THE FIRST APPROVAL
*ZAYD ARMAN*
*CHAPTER- TWELVE:12*
*THE FIRST APPROVAL*
*JIDDAAH BARKUM*
——————————-
Budurwar ta ci gaba da takowa cikin natsuwa, duk wanda ke falon ya lura da inda ta dosa.
Wani murmushi mai cike da kwarin gwiwa ne kwance a fuskarta, ta san kyawunta, ta san yadda maza ke juyowa idan suka gan ta.
Har ta iso gaban Zayd, ta tsaya, ta ɗan karkatar da kanta kaɗan,
“Hi… Mr. Armaan.”
Muryarta ta fito a hankali, mai sanyi da taushi.
Zayd ya ɗago idanunsa ya kalle ta, sai dai kallon nasa… ba irin kallon da ta saba samu daga maza ba ne.
Idanunsa sunyi ja kaɗan saboda tasirin abin da ya sha, kallon ya yi nauyi, kamar yana ƙoƙarin tuna inda ya taɓa ganin ta.
Budurwar ta yi murmushi,
“I’ve heard a lot about you.”
Shiru.
Zayd bai ce komai ba.
Ta ɗan yi dariya,
“I wasn’t expecting to finally meet you today.”
Har yanzu… shiru.
Imraan da sauran abokansa suka fara kallon juna,
“Yau CEO ya yi shiru sosai,” wani ya faɗa cikin dariya.
Budurwar ta ɗan sunkuyo kaɗan,
“Can I sit?”
Ba tare da ya kalleta ba, Zayd ya furta cikin ƙaramar murya,
“As you wish.”
Da sauri ta zauna kusa da shi, ta gyara gashinta, ƙamshin turarenta ya bazu tsakaninsu.
A hankali ta miƙa hannu,
“I’m Vanessa.”
Zayd ya kalli hannunta, na wasu daƙiƙu… bai motsa ba.
Daga ƙarshe ba tare da ya miƙa nashi hannun ba kawai yace,
“Zayd.”
Ta yi dariya,
“As if I don’t know.”
Duk waɗanda ke falon suka yi dariya.
Vanessa ta ci gaba da kallonsa,
“Do you know… you are even more handsome in real life.”
Kalmar ta sa wasu daga cikin samarin yin ihu cikin wasa,
“Woooh!”
Imraan ya busa iska yana dariya,
“Vanessa, ki rage mana.”
Amma Zayd… kamar ba ya jin abin da suke faɗa.
Numfashinsa ya fara nauyi, hasken falon na ƙara yi masa ƙarfi, sautin music ɗin ya fara gaurayawa cikin kunnuwansa.
Ya kai hannu ya dafe goshinsa.
Vanessa ta lura da hakan, murmushinta ya ɗan gushe,
“Mr. Armaan… are you okay?”
Zayd ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, sannan ya buɗe su a hankali,
“I am...” ya tsaya, ya haɗiye yawu,
“…fine.”
Vanessa ta ƙara matsowa kusa da shi, fuskarta cike da damuwa ta ƙarya, amma a zuciyarta tana jin wannan ita ce damar da ta daɗe tana jira,
“Mr. Armaan... I don’t think you’re okay.”
Zayd bai amsa ba, ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, numfashinsa na ci gaba da fita a hankali.
Vanessa ta waigo ta kalli Imraan,
“I think he needs to rest.”
Imraan ya ɗan ɗaga gira,
“Exactly,” ya yi murmushi yana jingina da kujera,
“A upstairs akwai guest rooms.”
Vanessa ta gyada kai da sauri,
“I’ll take him.”
Ta sake juyowa gare shi,
“Come on... let me help you.”
Ta miƙa hannunta a hankali.
Zayd bai motsa ba, sai dai numfashinsa ya ɗan ƙaru.
Vanessa ta ɗauka bai ji ta ba, ta ƙara matsowa kusa, a hankali ta kama gefen hannunsa,
“Please... ka zo.”
Da yatsunta suka taɓa fatar hannunsa… sai idanun Zayd suka buɗe lokaci guda.
Kallo ɗaya kawai ya yi mata, kallon ya sa murmushinta ya ɗan dusashe.
Kafin ta sake cewa komai… Zayd ya fizge hannunsa da ƙarfi.
Vanessa ta ja da baya saboda ƙarfin fizgar.
