THE STORM WITHIN
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-NINETEEN:19*
*THE STORM WITHIN*
*JIDDAAH BARKUM*
————-
…A wani ɓangaren kuwa…
Seeyama ta fito daga ɗakinta da sauri, fuskarta cike da tashin hankali, hawayenta na zuba ba ƙaƙautawa.
Kai tsaye ta nufi ɗakin Mommy Hauwa, ko sallama ba ta yi ba… ta tura ƙofar ta shiga,
“Mommy!”
Mommy Hauwa ta ɗago, da ta ga halin da Seeyama take ciki… sai ta miƙe tsaye,
“Seeyama! Me ya faru?”
Seeyama ta ruga ta rungume ta, ta fashe da kuka,
“Mommy… dama na faɗa miki…” ta kasa ƙarasa maganar saboda kukan da ya tokare mata maƙoshi.
Mommy Hauwa ta riƙe kafaɗunta,
“Calm down. Tell me what happened.”
Seeyama ta girgiza kai,
“Mommy... na faɗa miki akwai wani abu tsakaninsu. Amma kin ce a’a... kin ce social media ne kawai. Yanzu ga shi...”
Ta miƙa mata wayarta da hannun da ke rawa,
“Duk media suna ta nuna su. Hotuna suna ko’ina. Mutane suna ta magana. Mommy... don Allah ki ce mini wannan ba gaskiya ba ne.”
Ta sake fashewa da kuka.
Mommy Hauwa ta karɓi wayar, ta duba screen ɗin cikin nutsuwa, da taga hotunan sai ta zaro ido, ta dage kirjinta da ɗayan hannun, “Innalillahi Waa Innaa Ilaihirraji’un.”
Sai ta ajiye wayar Seeyama, ta juya da sauri, ta ɗauki wayarta, ta shiga contacts, ta danna sunan— Hajja Fateema.
Wayar ta shiga ringing, ring ɗaya… biyu… na uku… aka ɗaga,
“Assalamu Alaikum.”
Mommy Hauwa ta ɗan yi shiru na daƙiƙa guda, sannan ta ce cikin murya mai cike da damuwa,
“Wa’alaikumus Salam, Hajja Fateema... what is happening? What is all this I’m seeing all over the media?”
Ta saurara, fuskarta ta ƙara yin tsanani,
“Wallahi abin ya ba ni mamaki. Please... tell me what is going on.”
Wayar dake manne a kunnen Ummie ta ɗan yi nauyi, ta sauke wani dogon numfashi kafin ta ce cikin gajiyawar murya,
“Wallahi, Hauwa... abin da muka wayi gari da shi kenan.”
Ta ɗan lumshe idanunta,
“Mu ma ba mu san daga ina ya fito ba. Cikin dare kawai aka cika social media da hotuna. An yi fake articles... an yi editing...”
Muryarta ta soma rawa,
“Wallahi hankalina ya tashi sosai.”
Mommy Hauwa ta yi shiru na ɗan lokaci cikin tausayi, sai ta ce cikin nutsuwa,
“Hajja Fateema... ki kwantar da hankalinki. Kin san irin rayuwar manyan mutane. Da zarar mutum ya yi fice, sai a samu masu neman jawo shi ƙasa. Wannan ma zai wuce, In Sha Allah.”
Ummie ta dafe goshinta,
“Na fi tausayin yarinyar. Raihana ba ta san komai ba. Yarinya ce mai neman ilimi. Yanzu saboda mugun nufi na wasu... an jefa sunanta cikin abin da ba ta da alaƙa da shi.”
Mommy Hauwa ta girgiza kai cikin muryar tausayi, tace,
“Allah ba zai bar haka ba. Akwai ranar gaskiya. Duk wanda ya shirya wannan, Allah zai tona masa asiri.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da murya mai laushi,
“Ki kula da Zayd. Kar ya bari fushi ya rinjaye shi. Ke ce kika fi sanin halinsa. Idan ya yi shiru, ba yana nufin bai ji ciwo ba ne. Ki kasance kusa da shi.”
