ZAYD ARMAAN

THE FIRST STEP

by @jiddaahbarkum






*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER-TWENTY ONE:21*

*THE FIRST STEP*

*JIDDAAH BARKUM*

⸻

A hankali… Raihana ta gyara hijabin da ta saka, ta ɗa share fuskarta da gefen hijab din, tana ƙoƙarin rage alamun kukan da suka bayyana ƙarara a idanunta.

Ta ja wani dogon numfashi, sai ta buɗe labulen ɗakin a hankali.
Takunta ba ta da sauri kamar yadda aka saba, kowanne taku da take yi kamar tana ɗauke da wani irin nauyi a zuciyarta.

Da ta taka cikin falon… idanunta suka sauka kan matar da ke zaune cikin natsuwa a kan dadduma.
Koda yake ba taɓa haɗuwa da ita ba… amma kwarjini da kamalar matar sun sa Raihana ta tsaya na ɗan daƙiƙa.

Ummie kuwa… tun kafin Raihana ta iso gabanta… idanunta suka sauka a kanta.
Ta yi shiru, ba don rashin abin cewa ba… sai don abin da take gani ya taɓa mata zuciya.

Wannan ita ce yarinyar da duniya ta ɗauka tana cikin wata irin rayuwa, amma a gabanta… sai ta ga yarinya mai cike da kamala.
Fuskarta ta nuna alamun rama cikin kwanaki kaɗan, idanunta sun kumbura saboda yawan kuka, ko murmushi ma kamar ya manta hanyar da zai zo fuskarta.

Suhaila ma ta kasa ɗauke idanunta daga kanta, a zuciyarta ta ce,
“Subhanallah… ba ta yi kama da yadda social media ta gina ta ba ko kaɗan. Sai dai ta yi kama da yarinyar da aka zalunta.”

Umma ta ɗan kalli Raihana, Raihana ta ɗaga kanta,
“Ki ƙarasa.”

Nan take Raihana ta ƙarasa gaba cikin ladabi, ta ɗan durƙusa,
“Assalamu Alaikum.”
Muryarta ta fito a hankali… kamar wacce ta gaji da magana.

Ummie ta amsa cikin taushi,
“Wa Alaikumus Salam, ’yata.”
Raihana ta sake sunkuyar da kanta,
“Ina yini.”
“Lafiya lau Alhamdulillah.”

Shiru ya ratsa falon na wasu daƙiƙu, Raihana kuwa tana durkushe cikin ladabi, idanunta a ƙasa, ba ta san dalilin zuwan matar ba, ba ta san me za ta faɗa mata ba.
Sai kawai ta ji… tace,
“Matso ki zo kusa da ni.”
Muryar Ummie ce.

Raihana ta ɗan ɗago kai a hankali, ta kalli Umma, Umma ta yi mata alamar ta matsa.
A nutse ta ƙarasa, da ta iso kusa… sai Ummie ta miƙa hannunta, ta kamo nata cikin wani irin taushi irin na uwa.

Hannun Raihana yana rawa, Ummie ta ja ta a hankali,
“Zauna nan.”
Ta nuna gefenta a kan daddumar.

Raihana ta zauna cikin kunya da girmamawa, sai Ummie ta ɗaga hannu… ta shafa kumatunta a hankali.
Idanunta suka cika da hawaye, ta girgiza kai cikin tausayawa,
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un...” ta furta a hankali,
“Kin rame sosai…” kalaman suka fito daga zuciyarta.

Raihana ta sunkuyar da kanta, ta ji maƙoshinta ya tokare.
Ummie ta ci gaba da kallonta, sannan cikin wata murya mai cike da tausayi ta ce,
“Ki kalle ni, ’yata.”

A hankali Raihana ta ɗago idanunta, da idanunsu suka haɗu… sai Ummie ta ga irin tsoron da ke cikinsu, irin ciwon da take ɓoyewa, irin zaluncin da mutane suka yi mata ba tare da sun saurare ta ba.

Ba tare da ta ƙara wata magana ba… sai Ummie ta buɗe hannayenta,
“Zo nan...”
Kafin ta ankara… Ummie ta jawo ta cikin jikinta, ta rungume ta tamkar ɗiyarta ta cikinta, ta shafa bayanta a hankali,
“Shhhh... ya isa haka...”

A wannan lokacin… ƙarfin da Raihana take ta ƙoƙarin nunawa ya rushe gaba ɗaya, ta fashe da kuka mai sauti, kuka irin wanda mutum ya daɗe yana dannewa a zuciyarsa, ta manne da Ummie tana kuka.

Ummie ta ƙara matse ta cikin jikinta, ta shafa kanta cikin taushi,
“Ki yi shiru, ’yata. Na sani... na san ba ki aikata komai ba.”
Raihana ta ɗago kanta cikin mamaki.

