THE TURNING POINT
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-ELEVEN: 11*
*THE TURNING POINT*
*JIDDAAH BARKUM*
⸻
Suhaila ta bi ƙofar da idanunta har sai da ta rufe, sai ta saki ƙaramar dariya,
“Wallahi Ummie...”
Ta girgiza kai,
“Akhii ɗin nan idan ba ku matsa masa ba, zai kai shekara arba’in bai yi aure ba.”
Ta ɗan taɓe baki,
“Shi fa ko a jikinsa, office kawai ya saka gaba, meeting, business, travelling, kullum haka.”
Ummie ta yi murmushi tana girgiza kai,
“Ki bar shi. Zayd ba ya son a matsa masa kan abin da bai shirya ba.”
Suhaila ta ja numfashi,
“Amma fa Seeyama za ta mutu da jira.”
Ta ɗan yi dariya,
“Kin san Ummie, Seeyama ba ta kula ko wani namiji gaba ɗaya, duk saboda Akhii. Kullum shi take bi da addu’a, shi take jira, shi kuma ko kallonta bai yi.”
Ummie ta ɗan yi shiru kafin ta ce cikin nutsuwa,
“Soyayya ita kaɗai ba ta isa aure ba. Idan zuciyar mutum ba ta karkata ba, dole ne a bar komai a hannun Allah.”
Ta ɗan gyara zamanta,
“Allah ne Mai kawo lokaci. Idan lokacin Zayd ya yi... babu wanda zai hana abin faruwa.”
Suhaila ta turo baki,
“To ni dai ina son ranar da zan ga Akhii ya ce yana son wata.”
Ta yi dariya,
“Wallahi sai na yi sujadar godiya.”
Ummie ta kasa riƙe dariyarta,
“Ke kam ba za ki taɓa daina surutu ba.”
Suhaila ta rungume hannun Ummie tana dariya,
“Ni fa gaskiya nake faɗa. Saboda idan Akhii ya ci gaba da wannan halin...”
Ta ɗan ɗaga gira cikin sigar wasa,
“Ko yarinyar da Allah Ya rubuta masa za ta gaji da jiransa.”
Ummie ta girgiza kai tana murmushi,
“Allah Ya shirye ki, Suhaila.”
“Ameen...” ta amsa cikin dariya,
“Amma ki rubuta wannan magana, Ummie... ranar da Akhii ya ce yana son wata, wallahi gidan nan ba zai kwana lafiya ba saboda murna.”
————-
Zayd na fita daga falon, kai tsaye ya nufi wajen motarsa.
Kamar yadda ya saba, driver ɗinsa ya yi saurin matsowa domin ya buɗe masa ƙofar motar.
Sai dai Zayd ya ɗaga hannu a hankali,
“Ba sai ka zo ba.”
Driver ɗin ya tsaya,
“Sir?”
“Yau ni kaɗai zan fita.”
“Okay, sir.”
Ya juya ya kalli guards ɗin da ke bakin ƙofar gidan,
“Ba na buƙatar escort. Kar ku biyo ni.”
“Understood, sir.”
Ya shiga motar, ya kunna engine ɗin.
Bayan ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙu, ya fice daga Armaan Mansion cikin nutsuwa.
Ba shi da wani takamaiman inda zai nufa, kawai dai ya gaji da zaman gida, yana jin yana buƙatar ɗan fitar da kansa ya sha iska.
Ba tare da wani dogon tunani ba, ya juya steering ɗin motar zuwa hanyar guest house ɗinsa.
Ba ko yaushe yake zuwa can ba, a mafi yawan lokuta, Imraan ne ke mamaye wajen tare da abokansa, kuma Hakan bai dame shi ba, tunda an gina guest house ɗin ne domin hutu da baƙi.
Ya ɗan kalli agogon hannunsa, 3:15 PM.
Ya sake maida hankalinsa kan hanya, cikin nutsuwa yake tuƙi, ba gudu, ba sauri.