Ummie ta gyada kai a hankali,
“In Sha Allah. Na gode sosai, Hauwa. Ki yi mana addu’a. Allah Ya bayyana gaskiya.”
“Ameen.”
Suka yi sallama, kiran ya ƙare.
Mommy ta sauke wayar a hankali kan tebur, ta ɗan zauna tana kallon screen ɗin wayar na wasu daƙiƙu, sai ta ɗaga kai.
Seeyama har yanzu na tsaye gabanta, idanuwanta sun kumbura saboda kuka.
Mommy Hauwa ta miƙa hannu ta kamo nata, ta matse shi cikin tausasawa,
“Seeyama... ki daina kuka. Na ce miki ko? Ba kowace magana da ake yi a social media ake ɗauka da muhimmanci ba. Idan mutum yana da suna... za a samu masu son su ɓata shi. Amma gaskiya ba ta ɓuya har abada.”
Ta share mata hawayen da ke kumatunta,
“Ki je ki yi alwala. Ki yi raka’a biyu. Ki bar komai a hannun Allah.”
Seeyama ta goge idanuwanta, ta gyada kai,
“Okay, Mommy.”
Ta juya a hankali, ta fita daga ɗakin.
Da ƙofar ta rufe… shiru ya mamaye ɗakin.
Mommy Hauwa ta jingina da kujerarta, na ɗan lokaci… ba ta motsa ba.
Sai kuma… a hankali… wani siririn murmushi ya bayyana a gefen bakinta, murmushin da bai kai idanuwanta ba.
Ta ɗauki kofin shayinta, ta kurɓa kaɗan, sannan ta furta cikin ƙasa-ƙasa, kamar tana magana da kanta,
“Everything is going exactly as planned.”
⸻
*MALALI*
Bintu ta ƙaraso a hankali, tana kallon yanayin da ya mamaye tsakar gidan, ta miƙa hannu ta kamo hannun Mama Sabuwa,
“Mama... dan Allah ki zo mu koma ɗaki. Ki barsu da abin da yake damunsu.”
Mama Sabuwa ta juyo ta kalli Umma da wani irin kallo mai cike da gamsuwa, kafin taɓe baki,
“To ai na faɗi gaskiya ne.”
Ta ja tsaki,
“Borin kunya dai ake yi. Yanzu dai kowa ya gani. Allah dai Ya kyauta.”
Har yanzu magana takeyi ƙasa-ƙasa, Bintu ke jan ta zuwa ɗaki.
Da suka shiga ɗakin… Bintu ta rufe ƙofar, ta juya ta kalli mahaifiyarta,
“Mama... wallahi bai kamata kina magana haka ba. Sun riga sun shiga wani hali. Ki barsu da abin da yake damunsu mana.”
Mama Sabuwa ta watsa mata wani kallo,
“Ke dallah! Rufe min baki. Yau kin zama mai min wa’azi kenan? A yi irin wannan abu kina so in yi shiru? Ai ba a taya kishiya jimami. Musamman kishiya mai sumu-sumu irin Hajara.”
Ta ɗaga hannayenta sama,
“Ya Allah... na gode Maka da Ka nuna min wannan rana.”
Ta yi murmushin mugunta,
“Ina son naga shegen da zai ce zai auri Raihana yanzu. Yarinya kullum sai ta dinga kallon mutane a gantale. Tana jin kanta wata tsiya... saboda kawai Allah Ya ba ta kyau. Saboda tana karatun likita. Saboda ana ta yabonta. To yau ga shi... Allah Ya sauke ta ƙasa.”
Bintu ta sauke numfashi,
“Mama... ni yanzu Hajiya ta kira ni. Ta ce zan taya su rabon kaya a foundation ɗinta. Ta ina zan fita? Ga Baffa yana zaune a tsakar gida. Ga kuma abin da ya faru.”
