ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER TEN

by @hindatuauwal


Amma kalmar da wata daga cikinsu ta furta ta sa ƙafafuwanta suka tsaya cak.

“Idan mace ta kasa zama ƙyauren gidanta, ba laifi ba ne don wata ta girgijeta ta dasa kanta a wannan gidan.”


Cikin izgilanci suka kwashe da dariya. Wata ta kuma cewa"Wallahi wasu matan suna tunanin aure kawai zama da miji ne. Sai wata ta zo ta nuna musu yadda ake riƙe gida.”

Suka sake yin dariya.

Zainab ta lumshe idanunta. A hankali wani zafi ya mamaye ƙirjinta.

Ta ji kamar an cire mata fata daga zuciya aka bar ta a buɗe, kowa yana zuwa yana taka ta.

Tai gumm!babu bakin magana tashin hankalin da take ciki kaɗai ya isheta. Ga ƙafafuwan ta da sukai wani irin sagewa kamar wacce take tsakiyar annoban gudawa.




Tabuɗe ɗakinta ta shiga kunnuwanta na jiyo mata sautin dariyan su. Yaraf ta zube a kujerar tana jan numfashi kamar mai ɗan ɗanashi ko zata sami rangwamen wani mai ɗan sanyi sanyi da yafi wanda ke cikin huhunta yana barazanar tarwatsa zuciyar ta.

Amma a cikin zuciyarta, kalmar “ƙyauren gidanta” ta maimaita kanta sau da yawa.

Ƙyauren gidanta...

Ta tuna yadda ta yi ta kare gidanta. Yadda ta yi ta haƙuri. Yadda ta yi shiru a lokutan da ya kamata ta yi magana. Yadda ta zauna tana gyara abin da ba ita ta ɓata ba. Yadda ta ɗauki Ahmed a matsayin gidanta.

Yanzu kuma ita ce wadda aka ce ta kasa zama ƙyauren gidanta.

Hawaye suka cika idanunta.

Ta yaya za ta bayyana wa mutanen da ke dariya cewa abin da suke gani a matsayin gazawa, shi ne abin da ta sadaukar da dukkan rayuwarta domin kada ya faru?

Ta yaya za ta ce musu ba ta rasa gidanta ba ne saboda ba ta yi ƙoƙari ba...

Sai dai saboda mutumin da ta ɗauka a matsayin gidanta ya daina ganinta a matsayin wani ɓangare na gidan?

Hawayen suka gangaro. Ta share su da sauri.


"Mami....Mami! Kalla!"


Maganar Ramlat yasanyata ɗago jajayen idanuwanta ta sauke akan littafin dake hannunta yayinda sauran suka biyo bayan ta da sallamar su.



Cikin sanyin jiki ta amshi littafin, bayan ta amsa sallamar su. Ta sauke idanunta kan murfin littafin, kafin ta buɗe shi a hankali.

A shafi na farko kuwa, wani hoto ne ya ja hankalinta.

Hoton wata mata ce, wadda fuskarta ta yi kama da tata sosai. Yara huɗu ne a zagaye da ita, suna dariya cikin nishaɗi, ita kuma tana musu wannan murmushin nata na Murmushin Uwa Mai Ɗauke da Sirrin Zuciya.

Murmushin da ya saba ɓoye damuwarta domin farin cikin yaranta.

A ƙasan hoton kuwa, an rubuta da Turanci:

“Even without Abba, our family will never lose its happiness because of Mami. She is our protector. As long as we have Mami in our lives, everything will be alright.”

Zainab ta tsaya cak.

Idanunta suka koma kan hoton, tana kallon yadda aka zana ta tare da yaranta. Yadda suke dariya, yadda suka manne da ita, da yadda ta rungume su cikin farin ciki.

Ta ɗan ja da baya, ta share hawayenta da bayan hannunta, sannan ta kalli sauran yaran da suke tsaye kusa da su.
Ta yi musu murmushi, irin murmushin nan nata da ke ɓoye abubuwa da yawa.

“Ku zo nan, yarana.”

Dukkansu suka ƙaraso, suka rungume ta.

Zainab ta lumshe idanunta, tana jin ɗuminsu a jikinta.

