SHADOWS OF THE NIGHT
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-SEVEN: 7*
*SHADOWS OF THE NIGHT*
*JIDDAAH BARKUM*
————————
Yaya Hamza ya fito daga ɗakinsa ya tsaya a layinsu kawai, ya zuba wa waje da ido.
Shi bai san ma ta ina zai fara neman Bintu ba. A taƙaice ma, bai san inda ta je ba. Kuma ya san ba zai fara tambayar Baffa wani ƙarin bayani ba, musamman da ya san yanzu a fusace yake. A irin muryar da Baffa ya yi magana, ya san ba zai amsa tambaya ba. Kawai a cika umarninsa.
Ya duba wayarsa, 11:30 PM.
Ya dafe kugunsa da hannayensa biyu, cikin rashin sanin ta ina zai fara.
Can sai hasken wata mota da ta ke ƙoƙarin shigowa layin ya haske masa ido. Ya saka hannu ya kare idanunsa.
A hankali motar ta ƙaraso ta samu gefe, nesa da inda yake, aka yi parking.
Har kusan mintuna biyar ba a kashe hasken motar ba, sannan kuma ba a fito ba.
Sai daga baya mutumin da ke driver’s seat ya fito, ya zagayo wajen passenger seat ya buɗe a hankali.
Wacce ke wajen ta fito.
Da farko bai gane wace ba.
Sai da ta juya da kyau.
Yaya Hamza ya zaro ido da tsananin shock, “Bintu…”
Bakinsa ya furta a hankali.
Ba su kula ma akwai wata halitta a wajen ba.
Shi kam, tsananin mamaki ne ya hana shi magana.
Yanzu duk dokokin Baffa, da yadda kowa ke tsoronsa. Samari ma baya barinsu zuwa wajen ‘ya’yansa da dare, sai dai da yamma.
Amma a ce Bintu ce za ta hau motar saurayi har ƙofar gidansu a irin wannan lokacin?
Tunaninsa ya tsaya a daidai lokacin da mutumin ya buɗe back seat, ya ciro manyan shopping bags, sannan ya miƙa mata.
Ta amsa tana murmushi.
Suka ɗan yi magana, sai ta fara tafiya a hankali.
Shi kuma ya nufi motarsa, ya yi reverse ya bar unguwar.
Da ta zo daidai gefen da Yaya Hamza yake, kawai ta ji an ce,
“Sannu... yau za ki ci ubanki wallahi.”
Kafin ma ta gane waye ya yi maganar, ya ɗauke ta da wani mahaukacin mari.
Sai ta fashe da ƙara.
Ta kwasa da gudu, har yanzu ledojin na ƙanƙame a hannunta.
Da gudu ta shiga gida, Yaya Hamza na biye da ita a baya.
Kai tsaye ta faɗa ɗakin Mama Sabuwa.
Ta na shiga... ta fashe da wani irin kuka mai ƙarfi,
“Mama...”
Mama Sabuwa ta miƙe a firgice,
“Bintu! Ina kika tsaya? Zaki kashe min aure! Allah ne kaɗai ya rufa min asiri, Malam bai sake ni ba.”
Ta ƙarasa maganar tana sauke numfashi.
Sai kuma idanunta suka sauka kan manyan ledojin da Bintu ke riƙe da su, sai ta ɗan sassauta.
“A’a... waye ya ba ki waɗannan? Kar dai kin samo saura—”
Kafin ta ƙarasa maganar...
A ka banko labulen ɗakin da ƙarfi.
Bintu ta firgita. Da sauri ta ruga ta buya a bayan Mama Sabuwa.
Baffa ne, tare da Yaya Hamza.
Yaya Hamza kai tsaye ya nufi bayan Mama Sabuwa domin ya finciko Bintu.
Da sauri Mama Sabuwa ta riƙe Bintu gam, ta tare shi da jikinta.
