THE CHOSEN ONE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER TEN: 10*
*THE CHOSEN ONE*
*JIDDAAH BARKUM*
————————
*KADUNA MEDICAL UNIVERSITY*
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, babban Conference Room na Faculty of Medicine ya cika da manyan lecturers daga sassa daban-daban.
A gaban ɗakin kuwa, Dean of Faculty, Professor Ibrahim Sani, na zaune tare da Head of Department na Community Medicine, shugaban Student Affairs da wasu professors masu shekaru da gogewa.
A hankali Dean ya gyara microphone ɗin da ke gabansa,
“Good morning, colleagues.”
“Good morning, sir,” suka amsa gaba ɗaya.
Ya ɗan yi murmushi,
“Thank you all for coming at such short notice.”
Ya ɗaga brown envelope ɗin da aka kawo masa da safe,
“As most of you already know, Armaan Group of Companies has officially confirmed its partnership with Kaduna Medical University for this year’s Medical Innovation and Community Health Outreach.”
Nan take ɗakin ya kaure da ɗan tafi.
Dean ya ci gaba,
“This is one of the biggest collaborations our faculty has ever received.”
Ya ɗan dakata,
“The event will include free medical outreach, research presentations, scholarship announcements and the commissioning of a brand-new Medical Simulation Laboratory.”
Professor Musa ya gyada kai,
“This is a huge opportunity.”
“It certainly is,” Dean ya amsa.
Sai ya ɗan gyara zama,
“However...”
Nan take ɗakin ya yi shiru,
“There is one responsibility they have entrusted to this faculty.”
Dukkan idanu suka dawo kansa.
“They requested that we nominate one outstanding final-year medical student who will represent the entire student body and deliver the keynote speech.”
Nan take aka fara ɗan magana a tsakanin lecturers.
Professor Amina ta ce,
“So... who are we considering?”
Dean ya jingina da kujerarsa,
“That is exactly why I called this meeting.”
Ya ɗora hannu kan tebur,
“I want merit, no favoritism, no influence, no politics. The best student should represent this university.”
Dukkan su suka gyada kai cikin amincewa.
Professor Idris ne ya fara magana,
“If we’re talking about academics... I believe Raihana deserves to be considered.”
Mutane da dama suka gyada kai.
Professor Fatima ta ɗora da cewa,
“Not only academics. She’s respectful, she’s disciplined, and she has never been involved in any misconduct.”
Student Affairs Officer ya ce,
“Even during community postings... patients always commend her.”
Professor Musa ya ce,
“I supervised her research. Outstanding work.”
Dean ya rubuta wani abu cikin notebook ɗinsa,
“Any other names?”
Professor Ahmed ya ce,
“There are two or three brilliant students, but if we’re choosing someone who combines academic excellence, leadership, confidence and good character... Raihana stands out.”
Dean ya sake kallon sauran lecturers,
“Does anyone disagree?”
Dukkan ɗakin ya yi shiru, ba wanda ya ɗaga hannu.
Professor Ibrahim ya ɗan yi murmushi,
“So... I believe we have a unanimous decision. Raihana Musa Maiturare.”
Nan take aka ji ɗan tafi a hankali daga wasu lecturers.
Dean ya ɗauki biro ya sa hannu a nomination form,
“Congratulations to her... although she doesn’t know yet.”
Suka yi murmushi.
Dean ya miƙa takardar ga Student Affairs Officer,
“Please ask her to come to my office after her Community Medicine lecture.”
“Yes, sir.”
Ya miƙe yana tattara takardunsa,
“And remember... when she comes, I don’t want unnecessary attention. Let’s keep this confidential until the official announcement.”
“Understood, sir.”
Meeting ɗin ya ƙare, lecturers suka fara fita ɗaya bayan ɗaya.
A wajen corridor kuwa, Student Affairs Officer ya tsaya yana kallon timetable ɗin final-year students.
Ya zaro wayarsa, ya kira wani administrative staff,
“Hello. Yes, sir. Immediately Community Medicine lecture ends, tell Raihana Musa that the Dean wants to see her in his office... personally.”
“Right away, sir.”