A lokaci guda… Zayd ya miƙe tsaye cikin wata irin wahala, jikinsa yana neman ya kasa ɗaukar nauyinsa, sai dai ya dafe bayan kujerar da hannunsa domin kada ya faɗi.
Numfashinsa ya yi nauyi, idanunsa sun juye.
Amma muryarsa… har yanzu cike take da wani irin ƙarfi,
“Don’t...” ya haɗiye yawu,
“…touch me.”
Wurin ya yi tsit, duk dariyar da ake yi ta ɗauke lokaci guda.
Vanessa ta tsaya tana kallonsa cikin mamaki.
Imraan kuwa… murmushin da ke fuskarsa ya ƙara faɗaɗa, a zuciyarsa ya ce,
“Kai... yau dai wata za ta karya perfection ɗin CEO.”
Ya ɗan yi dariya a hankali,
“Relax, bro. She’s only trying to help.”
Zayd bai ma kalle shi ba, a hankali ya sake komawa ya zauna kan kujerarsa, ya dafe goshinsa, ya runtse idanunsa na wasu daƙiƙu.
Jikinsa na ci gaba da ba shi saƙon cewa wani abu ba daidai ba ne, shi kuwa… har yanzu bai san cewa amintaccen ɗan’uwansa ne ya jefa shi cikin wannan yanayin ba.
Vanessa ta tsaya tana kallonsa cikin mamaki, har yanzu tana jin zafin yadda ya fizge hannunta, ta yi ƙoƙarin murmushi,
“Oh... I’m sorry. I was only trying to help.”
Zayd bai kalleta ba, numfashinsa ya ci gaba da fita a hankali, ya dafe goshinsa da tafin hannunsa.
Wani irin bugun zuciya yake ji wanda ya dade bai ji ba, komai na ƙara rikicewa a idanunsa, kiɗan da ake kunnawa kamar ana buga shi ne a cikin kansa.
Imraan kuwa… har yanzu murmushi ne kwance a fuskarsa, ya jingina da centre table yana kallon Zayd.
A zuciyarsa ya ce,
Allah yasa wannan ta karya duk wani girman kanka yau.
Sai ya yi ƙaramar dariya,
“Relax, bro. Ba wani abu ba ne. Just enjoy yourself.”
Bai gama rufe baki ba… sai ya lura da wani abu.
Numfashin Zayd ya ƙara nauyi, fuskarsa ta fara ɗan sauya launi, yana haɗiye yawu da ƙyar.
Glass ɗin da ke hannunsa ya fara rawa.
Murmushin Imraan ya ɗan dusashe,
“Rascal...?” ya kira a hankali.
Zayd bai amsa ba, ya runtse idanunsa.
Da ya sake buɗe su… sai ya ɗaga glass ɗin ya kalla, na wasu daƙiƙu, sannan idanunsa suka sauka kan Imraan.
Kallon… mai sanyi, amma mai nauyi.
“What...” ya haɗiye yawu,
“…did you put in this?”
Falon gaba ɗaya ya yi tsit, duk wanda ke wajen ya maida hankalinsa kansu.
Imraan ya yi wata dariyar ƙarya,
“A’a mana. Orange juice ne kawai.”
Zayd ya ci gaba da kallonsa, ba ya ko ƙyaftawa,
“What... did you... put... in this?”
Kalmar ta fito da wahala.
A wannan karon… Imraan ya fara jin zuciyarsa ta buga, ya yi dariya yana son mayar da abin wasa,
“Come on, rascal. Just a little whisky. Ba wani abu ba ne. Na ce ai gobe ma za ka manta.”
Wurin ya sake yin tsit, kamar an kashe music ɗin, kowa ya zuba wa Zayd ido.
Na wasu daƙiƙu… bai ce komai ba, sai ya sauke idanunsa, ya kalli glass ɗin.
A hankali ya miƙe tsaye, jikinsa ya ɗan yi karkarwa, sai ya ajiye glass ɗin a kan centre table ba tare da ya fasa shi ko ya jefa shi ba.
Ya ɗaga kansa, ya kalli Imraan.
Muryarsa ta fito a hankali… amma kowace kalma ta sauka da nauyi,
“You... broke my trust.”
Kalmar ta tsaya a zuciyar Imraan, duk murmushinsa ya mutu.