Bayan wasu mintuna kaɗan ya isa ƙofar guest house ɗin.
Maigadin na hango motarsa daga nesa ya miƙe tsaye cikin girmamawa, da sauri ya buɗe gate,
“Good afternoon, sir.”
Zayd ya ɗaga masa kai kaɗan kawai, alamar ya amsa.
Motar ta kutsa cikin compound ɗin cikin natsuwa, ya yi parking a wurin da aka tanada.
Yana fitowa daga motar, idanunsa suka sauka kan wata baƙar Mercedes G-Wagon, sai wasu manyan SUVs guda biyu da bai san masu su ba.
Ya ɗan haɗe gira,
“Imraan yana da baƙi kenan...”
Yana nufar entrance ɗin gidan, tun daga compound yake iya jin hayaniya.
Sautin kiɗa mai ƙarfi na tashi daga cikin gidan, lokaci zuwa lokaci kuma ana jin dariya da tafi.
Zayd ya sauke numfashi a hankali, ya girgiza kai kaɗan,
“Wannan Imraan...”
Ya ƙarasa bakin ƙofar, ba tare da ya tsaya ba, ya tura ta ya shiga.
Da ƙofar ta buɗe, idanunsa suka fara yawo cikin falon.
Falon ya sauya tamkar wani private lounge, manyan sofas ne cike da samari.
A tsakiyar centre table kuwa, akwai faranti cike da snacks iri-iri: chicken, barbecue, pizza, burgers, fruits, soft drinks, sai kuma kwalabe da dama na giya a warwatse a kan tebura, wasu har an buɗe su.
A gefe guda kuma hayakin shisha ya cika iska, yana gauraye da ƙamshi mai nauyi.
Kiɗan da ke tashi daga speakers ya mamaye ko’ina, wasu na hira, wasu na dariya, wasu kuma suna wasa da cards.
Da ƙofar ta buɗe, duk idanu suka juya lokaci guda, hayaniyar ta ɗan lafa.
Imraan ne ya fara hangoshi, da fara’a ya miƙe tsaye,
“Wallahi!” ya fashe da dariya,
“Ni har na fara tunanin ba ka san hanyar zuwa guest house ɗin nan ba.”
Duk suka yi dariya.
Ya ƙaraso yana buɗe hannayensa,
“Maraba da CEO!”
Ya tsaya gaban Zayd yana kallonsa daga sama har ƙasa, sai ya girgiza kai da murmushi,
“Kai ma ka zo service ne yau?”
Nan take falon ya kaure da dariya.
Zayd kuwa ya zuba masa ido cikin natsuwa, fuskarsa ba ta nuna ko dariya ko ɓacin rai ba.
Ya ɗan kalli kwalaben giyar da ke kan teburi, ya kalli shishar da hayakinta ke tashi, sannan ya maida kallonsa kan Imraan,
“Na ga kamar na zo a lokacin da bai dace ba,” ya faɗa cikin nutsuwa.
Imraan ya sake dariya,
“A’a mana. Ka zo a daidai. Ko da ba za ka sha komai ba, ka zauna mu yi hira.”
Ya ɗan matso kusa da shi yana rage murya,
“Ko dai yau ka gaji da zama Mr. Perfect?”
Zayd ya yi murmushi kaɗan kawai, bai ce komai ba.
Ya nufi ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗan nesa da sauran mutanen, ya zauna cikin nutsuwa.
Idanunsa suka sake zagayawa falon.
A gefe guda wasu na ci gaba da wasan cards, wasu kuma na ta hira cikin dariya, sautin music ɗin ya ci gaba da tashi a hankali, yayin da wasu ke ɗauke da glasses a hannunsu.
Imraan ya karasa gaban Zayd yana gyara rigarsa,
“To bari na kawo maka ruwa ko juice,” ya faɗa yana kashe wa Zayd ido,
“Ai yau kai ne guest ɗina.”