A cikin zuciyarta kuwa, ta furta: “Ya Allah, idan har akwai wani abu da ya rage min a duniya, to su ne. Ka ba ni ƙarfin da zan iya zama mafaka gare su, ko da kuwa ni kaina ina neman mafaka.”

Ta sake kallon hoton.

A wannan karon, ba ta ga wata mace mai murmushi kawai ba.

Ta ga kanta. Ta ga yaranta. Ta ga wani sabon nauyi da rayuwa ta ɗora mata.

Kuma a ƙarƙashin wannan nauyin, ta fara fahimtar ma'anar kalmar da ta daɗe tana furtawa:

“Kowace mace ita ce kariyar gidanta.”


Idanuwanta ta ɗago tasauke akan Khalid dake zaune kusada ita. Daga can ƙasan zuciyar ta take samun wani sabon fata arayuwa. Adaa tasare amma ayanzu tana jin zata iya jure fiyeda duk abinda ya faru abaya saboda rayuwar waɗannan yaran nata.



Khadijah data kafe hoton da kallo tace"Mami kinga yadda Khalid ya zanani da ƙaton kai kamar ƙwallon Ronaldo "


Dariya sukayi harda ita Zainab din da bata cikin yanayin nishadi.


Wannan ita ake kirada uwa. Zata iya jure komai dan kawai taga murmushi akan fuskar yaranta. 



Har yanzu kalmar nan na zaune daram a zuciyarta farin cikin iyali shine samada komai arayuwa**


     *JAMILA*

Jamila na zaune ita kaɗai a cikin bedroom ɗinta, tana kallon talabijin. A jikinta akwai wata siririyar riga ta barci, yayin da wayarta take gefenta. Lokaci zuwa lokaci takan ɗauke idanunta daga talabijin ta kalli wayar, kafin ta sake mayar da su kan abin da take kallo.

Kwatsam sai ƙofar ɗakin ta buɗe.

Ba tare da ta yi tsammanin ganin kowa ba, sai kawai ta hangi wani mutum yana shigowa.

Ta ƙyale idanunta a kansa.

Raihan?

Ta sake kallonsa.

Anya kuwa Raihan ne? Ko kuwa gizo nake gani?

Ta ɗan miƙe kanta, tana ƙoƙarin tabbatar da abin da take gani.

To, idan shi ne, yaushe ya shigo? Bayan ban jima da dawowa daga falon nan ba fa!

Ta murza idanunta a hankali, sannan ta sake buɗe su.

Har yanzu shi take gani.

Raihan ne.

Da gaske.

Wani irin yanayi ya mamaye zuciyarta. Ta kasa fahimtar abin da yake faruwa. Kafin ta samu damar tambayar kanta wani abu, sai ta ga yana takowa zuwa gabanta.

Ya ƙaraso gaban gadon, ya ja kujerar hutawa dake gabansa, sannan ya zauna.

Ya ɗora idanunsa a kanta tare da murmushi.

"Hi, Aunty."

Jamila ta kasa amsawa.

Ba don ba ta ji shi ba, sai don kalmar da ya kira ta da ita ta tsaya a wani wuri mai zurfi a cikin zuciyarta.

Aunty.

Wannan kalmar da ta saba ji daga gare shi, amma a wannan daren sai ta ji ta da wani irin sabon yanayi.

Ta kalli fuskarsa.

Wataƙila saboda ta daɗe tana ganin sa a matsayin wanda yake nesa da ita, ko kuma saboda ba ta shirya zuwansa ba ne, amma a yanzu ko amsa masa sallamar da ya yi mata ta gagare ta.

Raihan ya ɗan karkatar da kansa, yana nazarin fuskarta.

Kafin ta ankara, sai ya miƙo hannunsa ya ɗora tafin hannunsa a goshinta.

"Are you okay?"

Jamila ta ɗan firgita.

Ba wai saboda tambayar ba, sai saboda yadda hannunsa ya sauka a goshinta cikin kulawa.

Ta ɗaga idanunta zuwa gare shi.

"Yes," ta amsa cikin wata murya mai rauni.

Raihan bai cire hannunsa nan take ba.

"Are you sure?"

Ya sake tambaya, wannan karon yana kallonta da kulawa.

Jamila ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙogwaro.

"Yes."

Ta yi saurin mayar da kallonta ga talabijin.