Bai taɓa jin Zayd ya yi magana da shi cikin irin wannan murya ba, ba ihu ba, ba zagi ba, ba faɗa ba, kalma huɗu kawai, amma sun fi mari zafi.
Imraan ya yi saurin matsowa kusa da shi,
“Rascal... wallahi wasa nake yi. I didn’t mean—”
Zayd ya ɗaga hannu, alamar ya yi shiru, bai ƙara son jin komai ba.
Ya juya a hankali, ya nufi ƙofar falon.
Sai dai taku biyu kacal ya yi… komai ya fara juyawa a idanunsa, ya dafe bango, numfashinsa ya ƙara nauyi.
Vanessa ta yi saurin matsowa,
“Please... let me help you.”
Kafin ta kai gare shi… sai ya sake ja da baya,
“Don’t.”
Kalmar ta fito da ƙarfi fiye da yadda yake zato.
Vanessa ta tsaya cak.
Imraan ya fara firgita, ya yi saurin kama kafaɗarsa,
“Rascal. I don’t think you should drive. Ka huta tukuna.”
Zayd ya kawar da hannunsa, a hankali, amma cikin ƙarfi,
“I said... don’t touch me.”
Yanzu kam... duk wanda ke falon ya gane abin ba wasa ba ne, babu wanda ya sake dariya, kiɗan ma wani daga cikinsu ya kashe shi, wurin ya yi tsit.
Zayd ya zaro key ɗin motarsa daga aljihu, ba tare da ya sake kallon kowa ba… ya buɗe ƙofar, ya fita.
Imraan ya bi bayansa da sauri,
“Rascal! Zayd! Please tsaya!”
Amma bai waigo ba, ya ci gaba da tafiya cikin wani irin yanayi da baćin rai da bai taɓa shiga irinsa ba.
Imraan ya tsaya a bakin ƙofar yana kallonsa, a karon farko… tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa,
“Ya Allah... kar abin nan ya wuce yadda na zata...”
⸻
A can Armaan Mansion kuwa…
A cikin babban master bedroom na Ummie.
Ɗakin… tamkar wani sashe ne na fadar sarauniya, komai a cikinsa yana kururuwa da alfarma.
Babban king-size bed mai launin ivory, an kawata shi da duvet masu laushi da pillows iri daban-daban, dogayen labulaye masu launin champagne suna saukowa har ƙasa, yayin da hasken yammacin rana ke ratsawa ta cikinsu cikin nutsuwa.
Crystal chandelier mai ɗaukar ido na rataye daga sama, yana ƙawata ɗakin da walƙiya mai sanyi.
A gefe kuwa akwai elegant sitting area mai sofas na zamani da centre table da aka yi da marble, furanni masu ƙamshi suna cikin crystal vase, yayin da ƙamshin oud mai tsada ya gauraye ko’ina cikin ɗakin.
Komai… yana bayyana cewa wannan ba ɗakin kowa ba ne, ɗakin matar marigayi Alhaji Abdulrahman Armaan ne.
A kan ɗaya daga cikin sofas ɗin Ummie ke zaune tare da baƙuwarta, Hajiya Hauwa, ƙanwar marigayi Alhaji Armaan, kuma mahaifiyar Imraan da Seeyama, gefenta kuma Seeyama ce zaune.
A gabansu akwai ƙaramin marble stool da aka jera drinks iri-iri, fruits da snacks.
Hajiya Hauwa ta ɗauki glass ɗin fresh grape juice da ke gabanta, ta kurɓa kaɗan cikin kasaita, sannan ta mayar da glass ɗin a hankali, ta yi murmushi,
“Hajja Fateema... wallahi kina bani mamaki.”
Ummie ta ɗan yi murmushi kawai.
Hajiya Hauwa ta ci gaba,
“Yadda Zayd yake girmamaki da jin maganarki ai ni na san...” ta ɗan yi dariya,
“Ko wuta kika rura kika ce masa, ‘Zaydu zo ka shiga,’ wallahi zai shiga ba tare da ya yi gardama ba.”
Ummie ta girgiza kai tana murmushi,
“Kada ki faɗi haka.”
Amma Hajiya Hauwa ba ta tsaya ba,
“To me ya sa kika tsaya kina zuba masa ido? Kullum kina cewa idan lokaci ya yi shi da kansa zai yi aure.”