Zayd ya ɗago ya kalle shi da wani irin kallon gargadi,
“Imraan... kada ka raina min hankali.”
Imraan ya dafe ƙirji kamar wanda aka zarga da laifi,
“Wallahi! I promise... ba zan ba ka wani abu da zai bugar da kai ba.”
Mutanen da ke kusa suka yi dariya,
“CEO ai ya san halinka,” ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana murmushi.
Imraan ya taɓe baki,
“Ku dai ku tsaya ku gani.”
Ya juya ya nufi mini bar ɗin da ke wani gefen falon.
Da ya juya baya, murmushi mai cike da mugunta ya bayyana a fuskarsa.
Ya ɗauki crystal glass mai tsabta, da farko ya zuba orange juice kaɗan a ƙasa, sai ya ɗauki wata kwalbar whisky mai tsada, ya zuba kaɗan cikinta, ya haɗa da wasu ice cubes, ya ɗan jujjuya glass ɗin.
A kallon farko... ko wa zai rantse juice ne kawai.
Ya juyo yana murmushi,
“Special drink... ga shi.”
Zayd ya karɓa ba tare da wata-wata ba, ya ɗan kalli glass ɗin,
“Orange?”
Imraan ya gyada kai da sauri,
“Fresh juice. Na musamman ma.”
Zayd ya sake kallonsa na ɗan lokaci, sai ya ce,
“Allah Ya sa ba ka shirya min wani wasan banza ba.”
Imraan ya sa hannu a ƙirji,
“Ni? Wallahi ka ci amanata idan ka yi wannan tunanin.”
Dariya ta sake tashi daga wasu da ke falon.
Zayd ya girgiza kai kawai, ya kai glass ɗin bakinsa, ya kurɓi kaɗan.
Sanyin ice ɗin ya fara ratsawa maƙogwaronsa, ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙu, sai ya sake ɗan kurɓa.
Imraan kuwa... tun daga gefe yake kallonsa, yana cizon leɓensa don kada dariya ta kufce masa.
Abokansa ma suka fara kallon juna cikin ɓoyayyen murmushi.
Ɗaya daga cikinsu ya raɗa masa a hankali,
“Ka tabbata wannan ba zai gano ba?”
Imraan ya yi murmushi yana girgiza kai, cikin muryar rada yace,
“Ba zai gano ba... sai dai idan tasirin ya fara aiki.”
Zayd kuwa bai san komai ba, yana ci gaba da shan abin cikin natsuwa, yana zaton orange juice ne kawai.
Shi kuwa bai san cewa... a wannan karon, Imraan ya yi amfani da amincewar da yake da ita a kansa wajen shirya masa ƙaramin wasa ba.
Sai dai... bai wuce wasu daƙiƙu ba.
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa a hankali, ya ji wani irin zafi mai laushi yana fara ratsawa cikin maƙogwaronsa, kafin ya bazu zuwa ƙirjinsa.
Ya ɗan gyara zamansa, ya kai hannu ya sassauta maɓallin wuyan kaftan ɗinsa, numfashinsa ya ɗan yi nauyi.
Ya sake kai glass ɗin bakinsa ba tare da tunani ba, ya ƙara kurɓa kaɗan.
A wannan karon... komai ya fara sauyawa.
Sautin music ɗin da tun farko yake ji a nesa, sai ya fara shiga kunnuwansa da ƙarfi fiye da yadda yake.
Hayaniyar falon ta fara gaurayawa cikin kansa, ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
Da ya sake buɗe su... sai ya ji kamar hasken chandelier ɗin falon ya ƙaru fiye da yadda ya kamata.
Ya ɗan dafe goshinsa,
“What’s...” kalmar ta tsaya a maƙogwaronsa.
Sai ya ɗan girgiza kai, kamar yana ƙoƙarin tarwatsa wani abu daga cikinsa.
A karon farko cikin kwanakin nan da ya dade bai sha komai ba, ya ji kansa yana yi masa wani irin nauyi da ya dade bai ji ba.
