ZAYD ARMAAN

THE KNOCK OF DESTINY

by @jiddaahbarkum






*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER-SIXTEEN:16*

*THE KNOCK OF DESTINY*

*JIDDAAH BARKUM*
————-

A daren ranar… iskar dare mai sanyi tana ratsawa cikin bishiyoyin mangwaron da ke tsakar gidan.
Fitilar da ke manne a jikin bango tana zuba haske mai laushi.
An shimfiɗa sabuwar dadduma a gefen ɓangaren da ɗakin Yaya Hamza yake, a kanta aka ajiye matashin kai guda biyu.

Baffa Musa ne ya shigo tare da wani matashi mai tsananin nutsuwa.
Dogon saurayi ne, mai ɗan haske, sanye cikin farin babban riga mai ɗan aikin zare, sai hularsa ƙaramar yar Katsina.
Kamshin turarensa ya cika wajen.

Baffa ya nuna masa wajen zama,
“Zauna, Haris.”
“Nagode, Baffa.”
Ya zauna cikin ladabi.

Sai ya nufi cikin gida ya tadda Umma a baranda tana kwashe shanya.
Baffa ya kalli Umma,
“Ki kira Raihana.”
Umma ta gyada kai,
“To.”

A cikin ɗaki… Maryam ta yi saurin kallon Raihana,
“Kin ji?”
Raihana ta gyada kai,
“Na ji.”
Zuciyarta ta fara bugawa, ba wai saboda tsoro ba… sai saboda ta san dalilin zuwan baƙon.

Umma ta daga labule sai ta yi murmushi,
“Ki fito cikin nutsuwa.”
Maryam ta yi dariya,
“Ki dai daina rawar jiki.”
Raihana ta harare ta, Maryam tayi dariya,
“Eh, ai fuskar ki ce kawai ta faɗa.”
Duk suka yi dariya.

Raihana ta gyara hijab ɗinta.
Baffa ya nuna mata hanya yana gefen ɗakin Hamza, “and behave well.”
Ta jinjina kai a hankali sannan ya ce, “je ki.”
Ta tafi a nutse har inda yake,
“Assalamu alaikum.”
Haris ya ɗan sunkuyar da kansa,
“Wa alaikumus salam.”
Bai zuba mata ido ba, sai dai ya amsa cikin mutunci.

“Bismillah ki zauna mana,” ya faɗa yana matsowa can gefe yana mata waje.
A nutse ta nemi waje ta zauna.
“Ina yini,” ta faɗa tana wasa da gefen hijabinta.
“Lafiya kalau, likita ya karatu.”
Tayi murmushi kadai batace komai ba, sai shima yayi shiru kawai yana kallonta.

Na ɗan lokaci… shiru ya ratsa tsakaninsu, sai ƙar iska kawai ake ji.
Haris ya yi murmushi kaɗan,
“Da alama... kin fi ni jin kunya.”
Raihana ta ɗan yi murmushi,
“Ni ma ban saba irin wannan zaman ba.”
Ya faɗa haryanzu idanunshi akanta, ta sake murmushi batace komai ba.

Sai yanayin ya ɗan saki.
Haris ya gyara zamansa,
“Da farko... ina so ki sani cewa ban zo ne saboda an ce in zo ba kawai. Na zo ne saboda ina da sha’awar sanin wacece Raihana.”

Ta ɗaga ido ta kalle shi.
Ya ci gaba,
“Ko kin tuna wani dinner da aka yi watanni baya?”
Ta yi tunani, sai ta gyada kai,
“Lokacin da na dinga bin ku hau mota na kai ku gida... amma kuka ce a’a.”
Ta yi murmushi,
“Eh. kukace kunada hanyar da za ku koma.”

Raihana ta ɗan yi dariya kadan data tuna abinda ya faru ranar,
“Nan ne fa. Na tsaya ina kallonku. Na yi mamakin yadda mutane da yawa suke neman irin wannan damar a lokacin, nn ba da kowa a hanya ga dare... amma ke kika ƙi cikin sauƙi.”