Ummie ta share mata hawaye da gefen mayafinta, ta ce cikin tabbaci,
“Ba ke suka nufa ba. Makiyan Zayd ne suka shirya wannan mugun abu. Sun kasa samun hanyar da za su rusa shi... shi ya sa suka yi amfani da ke. Kin zama marar laifi da aka jefa a gaba domin a ɓata masa suna.”

Ta kama hannayen Raihana da hannu biyu,
“Saboda haka... kada ki taɓa ɗaukar laifin da ba naki ba. Ba ke kika janyo wannan fitinar ba. Ke ma an zalunce ki kamar yadda aka zalunci Zayd.”

Falon gaba ɗaya ya yi tsit, Umma ta goge hawayenta, Suhaila kuwa idanunta sun cika da ƙwalla.
Ta fara fahimtar dalilin da ya sa Ummie ta nace sai ta zo da kanta ganin Raihana, wannan ba ziyar alfarma ba ce… ziyarar uwa ce ga wata yarinya da aka jefa cikin fitinar da ba ta aikata ba.

Ummie ta ci gaba da shafa bayanta cikin rarrashi, har sai da kukan Raihana ya fara raguwa.
Ta ɗan janye ta kaɗan daga jikinta, sannan ta ɗaga hannunta ta share sauran hawayen da suka rage a kumatunta, ta yi murmushi mai cike da tausayawa,
“Ya isa haka, ’yata.”
Ta dafa kumatunta a hankali,
“Ki daina bari maganganun mutane su karya miki zuciya. Wallahi... wannan ba ƙarshen rayuwarki ba ne.”

Raihana ta yi ƙasa da kanta, tana jin kalamanta suna sauka a zuciyarta kamar ruwa mai sanyaya wuta.
Ummie ta ci gaba cikin natsuwa,
“Ki sani... akwai bambanci tsakanin abin da mutane suke faɗa... da abin da Allah Ya sani. Allah Ya san ba ki aikata wannan abin ba. Mu kuma... mun yi bincike. Binciken da ya tabbatar mana da cewa ke ma an zalunce ki.”

Ta sake matse hannun Raihana,
“Ba ke suka nufa ba. Makiyan Zayd ne suka nemi hanyar da za su rusa sunansa.”
Ta girgiza kai cikin takaici,
“Da suka kasa samun wata hanya... sai suka yi amfani da ke. Sun jefa sunanki cikin abin da ba ki da alaƙa da shi.”

Raihana ta sake lumshe idanunta, hawaye suka taru amma wannan karon ba irin na rashin ƙarfi ba ne… hawaye ne na jin cewa akwai wanda ya gaskata ta.

Ummie ta ɗan yi murmushi,
“Saboda haka... daga yau ina so ki daina ɗora wa kanki laifin da ba naki ba.”
Ta shafa kanta,
“Kin ji ko?”
Raihana ta gyada kai a hankali.

“Good girl.”

Falon ya yi tsit na wasu daƙiƙu, sai Ummie ta juya ta kalli Umma cikin ladabi,
“Mama...”
Umma ta amsa cikin sanyin jiki,
“Na’am Hajiya.”
Ummie ta ɗan yi shiru kafin ta ce,
“Babanta yana nan ne? Zan so in gan shi idan zai yiwu.”

Umma ta yi murmushi cikin girmamawa,
“Yana nan ai Hajiya... sai dai yau ƙarshen mako ne.”
Ta ɗan yi shiru kaɗan,
“An gayyace shi ɗaurin aure ne a unguwa, shi ya sa ya fita tun da safe.”
Ta sake kallon agogon bango,
“Amma ba zai daɗe ba, in shaa Allah. Na san yanzu haka ma yana kan hanyarsa ta dawowa.”

Ummie ta gyada kai cikin fahimta,
“Alhamdulillah.”
Sai ta yi murmushi,
“To ba damuwa... za mu jira shi.”

Da wannan amsar… Umma ta ƙara mamaki a ranta, domin daga yadda take magana, da yadda take son ganin Baffa Musa da kanta… Umma ta fahimci akwai wani muhimmin abu da ke tafe.
Suhaila kuwa ta zuba wa Ummie ido cikin mamaki, tun lokacin da suka fito daga gida, Ummie ba ta bayyana mata manufar wannan ziyarar ba.
Yanzu kuma... da ta ji ta ce za su jira Baffa Musa... sai zuciyarta ta fara bugawa da sauri,
“Me yake shirin faruwa ne?” tambayar ta sake yawo a ranta, yayin da falon ya sake komawa cikin nutsuwa, kowa na jiran dawowar maigidan.