Ta ɗan ja numfashi,
“Ni kam yanda na san Zayd... wallahi idan aka ce a zuba masa ido kawai... ba zai yi aure daga yau har a tashi duniya ba.”
Seeyama da ke zaune gefen mahaifiyarta ta sunkuyar da kanta cikin kunya, ta san inda maganar ta dosa.
Hajiya Hauwa ta gyara zamanta, ta sake ɗaukar glass ɗinta,
“Ba don Seeyama ’yata ba ce...” ta ɗan yi murmushi,
“Amma ina da yaƙinin idan aka aura masa ita... wallahi, billahi sai kin ga canji tare da Zayd.”
Ta ɗan yi dariya,
“Mace fa... shi ba waliyyi ba ne da za a ce zai zauna gida ɗaya da mace ya zuba mata ido.”
Sai ta ɗan ɗaga gira,
“Ko dai...” ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Sai idan ba shi da lafiya.”
Seeyama ta dafe fuskarta cikin kunya,
“Mummy... please mana.”
Hajiya Hauwa ta fashe da dariya,
“Ke kuwa me ya sa kike jin kunya? Ba gaskiya nake faɗa ba?”
Seeyama ta ƙara sunkuyar da kanta.
Ummie kuwa... ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ta maida kallonta kan Seeyama, ta yi mata murmushi mai cike da taushii,
“Seeyama...”
“Na’am, Ummie.”
“Ina ganin yanzu Suhaila ta gama abin da take yi. Je ki ɗakinta mana. Ku ɗan zauna ku yi hira.”
Seeyama ta ɗan kalli mahaifiyarta, sai kuma ta kalli Ummie.
A zahiri ta yi murmushi,
“To, Ummie.”
Sai dai... a zuciyarta ba haka take so ba, ta san sarai, Ummie na son ta ba su wuri ne domin ta yi magana da Hajiya Hauwa ita kaɗai.
Ba tare da ta ƙara cewa komai ba… ta miƙe tsaye cikin nutsuwa, ta gyara mayafinta, ta yi musu sallama cikin ladabi,
“To, Allah ya sa albarka.”
Ummie ta amsa cikin murmushi, Hajiya Hauwa ma ta ɗaga mata kai.
Seeyama ta juya, ta taka zuwa bakin ƙofar ɗakin, ta buɗe ta a hankali, da ta fita… sai ta ja ƙofar ta rufe musu cikin nutsuwa.
Nan take… shiru ya mamaye ɗakin, sai sautin AC da ƙamshin turaren oud mai laushi da ke yawo a cikin ɗakin.
Ummie ta ɗan gyara zamanta, ta ɗauki glass ɗinta ta sake kurɓa kaɗan, sannan ta ɗaga idanunta ta kalli hajiya Hauwa kai tsaye, ta yi murmushi cikin natsuwa.
Sai ta ɗan gyara zamanta kafin ta ce cikin murya mai cike da hikima,
“Hauwa... kin san ina son Seeyama kuma ina kallonta ne tamkar ’yata, kuma babu abin da zai fi faranta min rai idan Allah Ya haɗa ta da gidan da zai ba ta kwanciyar hankali.”
Ta ɗan dakata,
“Amma aure... ba a gina shi da son zuciyar iyaye ko burin dangi kaɗai.”
Ta kalli Hajiya Hauwa kai tsaye,
“Zuciya ni’ima ce daga Allah. Ba ni, ba ke, ba kuma Seeyama... ba wanda yake da ikon karkatar da zuciyar Zayd idan Allah bai rubuta hakan ba.”
Ɗakin ya ɗan yi shiru, Hajiya Hauwa ta sauke ajiyar zuciya, ta san Ummie tana faɗin gaskiya, amma duk da haka… har yanzu tana da buri guda ɗaya a zuciyarta, ta ga Seeyama ta zama matar Zayd Armaan.
⸻
*MALALI*
*Baffa Musa Residence*
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare… iskar dare mai ɗan sanyi na kaɗa ganyen bishiyoyin da ke bakin gidan, ana jin sautin kwadi daga nesa, yayin da unguwar ta fara nutsuwa bayan an idar da sallar Isha’i.
A dai-dai lokacin… ƙofar gidan ta buɗe.
Baffa Musa da Hamza ne suka shigo tare, Hamza na riƙe da hularsa a hannu, yayin da Baffa Musa ke taku a hankali cikin kasaitar dattijo.
