THE TRUTH EMERGES BUT THE DAMAGE REMAINS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER -TWENTY:20*
*THE TRUTH EMERGES… BUT THE DAMAGE REMAINS*
*JIDDAAH BARKUM*
————————————
Kwanaki huɗu kenan… tun bayan da scandal ɗin ya balle.
Armaan Cyber Security Division, Digital Forensics Unit, International AI Experts, Legal Team, da kuma wasu manyan kamfanonin da suka ƙware wajen binciken cyber crimes.
Kowa bai san barci ba a kwanakin nan da suka biyo baya.
An tattara hotuna guda ɗari da goma sha uku, 113, da suke yawo a internet.
An binciki kowanne daban, pixel by pixel, frame by frame, reflection, lighting, facial mapping, metadata, AI fingerprints, compression patterns, har zuwa source files.
Babu abin da aka bari.
A ƙarshe… rahoton da aka daɗe ana jira ya fito, Official Digital Forensic Report.
*RESULT:*
“All circulating images involving Mr. Zayd Armaan and Miss Raihana are AI-generated composite images.”
Rahoton ya bayyana cewa… an yi amfani da hotuna na gaske da aka ɗauka a event, sai aka ɗauke su, aka saka su cikin Advanced Generative Artificial Intelligence software, aka ƙirƙiri sababbin hotuna, aka canja muhalli, aka canja haske, aka canja poses, aka ƙara abubuwan da ba su taɓa faruwa ba.
Experts daga ƙasashe uku daban suka tabbatar da sakamakon ɗaya, babu wani hoto ko guda da ya kasance na gaske, dukkansu… ƙirƙirarru ne.
Da rahoton ya fito… Legal Team ta fara aiki, court orders suka fara fita, official takedown notices aka tura.
Instagram, Facebook, X, TikTok, YouTube, blogs, news websites.
Cikin sa’o’i kaɗan… hotunan suka fara ɓacewa ɗaya bayan ɗaya.
Manyan bloggers da suka fara wallafawa… suka fara gogewa, wasu suka fitar da public apology,
“Following the findings of independent digital forensic investigators, we have removed the earlier publication.”
Wasu suka rubuta,
“We sincerely apologize to Mr. Zayd Armaan and Miss Raihana, the published materials have now been confirmed to be AI-generated.”
Wasu ma comments section suka rufe gaba ɗaya saboda yawan zagi da suka fara samu.
A hankali… trending hashtag ɗin ya fara sauka, sai wani sabon hashtag ya hau,
#AIManipulation, #JusticeForRaihana, #FakeScandal
⸻
Amma… a wajen Zayd… ba a nan ya tsaya ba.
Ya ce wa Sameer cikin murya mai sanyi,
“I don’t want the posts only. I want the person who started all this.”
“A nemo min ko waye ya fara wallafa hotunan a shafinsa.”
Nan take… cyber investigation ta koma mataki na gaba, aka fara tracing, an bi timestamps, an bi original upload, an bi servers, an bi VPN, an bi crypto payments, an bi burner emails, har zuwa account na farko da ya fara wallafa hoton.
Bayan kwana biyu… an gano shi, wani blogger ne, ba babban influencer ba, sai dai… shi ne farkon wanda ya saki hoton, daga gare shi ne… dubban accounts suka ɗauka suka ci gaba da yaɗawa.
Legal Team ta fitar da arrest warrant nan take, aka miƙa bayanansa ga hukumomin tsaro.
Sai dai… lokacin da aka isa inda yake… an tarar, ya riga ya bar ƙasar.
Immigration records suka nuna… awanni kaɗan kafin a gano asalinsa… ya hau jirgi, ya fice daga ƙasar.
Destination… ba a bayyana ba.
Sameer ya sauke rahoton a gaban Zayd,
“He disappeared.”
Zayd ya ɗan yi shiru, ya rufe file ɗin, sannan ya ce cikin natsuwa,
“People run because they know they’ll eventually be found. He won’t stay hidden forever.”