Mama Sabuwa ta yi shiru, sai idanunta suka ƙanƙance, wata dabara ta fara ratsawa cikin zuciyarta.
A hankali ta ce,
“Shi ya isa ya hana ki fita?”
Bintu ta ɗaga gira,
“Mama?”
Mama Sabuwa ta miƙe tsaye,
“Je ki shiga ciki. Ki shirya. Ki saka kayan kirki. Ki bar min sauran.”
Bintu ba tare da ta fahimci abin da ke zuciyar mahaifiyarta ba ta amsa,
“To Mama.”
Ta shiga ɗaki.
Bayan kusan mintuna goma… ta fito cikin doguwar rigar atamfa mai kyau, ta ɗauki jakarta,
“Mama na shirya.”
Mama Sabuwa ta kalleta daga sama har ƙasa, ta gyada kai,
“Da kyau.”
Sai ta miƙa mata hijabi,
“Ki ɗora wannan a kai.”
Bintu ta karɓa,
“Amma Mama ai...”
“Na ce ki ɗora.”
Ba tare da ta ƙara musu ba, Bintu ta saka hijabin.
Mama Sabuwa ta yi wani siririn murmushi wanda Bintu ba ta lura da shi ba,
“Mu je.”
Suka fito daga ɗakin.
A lokacin… har yanzu Baffa Musa, Umma, Mama Indo da sauran mutanen gidan suna zaune a varanda, shiru ne ya mamaye wajen, kowa na cikin tunaninsa.
Mama Sabuwa ta riƙe hannun Bintu tana tafiya cikin natsuwa har suka iso bakin ƙofar fita, sai ta tsaya, ta juyo ta ce cikin ɗaga murya kaɗan, yadda mutanen varanda za su ji,
“Bintu... yi sauri ki je. Duk abinda na lissafa ki siyomin, karki manta ko daya. Sadeeya tundazu tayi gana zuwa kasuwa, karki barta tayi ta jira.”
“Karki bata lokaci kin ji?”
“To Mama,” Bintu ta amsa cikin ladabi, ta juya ta fita… yayin da Mama Sabuwa ta tsaya tana kallon mutanen da ke varanda da gefen ido, kamar tana jiran yadda, ko akwai wanda zai mayar da martani.
Tsakar gidan ya sake yin tsit.
Baffa Musa na zaune a kan tsohuwar kujerar katako da ke ƙarƙashin varanda, hannayensa a ɗaure a ƙirji, kansa a ɗan sunkuye kamar wanda nauyin tunani ya yi masa yawa.
A gefensa kaɗan… Umma na zaune a kan tabarma, idanunta sun kumbura saboda kuka, hannunta ɗaya dafe da habarta, ɗaya kuma tana goge hawayen da suka ƙi tsayawa.
Mama Indo na zaune kusa da ita, tana ta shafa bayanta lokaci zuwa lokaci tana rarrashinta cikin ƙananan kalamai.
A ɗaya gefen tabarmar kuwa… Maryam ce ta rungume Raihana tsam, ta riƙe ta tamkar ƙaramar yarinya.
Raihana kuwa ta jingina jikinta a kafaɗar Maryam, idanunta sun yi ja, amma hawaye ma sun ƙare.
A ɗan nesa da su… Mama Sabuwa ta dawo tana wata tafiya cikin takun da ke nuna isa, ta ja wata kujera da gangan ta zauna daidai inda za ta iya ganin kowa.
Ta gyara zamanta, ta ɗaure hannu a ƙirji, ta taɓe baki, sai ta yi shiru, amma kallon rainin hankali bai bar fuskarta ba.
Baffa ya ɗauki lokaci bai ce komai ba, kamar yana tattara kalmomin da zai faɗa.
