har yanzu kanta a sunkuye yake, tana jin kasancewarsa a kusa da ita, tana ƙoƙarin danne duk wani reaction da zai iya bayyana a fuskarta, but honestly, with that perfume filling the room, staying calm was becoming a serious challenge, “Good morning, Mummy,” Zayd ya faɗa cikin muryarsa mai sanyi, yana kallon Hajiya Hauwa da lumsasshun idanunshi, Hajiya Hauwa ta washe baki da murmushi, “Morning, son, ya kake? Ashe kun dawo kuma? Ba labari ba sai da na zo na ga ƙofar a buɗe, na ce bari dai na shigo in ga ni ko ta tare ko dai wani gyaran akeyi,” ta ɗan yi dariya a hankali, tana gyara zamanta kafin ta ci gaba da kallon Zayd, “Amma sai na tarar da Suhaila a zaune ita ma, ita ma ta zo, kuna can sama lokacin,” Zayd ya ɗan ɗaga gira, yana kallon Suhaila na ɗan lokaci, wacce ta fito ta ajiye abincin Raihana akan dining table, sannan ta zagayo ta zauna a kujerar data rage a falon empty, kafin ya mayar da idanunsa kan Hajiya Hauwa, “Eh, Mummy, mun dawo,” “Madallah lale marhaban,” Hajiya Hauwa ta amsa da murmushi, sannan a hankali ta juya kanta zuwa ga Raihana wadda har yanzu take zaune cikin nutsuwa, kanta a ɗan sunkuye, “Kaga yar tawa ma…” Ta faɗa tana kallon Raihana da wani irin murmushi, “Kunya ta hana ta magana da ni, tun da muka gaisa, bata sake cewa komai ba,” ta yi magana ne cikin wasa, amma idanunta suna kan Raihana, tana jiran ta ɗago kai ta ce wani abu, Raihana ta motsa yatsunta a hankali, ta haɗe su wuri guda, ta ji kamar duk idanun da ke cikin ɗakin sun koma kanta, musamman na Zayd, duk da cewa ba ta da tabbacin ko yana kallonta ɗin.
“Say something daughter,” Hajiya Hauwa ta sake fada tana murmushi, idanunta kan Raihana, “Um… Mommy, ba haka ba ne,” ta faɗa a hankali, muryarta ƙasa-ƙasa, “To, yaya ne?” Hajiya Hauwa ta tambaya cikin murmushi, “Ko na tsorata ki ne?” “A’a,” tayi saurin amsawa, “Then why are you so quiet, my dear?” Raihana ta ɗan buɗe baki, amma kafin ta samu amsar da za ta bayar, sai ta ji ƙamshin turaren Zayd ya sake bugun hancinta, ta haɗiye yawu, ta mayar da kanta ƙasa, tana ƙoƙarin acting kamar komai is normal, a gefe guda kuwa, Seeyama ta yi shiru tana kallon yadda mahaifiyarta ke magana da Raihana cikin wannan kulawar, her lips tightened slightly, amma ta danne maganar da ta taso a bakinta, zuciyarta kuwa da za a bude Allah kadai ya san me ke ciki, Zayd kuwa ya ajiye wayarsa a kan cinyarsa, ya ɗan jingina da kujerar, yana kallon Mommy da fuskar da ba ta bayyana abin da yake tunani, “Maybe she’s still trying to get used to the house,” ya faɗa a hankali, Hajiya Hauwa ta juyo gare shi, “Perhaps, amma kuma sai tayi kamar baƙuwa a gidan mijinta?” Zayd bai yi saurin amsawa ba, ya ɗan karkatar da kansa, idanunsa suka sauka a kan Raihana na ɗan lokaci, “Baƙuwa?” ya maimaita a hankali, Raihana ta ji gabanta ya faɗi, ya Allah, don Allah kada ya fara wani abu a gaban su, amma Zayd ya kawar da idanunsa daga kanta, ya mayar da su kan Hajiya Hauwa, “She’ll be fine, Mummy,” ya faɗa ne kawai, calmly, ba tare da wani ƙarin bayani ba, Seeyama ta ji wani malolon bakinciki ganin kamar ba wanda yake ta ita a wajen, kowa Raihana, ciki harda uwar da ta haifeta? Lalle.