Amma… ko da gaskiya ta fito… ba kowa ya yarda ba.
A social media… sabuwar muhawara ta fara,
“Ai kuɗin Zayd ne suka yi wannan.”
“An biya experts.”
“An sayi bloggers.”
“An yi amfani da iko aka goge komai.”
Wasu suka ce,
“Idan ba gaskiya ba ne… me ya sa sai bayan kwanaki aka fito da rahoto?”
Wasu kuma suka ƙi yarda gaba ɗaya,
“Ai masu kuɗi komai za su iya. Internet ba ya ƙarya.”
Sai wasu suka mayar da martani,
“Internet ne ma ya fi ƙarya yanzu. AI na iya ƙirƙirar komai.”
Amma… ko da hujjoji suna gaban idanu… wasu mutane sun riga sun yanke hukunci, ba sa neman gaskiya, suna neman abin da zai tabbatar musu da abin da suka riga suka gaskata.
Domin… a wasu lokuta… gyara suna ya fi wahalar kare shi tun farko.
————————-
*ARMAAN MANSION*
Da misalin ƙarfe goma na safe… hasken rana ya fara ratsawa ta manyan glass windows na mansion ɗin, yana ƙara fito da kyawun cikin gidan.
Komai na gidan cikin tsafta yake, fresh flowers masu ƙamshi an sauya su a manyan flower vases, ƙamshin oud mai taushi ya gauraya da na vanilla diffuser, yana ba falon wani irin nutsuwa da ƙamshi na alfarma.
A hankali… Ummie ta fito daga upstairs, takunta cike da nutsuwa da kwarjini.
Sanye take cikin wata doguwar Dubai luxury lace mai launin chocolate brown mai zurfi, lace ɗin cike take da lafiyayyun Swarovski stones da ke walkiya duk lokacin da hasken ya bugi jikinta.
Ɗinkin flowing boubou ne mai faɗi, amma yadda aka tsara shi ya zauna a jikinta cikin matuƙar armashi, yana ƙara fito da kamala da darajar da Allah Ya yi mata.
Mayafi mai launin kayan nata ne aka tooling da ƙananan stones a gefuna, ta yafa shi cikin tsari irin na manyan mata masu cikar kamala.
A hannunta kuwa… Rolex mai sauƙin kyau ce, a wuyan hannu kuma… mundayen zinariya masu kauri amma masu tsari.
Ɗan ƙaramin diamond brooch ne ya riƙe mayafin a kafaɗarta, ta ci uban gwalagwali hannu da wuya kamar ba da kuɗi aka siya ba.
Fuskarta cike take da natsuwa, sai ƙamshin turarenta mai daɗin gaske da ya fara cika wajen tun kafin ta iso ƙasa.
Tun kafin ta ƙaraso ƙarshen stairs… Kubura ta fito da sauri daga kitchen corridor,
“Assalamu alaikum Hajiya.”
“Wa alaikumus salam, Kubura.”
Kubura ta ƙaraso cikin girmamawa, ba tare da ɓata lokaci ba ta karɓi handbag ɗin Ummie da hannaye biyu.
Suna isa babban falo… Kubura ta ɗan durƙusa ta ajiye jakar a gefen kujerar da Ummie ta saba zama.
Ummie ta zauna cikin nutsuwa, Kubura kuma ta zauna ƙasa kusa da ita cikin ladabi, ta ɗan yi murmushi kafin ta ce,
“Hajiya... yau weekend ne. Shin za a dafa abincin rana ne yanzu? Ko akwai wani abu da kike buƙatar a tanada kafin ki dawo?”
Ummie ta kalleta, sai murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Kubura...” ta girgiza kai cikin wasa,
“Har yaushe zan hana ki wannan zubewar nan? Kin zo kin sake zama a ƙasa. Ban taɓa son haka ba.”
Kubura ta yi murmushi tana ɗan sunkuyar da kai,
“Wallahi Hajiya... na fi jin daɗi idan ina zaune a haka.”