Daga ƙarshe… ya ɗaga kansa a hankali, idanunsa suka sauka kan Raihana, cikin murya mai cike da tausayawa ya kira,
“Raihanatu...”
Raihana ta ɗaga kai a hankali, idanunsu suka haɗu, ta buɗe baki kamar za ta yi magana… amma kalmomin suka maƙale a maƙoshinta, ta kasa cewa komai.
Baffa ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali, ya gyada kai a hankali,
“Na san ba ki aikata abin da ake yaɗawa ba.”
Kalmar ta fito daga bakinsa ba tare da wata shakka ba, kamar alƙawari, kamar hukunci.
Raihana ta sake fashewa da kuka, Umma ta runtse idanunta tana ƙara gode wa Allah cewa aƙalla mijinta bai yi gaggawar yanke hukunci ba.
Baffa ya ɗaga hannu cikin alamun kwantar da hankali,
“Ki saurare ni. A rayuwa... mutuncin mutum shi ne mafi girman abin da yake da shi. Idan Allah Ya jarabce ki da irin wannan fitina... ba da gudu ake tsere mata ba. Da haƙuri... da addu’a... da kuma gaskiya ake cin ta.”
Ya ɗan yi shiru, zuciyarshi ta hasko masa hotunan da ke kan wayar, sai ya sake kallon Raihana,
“Na yarda da tarbiyyarki. Na yarda da abin da muka koya miki. Kuma na yarda Allah ba Ya barin gaskiya ta ɓuya har abada.”
Ya sauke numfashi, muryarsa ta yi nauyi,
“Saboda haka... kada ki bari maganganun mutane su karya miki zuciya.”
Ya ɗan yi shiru, sai ya ci gaba cikin natsuwa,
“Ki kwantar min da hankalinki. Ki nutsu. Kada ki ɗaga wa kanki hankali a kan abin da mutane suke faɗa. Ki toshe kunnuwanki ga maganganunsu. Ki kuma rufe idanunki ga duk abin da zai ƙara tayar miki da hankali.”
Ya ɗora hannunsa a kan hannun kujerar da yake yana kallonta da idanu masu cike da tausayawa,
“Ki tuna da abu ɗaya, Raihanatu... ƙarya fure take, ba ta taɓa yin ‘ya’ya ba. Ko ta yi yawo har ƙarshen duniya... ranar da gaskiya ta fito, ita ce za ta tsaya, ƙarya kuma ta rushe. Saboda haka... ki bar wannan al’amari ga Allah. Shi ne mafi kyawun Mai bayyana gaskiya.”
Ya ja dogon numfashi,
“Sannan ina son ki fahimci wani abu. Daga yau... ba na son ki koma makaranta.”
Da sauri Raihana ta ɗago kanta.
“Ba saboda na yarda da abin da ake faɗa ba. A’a. Saboda ina son na kare ki. A yanzu hankulan mutane sun tashi. ’Yan jarida na iya zuwa. Masu ɗaukar bidiyo na iya binki. Wasu kuma ba neman gaskiya suke ba... abin da suke nema shi ne su samu abin da za su ƙara yaɗawa. Ba zan bari ki shiga cikin wannan yanayin ba.”
Ya nuna ƙasa da yatsansa,
“Za ki zauna a gida. Har sai wannan hayaniyar ta lafa. Har sai gaskiya ta fito fili. Karatunki ba zai gudu ba. Karatun ba zai fi mutuncinki muhimmanci ba. Idan Allah Ya nufa, za ki koma ki ci gaba daga inda kika tsaya.”
Ya yi murmushi mai laushi,
“Amma a wannan lokacin... lafiyarki da kwanciyar hankalinki su ne suka fi komai muhimmanci.”
Raihana ta kasa magana, hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka sake zubo, ta sunkuyar da kanta, cikin rawar murya ta ce,
“Na ji, Baffa... zan yi haƙuri. Zan yi addu’a.”