Hajiya Hauwa ta ɗan kalle shi, kamar tana ƙoƙarin fahimtar abin da ke ɓoye a bayan wannan amsar tasa, daga nan ta mayar da hankalinta kan matan biyu da ke gabanta, “To, since we’re all here, I think it’s time we talked properly,” Seeyama ta gyara zamanta nan take, tana jiran abin da mahaifiyarta za ta faɗa, yayin da Raihana ta ɗan ɗaga kai a hankali, Zayd kuwa ya sake ɗaukar wayarsa, kamar maganar ba ta dame shi ba sam, but judging from the slight shift in his expression, he was listening, Hajiya Hauwa ta gyara zamanta, sannan ta mayar da hankalinta kan Zayd, “Dama Seeyama ta nemi Rabi ne ta zo ta zauna da ita, saboda ta ɗan dinga koya mata house chores, tunda ka san ita babu abin da ta iya,” ta faɗa cikin sauƙin murya, tana kallon ɗiyarta a taƙaice kafin ta ci gaba, “Amma yanzu tunda ta yi aure, kaga dole ta koya, tunda ba zai yiwu ace mace kamar ta ba ta iya yi wa kanta komai ba a gidan miji, sai dai ka zauna ana maka komai,” Seeyama ta ɗan motsa a kujerarta, amma ba ta ce komai ba, idanunta suna kan mahaifiyarta, tana sauraron maganar da ta fara zargin ba za ta yi mata daɗi ba, “Shi ne na ga idan Rabi ta zo, za ta ɗan yi ƙoƙarin saita ta a hanya, na faɗa mata dai, amma ta dakata, na fara neman izinin mai gidan tunda ba zai yiwu a ɗauko wata daga waje a kawo maka gida ba tare da yardarka ba,” ta ɗan dakata, tana kallon Zayd da murmushi, “Sai kuma ita ma Raihana, tunda na kawo wa Seeyama mai taimako, ita ma ya kamata a duba nata ɓangaren, shi ne na ce, me zai hana na samo wata yarinya da za ta dinga kama mata ƙananan ayyukan gidan? Tunda gidan yana da girma, ba zai yiwu ace dare ɗaya ta saba da komai ba, you know, it takes time,” ta dan gyara mayafinta daya zame da shoulder dinta, sannan ta ƙara da cewa, “Kaga, gradually idan ta saba, za ta iya ci gaba da harkokinta, ba na son a ɗora mata abubuwa da yawa lokaci guda, amma dai, ya kake gani?”
Da ta gama, sai ɗakin ya yi shiru na ɗan lokaci, Seeyama ta buɗe baki, hancinta da idanunta kawai ta zuba wa Hajiya Hauwa, tana kallonta kamar wadda aka tai kawa mari bata ankara ba, she was completely speechless, ba don ba ta fahimci abin da mahaifiyarta ta faɗa ba, sai don ba ta taɓa tsammanin za ta ji irin wannan magana daga gare ta ba, Rabi za ta zo ta zauna da ita, amma yanzu sai ga shi mahaifiyarta tana maganar samo wa Raihana ma mai taimako, wannan wane irin abu ne kuma, is Mommy actually fine? Fuskarta ta nuna mamaki, rashin yarda, da ɗan bacin rai a lokaci guda, ta kasa tantance wanne yanayi ya fi dacewa ta nuna, don haka kawai ta ci gaba da kallon Hajiya Hauwa, Suhaila kuwa, wadda ke zaune a gefe, ita ma ta zuba wa Hajiya Hauwa ido, a zahiri, abin ya ba ta mamaki sosai, she felt as if she was watching a scene from a movie, musamman ganin yadda Hajiya Hauwa ta gabatar da maganar cikin sauƙi, kamar ba ta san irin tasirin da za ta yi a kan Seeyama ba, Raihana kuwa har lokacin ba ta ɗago kanta ba, tana zaune cikin nutsuwa, hannayenta a haɗe a kan cinyarta, maganar neman mata mai taimako ta ba ta mamaki, amma ba ta san abin da ya kamata ta ce ba, a ganinta, wannan magana ce da ta shafi gidan, don haka ta fi son ta yi shiru ta saurara.
Zayd ya ɗan ɗaga kansa a hankali, fuskarsa tana nan cikin nutsuwa, babu wata alamar mamaki ko rashin jin daɗi, ya kalli Hajiya Hauwa na ɗan lokaci, kamar yana nazarin abin da ta faɗa, sannan ya amsa a taƙaice, “It’s fine, Mummy,” Hajiya Hauwa ta wage baki da murmushi nan take, “Yauwa, son! Dama na san ba za ka ƙi ba,” ta gyada kai, tana kallonsa cikin gamsuwa, “Amma ai yanada kyau a ba ka girmanka as the head of the house, dole ne na nemi izininka kafin in yi irin wannan abu, ba na son a ce na shigo gidanka ina yanke hukunci ba tare da na sanar da kai ba,” Zayd ya ɗan gyara zamansa, ya jingina da kujerar cikin natsuwa, “That’s fine, Mummy,” ya sake faɗa, kamar maganar ba ta da wani nauyi a wajensa, amma a gefe guda, Seeyama har yanzu tana kallon mahaifiyarta da wani irin expression da ya nuna a fili cewa ba ta gamsu da abin da ta ji ba, domin a tunaninta, zuwan mahaifiyarta gidan nan zai taimaka mata wajen samun abin da take so, ba ta san cewa maganar da ta zo da ita za ta ƙara sanya ta jin kamar an mayar da ita gefe ba.