“Hamza! Cika min yarinya! Saboda ba ka da mutunci, a gabana zaka dake ta? Har ta buya bayana kana binta? Za ka dake ta saboda ga jakaa ka samu?”
Hamza ya tsaya. Ya runtse ido na wasu daƙiƙu, kafin ya buɗe su cikin takaici.
“Mama, yarinyar nan fa daga motar wani saurayi ta fito a daren nan. Ba tsoron komai ta sa ya kawo ta har ƙofar gidan nan. Yanzu mutane ba sai su zage mu ba, su zagi mahaifinmu. Duk ƙoƙarin da yake yi a kanmu ya zama a banza. Wallahi Bintu ba ta da mutunci. Idan aka ci gaba haka... ina tsoron wata rana—”
“Hamza!” Mama Sabuwa ta katse shi da tsawa,
“Idan ka sake aibata min yarinya... Allah Ya isa! Nonon da na ba ka!”
Hamza ya buɗe baki, ya tsaya yana kallonta cike da mamaki.
Mama Sabuwa ta nuna masa ƙofa, “Fita min a ɗaki. Banza. Solobiyo. Mara son ci gaban ’yar uwarsa.”
Baffa kuwa... tun shigowarsa tsaye yake. Yay i shiru, yana kallonsu kawai. Bai ce uffan ba.
Sai bayan Mama Sabuwa ta gama, ya juya ya kalli Hamza.
“Je ka abinka, Hamza. Allah Ya yi maka albarka.”
Muryarsa cike take da nutsuwa, ba fushi, ba hayaniya.
Hamza ya kalli Baffa, ya gyada kai cikin girmamawa, “Na gode, Baffa.”
Sai ya juya, ya fita daga ɗakin.
Da fitarsa... Baffa ya maida kallonsa kan Mama Sabuwa, wacce har yanzu take hura hanci cikin fushi.
“Ni zaki zaga? Ni zaki ci wa mutunci? Sabuwa... ba Hamza ba. Duk abin da ya yi... ni ne na sa shi.”
Ya nuna Bintu da hannu, “Ga ta nan. Na bar miki ita. Ki yi duk yadda kika ga dama da ita.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba cikin murya mai nauyi,
“Amma ina so ki sani... duk wani abu da za ta aikata, da kuma duk abin da zai biyo baya... to ki sani, ke ce za ki ɗauki alhaki. Ba ni ba.”
Daga haka ya juya, ya fice daga ɗakin.
Ya na fita... Mama Sabuwa ta zabga wani uban tsaki,
“Mtswww! Toh sai me? Kawai ka haifi ɗanka, ka dinga masa baƙin ciki. Yarinya ta samo saurayi, ɗan babban gida. Ya kawo ta a mota, har da tsaraba. Sai kuma ka ɗauki baƙin hali ka ɗorawa kanka. Idan ɗan iska ne, zai kawo ta har gida ne? Haba! A dinga abu da tunani mana.”
Mama Sabuwa ta dubi Bintu cike da zaƙuwa, sai ta kama hannunta ta zaunar da ita bakin gado.
“Ke Bintu, ina kika tsaya a daren nan? Ba kya tsoron ki haɗu da mugayen mutane a hanya? Kin manta yanzu gari ba tsaro?”
Sai Bintu ta turo baki,
“Mama, wani ne fa a wajen. Na fito zan taho, sai yace yana sona. Shi ne yace zai kai ni gida. Kuma da na shafa wannan humrar da kika ba ni bayan mun shiga mota... shi ne fa yace mu tsaya. Ya yi min siyayya, har da kuɗi ma ya ba ni.”
Ta ƙarasa tana buɗe jakarta, ta ciro bandir ɗin sabbin ₦500 notes.
Mama Sabuwa ta zaro ido, “Ke! Dan Allah!!”
“Wallahi Mama. Kuma na yi kawaye ’yan gayu. Har numbers ɗinsu na karɓa.”