Baffa ya gyada kai cikin gamsuwa,
“Haka nake so. Ki yawaita istigfari. Ki riƙe Al-Qur’ani. Ki kusanci Allah fiye da da. Domin idan Allah yana tare da mutum... babu wanda zai iya rushe shi.”
Sai ya ɗaga hannayensa sama kaɗan,
“Allah Shi ne Shaida. Wallahi ranar da gaskiya za ta bayyana... waɗanda suka ƙirƙiri wannan ƙarya su ne za su nemi inda za su ɓoye fuskokinsu.”
Tsakar gidan ya sake yin tsit, Umma ta share hawayenta.
Ita kuwa Raihana… ta sunkuyar da kanta, hawayen da ke zuba daga idanunta ba na kunyata ba ne a wannan karon… na samun ƙarfin gwiwa ne daga kalaman mahaifinta.
⸻
Daren ranar… gidan ya yi tsit.
Ko da yake fitilun tsakar gidan suna ci gaba da haskakawa, amma zuciyar Raihana ta fi kowane lungu na gidan duhu.
Tana kwance a kan gadonta, ba bacci take ba, idanunta a rufe suke kawai, ƙirjinta kuwa tamkar an ɗora masa dutse.
Tun bayan abin da ya faru da safe… rayuwarta ta sauya cikin sa’o’i kaɗan.
Wayarta da ba ta cika samun kira ba… yau ta kasa yin shiru, tun safe har dare… notifications ba su daina shigowa ba.
Da farko ta yi ƙoƙarin buɗe wasu messages, sai dai abin da ta gani… shi ya sa ta yi nadamar buɗewa:
“Raihana, da gaske kina tare da Zayd ne?”
“Ashe shi ne ya sa kika samu scholarship?”
“Wallahi ban taɓa zaton haka daga gare ki ba.”
“Ki yi haƙuri, komai zai wuce in shaa Allah.”
“Ignore them, Allah Ya san gaskiya.”
Wasu forwarding suke mata hotunan, wasu links na blogs, wasu screenshots na comments, wasu tambayoyi, wasu kuma zarge-zarge.
A ƙarshe… ta daina buɗe komai, ta kashe data, ta ajiye wayar a gefen pillow, ta rufe idanunta.
Amma ko ta rufe idanun… maganganun mutane ba su bar zuciyarta ba.
Ta ji kamar duniya gaba ɗaya ta juya tana kallonta, kamar kowa yana yanke mata hukunci ba tare da ya ji ta ba.
Wani irin zafi ya tokare mata maƙoshi, sai dai ta hana kanta kuka, domin ta gaji da kuka.
A dai-dai wannan lokacin… wayarta ta sake haskawa, rrrnnn… ta yi ringing.
Ba ta motsa ba, ta ƙyale ta har ta katse.
Daƙiƙu kaɗan bayan haka… ta sake yin ringing, har yanzu ba ta ɗauka ba, ta sake katsewa.
Sai aka sake kira, na uku, na huɗu, na biyar, ringing ɗin wayar ya ci gaba da maimaituwa.
Raihana ta buɗe idanunta a hankali, cikin kasala ta juya kanta ta kalli screen ɗin wayar.
A dai-dai lokacin… kira na shida ya sake shigowa, sunan da ya bayyana ya sa zuciyarta bugawa,
*HARIS CALLING...*
Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi, Haris… tun safe yana ta neman ta, amma ba ta da ƙarfin yin magana da kowa.
Sai yanzu… a hankali ta miƙa hannu, ta ɗauki wayar, ta ɗan share hawayen da ya taru a gefen idanunta, sannan ta ɗaga kiran,
“Assalamu alaikum...” muryarta ta fito a hankali, rauni da gajiya sun bayyana ƙarara cikinta.
A ɗaya ɓangaren… shiru ya biyo baya na wasu daƙiƙu, sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, kamar wanda aka sauke masa wani babban nauyi daga ƙirji, muryarsa ta fito cike da sanyi,
“Wa alaikumus salam... na zata ba za ki ɗaga ba.”