Ummie ta ɗan taɓe baki cikin raha,
“Ni kuma ba na jin daɗi. Ke ma mutum ce kamar kowa. Idan na zauna a kujera, ke ma ki zauna. Kada ki riƙa zubewa ƙasa kullum.”
Kubura ta yi dariyar kunya,
“To Hajiya. In shaa Allah ba zan sake ba.”
Ummie ta gyada kai cikin gamsuwa,
“Game da girkin kuma... ki dafa abin da kowa yake so. Ni ba zan daɗe ba. In shaa Allah kafin Azahar zan dawo.”
Kubura ta amsa da sauri,
“To Hajiya.”
A dai-dai wannan lokacin… sautin takun ya gauraye wajen daga upstairs, Suhaila ce ke saukowa.
Sanye take cikin wata kyakkyawar flowing abaya mai launin dusty rose, an yi mata embroidery na silver a wuyan rigar da cuffs ɗin hannu cikin matuƙar tsari.
A ƙafarta fararen sandals masu sauƙin kyau, ƙaramar handbag ta rataya a kafaɗarta, ba ta yi kwalliya mai yawa ba, sai lip gloss mai laushi da ƙamshin turare mai daɗi.
Ta ƙaraso tana murmushi,
“Assalamu alaikum Ummie.”
“Wa alaikumus salam, sweetheart.”
Ta zauna kusa da Ummie, sai ta ɗan karkatar da kai,
“Ummie... ina za mu je ne?”
Ummie ta kalleta, sai ta yi murmushi mai cike da nufin ɓoye sirri,
“Ki yi haƙuri. Za ki gani idan mun isa.”
Suhaila ta turo baki cikin shagwaba,
“Ummie fa... kullum surprise.”
Ummie ta yi dariya a hankali.
A dai-dai lokacin… aka buɗe ƙofar falon, Sameer ya shigo cikin nutsuwa.
Da ya hango Ummie… sai ya ƙaraso, ya ɗan sunkuyar da kansa cikin girmamawa,
“Assalamu alaikum, Ummie.”
“Wa alaikumus salam, Sameer. Barka da safiya, fatan kun tashi lafiya.”
“Lafiya lau Alhamdulillah. Allah Ya ƙara lafiya.”
“Ameen.”
Sai ya juya ya kalli Ummie cikin ladabi,
“Ummie... komai ya kammala. Za mu iya tafiya duk lokacin da kika shirya.”
Ummie ta gyara mayafinta a hankali, sannan ta ce,
“Sameer... ba na son a fita da motoci da yawa yau.”
Sameer ya ɗaga kai cikin nutsuwa,
“Motar guda ɗaya ta isa. Daga ni... ke,” ta nuna Suhaila, “sai kai. Shi kenan. Babu sauran convoy.”
Sameer ya ɗan yi mamaki,
“Hajiya... security fa?”
Ummie ta yi murmushi cikin natsuwa,
“Kar ka damu. Inda za mu je ba wajen hayaniya ba ne. Sannan wani lokaci... mutum yana buƙatar fita cikin sauƙi ba tare da jan hankalin duniya ba.”
Sameer ya gyada kai cikin girmamawa,
“Yanda kika ce Ummie.”
Ummie ta miƙe tsaye a nutse, kwarjininta ya cika wajen,
“To mu je.”
Suhaila ta miƙe tana biye da ita, Sameer kuwa ya yi gaba domin ya buɗe musu ƙofa.
Ba tare da hayaniya ko dogon jerin motoci ba… su uku kaɗai suka nufi wajen motar, yayin da iska mai laushi ke kaɗa mayafin Ummie, tana ƙara fito da kwarjini da kamalar da take ɗauke da ita.
Kai tsaye… motar Mercedes-Maybach ɗin ta fice daga Armaan Mansion, Sameer ne ke tukawa cikin nutsuwa, Ummie na zaune a bayan mota gefen dama, Suhaila kuma na gefenta.