Numfashinsa ya ɗan fita a hankali, idanunsa kuwa... suka fara canja launi, farin idanuwan suka yi ja-ja kaɗan saboda tasirin abin da ya sha.
Imraan na kallonsa daga gefe, da ya lura da canjin, sai ya haɗe leɓɓansa yana ƙoƙarin danne dariya,
“Alama ta fara aiki...” ya faɗa a hankali.
Ɗaya daga cikin abokansa ya buge shi a kafa,
“Wallahi idan ya gane kai ka yi...”
Imraan ya ɗaga kafaɗa,
“Relax. A gobe zai manta.”
A dai-dai wannan lokacin... ƙofar wani private lounge da ke gefen falon ta buɗe a hankali.
Wata budurwa ta fito, sanye take cikin shiga mai ɗaukar ido, hannunta riƙe da wayarta.
Da idanunta suka sauka kan Zayd... sai ta tsaya cak, idanunta suka buɗe sosai,
“Waaaw... my crush is here!”
Da sauri ta juya wajen Imraan,
“Dama ka san Mr. Armaan zai zo? Ba ka faɗa min ba!”
Imraan ya yi dariya,
“Ni ma ban sani ba. Ganinshi kawai na yi unexpectedly.”
Budurwar ta cije leɓenta tana murmushi,
“You’re so mean.”
Ta gyara gashinta a hankali, ta na ɗan shafa gefen wuyanta, sannan ta ɗaga kanta cikin wani irin kwarjini.
Ta fara taku, catwalk mai cike da nuna isa, taku ɗaya... sai wani, har ta fara dosar inda Zayd yake zaune.
Shi kuwa... ya ɗago idanunsa a hankali.
Idanun da suka canja launi gaba ɗaya saboda tasirin abin da ya sha... suka sauka a kanta.
Amma ba wai yana kallonta da sha’awa ba, sai dai kamar mutumin da yake ƙoƙarin fahimtar abin da idanunsa suke gani, yayin da kansa ke ci gaba da ɗaukar wani irin nauyi da ba ya iya fassarawa.
⸻————-
*MALALI*
Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, ƙofar Gidan Baffa Musa ta buɗe a hankali.
Raihana ce ta shigo, abaya ɗinta mai launin cream ta sauko cikin tsari, yayin da ƙaramar veil ɗinta ke zaune da kyau a kanta, a hannunta kuwa jakarta ce da wasu littattafai.
Da ta taka cikin tsakar gidan, ƙamshin miyar da Umma ke dafawa ya bugi hancinta, ya sa wani lallausan murmushi bayyana a fuskarta.
Daga kitchen kuwa, Umma ta fito riƙe da ludayi a hannu, da ta hango Raihana, sai fuskarta ta haskaka,
“Alhamdulillah... kin dawo.”
Raihana ta ƙarasa gare ta cikin ladabi,
“Na dawo, Umma.”
Ta ɗan rungume ta cikin girmamawa,
“Sannu da zuwa.”
“Yauwa, Umma.”
Maryam ma ta fito daga ɗakinsu da sauri,
“Ray!” ta ƙaraso da fara’a ta karɓi jakarta daga hannun Raihana,
“Sannu da zuwa.”
“Yauwa, Maryam.”
Maryam ta kalli fuskarta da kyau,
“Kin gaji ne?”
Raihana ta yi murmushi,
“Kaɗan.”
“Ko yau ma library kika tsaya?”
“Eh, na ɗan tsaya kaɗan.”
Umma ta kalli ’yarta cikin kulawa,
“Je ki canja kaya tukuna. Sai ki zo ki ci wani abu.”
“To, Umma.”
Raihana ta juya ta nufi ɗakinsu.
Sai dai kafin ta shiga... ta tsaya cak, ta waigo ta kalli Umma,
“Umma...”
“Na’am, ’yata.”
“Bayan na canja kaya... ina da labari.”