Mama Sabuwa ta yi wata irin dariya, “Kaji rabo ai na faɗa miki. Kai barka! Gaskiya maganin Mai Tsidau yana aiki. Daga karɓowa amfani ɗaya kenan ya yi haka?”
Sai Bintu ta ci gaba, “Ita Raihanar da kike ganin zata dusashe ni... sai gashi ko kallo ba su isheta ba. Ni suka kula. Ba ki ga yadda suka dinga ja na ba? Anata harkar arziki. Kuma Mama... da farko fa an hana ta shiga. Ni na ɗauke shegen pass ɗinta na shiga tun a mota kafin mu je.”
Ta ƙarasa tana dariya, “Tana can tana surutu. Kin ganshi?”
Ta saka hannu a rigarta, ta ciro gate pass ɗin.
Suka sake fashewa da dariya tare.
“Toh... ya aka yi ta shiga?” Mama Sabuwa ta tambaya.
Bintu ta tabe baki, “Watace ta zo tana da extra, shi ne ta ba ta.”
Ta girgiza kai tana murmushi, “Bari mu gani... meye a cikin ledar?”
Ta ƙarasa tana janyo ledojin kusa da ita.
———-
Raihana ta durƙusa a gaban Ummanta cikin sanyin jiki.
Aminu da Yusuf duk sun riga sun yi barci, amma Umma tana zaune a falo. Ta rasa yadda za ta yi saboda damuwar da ta cika zuciyarta.
Raihana ta ɗago kai ta kalli Ummar, kafin a hankali ta matsa kusa da ita.
Ta ɗora kanta kan cinyarta, sannan ta riƙe hannunta cikin taushin murya.
“Umma... ki yi haƙuri. Na san na ja miki bacin rai a wajen Baffa. Wallahi ba da gangan na yi ba. Ba mu samu shiga da wuri ba. Amma dan Allah ki yi haƙuri. Ba zan sake ba.”
Umma ba ta ce komai ba, sai ta ci gaba da kallonta cikin shiru.
Bayan ɗan lokaci ne ta buɗe baki cikin nutsuwa, “Waye ya dawo da ku?”
Gabban Raihana ya faɗi. Ta ɗan ɗago kanta daga cinyar Ummarta, ta haɗiye yawu.
Kafin ta samu ƙarfin yin magana... Umma ta sake cewa,
“Kar ki yi min ƙarya. Ki faɗa min gaskiya. Ko ni ban gan ki ba... Ubangijin Al’arshi yana ganinki.”
Nan take hawaye suka zubo wa Raihana. Ta goge su da bayan hannunta.
Cikin murya mai cike da tsoro da fargabar abin da Umma za ta ce, ta buɗe baki,
“Wallahi Umma... mun fito muna neman abin hawa. Duk wanda muka tsayar sai ya ce ba zai je ba. Daga baya ne wani mutum ya tare mu a hanya. Na dage ba za mu hau ba... amma ya dinga mana magiya. Yana ta rantse mana cewa ba zai cutar da mu ba. Har daga ƙarshe...”
Ta sake haɗiye yawu da ƙyar, “…Maryam da Khausar suka dage sai mun hau. Shi ne ya kawo mu har bakin layin nan.”
Ta ƙarasa tana sauke kanta ƙasa. Zuciyarta kuwa na bugawa da ƙarfi, tana jiran abin da Umma za ta ce.
Umma ta yi shiru na wasu daƙiƙu. Ta shafa kan Raihana a hankali.
“Alhamdulillah da Allah Ya dawo da ku lafiya.”
Ta sauke numfashi, “Sai dai... ki san abin da ya fi bani tsoro? Ba mutumin nan ba. Qaddara ce.”
Raihana ta sunkuyar da kai.