Dama already Sameer ya riga ya san inda za su je, dan haka kawai hanya suka ɗauka.
Babu wanda ya sake magana, sai ƙar AC mai laushi da kuma karatun Qur’ani da ke tashi a hankali cikin motar.
Bayan kusan mintuna talatin… manyan titunan unguwar suka ƙare, motar ta fara shiga ƙananan layukan Malali.
Suhaila ta fara kallon wajen ta window, idanuwanta cike da mamaki, ta sake kallon Ummie,
“Ummie...”
Ummie ta juyo gare ta,
“Hmm?”
“Wai ina ne nan? Ko dai aikin foundation ɗin ne za mu je?”
Ummie ta yi murmushi, murmushin da bai bayyana komai ba,
“Za ki gani. Mun kusa.”
Suhaila ta ɗan turo baki,
“Haba Ummie... kullum sai kina ɓoye min abu.”
Ummie ta yi dariya a hankali,
“Ki yi haƙuri. Surprise idan an faɗa kafin lokaci... ba ya ƙara zama surprise.”
Sameer ma ya ɗan yi murmushi yana kallon su ta mirror.
Bayan mintuna kaɗan… ya rage gudun motar, sannan ya tsaya a gaban wani gida mai tsari na Hausawa, ya kashe engine, ya juya cikin ladabi,
“Ummie... mun iso.”
Ummie ta ɗaga kai, ta kalli gidan, ta sauke numfashi,
“Alhamdulillah.”
—————
A cikin gidan kuwa… Umma ce tsaye a bakin famfon tsakar gida, tana wanke kayan miya domin girki, gefenta akwai kwando cike da alayyahu da yakuwa.
Mama Indo kuwa… na zaune a kan kujera ƙarƙashin inuwa, tana yanke farce cikin nutsuwa.
Yayin da… Mama Sabuwa ke zaune kusa da turmi, “bug!… bug!… bug!” amo yake tashi yayin da take daka barkono, lokaci zuwa lokaci tana attishawa sai ta goge hanci da gefen zaninta.
Sai dai… a dai-dai lokacin… suka ji ƙar wata mota ta tsaya a bakin gida, kowa ya ɗaga kai.
Mama Sabuwa ta fara magana,
“Waye kuma wannan?”
Mama Indo ta miƙe kaɗan tana leƙawa.
A daidai lokacin… aka buga ƙofar gida,
“Assalamu Alaikum.”
Muryar Sameer ce.
Mama Indo ta amsa da sauri,
“Wa Alaikumus Salam.”
Maryam ce ta fito daga ɗaki, ta nufi ƙofar, ta buɗe, da ta ga mutanen tsaye a waje… sai ta tsaya cak, saboda irin motar da mutanen.
Ta yi saurin cewa,
“Sannu da zuwa.”
Sameer ya yi murmushi,
“Sannu. Hajiya na son shiga.”
Maryam ta matsa gefe,
“Bismillah.”
Da suka shiga… Umma na wajen famfo, har yanzu hannunta ɗan jike yake, Mama Indo ma ta miƙe tsaye.
Mama Sabuwa kuwa… da ta ga irin lace ɗin da Ummie take sanye da shi… idanuwanta suka yi walkiya,
“Innalillahi...” ta faɗa a ranta,
“Ashe ita ce hajiyar da Bintu ke zuwa wajen foundation?”
Nan take… fuskarta ta canja, ta yi saurin goge hannunta, ta yi murmushi ta washe haƙora, ta ƙaraso da sauri,
“Ahhh... sannunku da zuwa. Barkan zuwa. Sannunku. Bismillah.”
Mama Indo ma ta taso da sauri ta kawo kujera,
“Kuzo ku zauna.”
Ummie ta yi musu murmushi cikin nutsuwa,
“Nagode.”
Ta zauna a hankali, Suhaila ma ta zauna kusa da ita.