Raihan ya ɗan yi murmushi, sannan ya cire hannunsa daga goshinta.

Shi ma ya karkatar da kansa zuwa talabijin ɗin.

"Wannan wani film ne?"

Jamila ta ɗan yi shiru kafin ta amsa.

"Me Before You."

"Oh."

Ya ɗan gyara zamansa a kujerar.

"Na tuna wannan film ɗin."

Jamila ta juya ta kalle shi.

"You've watched it?"

"Yes."

Ya yi murmushi kaɗan.

"Actually, na taɓa kallonsa tun da daɗewa."

Jamila ta mayar da idanunta kan talabijin.

"To, ka tuna labarinsa?"

Raihan ya ɗan yi dariya.

"Of course. Labarinsa ba irin wanda mutum zai manta da shi ba ne."

Ya ɗan dakata, sannan ya fara ba ta labarin.

"Will Traynor, wani attajiri ne wanda yake rayuwa cikin jin daɗi. Amma bayan haɗarin da ya same shi, sai rayuwarsa ta sauya gaba ɗaya. Daga baya aka ɗauko Louisa Clark domin ta riƙa kula da shi..."

Yayin da yake magana, Jamila tana sauraron sa.

A wasu lokutan takan kalli talabijin, wani lokacin kuma ta ɗan karkatar da kanta gare shi.

Raihan ya ci gaba da ba ta labarin cikin natsuwa, yana bayyana yadda Louisa take ƙoƙarin sa Will ya sake samun farin ciki a rayuwarsa.

"Amma abin da ya fi ɗaukar hankalina a film ɗin shi ne yadda rayuwar mutum za ta iya sauyawa saboda wani da bai taɓa tsammanin zai taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa ba."

Jamila ta ɗan kalle shi.

"Really?"

Ya gyada kai.

"Yes."

Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa:

"Sometimes, mutum yana tunanin ya san abin da yake so. Amma sai wani abu ya faru da shi, ya gane cewa akwai wasu abubuwan da bai taɓa lura da su ba."

Jamila ta mayar da kallonta ga talabijin.

Ta ji kalamansa sun shiga cikin zuciyarta fiye da yadda ta yi tsammani.

Ba ta san dalilin da ya sa ta ji haka ba.

Wataƙila saboda tana zaune kusa da shi ne.

Ko kuma saboda tun bayan dawowarsa, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a zuciyarta waɗanda har yanzu ba ta iya fassara su.

Raihan ya ci gaba da magana.

A hankali, hira ta koma kan wasu abubuwa daban-daban.

Wani lokaci Jamila tana yi masa tambaya, wani lokaci kuma shi yake tambayarta.

Akwai lokutan da dariya takan kubuce mata ba tare da ta shirya ba.

Kuma duk lokacin da hakan ta faru, sai ta ɗan yi shiru, kamar tana mamakin yadda ta sami damar yin dariya a gabansa cikin sauƙi.

Lokaci ya ja.

Daren ya ƙara zurfi.

Amma duk da haka, Jamila ba ta son ta tambaye shi lokacin da zai tafi.

Ba don tana son ya zauna ba.

Aƙalla haka take ƙoƙarin gaya wa kanta.

Sai dai duk lokacin da ta ɗauke idanunta daga talabijin, sai ta tsinci kanta tana kallonsa.

Yana magana.

Yana murmushi.

Yana kallon film ɗin.

Wani lokaci kuma idanunsu sukan haɗu, sai ta yi saurin mayar da nata gefe.

A karo na ƙarshe da ta kalle shi, sai ta tarar da shi yana kallonta.

Ta yi saurin kau da kai.

Raihan ya yi murmushi, amma bai ce komai ba.

Ya sake kallon talabijin ɗin.

Dare ya yi sosai.

A ƙarshe, Raihan ya miƙe daga kujerar.

"Okay, Aunty. I think it's time for me to go."

Jamila ta ɗago idanunta.


"Oh."


Kalmar ta fito a hankali.

Raihan ya kalleta.


"Good night"

Ya matso kusada gadon.


Jamila tana zaune a gefen gadon, don haka taɗaga kanta tana kallonsa.


Sai kawai taga ya sunkuyo gareta.


Kafin ta fahimci abinda yake shirin yi, sai taji laushin leɓunansa a goshinta.