Umma ta lura da yanayin muryarta. Ba muryar damuwa ba ce, ba kuma ta baƙin ciki ba, sai dai muryar mutum mai ɗauke da wani babban labari.
Ta yi murmushi cikin kwanciyar hankali,
“To, babu matsala. Ina jiranki.”
Raihana ta gyada kai,
“To.”
Ta shiga ɗakinsu a hankali.
Maryam ta bi bayanta da kallo, sannan ta juya ta kalli Umma,
“Umma... kina ganin me ya faru?”
Umma ta girgiza kai a hankali,
“Ban sani ba. Amma na san akwai wani abu da take son gaya mana.”
Ta ɗan yi murmushi,
“Kuma ina fata alkhairi ne.”
Maryam ta yi murmushi ita ma,
“In sha Allah.”
A cikin ɗakin kuwa... Raihana ta rufe ƙofar a hankali, ta ajiye jakarta a kan wani dan table da take karatu, ta zauna bakin katifarta.
Ta sauke ajiyar zuciya mai nauyin farin ciki.
Kalaman Dean suka sake dawo mata cikin kunne,
”...Faculty ta zaɓe ki wakilci dukkan ɗaliban Faculty of Medicine...”
Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, har yanzu... da wuya ta yarda cewa ita ce aka zaɓa.
Wani murmushi mai cike da godiya ya bayyana a fuskarta, a hankali ta furta,
“Alhamdulillahi Rabbil-’Alameen. Ya Allah... Ka ba ni ikon sauke wannan amanar, Ka sanya alkhairi a cikinta.”
Ta buɗe idanunta cikin natsuwa. Sai wani abu ya sake dawo mata, *ARMAAN*... waye wannan??
Bata bawa abin mahimmanci ba, sai ta miƙe ta buɗe wardrobe ɗinta, ta cire abayar da ta sa tun safe, ta rataye ta cikin tsari.
Daga nan ta fito tsakar gida ta ɗauki bokiti ta fito zuwa bandakin tsakar gida, ta debo ruwa daga babban tankin da ke gefe, ta shiga bandakin.
Bayan ta yi wanka, ta fito cikin walwala, iskar yammacin ranar na kaɗa ƙarshen hijabin da ta rataya a kafaɗarta.
Ta koma ɗakinsu, ta shafa mai kaɗan, sannan ta canja zuwa atamfa mai sauƙin kyau, ta ɗaura ƙaramar mayafi da ya dace da kayan.
Da ta gama shiryawa, ta fito zuwa tsakar gidan.
Kafin ta zauna, sai ta ɗan leƙa ɗakin Mama Indo.
Mama Indo na zaune a tabarma, tana ware kayan wanki cikin nutsuwa, da ta hango Raihana, ta ɗago kai,
“An dawo kenan?”
Raihana ta yi murmushi cikin ladabi,
“Eh, Mama. Sannu da gida.”
“Yauwa Sannunku da zuwa.”
Mama Indo ta sake maida hankalinta kan aikin da ke gabanta, Raihana kuma ta juya ta nufi tsakar gidan.
A daidai lokacin Maryam ta leƙo daga ɗakinta, da ta ga Raihana ta gama shiryawa, sai ta fito gaba ɗaya,
“Kin gama?”
Raihana ta gyada kai,
“Eh, na gama.”
“To mu je mu ci abinci.”
Ta ƙara da cewa cikin shagwaɓa,
“Ke nake ta jira tun ɗazu.”
Raihana ta yi dariya a hankali,
“Har yanzu baki ci abinci ba?”
Maryam ta ɗan langwaɓe kai,
“Kin san ba na son cin abinci ni kaɗai. Tun da Bintu ta daina zama tana cin abinci tare da mu... sai na fi son in jira ki.”
Raihana ta kalli ƙanwarta da wani lallausan murmushi, ta girgiza kai,
“To mu je.”