Umma ta ci gaba, “Ba kowanne mai murmushi ne amintacce ba. Ba kowanne mai rantsewa da Allah ne mai gaskiya ba. Shaiɗan ma ya san yadda ake amfani da kalmomi masu daɗi.”
Ta kama hannun Raihana,
“Allah Ya tsare ku yau. Amma ba kowace rana ake samun irin wannan kariyar ba. Ki yi alƙawari da ni... duk inda kika ga zuciyarki ta ce a’a, a inda ya dace ba wai son rai ba. Ko duniya gaba ɗaya ta ce eh... ki bi zuciyarki. Saboda mumini idan Allah yana son ya tsare shi... sai Ya sa zuciyarsa ta kasa amincewa da wani abu.”
Raihana ta fashe da kuka, “Na yi alƙawari Umma.”
Umma ta rungume ta, “Allah Ya kiyaye min ke. Ni ba na tsoron fushin Baffa... abin da nake tsoro shi ne wani abu ya faru dake.”
Kalmar ta tsaya wa Raihana a zuciya. Ta ƙara matse Umma tana kuka.
A hankali Umma ta ce, “Ki tashi... ki je ki kwanta. Allah Ya tashe mu lafiya.”
Raihana ta goge hawayen fuskarta da bayan hannunta, cikin sanyin murya ta ce, “Toh Umma.”
Ta miƙe a hankali. Kafin ta juya ta nufi ɗakinta, ta sake kallon Umman nata na ɗan lokaci. Sai ta juya ta tafi.
Umma kuwa... ta bita da kallo har sai da ta ɓace cikin corridor.
Ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Ta ɗaga hannayenta sama,
“Ya Allah... Ka tsare min ‘ya’yana. Ka nisanta su daga fitinar zamanin nan. Ka sa su kasance cikin amincinka a ko’ina suka shiga.”
Ta share hawayen da suka taru a gefen idanunta. Sannan ta miƙe a hankali.
Ta kashe fitilar falon... ta nufi ɗakinta, zuciyarta cike da wani irin nauyin da ba ta iya fassarawa.
⸻
*ZAYD ARMAAN*
A hankali Zayd ya miƙe daga kan kujerar da yake zaune. Ya ɗan gyara hannun rigarsa, sannan idanunsa suka sauka kan agogon hannunsa. Lokaci ya ja sosai.
Ya ɗaga kansa ya kalli Imraan, wanda har yanzu yake kwance cikin natsuwa kamar babu wani abu da yake damunsa a duniya.
“I have to take my leave.”
Muryar Zayd ta kasance cikin nutsuwa, babu wata alamar gaggawa a fuskarsa.
Imraan ya ɗaga gira yana kallonsa, “Already?” ya faɗa cikin mamaki, sannan ya miƙe tsaye.
“Amma da ka bari mu je birthday party ɗin nan mana, rascal.”
Ya yi murmushi mai cike da mugunta,
“Wallahi zai yi kyau. Akwai zafafan babes a can. Kai ma watakila wannan karon zaka samu wadda zata karya wannan Mr. Perfect ɗin naka.”
Ya fara dariya yana girgiza kai,
“Ni dai ina mamakin yadda zaka iya zama mutum kamar kai, amma ka ƙi duk wani abu da yake sa mutum jin daɗin rayuwa.”
Zayd bai amsa ba. Kai tsaye ya nufi ƙofa kamar bai ji komai ba.
Da ya kusa fita sai ya tsaya kaɗan,
“I don’t have time for that nonsense.”
Ya faɗa cikin sanyin murya, sannan ya ci gaba da tafiya.
Imraan ya fashe da dariya,
“Look at you, Mr. Perfect. A ranar lahira fa kar ka yi tsammanin za ka je da suit ɗinka da wannan serious face ɗin naka.”
Zayd bai kalle shi ba, sai dai ɗan murmushi kaɗan ya bayyana a gefen bakinsa wanda Imraan bai samu damar gani ba, “Very funny.”