Wayar ta katse.
A daidai wannan lokacin kuwa, ba tare da ta san komai ba, Raihana na zaune a cikin lecture theatre tana rubuta notes cikin natsuwa.
Lecture ɗin Community Medicine ya zo ƙarshe,
“That will be all for today,” lecturer ɗin ya faɗa yana rufe file ɗinsa.
Nan take ɗalibai suka fara tattara littattafansu, hayaniyar tattaunawa ta mamaye lecture theatre.
Raihana ta rufe notebook ɗinta cikin nutsuwa, ta saka biro a cikin purse ɗinta.
Haulat ta matsa kusa da ita,
“Zaki je library ne yau?”
Raihana ta gyada kai,
“Ina da wasu topics da nake son dubawa.”
Zaynab, wata course mate ɗinsu, ta yi murmushi,
“Ke dai kullum karatu.”
Raihana ta yi dariya a hankali,
“Final year ne fa.”
Kafin su ƙara wata magana, wani staff na Faculty ya tsaya a bakin ƙofar lecture hall,
“Excuse me...”
Dukkan ɗaliban suka waigo,
“Wacece Raihana Musa?”
Raihana ta ɗaga hannu,
“Ni ce.”
Staff ɗin ya yi mata murmushi,
“Dean yana son ganinki yanzu.”
Ta ɗan yi mamaki,
“Yanzu?”
“Eh, yanzu.”
“To.”
Haulat ta kalle ta,
“Kin san dalili?”
Raihana ta girgiza kai,
“A’a. Wataƙila wani abu ne game da project. In sha Allah alkhairi ne,” Haulat ta ce.
Raihana ta gyara books dinta ta ɗauki jakarta sannan ta kama hanyar Administrative Block.
Da ta isa bakin office ɗin Dean, ta tsaya na ɗan lokaci, ta daidaita numfashinta, sannan ta buga ƙofar a hankali.
“Shigo.”
Ta buɗe ƙofar, da sallama ta shiga,
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam,” Dean ya amsa yana murmushi.
Ta ƙarasa cikin ladabi,
“Good morning sir.”
“Morning,” ya amsa har yanzu da murmushi a fuskarsa,
“Zauna, ’yata.”
“Nagode, sir.”
Ta zauna a gefen kujerar da ke gabansa, hannayenta a haɗe cikin nutsuwa.
Dean ya ɗan kalleta na wasu daƙiƙu,
“Yaya karatu?”
“Alhamdulillah.”
“Ba wata matsala?”
“A’a, Alhamdulillah.”
Ya gyada kai,
“Hakan ya yi kyau.”
Sai ya buɗe wani file da ke gabansa,
“Kin san dalilin da ya sa na kira ki?”
Ta girgiza kai,
“A’a, ban sani ba.”
Dean ya yi murmushi,
“Da farko, ina so na yaba miki.”
Ta ɗago kai kaɗan,
“Mun duba sakamakon karatunku, halayenki da kuma rahotannin lecturers.”
Ya ci gaba,
“Kusan kowa ya yi magana mai kyau a kanki.”
Raihana ta sunkuyar da kai,
“Alhamdulillah.”
“Babu lecturer da ya kawo ƙorafi game da ke, haka kuma, kina cikin ɗaliban da suka fi ƙoƙari a year dinku.”
Ta ce cikin farinciki,
“Nagode sosai, sir.”
Dean ya ɗauki wata takarda ya miƙa gabanta,
“Faculty ta yi zama yau. Mun tattauna sosai, daga ƙarshe kuma... an zaɓe ki ki wakilci dukkan ɗaliban Faculty of Medicine.”
Idanun Raihana suka ɗan buɗe cikin mamaki,
“Ni...?”
Dean ya yi murmushi,
“Eh, ke. Za ki gabatar da jawabin ɗalibai a babban taron haɗin gwiwa tsakanin Kaduna Medical University da Armaan Group of Companies.”
Na ɗan lokaci ta kasa cewa komai.
*ARMAAN???*
Ta maimaita a zuciyarta.
Ba don ba ta farin ciki ba, sai don mamakin me kuma zai sake hadata da wnn sunan??