Raihana ta ce a hankali,
“Ban ga wani dalilin hawa motar wanda ban sani ba. Shi ya sa.”
Haris ya gyada kai cikin gamsuwa,
“Wannan ne ya fara ɗaukar hankalina. Na ce a raina... ‘yarinyar nan tana da abin da ya fi kyau ko kwalliya.’”
Ya ɗan yi shiru,
“Sai daga baya na fara tambaya a kanki. Na ji kina da ladabi. Kina da ilimi. Kuma kina da kyakkyawar tarbiyya.”
Ya yi murmushi,
“Shi ya sa na nemi izinin Baffa. Saboda ban yi imanin shiga rayuwar mace ta wata hanya ba sai ta ƙofar iyayenta.”

Raihana ta sauke idanunta cikin kunya,
“Nagode.”
Haris ya yi murmushi,
“Kar ki damu. Ban zo da gaggawar neman amsa ba. Ina so ne kawai mu fara sanin juna. Idan Allah Ya sa alkhairi, zai haɗa zukatanmu. Idan kuma ba haka ba... za mu ci gaba da girmama juna.”

Raihana ta ɗaga kai a hankali, ta ce cikin nutsuwa,
“Ni ma abin da zan iya faɗa shi ne... ina girmama shawarar iyayena. Kuma duk abin da Allah Ya ƙaddara... shi ne mafi alkhairi.”
Haris ya yi murmushin gamsuwa,
“Wannan amsar kaɗai... ta ƙara tabbatar min cewa ban yi kuskure ba wajen zuwa nan.”

⸻

*ARMAAN MANSION*

Dare ya riga ya yi, fitilun da suka kewaye katafaren Armaan Mansion suna haskaka lambun gidan cikin wani irin kyau.
A babban family lounge kuwa… Ummie na zaune a kan doguwar sofa mai launin ivory, a gabanta akwai cup ɗin green tea, tana duba wani littafi a hankali.

Suhaila kuwa… tun da suka dawo daga jami’a, wayarta ba ta huta ba, ta na ta kallon hotunan event ɗin.
Wani lokaci ta yi murmushi, wani lokaci kuma ta ƙara zoom.
Can… sai ta tsaya cak,
“Subhanallah...” ta furta a hankali.

Ta sake yin zoom kan hoton da ta ɗauka lokacin da Raihana ke karɓar certificate daga hannun Zayd.
Hoton ya fito da tsananin kyau.
Zayd cikin charcoal grey suit, Raihana kuma cikin emerald green abaya, dukansu suna tsaye cikin professionalism.
Sai dai… kyamarar tayi capturing lokacin da hasken flash ya bugi fuskar Raihana, fuskarta ta fito fes, idanunta suna haske, murmushinta mai sauƙi ya ƙara mata kwarjini.

Suhaila ta miƙe da sauri,
“Ummie... please... kalli wannan hoton da kyau.”
Ummie ta ɗago kanta tana murmushi,
“Lafiya dai?”
Suhaila ta miƙa mata wayar,
“Wallahi dan ma ba ki ganta a zahiri ba. Subhanallah... yarinyar nan ta haɗu sosai.”

Ummie ta karɓi wayar, ta ɗan kalli hoton, ta yi murmushi,
“Masha Allah. Kyakkyawar yarinya ce.”
Suhaila ta zauna kusa da ita,
“Ba kyau kaɗai ba fa, Ummie. Ga wani haɗaɗen Turanci. Ga nutsuwa. Ga mutunci. Wallahi ta burgeni.”
Ummie ta yi dariya,
“Tun da kuka dawo... ban ji wani suna daga bakinki ba sai Raihana.”
Suhaila ta yi dariya,
“Saboda ta cancanci a yi maganarta.”

Sai kuma… kamar wani abu ya faɗo mata, ta sake karɓar wayar, ta yi zoom sosai, idanunta suka ƙanƙance,
“Wait...” ta ɗaga kai da sauri,
“Ummie... kin tuna ranar da Akhi ya kai ni bikin Asiya?”
Ummie ta ɗan yi tunani,
“Eh...”
Suhaila ta gyara zamanta cikin ɗoki,
“Kin tuna na ba wata gate pass ɗin seeyama da tace ba zata je ba? Saboda security sun hana ta shiga.”
Ummie ta gyada kai tana murmushi,
“Wacce kika ce an samu hayaniya an entrance? Daga baya ma kika ce yarinyar ta yi miki godiya.”
“Exactly Ummie.”