Maryam ta yi saurin ɗauko tabarma, suka fito tsakar gidan, suka shimfiɗa ta ƙarƙashin bishiyar mangwaro inda suka saba cin abinci.
Mama Indo ta ji duk tattaunawar tasu, sai dai ba ta ce komai ba, ta ci gaba da ware kayan wankin da ke gabanta cikin nutsuwa, fuskarta ba ta nuna komai ba.
⸻
Suka zauna a kan tabarmar, Maryam ta jawo farantin shinkafar da wake an yanka salad da tumatir harda su cucumber zuwa gabansu,
“Bismillah,” ta faɗa tana ɗaukar cokali.
“Bismillah,” Raihana ta amsa da murmushi.
A ɗaya gefen tsakar gidan kuwa, Umma na zaune a kan ƙaramin tabarma.
Gaban ƙafafunta akwai babban kwanon kubewa da wuƙa a hannu, a hankali take yanka kabewar da za ta yi miyar dare, lokaci zuwa lokaci kuma tana jefa wadda ta gama cikin wani babban roba da ke gabanta.
Sai dai duk da tana aikinta... kunnenta yana wajensu, ta san idan Maryam na tare da Raihana, ba za a rasa hira ba.
Shiru ne ya ɗan ratsa wajen, sai sautin cokulan da suke bugun farantin kaɗai ake ji.
Can kuma... Raihana ta ɗago idanunta ta kalli Umma,
“Umma...”
Umma ta ɗaga kai daga abin da take yi,
“Na’am, ’yata.”
Raihana ta ɗan yi murmushi,
“Akwai wani abu da nake son gaya miki.”
Maryam ta dakatar da cin abincin da take yi, ta waigo tana kallon Raihana,
“Lafiya dai?”
Raihana ta yi dariya kaɗan,
“Lafiya ƙalau.”
Umma ta ajiye wuƙar da ke hannunta, ta mayar da hankalinta gaba ɗaya kan Raihana,
“To, muna saurarenki.”
Raihana ta sauke numfashi a hankali,
“Yau... bayan Community Medicine lecture ɗinmu ya ƙare... wani staff daga Faculty ya zo ya ce Dean yana nemana an office ɗinsa.”
Maryam ta zaro ido,
“Dean?”
“Eh. Na yi mamaki ma, ban san dalilin da ya sa yake nema na ba.”
Umma ta yi shiru tana sauraro.
Raihana ta ci gaba,
“Da na shiga office ɗinsa, ya fara tambayata yadda karatu yake. Daga baya ya ce Faculty ta yi meeting yau da safe.”
Maryam ta sake matsowa kusa da ita,
“To me suka ce?”
Raihana ta yi murmushi mai cike da kunya,
“Sun ce... bayan sun duba sakamakon karatunmu, halayenmu da rahotannin lecturers... sun zaɓe ni. Ni zan wakilci dukkan ɗaliban Faculty of Medicine a babban taron haɗin gwiwa tsakanin Kaduna Medical University da...”
Ta ɗan dakata,
“...Armaan Group of Companies.”
Na ɗan lokaci... wurin ya yi tsit.
Maryam ta zuba wa Raihana ido kamar ba ta ji daidai ba,
“Ke... da gaske?”
Raihana ta gyada kai tana murmushi,
“Da gaske.”
“Subhanallah!” Maryam ta faɗa cikin farin ciki, ta kama hannun Raihana,
“Rayy! Wannan ai babban abin alfahari ne!”
Umma kuwa... ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, sai ta ɗaga hannayenta sama cikin godiya,
“Alhamdulillahi Rabbil-’Alameen.”
Ta sauke hannayenta, idanunta suka sauka kan Raihana cike da ƙauna da alfahari,
“Na san Allah ba Ya tozarta ƙoƙarin bawa. Tun kina ƙarama kina dagewa da karatu, ga shi yau Allah Ya fara ɗaukaka ki.”
Raihana ta sunkuyar da kanta cikin farinciki,
“Alhamdulillah.”