Raihana ta lumshe idanunta, ta jingina kanta da headboard ɗin gadon, ba ta ce komai ba.
Haris ya sake yin magana cikin kulawa,
“Wallahi... na kira sau da yawa ne ba don na dame ki ba. Na kira ne saboda...” ya ɗan tsaya, “…na san kina cikin wani irin hali yanzu.”
Shiru ya sake ratsa layin, sai sautin numfashin Raihana kawai ake ji.
Haris ya ci gaba da cewa cikin tausasawa,
“Kin ci wani abu kuwa…?”
Sai lokacin ma ta tuna da cewa yau fa bataci komai, amma duk da haka batace komai ba, sai kawai tayi shiru.
Haris ya ɗan yi murmushi mai cike da tausayawa,
“Kin san me ya sa na kira?”
Raihana ta girgiza kai a hankali, ko da yake ba ya ganinta,
“A’a...”
Haris ya sauke numfashi,
“Ba don na tambaye ki wani abu ba. Ba don na ji wani bayani daga gare ki ba. Ba kuma don na ƙara miki wani nauyi ba.”
Ya ɗan yi shiru,
“Na kira ne kawai... don na ji muryarki.”
Raihana ta runtse idanunta, wannan kalmar kaɗai ta sa zuciyarta ta sake rauni.
Haris ya ci gaba cikin sanyin murya,
“Tun safe ina ta kiran ki. Da na ga ba ki ɗagawa... na ce wataƙila kina buƙatar a ba ki lokaci. Amma yanzu na ji daɗin kin ɗaga.”
Shiru ya sake ratsawa, sai bugun zuciyarsu, sai numfashin Raihana kaɗai ake ji daga ɗaya ɓangaren.
Haris ya sake magana,
“Kin ci wani abu?”
Ta girgiza kai kafin ta tuna ba ya ganinta,
“A’a...”
Ya ɗan yi shiru,
“Rayhaan... ko da ba don yunwa ba... ki ci wani abu kaɗan. Ki kula da kanki. Muhimmiyar rayuwa ce a gabanki.”
Muryarsa cike take da kulawa, ba tausayin da zai karya mutum ba… kulawar da ke ƙoƙarin ɗaga mutum tsaye,
“Ki yi alwala idan ba ki yi ba. Ki karanta abin da ya sauƙaƙa. Ki yi raka’a biyu. Sannan ki kwanta. Ki bar sauran komai ga Allah. Wallahi... wannan ba shi ne ƙarshen rayuwarki ba. Wannan jarabawa ce. Kuma in shaa Allah... za ta wuce.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya yi magana cikin wata irin nutsuwa mai ratsa zuciya,
“Idan kina jin kamar duniya ta juya miki baya... ki tuna... akwai mutanen da har yanzu suna tsaye a bayanki. Iyayenki. ’Yan uwanki. Ni ma... ina cikinsu. Ba zan taɓa barin ki ki fuskanci wannan ke kaɗai ba.”
Ta lumshe idanunta tana jin maganganunsa na ratsa zuciyarta, a hankali ya cigaba,
“Komai yana da mafita in shaa Allah.”
Ta amsa da ƙyar,
“In shaa Allah...”
Kafin a nutse ya ce,
“Good night, Rayhaan.”
“Good night...” ta amsa da muryar da ta dashe.
Ta sauke wayar a hankali, ta jingina da headboard na gadonta, wayar na hannunta, ta kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta kashe ta gaba ɗaya.
A karon farko tun bayan abin da ya faru… ta ji zuciyarta ta ɗan sauya.
Ba don matsalar ta ƙare ba… sai don ta tuna cewa har yanzu akwai mutanen da ba sa yanke hukunci kafin su ji gaskiya.
Mutanen da kasancewarsu kaɗai… na iya rage nauyin da zuciya ke ɗauke da shi.