Suhaila ta sake kallon hoton, sai ta dafe goshinta,
“Ya Allah... wallahi ita ce.”
Ummie ta ɗan ɗaga gira,
“Wace?”
“Waccan yarinyar! Wadda na ba gate pass. Wallahi ita ce. Dan Allah duba da kyau.”
Ta sake miƙa mata wayar,
“Ranar dare ne. Kuma gaskiya ban tsaya na kalleta sosai ba. Amma yanzu... da na sake kallon hoton nan... na gane ita ce.”

Ummie ta sake kallon hoton, ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta yi murmushi,
“Duniya kenan.”
Suhaila ta yi dariya,
“Very small. Da ban bata pass ba maybe da ban santa ba ma gabadaya.”
Ummie ta girgiza kai cikin natsuwa,
“Kar ki manta... abin da Allah ya ƙaddara... ko da ba ta wannan hanya ba... wata hanyar zai kawo shi.”
Suhaila ta yi murmushi,
“Hakane. Amma wallahi... ina son yarinyar nan. Ba tare da wani dalili ba. Ina jin akwai wani abu a tattare da ita.”

A daidai lokacin… suka ji takun sawu daga saman stairs.
Zayd ne, ya sauko cikin simple black joggers da farar T-shirt, wayar sa ce a kunnensa,
“…Yes, move the meeting to nine o’clock. No problem. I’ll review the documents before then.”
Ya katse kiran.

Yana wucewa ta family lounge… sai ya hango Suhaila da Ummie suna kallon waya tare, ya tsaya,
“Me kike fadawa ummie na?”
Suhaila ta yi saurin kashe screen ɗin wayar, ta yi murmushi irin na masu shirin tsokana,
“Nothing. Girl’s discussion.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“Really?”
“Really.”
Ya girgiza kai kaɗan, ba tare da ya ƙara tambaya ba… ya ci gaba da tafiya zuwa kitchen domin ɗaukar ruwa.

Da ya ɓace daga ganinsu… Suhaila ta saki dariya,
“Kin ga Akhi? Da ya ga hoton nan ma... da cewa zai yi ‘She prepared well.’”
Ummie ta kasa riƙe dariyarta, ta ɗan taɓi goshin Suhaila,
“Ke kam... ki kyalemin yaro haka.”
Suhaila tayi dariya kawai.

A ɗaya ɓangaren gidan… Zayd ya cika glass ɗinsa da ruwa, ya jingina da kitchen island yana sha cikin nutsuwa.
Bai san ba… a cikin family lounge… ana ta tattaunawa a kan yarinyar da ya ɗauka cewa ta kasance ɗaya daga cikin dubban mutanen da yake haɗuwa da su a rayuwa.
Shi bai sani ba… amma ƙaddara ta riga ta fara haɗa sunansu… ko da kuwa zuciyarsa har yanzu ba ta fahimci hakan ba.

Family lounge ɗin har yanzu cike yake da dariyar Suhaila.
Wayar Suhaila da ke saman cushion ta fara ringing, ta ɗauka ba tare da ta duba ba.
Da ta ga sunan da ya bayyana… sai ta yi murmushi,
“Seemaa...” ta danna receive,
“Hi, Seema.”

Daga can… muryar Seeyama ta fito cike da fara’a,
“Suhaila! Dan Allah... ina Yaya?”
Suhaila ta ɗaga idanunta, ta leƙa hanyar kitchen ɗin da Zayd ya shiga ɗazu,
“Yana nan.”
Da sauri Seeyama ta ce,
“Please mana... bashi wayar. Ina son magana da shi.”
“Okay,” ta amsa.
Ta miƙe daga kan sofa, Ummie ta bita da kallo tana murmushi kawai.

⸻
*Kitchen ɗin…*

Zayd na tsaye ya gama shan ruwan da ya zuba a glass, ya ajiye kofin a hankali.
A daidai lokacin… Suhaila ta shigo,
“Akhii...”
Ya waigo ya kalle ta, sai ya ga wayarta a hannunta, ya ɗaga gira kaɗan.
Alamar… “What?”
Suhaila ta matso kusa da shi, ta ɗan matsar da wayar daga kunnenta, ta yi masa rada,
“Seeyama ce. Tana son magana da kai.”

Zayd ya sauke idanunsa kan wayar, sai ya girgiza kai a hankali,
“No.”
Suhaila ta yi ƙaramin murmushi,
“Please mana. Ta ce tana ta kiranka wai ba ka ɗauka ba.”
Zayd ya sauke numfashi, kamar ba zai karɓa ba… sai kuma daga ƙarshe… ya karɓi wayar daga hannunta, ya ɗora ta a kunnensa.
Bai ce komai ba, shiru kawai ya yi.