Umma ta yi murmushi,
“Allah Ya ƙara buɗe miki ƙofofin alkhairi. Allah Ya ba ki ikon sauke wannan nauyi.”
“Ameen.”
“Ameen,” Maryam ta amsa da fara’a.
Sai ta yi dariya tana girgiza Raihana kaɗan,
“Rayy... yanzu fa za ki yi speech a gaban manyan mutane!”
Raihana ta yi murmushi tana girgiza kai,
“Shi ne ma nake ta tunani. Dean ya ce akwai kusan mako guda kawai na shirya jawabin.”
Umma ta yi murmushi cikin kwanciyar hankali,
“Kada ki ji tsoro. Ki yi tawakkali ga Allah. Idan Shi ne Ya zaɓe ki ta wannan hanya... Shi ne kuma Zai ba ki ikon cin nasara da abinda aka ɗora miki.”
Kafin su ƙara wata magana... sai aka ji sallama daga bakin ƙofar gidan,
“Assalamu alaikum...”
Wani ƙaramin yaro ne ya shigo tsakar gidan, ya tsaya cikin ladabi kafin ya ce,
“Ana sallama da Bintu.”
Da sauri Mama Sabuwa ta fito daga ɗakinta, tana gyara zaninta,
“Je ka ce ga ta nan zuwa yanzu.”
“To.”
Yaron ya amsa, ya juya zai fita.
Sai Mama Sabuwa ta ɗaga murya,
“Bintu! Ki fito mana. Kin ga har an zo ana jiranki.”
Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da cewa,
“Ki hanzarta, kin ji? Domin ki samu dawowa da wuri.”
“To, Mama.”
Ba a jima ba... Bintu ta fito.
Da ta taka cikin tsakar gidan... sai wani irin ƙamshin turare mai uban uban yawa har yana hawa kai ya cika wajen.
Kitsonta kuwa... an yi masa dogon attachment mai kyau da ya sauko har kusa da gadon bayanta.
Fuskarta cike take da kwalliya mai ɗaukar ido, lips ɗinta na kyalli, yayin da eyelashes ɗinta suka ƙara fito da idanunta.
Sanye take da fitted gown mai matuƙar damewa ta bi jikinta, ta kwanta tana fito da surar jikinta ta kusan kowane ɓangare.
Takalminta mai tsini yana ɗaukar hasken yammacin rana, yayin da ƙaramin handbag da ke hannunta ya kammala shigar.
Da ka ganta... za ka rantse wani babban dinner ko red carpet event za ta halarta.
Mama Sabuwa ta washe baki cikin jin daɗi,
“Kai, maa shaa Allah! Bintoto! Son kowa... kin wanda ya rasa!”
Ta ƙarasa gare ta tana gyara mata gefen rigar,
“Allah ya ƙara miki kyau. Wallahi duk wanda ya gan ki sai ya juyo ya sake kallonki.”
Bintu ta yi murmushi cike da jin daɗin yabon.
Mama Sabuwa ta shafa mata kafaɗa,
“Je mana, Allah Ya tsare. Amma ki kula da kanki. Kuma ki dawo da wuri, kin ji?”
“To, Mama.”
Bintu ta amsa tana ɗan gyara gashinta, ba tare da ta tsaya ƙara magana da kowa ba... ta juya ta nufi ƙofar gida cikin tafiyarta mai cike da isa.
Har ta fita.
Idanun waɗanda ke tsakar gidan suka bita har ta ɓace daga ganinsu.
Maryam ta kalli ƙofar na ɗan lokaci, sannan ta maida kallonta kan farantin gabanta.
Umma kuwa ta sauke numfashi a hankali, ba ta ce komai ba, ta ci gaba da yankan kabewar da ke gabanta cikin nutsuwa, yayin da Raihana ita kam hankalinta na kan abincinta, ko dagowa batayi ba duk da cewa zuciyarta ta lura da bambancin yadda kowa ke kallon rayuwa a cikin gidan.
Not edited