Mama Sabuwa kuwa… tunani ɗaya ne kawai ke kanta,
“Lallai ashe wannan itace hajiyar Bintu tabdijamm,” ta faɗa a ranta tana ta faman murmushi.
Sai kuma tayi zumbur tace,
“Wallahi da mun sani ai da mun yi wani shiri. Kai baƙi irin ku ai...”
Umma ta ɗan yi murmushi kawai daga can inda take, sai ta ce,
“Sannu da zuwa.”
Ummie ta gyada kai,
“Yauwa, sannu da aiki.”
Umma ta ɗan yi murmushi ta cigaba da aikinta.
Na ɗan lokaci… shiru ya ratsa tsakar gidan, sai sautin tsuntsaye kawai ake ji.
Daga nan… Ummie ta ɗago kanta, ta kalli Mama Sabuwa da murmushi, ta ce cikin ladabi,
“Mama... ina Raihana take?”
Da sunan ya fita daga bakin Ummie… “Raihana,” sai jikin Umma ya yi wani irin sanyi, ta kasa cewa komai, sai dai idanunta suke binsu cikin mamaki da rashin fahimta.
“Wace irin mace ce wannan? Me ya kawo ta gidan nan? Kuma me take nema da Raihana?” tambayoyi ne suka cika mata zuciya.
Murmusshin da ke fuskar Mama Sabuwa ya mutu nan take, tamkar an zuba mata ruwan sanyi, ta kalli Ummie, sannan ta kalli Umma,
“Raihana?” zuciyarta ta buga,
“To... ba hajiyar foundation ba ce kenan? To me ya kawo ta gidan nan?”
Umma kuwa… fuskarta ta nuna mamaki, sai kuma wani irin annuri ya bayyana a idanunta, ta yi saurin amsawa cikin girmamawa,
“Tana ɗakinta.”
Ummie ta gyada kai cikin tausayawa, ta ce a hankali,
“Idan ba damuwa... ina so in ganta.”
Umma ta yi saurin cewa,
“Ba damuwa. Mu shiga ciki.”
Ta juya gaba.
Ummie ta miƙe a hankali, Suhaila ma ta tashi ta bi bayanta.
Yayin da… Mama Sabuwa ta ci gaba da binsu da ido har suka shige ciki, ta kasa ɓoye mamakinta.
A hankali ta matso kusa da Mama Indo, ta raɗa mata cikin ƙasa-ƙasa,
“Haba... wai su... sun san Raihana ne?”
Mama Indo ta kalleta, ta ɗan taɓe baki,
“Allah ne kaɗai Ya san abin da zai faru.”
Mama Sabuwa ta haɗiye yawu, a karon farko… ta fara jin wani irin faɗuwar gaba, domin ta fahimci… ba duk abin da take zato ba ne yake zama gaskiya.
———————-
Falon Umma ba wani falon alfarma ba ne, ba marble ba ne, ba chandelier mai tsada ba ne, ba imported furniture ba ne.
Amma… da zarar mutum ya taka ƙafarsa ciki… abin farko da zai ji shi ne… tsafta.
Farin tiles ɗin falon suna sheƙi kamar an gama gogewa a wannan lokacin, a gefe akwai sofas masu kyau da aka kula dasu sosai, an shimfiɗa mata fararen lace covers masu ƙamshi.
A jikin bango kuwa… akwai wasu frames na ayoyin Al-Qur’ani da hoton Ka’aba, a gefe kuma wata ƙaramar bookshelf ce mai cike da Al-Qur’anai, littattafan Hadisi da na addini, sai TV LG plasma.
An shimfiɗa wata sabuwar dadduma mai laushi a tsakiyar falon, duk da sauƙin kayan cikin gidan… falón na ɗauke da wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali, kuma… kamshin turaren wuta ya mamaye ko’ina, ba ƙamshi mai nauyi ba… sai wani irin ƙamshi mai sanyi da ke sa zuciya ta natsu.