Ta sauke numfashi,
“Nagode sosai da wannan dama sir. Ina fatan ba zan ba ku kunya ba.”
Dean ya gyada kai cikin gamsuwa,
“Shi ya sa ma aka zaɓe ki. Ba wai saboda kin fi kowa wayo ba kaɗai, har da tarbiyya, natsuwa da kuma yadda kike wakiltar makaranta.”
Ya ɗan matsa file ɗin gabanta,
“Akwai kusan mako guda kafin taron. Ki fara shirya jawabi. Ba sai ya yi tsawo ba, amma muna son ya kasance mai ma’ana.”
“Zan yi iya ƙoƙarina, In sha Allah.”
“Allah Ya taimaka.”
“Ameen.”
Dean ya sake murmushi,
“Kuma... wannan labarin a yanzu ya tsaya tsakaninki da Faculty. Ba a fitar da sanarwar a hukumance ba tukuna.”
Ta gyada kai,
“Za a kiyaye.”
“Madalla.”
Ta miƙe tsaye,
“Nagode sosai, sir.”
“Allah Ya ba ki sa’a.”
“Ameen.”
Ta yi sallama ta fita daga office ɗin cikin nutsuwa.
Amma da ƙofar ta rufe, ta tsaya na ɗan lokaci a corridor.
Zuciyarta na bugawa a hankali.
*ARMAAN???*
Zuciyarta ta sake ambatar sunan, sai kuma wani tunanin.
Ba ta taɓa tsammanin za a ɗora mata irin wannan babban nauyi ba.
Ta ɗago idanunta tana kallon harabar makarantar, a zuciyarta ta furta cikin sirri,
“Ya Allah... Ka ba ni ikon sauke wannan nauyi.”
————————
*ARMAAN MANSION*
Suhaila na kwance sharaf a kan doguwar kujera da ke falon gidan, wayarta riƙe a hannu.
Tun daga Instagram ta koma TikTok, daga TikTok kuma ta tsinci kanta a Snapchat, tana ta yawo a social media kamar wacce ke da wata muhimmiyar manufa.
Lokaci-lokaci sai ta yi murmushi ita kaɗai idan wani video ya bata dariya.
Ko kaɗan ba ta lura da lokacin da Ummie ta fara saukowa daga saman stairs ba.
A hankali Ummie ta ƙaraso falon, ta zauna a kujerar da ke kusa da ita.
Na wasu daƙiƙu tana kallon Suhaila kawai, sannan ta girgiza kai,
“Wannan shi ne aikin kenan?”
Suhaila ba ta ma ɗaga kai ba,
“Hmm?”
Ummie ta ɗan ɗaga murya,
“A yi ta danna waya, Instagram, TikTok, WhatsApp... kwata kwata ba kwa gajiya.”
Sai ta sauke ajiyar zuciya,
“Wallahi ban ma tuna yaushe ne lokaci na ƙarshe da na ga kina karatun Al-Qur’ani ba, ko kina zaune kina duba notes ɗinki. Wannan zamanin na waya dai... Allah Ya shirye ku.”
A wannan karon Suhaila ta ɗago kai, ta turo baki kamar ƙaramar yarinya,
“Ummie... group ɗin school fa nake dubawa. Ko wani lecturer ya turo cewa lecture din gobe ya fasa. Ba wani abin daban ba.”
Ummie ta kalle ta da idon da ya nuna sarai ba ta yarda ba,
“Ni za ki faɗawa haka?”
Suhaila ta yi murmushi mai laifi,
“Wallahi da gaske.”
Ummie ba ta sake cewa komai ba, ta san Suhaila. Idan ta ce group ɗin school... to tabbas tsakanin videos ɗari akwai message ɗaya na school. Sai dai ta ƙyale ta.
Shiru ya ɗan ratsa falon.
Can kuma sai Suhaila ta kashe wayar, ta miƙe zaune, ta matsa kusa da Ummie, ta jingina jikinta da ita kamar ƙaramar yarinya,
“Ummie...”
“Na’am?”
Ta ɗan yi murmushi,
“Dan Allah... yaushe Akhii zai yi aure ne?”