Kafin su shiga cikin tsakar gidan… Hamza ya ɗan tsaya, ya dubi Baffa Musa,
“Baffa...”
Baffa Musa ya waigo gare shi,
“Na’am, Hamza.”
Hamza ya ɗan ja numfashi,
“Akwai abin da nake son sanar da kai.”
Baffa Musa ya gyada kai,
“Ina sauraronka.”
Hamza ya ɗan rage muryarsa,
“Game da Haris... yaron da ya zo neman izinin fara neman soyayyar Raihana.”
Baffa Musa ya tsaya cak, ya haɗe hannayensa a bayansa,
“Eh... me ka gano?”
Hamza ya gyara tsayuwarsa,
“Kamar yadda ka umarce ni... na gudanar da bincike sosai. Ba wai na tambayi mutum ɗaya ko biyu kawai ba, na bi ta wuraren da ya yi karatu, na tambayi waɗanda suka yi aiki tare da shi, har ma na samu damar jin ta bakin maƙwabta da waɗanda suka san iyalinsu.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba,
“Alhamdulillah... duk inda na je... abu ɗaya nake ji.”
Baffa Musa ya ɗaga gira,
“Wane abu?”
Hamza ya yi murmushi,
“Sun ce Haris mutum ne mai tarbiyya, mai ladabi, mai nutsuwa, ba ya shaye-shaye, ba ya yawan shiga banza, kuma yana da tsoron Allah.”
Ya ɗan dakata,
“Yana aiki a wani babban kamfanin gine-gine na ƙasa, kuma Alhamdulillah aikinsa yana tafiya da kyau. Na kuma binciki danginsu. Iyaye ne masu mutunci, gida ne da aka san su da addini da kyakkyawar mu’amala.”
Baffa Musa ya yi shiru, ya ci gaba da sauraron Hamza ba tare da katse shi ba.
Hamza ya ƙara da cewa,
“Gaskiya Baffa... ban ga abin da zai sa mu ce a’a ba.”
Na wasu daƙiƙu… Baffa Musa bai ce komai ba, sai ya sauke numfashi cikin natsuwa, wani lallausan murmushi ya bayyana a gefen fuskarsa,
“Hamza... Alhamdulillah.”
Hamza ya ɗago kai.
Baffa Musa ya ci gaba,
“Abin da ka binciko... shi ne dai-dai abin da ni ma na samu.”
Hamza ya ɗan yi mamaki,
“Baffa kai ma ka gama naka binciken?”
Baffa Musa ya yi murmushi, ya ɗaga kai kaɗan,
“Hamza... Raihana ba ’yata kaɗai ba ce, amanar Allah ce. Ba zan taɓa yanke hukunci a kan rayuwarta ba tare da na tabbatar da abin da zan yi ba.”
Ya ɗan yi shiru,
“Na tura mutane na. Na yi tambaya ta inda ya kamata. Kuma duk rahoton da ya dawo min... ya zo daidai da naka.”
Hamza ya sauke ajiyar zuciya,
“Alhamdulillah.”
Baffa Musa ya gyara tsayuwarsa,
“Saboda haka... in sha Allah... zan ba Haris damar fara neman soyayyar Raihana.”
Ya ɗan ɗaga yatsarsa,
“Amma... komai yana hannun Raihana. Ba za a tilasta mata komai ba. Idan zuciyarta ta karɓe shi... Alhamdulillah. Idan kuma ba ta amince ba... babu wanda zai matsa mata.”
Hamza ya yi murmushi cikin gamsuwa,
“Wannan shi ne adalci, Baffa.”
Baffa Musa ya gyada kai,
“Domin aure... ba ya ginuwa da kyawun suna kaɗai. Zuciya ma tana da nata hukuncin.”
Su biyun suka yi shiru na ɗan lokaci, iskar dare ta sake kaɗawa a hankali.
Sai Baffa Musa ya ɗan taɓa kafaɗar Hamza,
“Allah Ya yi albarka.”
Hamza ya yi murmushi,
“Aamiin Yaa Allah, Baffa.”
Su ka taka cikin tsakar gidan tare… bayan sun shiga tsakar gidan… Hamza ya nufi hanyar dakin Mama Sabuwa bayan ya yi wa Baffa Musa sallama.
Shi kuwa Baffa Musa… kai tsaye ya nufi ɗakin Umma.