————————
*ARMAAN MANSION*
Falon Ummie ya yi shiru mai nauyi, babu wanda ke da walwala, kowa fuskarsa cike take da damuwa.
Ummie na zaune a kan kujerar da ta saba zama, a gefenta Hajiya Hauwa ce, can gefe kuma Suhaila da Seeyama suna zaune cikin nutsuwa, babu wacce ke cewa komai.
A ɗaya gefen falon kuwa, ƙanin mahaifin Zayd, Alhaji Munzali, yana zaune yana kallon kowa cikin tunani.
Na ɗan lokaci… sai Hajiya Hauwa ta sauke wani dogon numfashi,
“Tirkashi... wallahi Hajja Fateema... wannan al’amarin ba ƙaramin abu ba ne.”
Ta ɗan yi shiru,
“Sai dai yanzu... mene ne mafita?”
Falón ya sake yin tsit, Ummie ta sauke idanunta ƙasa, ba ta da amsar da za ta bayar.
Hajiya Hauwa ta juya ta kalli Alhaji Munzali,
“Yaya... ni fa abin da ya fi daga min hankali ba ma hotunan ba ne.”
Ta ɗan taɓe baki,
“Maganganun mutane ne. Wallahi tun safe wayata ba ta daina ringing ba. Kowa magana yake yi. Wasu ma har cewa suke...”
Ta ɗan dakata kafin ta ƙarasa,
“Ashe shi ya sa Zayd ya ƙi aure kenan? Ashe wannan rayuwar yake yi a ɓoye? Kuɗi sun lalata shi? Mutumin da bai da aure, ai komai za a zata a kansa.”
Ta girgiza kai cikin takaici,
“Maganganu iri-iri. Wallahi abin ba daɗi.”
Seeyama ta sunkuyar da kanta, Suhaila kuwa ta matse yatsunta, Alhaji Munzali ya ɗan sauke numfashi, amma bai ce komai ba.
Sai Hajiya Hauwa ta ci gaba,
“Ni kam... da za ku ɗauki shawarata... a yi gaggawar ɗaura wa Zayd aure.”
Kowa ya ɗago kai ya kalleta.
Ta ci gaba da cewa,
“Da Seeyama. Ko ba komai... za a rage bakin mutane. Da zarar sun ji yana da mata... yawancin waɗannan surutai za su mutu da kansu.”
Ta girgiza kai,
“Amma yanzu... sun riƙe kalma ɗaya. Mutumin da bai da aure... ga kuɗi... me ake zato zai riƙa yi? Wallahi mutane ba su da kirki ko kadan. Ba sa neman hujja. Abin da suka ji shi suke yaɗawa.”
Ta kalli Ummie,
“Hajja Fateema... kafin wannan abin ya ƙara faɗaɗa... ina ganin ya kamata a yi tunani sosai.”
Shiru ya sake mamaye falon, sai a hankali… Alhaji Munzali ya ɗaga kansa, ya haɗe hannayensa, ya kalli Hajiya Hauwa da idanu masu natsuwa,
“Hauwa... maganar aure ba ƙaramin abu ba ce. Ba abin da ake yi saboda tsoron bakin mutane ba.”
Ya ɗan yi shiru,
“Sannan... idan muka ɗaura masa aure saboda mu rufe bakin jama’a... me zai hana gobe idan wata jita-jita ta sake fitowa a ce mu ƙara ɗaura masa wata matar?”
Ya girgiza kai,
“A’a. Ba haka ake warware irin wannan matsala ba.”
Ya juya ya kalli Ummie,
Falón ya sake yin tsit, kowa ya faɗa cikin zurfin tunani, domin sun fahimci cewa… wannan ba kawai yaƙi ne da ake yi wa Zayd ba, yaƙi ne da ake yi wa mutuncinsa, sunansa, da kuma duk wanda yake da alaƙa da shi.
Not edited