Ummie ta shiga falon tana kallon komai cikin nutsuwa, ba ta ga talauci ba… ta ga tsafta, ta ga tarbiyya, ta ga gidan da aka gina da halal.
Wani siririn murmushi ya bayyana a gefen bakinta.
Umma ta ƙaraso gefen daddumar, ta gyara ta da hannunta, sannan ta ce cikin ladabi,
“Bismillah Hajiya... nan za ki fi jin daɗi.”
Ummie ta yi murmushi,
“Nagode sosai.”
Ta zauna a kan daddumar cikin nutsuwa, Suhaila kuwa ta zauna a kan kujerar da ke kusa da ita, Umma ta zauna a ɗan nesa kaɗan.
Sai suka sake gaisawa cikin mutunci.
Bayan ƴan mintuna… Ummie ta ɗaga kanta, ta kalli Umma da murmushi,
“Mama... ina so na ga Raihana.”
Umma ta ɗan tsaya, har yanzu mamaki bai bar zuciyarta ba,
“Wacece wannan matar? Ta yaya ta san sunan Raihana? Kuma me yasa ta zo neman ganinta?”
Amma duk da haka… ba ta tambaya ba, ta miƙe cikin ladabi,
“To Hajiya. Bari na miki magana da ita.”
Ta juya ta nufi dakin Raihana.
A hankali ta buɗe labulen ɗakin Raihana, ɗakin ya yi shiru, labulen window a rufe yake sai ya sa dakin ya ɗan yi duhu kaɗan.
Raihana na kwance a kan gadonta, ba bacci take yi ba, amma idanunta a rufe suke, fuskarta ta rame cikin kwanaki kaɗan, kumburin idanunta ya nuna irin yawan kukan da ta ke yi.
Wayarta kuwa tana kashe a gefen pillow.
Umma ta tsaya tana kallonta na wasu daƙiƙu, zuciyarta ta ƙara taushi, a hankali ta ƙarasa bakin gadon, ta zauna gefenta, ta shafa kanta cikin tausayi,
“Raihanatu...”
Raihana ta buɗe idanunta a hankali, da ta ga Umma… ta yi ƙoƙarin miƙewa, amma Umma ta riƙe hannunta,
“A’a... ki tashi a hankali.”
Raihana ta zauna, ta kalli Umma,
“Lafiya Umma?”
Umma ta yi murmushi,
“Kinyi baƙuwa.”
Raihana ta sake kallon Umma da kyau, zuciyarta na bugawa,
“Baƙuwa…?”
Umma ta gyada kai,
“Eh. Wata Hajiya ce. Ta zo ne... saboda ke.”
Raihana ta sauke idanunta, sai kuma ta dago ta sake kallon Umma,
“Saboda ni?”
“Eh. Ban san ko daga ina ta san ki ba. Amma tana son ganinki.”
Ta shafa mata kumatu cikin tausayi,
“Tashi ki gyara fuskarki. Sannan ki saka hijabi ki fito. Ba na son ki fito da wannan fuskar.”
Ta yi murmushi tana ƙoƙarin ƙarfafa mata zuciya,
“Kin ji ko?”
Raihana ta yi shiru na ɗan lokaci, daga ƙarshe ta gyada kai a hankali,
“To Umma...”
Umma ta dafa kafaɗarta cikin ƙauna, ta miƙe ta fita daga ɗakin cikin nutsuwa.
Raihana kuwa… ta zauna na wasu daƙiƙu tana kallon ƙofar da Umma ta fita, har yanzu zuciyarta cike take da tambayoyi,
“Wacece wannan Hajiya? Me ya kawo ta nemana? Shin... akwai wani sabon abu kuma?”
Ta sauke numfashi a hankali, sannan ta miƙe daga kan gadon, ta nufi madubi ta tsaya tana dan kallon fuskarta, kafin a hankali ta juya ta ɗauki hijabinta ta saka, ta nufi kofa cikin nutsuwa…
Not edited