Imraan ya yi dariya, “See? Har murmushi ma kana boyewa.”
Suka sauka downstairs.
Da suka isa cikin falon, wata murya ta kira sunan Zayd, “Yaya!”
Nan take Seeyama ta miƙe da sauri daga inda take zaune.
Ta gyara EarPod dinta tana zuwa wajensu da sauri, tana tafiya da wani irin salon shagwaɓa kamar tana so kowa ya lura da ita.
“Ina ƙoƙarin kawo maka abinci ne fa.”
Ta faɗa da muryar taushin shagwaɓa.
Amma Zayd bai tsaya ba. Bai ma kalleta ba.
“Don’t mind, I’m full.”
Ya amsa a taƙaice.
Maganar ta sauka a kanta kamar ba ta shirya jin haka ba.
Ta tsaya a wajen tana kallonsa yayin da yake wucewa. Amma Zayd bai nuna wani abu ba.
Ya ƙarasa wajen mommy kai tsaye,
“Mommy, I’m leaving.”
Fuskar matar ta yi murmushi, “Okay, son. Thanks for coming.”
Zayd ya ɗan jinjina kai. Bai cika magana ba, amma yadda yake girmama ta ya nuna irin matsayinta a zuciyarsa.
Sai ta ƙara da cewa, “Ka gaida Ummie. Kuma ka tuna mata jibi ina nan tafe, okay?”
“Okay.”
Shi kaɗai ya amsa. Sannan ya juya ya nufi ƙofa.
Imraan ya biyo bayansa yana murmushi.
Mommy ta kalli Seeyama, sannan ta mata alama da ido. Kamar tana cewa: ki bishi mana.
Seeyama kuwa ba ta ɓata lokaci ba. Ta ɗauki mayafinta da ke gefen mommy ta bi bayansu.
Har suka isa compound. Zayd ya riga ya nufi motarsa yayin da Imraan yake kusa da shi.
Sai ya ji muryar Seeyama a bayansa, “Yaya!”
Sai Imraan ya juya, “Lafiya kike wani bin mutane haka?”
Ya faɗa yana kallon yadda take zuwa da sauri.
Seeyama ta turo baki, “Ni ba wajenka nazo ba.”
Ta yi kamar za ta wuce Imraan, “Ni magana nake so in yi da Yaya.”
Imraan ya ɗaga gira, “Wow.”
Ya kalli Zayd, “Apparently, I’m invisible.”
Zayd ya ɗan girgiza kai, “Imraan, ka matsa gefe,” yana dariya.
Seeyama ta sake matsowa kusa da Zayd,
“Yaya, ka ce fa za mu yi magana ranar nan.”
Ta ɗan sauke murya,
“Na yi maka WhatsApp message kusan week ɗaya kenan, amma baka buɗe ba.”
Zayd ya kalleta, “Yaushe kenan?”
Ta ɗan yi mamaki,
“Yaya... kaine fa da na kira ka ka ce kana busy. Shine ka ce in turo maka a WhatsApp.”
Ta yi shiru tana kallonsa.
Zayd bai ce komai ba na ɗan lokaci. Sai ya ce,
“Okay. Zan duba.”
Wani murmushi ya bayyana a fuskarta, “Toh ka duba.”
Bai amsa ba. Ya buɗe ƙofar mota.
Kafin ya shiga, ta matso kusa da shi sosai ta rage murya,
“I love you... and drive safe, okay?”
Ta ɗan yi murmushi.
Zayd ya tsaya na daƙiƙa. Amma bai ce komai ba.
Kawai ya shiga motar ya kunna engine.
Imraan ya matso yana daga hannu,
“Bye dude. Take care.”
Zayd ya ɗan jinjina kai.
Gateman ya buɗe gate.
Motar ta yi reverse a hankali, sannan ta fice daga gidan.
Seeyama ta tsaya tana kallon bayan motar har sai da ta ɓace.
---
***