Can… sai muryar Seeyama, ta sauke numfashi,
“Yaya... ina ta kiranka tun ɗazu. Baka ɗauka ba.”
Zayd ya amsa cikin gajeriyar murya,
“I’m busy.”
“Oh...” ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin shagwaɓa,
“Okay. Dan Allah ina da wata ƙaramar magana.”
Zayd bai ce komai ba, alamar tana iya ci gaba.

Seeyama ta yi saurin cewa,
“Birthday ne na best friend ɗina weekend. Kuma ta ce... everyone is coming with their fiancé.”
Ta yi dariya kaɗan,
“So... please... ka raka ni. Ko da na ɗan lokaci ne. Please, Yaya.”

Kitchen ɗin ya yi tsit.
Zayd ya jingina da kitchen island, ya lumshe idanunsa na daƙiƙa guda, sannan ya buɗe su.
Cikin nutsuwa ya ce,
“I’m sorry. I won’t be able to make it.”
Daga can… tace,
“Please mana. Half an hour ma ya isa. I just don’t want to go alone.”
“No,” ya amsa a nutse,
“Weekend ɗin nan ina da meeting. Kuma bayan haka... I don’t attend private parties unless there’s a reason.”

Seeyama ta yi shiru, sai ta sake gwadawa,
“Saboda ni ce na nema koh?”
Muryarsa ta ci gaba da kasancewa cikin natsuwa,
“I’ve already said no. It has nothing to do with you. I’m simply unavailable. Maybe another time.”

Shiru ya sake ratsa layin.
Daga ƙarshe… Seeyama ta yi murmushin dole,
“Okay... I understand. Thank you.”
Zayd bai ƙara cewa komai ba, ya cire wayar daga kunnensa, ya miƙa wa Suhaila,
“Here.”
Ta karɓa.

Kafin ta yi magana… shi kuwa ya juya, ya fice daga kitchen cikin nutsuwarsa.
Suhaila ta bi bayansa da kallo, sai ta ɗora wayar a kunnenta,
“Seema...”
Daga can… ta sauke ajiyar zuciya,
“Kin gani ko?”
Suhaila ta yi murmushin tausayi,
“Kin san halin Akhi. Idan ya ce no... to no ne.”
Seeyama ta yi dariya marar daɗi,
“Na sani. Na dai yi hoping ne...”
Suhaila ta girgiza kai,
“Ki yi haƙuri. In Sha Allah wani lokaci.”
“Okay,” Seeyama ta amsa a hankali, suka yi sallama.

Da Suhaila ta kashe wayar… sai ta leƙa hanyar da Zayd ya bi, ta girgiza kai tana murmushi,
“Wallahi Akhi... ko kaɗan ba ka canzawa.”

Daga can cikin corridor… Zayd yana tafiya zuwa study ɗinsa, fuskarsa kamar kullum… cike da natsuwa, kamar babu wata magana da aka yi da wata da taɓa mata zuciya.

⸻
A ɗaya ɓangaren gidan… Mama Sabuwa na zaune a gefen gadonta tana warware kayan da Bintu ta shigo da su.
Tun farko ta yi zaton kayan ciye ciye ne, amma da ta buɗe ledar… sai idonta ya sauka kan wani ɗan ubansun lace mai sheƙi, nan take ta dafe ƙirji,
“Innalillahi...”
Ta ɗaga leshin sama tana juyawa,
“Ke Bintu! Zo nan mana!”
Bintu ta ƙaraso tana murmushi,
“Na’am Mama?”

Mama Sabuwa ta sake kallon leshin, ta shafa shi da tafin hannunta,
“Wai... wannan leshin naki ne?”
“Eh mana.”
“Subhanallah! Wallahi daga gani ba ƙaramin kuɗi aka zuba a wannan ba. Ni dai da za a sayar da irin wannan... ai sai an sayi gidan nan.”
Bintu ta yi fari da ido,
“Ai wallahi Mama... Hajiyar nan tana da kirki sosai.”