Da ya isa bakin ƙofar… ya ɗan yi sallama cikin nutsuwa,
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam,” muryar Umma ta amsa daga ciki,
“Shigo.”
Baffa Musa ya tura ƙofar a hankali ya shiga.
Umma na zaune kan ɗa carport tana naɗe wasu kayan da ta gama gyarawa, a gefe kuwa… Raihana na zaune a ƙasa kan ƙaramin tabarma, a gabanta akwai notebook a buɗe tare da wasu papers da biro, da alama tana aikin shirya speech ɗinta ne.
Da suka hango Baffa Musa…
“Sannu da zuwa, Baffa,” Umma ta faɗa tana murmushi.
“Yauwa,” ya amsa cikin nutsuwa.
Raihana ma ta matsa kusa da shi,
“Sannu da zuwa.”
“Yauwa, ’yata.”
“Kuna lafiya?”
“Alhamdulillah,” suka amsa tare.
Baffa Musa ya zauna kan kujerar da ke gefen ɗakin, ya ɗan gyara zamansa, sai ya kalli Umma,
“Hajara...”
“Na’am.”
“Akwai magana da nake son mu yi.”
Umma ta lura da yadda muryarsa ta sauya, ta ajiye kayan da ke hannunta gaba ɗaya,
“Ina sauraronka.”
Baffa Musa ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan idanunsa suka sauka kan Raihana,
“Akwai yaron da ya zo kwanakin baya... ya nemi izinin fara neman soyayyarki? Tun ranar... ban yi gaggawar ba da amsa ba, saboda ba na son in ɗora rayuwar ’yata a kan zance ko zato.”
Ya ɗan yi shiru,
“Na gudanar da bincike. Ba ni kaɗai ba… har Hamza ma ya yi nasa binciken.”
Umma ta zuba masa ido tana sauraro.
Baffa Musa ya yi murmushi kaɗan,
“Alhamdulillah. Abin da muka samu ya kwantar mana da hankali.”
Ya ci gaba cikin natsuwa,
“An tabbatar mana cewa Haris matashi ne mai tarbiyya, mai ladabi, mai mutunci, mai tsoron Allah. Yana da aikinsa na halal, yana kuma riƙe da alhakinsa yadda ya kamata. Danginsu ma gida ne da aka san su da kyakkyawar mu’amala da addini.”
Ya ɗan dakata,
“Duk binciken da muka yi... bai nuna mana wani abin da zai sa mu hana shi ba.”
Umma ta sauke ajiyar zuciya.
Baffa Musa ya juya ya kalli Raihana,
“Saboda haka... in sha Allah... zan ba shi damar ya fara neman soyayyarki.”
Kalmar ta sa zuciyar Raihana bugawa da sauri, ta sauke idanunta ƙasa cikin kunya.
Baffa Musa ya ci gaba,
“Amma...” ya ɗan yi murmushi,
“Wannan ba yana nufin na aura miki shi ba ne, ko kaɗan. Na ba shi damar ne kawai ya zo ya gabatar da kansa cikin hanyar da Musulunci ya tanada.”
Ya ɗan jingina da kujerarsa,
“Ke ce za ki saurare shi, ke ce za ki yi istikhara, ke ce kuma za ki yanke hukuncin da zuciyarki ta amince da shi. In kin ga kin amince... Alhamdulillah. In kuma ba ki ji hakan a zuciyarki ba...” ya girgiza kai a hankali,
“Babu wanda zai matsa miki.”
Idanun Umma suka cika da gamsuwa, ta yi murmushi tana kallon mijinta,
“Allah Ya saka da alkhairi. Haka uba nagari yake. Yana ba ’yarsa kariya, amma kuma yana ba ta damar zaɓar abin da ya dace da rayuwarta.”
Baffa Musa ya yi murmushi cikin tawali’u,
“Mu dai abin da ya rage mana shi ne addu’a. Allah Ya zaɓa mata mafi alkhairi.”
Raihana tunda aka fara maganar bata dago ba, kanta na ƙasa, idanunta cike da kunya da girmamawa.
A gefen ɗakin kuwa… Umma ta ɗaga hannayenta kaɗan,
“Allahumma khir lana wakhtar lana.”
“Amin,” Baffa ya amsa sannan ya miƙe a nutse ya fice daga ɗakin.
Not edited