Ummie ta waigo tana kallonta,
“Lafiya?”
Suhaila ta yi dariya,
“Wallahi tun ranar da muka je bikin Aseeya, na kasa daina tunanin bikin. Komai yayi kyau, an yi hidima sosai. Sai na ce a raina... ni ma ina son na ga an yi irin wannan biki a gidanmu.”
Ummie ta yi dariya,
“Ko dai kin fara son a yi naki ne?”
Nan take Suhaila ta zaro ido,
“Kai Ummie!”
Ta dariya tana girgiza kai,
“Wallahi ba haka nake nufi ba. Akhii ne fa babba, shi ya kamata ya fara.”
Ummie ta shafa bayanta a hankali,
“Shi namiji ne, ke kuma mace ce. Ko yaushe zai iya aure, amma ita mace lokacinta kalilan ne.”
Suhaila ta turo baki,
“Ai Ummie...”
Ta ɗan matsa kusa da ita tana rage murya,
“Ku aura masa Seeyama mana.”
Murmushin da ke fuskar Ummie ya ƙara faɗaɗa,
“Kinsan fa irin son da take masa. Shi kuma ko kallonta baya yi.”
Suhaila ta girgiza kai,
“Wallahi son da take masa ma ya isa ya riƙe musu aure...”
Maganar ta tsaya cak, saboda... tun kafin ta ƙarasa, wani sanyin ƙamshi mai daɗi ya mamaye falon.
Turaren da ko bacci kake yi a gidan ana aka saka shi sai ka ji.
Idonta ya ɗaga zuwa saman stairs.
Daidai lokacin... Zayd ya fara saukowa.
Blue-black kaftan ɗinsa mai kyau ya zauna tamkar a jikinsa aka ɗinka, matching ɗin hular ya ƙara masa kwarjini, yayin da agogon azurfarsa ke ɗaukar hasken chandelier ɗin falon.
Kowace taka da yake yi cike take da nutsuwa da izza.
Har ya iso gabansu, ba tare da ya tsaya wani wuri ba, sai ya durƙusa a gaban Ummie, kamar yadda ya saba yi a duk lokacin da zai fita.
Ya kama hannunta cikin girmamawa, suka yi musabaha, sannan ya ɗaga hannun ya sumbace shi a hankali.
“Ummie...” ya kira cikin sassanyar murya,
“Zan fita.”
Ummie ta zuba masa ido.
Wani lokacin takan rasa abin da ya fi yi masa kyau. Suit ɗin office? Ko manyan kayan Hausa? Kananan Kaya ne? Ko kuma simple kaftan irin wanda yake sanye da shi yanzu?
Duk abin da ya saka... sai ka rantse kamar domin shi aka ƙera shi.
A hankali ta ɗora tafin hannunta kan kansa,
“To, Zayduna... Allah Ya tsare min kai. Allah Ya kiyaye ka daga dukkan wani sharri. Allah Ya albarkaci rayuwarka.”
Sai ta juya ta kalli Suhaila dake kallonsu da murmushi kwance a fuskarta,
“Kafin ga karasa data yar uwarka.”
“Ameen, Ummie,” ya amsa cikin ladabi.
“Ameen! Ameen!”
Shi ne kawai kalmar da ta ta maimaituwa a falon.
Zayd ya miƙe tsaye.
Yana zuwa daidai gaban Suhaila sai ya tsaya.
Ya miƙa hannu ya ɗan rankwashe ta a kai kaɗan, ba mai zafi ba,
“Parrot.”
Ya faɗa yana wucewa.
“Wayyoooo!”
Suhaila ta kama kanta tana fashewa da kukan ƙarya,
“Akhii! Me na yi maka ne?”
Ko juyowa bai yi ba, yana ci gaba da tafiya kawai ya ce,
“Surutu.”
Suhaila ta ɗaga murya daga bayansa,
“To ka tabbatar ba ka dawo gida hannu bakomai ba! Ka siyo min all the goodies out there!”
Zayd bai waiwaya ba, sai dai hannunsa ya ɗaga sama kaɗan, alamar ya ji abin da ta ce.
---
***