Mama Sabuwa ta ɗago da sauri,
“Wace Hajiya?”
Bintu ta zauna kusa da ita cike da annashuwa,
“Wallahi jiya abin mamaki ya faru. Ni da Hashim muka tsaya a wani shopping mall wai zai yi min shopping. A daidai lokacin... sai wata Hajiya ta zo ita ma siyayya. Ta tsaya tana kallona. Ni ma sai na yi mamaki. Can sai ta ce wai na burgeta sosai. Ta ce ina matuƙar kama da ’yarta da ta rasu shekaru da suka wuce.”

Mama Sabuwa ta dafe baki,
“Wayyo... da gaske?”
Bintu ta gyada kai,
“Har ta roƙe ni na ba ta number ɗina. Ta ce tana so mu riƙa gaisawa. Na ba ta. Sai fa na manta da ita gabadaya. Yau kuma... ina zaune tare da Zahraa... sai na ga message ɗinta a WhatsApp. Ta ce idan bani da abin yi in zo gidanta. Wai tana son ta nuna ni ga wata ƙawarta da ta san marigayiyar ’yarta.”

Mama Sabuwa ta kasa ko ƙyaftawa,
“To?”
Bintu ta yi wata irin ajiyar zuciya,
“Mama... wallahi ba ki ga gidan ba. Wayyo Allah... aljannar duniya kenan!”
Mama Sabuwa ta matsa kusa da ita,
“Yaya gidan yake?”
“Kaiii... falo ɗaya ma ya fi gidanmu gaba ɗaya. Ai toilet dinsu daya shine dakinki da dakin Mama Indo. Kai dan Allah,” Mama Sabuwa ta faɗa tana dade, “haba.”
“Wlh mama.”

Bintu ta ci gaba,
“Komai na alfarma. Marble. Manyan chandeliers. Kayan ɗaki masu tsada. Ko turaren gidan kaɗai... sai ka ji kamar kana cikin wani hotel na Dubai.”
Mama Sabuwa ta haɗiye yawu,
“Innalillahi...”
Bintu ta ci gaba,
“Sai ma’aikata suke ta zirga-zirga. Drivers. House helps. Guards. Komai cikin tsari.”

Mama Sabuwa ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ce cikin sha’awa,
“To... ita ce ta ba ki wannan leshin?”
“Eh.”
“Ba leshi kaɗai ba fa. Ta ba ni kuɗi ma.”
Mama Sabuwa ta zaro ido,
“Kuɗi kuma? Nawa?”
Bintu ta yi murmushi,
“Ta ce kar na faɗa wa kowa.”
Mama Sabuwa ta yi saurin cewa,
“Ni ai ba kowa ba ce.”
Dukansu suka yi dariya.

Bintu ta ce a hankali,
“Ta ba ni dubu ɗari biyu. Domin in siya abin da nake so.”
Mama Sabuwa ta dafe baki,
“Dubu... ɗari biyu? Saboda kawai kin je gidanta?”
“Eh.”
Mama Sabuwa ta girgiza kai tana kallon ’yarta kamar sabuwar halitta,
“Ke dai kina da farin jini. Wallahi duk inda kika je mutane sai sun so ki.”
Ta yi dariya,
“Ni kam haihuwa ta min rana. Da ni ce aka yi da irin wannan fuskar taki... da yanzu ni ma ina shiga gidajen masu kuɗi ana bani kyaututtuka.”
Bintu ta yi dariya,
“Mama...”

Mama Sabuwa ta ci gaba da zuga ta,
“Ki riƙe wannan Hajiyar da kyau. Kar ki sake sakaci. Irin waɗannan mutane idan suka so mutum... rayuwarsa sai ta canza.”
Ta ɗaga leshin tana sake dubansa,
“Wataƙila ma Allah ya buɗe miki ƙofar arziki ta wurinta.”
Ta ɗan rage murya,
“Kuma idan ta sake kiranki... kar ki ce ba za ki je ba. Ko da zan aikinki da kaina.”
Bintu ta gyada kai da sauri,
“In Sha Allah, Mama.”

Mama Sabuwa ta sake kallon leshin cikin kwaɗayi.
A ranta kuwa… tunani ɗaya ne kawai ke yawo,
“Idan wannan Hajiyar za ta iya ba Bintu dubu ɗari biyu da leshi saboda kama da ’yarta... to idan aka ƙara ƙulla zumunci... wataƙila arziki ya shigo gidan nan ta wannan hanya.”
Sai murmushi ya bayyana a gefen bakinta.
Ba don farin cikin Bintu ba… sai don irin abin duniya da ta fara hangowa daga wannan sabuwar alaqarrr….


***