Umma ta ɗan kalli baƙin nata, sai kuma ta dafa goshinta a hankali,
“Ahaf...” ta faɗa cike da kunya,
“Hajiya, ki yi haƙuri wallahi. Har yanzu ban kawo miki ko ruwa ba. Gaskiya na ji kunya.”
Ummie ta yi murmushi mai cike da sauƙi,
“Kai Mama... ba komai.”
Ta girgiza kai a hankali,
“Ai har yanzu safiya ce. Kada ki damu.”

Amma Umma ta ƙi yarda,
“A’a wallahi. Bai kamata ba.”
Ta miƙe da sauri,
“Dan jira ni.”
Ba tare da ta bari Ummie ta sake cewa komai ba, ta fita daga falon cikin hanzari.

Suhaila ta kalli Ummie ta yi murmushi,
“Umma tana da kirki sosai.”
Ummie ta ɗan sake bin falon da kallo,
“Tsafta... tarbiyya... da girmama baƙo. Waɗannan abubuwa ba kuɗi ke siya ba.”

Ba a wuce mintuna biyar ba… sai Umma ta dawo, a hannunta wani farin plate ne mai tsafta, a kai kuwa… an jera pure water guda huɗu cikin tsari.
Ta iso gabansu, ta ɗan durƙusa cikin ladabi, ta ajiye plate ɗin a kan ƙaramin centre table da ke gabansu,
“Ga ruwa Hajiya. Allah Ya sa ba za ki ce ya yi zafi ba.”

Ummie ta yi murmushi mai daɗi,
“Toh, mun gode sosai Mama.”
Ta ɗauki ɗaya daga cikin ruwan, ta buɗe a hankali.

Har yanzu suna cikin hirarsu… suna dan magana jefi jefi, ba a fi mintuna biyar ba da dawowar Umma… sai aka ji sallama daga tsakar gida,
“Assalamu Alaikum wa Rahmatullah...”
Muryar Baffa Musa ce.

Nan take Mama Sabuwa ta ɗago kai, ta amsa daga tsakar gidan,
“Wa Alaikumus Salam wa Rahmatullah.”
Mama Indo ta yi murmushi,
“Ga shi nan ma ya dawo.”

Baffa Musa ya shigo cikin tsakar gidan yana cire hularsa a hankali, sanye yake cikin farar shadda mai sauƙin kyau, an ɗora mata light brown babban riga, takalmansa na fata suna nuna tsafta da tsari, a hannunsa yana riƙe da ƙaramar ledar alawa da aka ba shi daga ɗaurin auren.

Da shigowarsa… ya fara gaisawa da mutanen gidan, kafin ya shigo ya riga ya ga motar da ke tsaye a kofar gidan, sai ya ɗaga gira kaɗan,
“Baƙi ne?”
Mama Indo ta yi murmushi,
“Eh.”
Ta ƙarasa kusa da shi,
“Akwai wata Hajiya ce da ta zo tare da wata yarinya da wani matashi.”

Baffa ya gyara babban rigarsa,
“Toh.”
Sai ya tambaya cikin mamaki,
“Su waye?”
Mama Sabuwa tayi ƙaraf ta sauke murya kaɗan,
“Wallahi... mu ma bamu santa ba. Amma...”
Ta ɗan yi shiru,
“Da suka shigo... abu na farko da ta tambaya shi ne... ‘ina Raihana take?’”

Baffa Musa ya tsaya cak, fuskarsa ta nuna mamaki,
“Raihana...?”
“Eh.”
“Kuma yanzu tana jiranka a falon Hajara.”

Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ya ɗaga kai ya ce cikin natsuwa,
“To, bismillah.”
Ya gyara hularsa da babban rigarsa cikin mutunci, sannan ya nufi falon da zuciyarsa cike da tambayoyi.

A hankali… Baffa Musa ya tura labulen falon, ya shigo da sallama,
“Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.”
Ummie da sauran waɗanda ke falon suka amsa a tare,
“Wa Alaikumus Salam wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.”

Da ya shiga… sai ya ɗan tsaya na ɗan lokaci, ya zuba musu ido cikin ladabi kafin ya ƙarasa.
Umma ta yi saurin cewa,
“Hajiya... ga maigidan gidan.”
Ummie ta miƙe kaɗan daga inda take zaune cikin girmamawa,
“Ina yini?”
Baffa ya yi murmushi,
“Lafiya lau Alhamdulillah. Sannu da zuwa.”
“Yauw, nagode.”

Ya ɗan waigo cikin falon, sannan ya zauna a kan kujerar da Umma ta nuna masa, bayan ya daidaita zamansa… sai ya sake kallon Ummie cikin ladabi, fuskarsa a washe, ya ce,
“Barka da zuwa gidanmu.”

Ummie ta yi murmushi mai cike da kamala,
“Nagode ƙwarai.”
Sai ta ɗan gyara zamanta kafin ta ce,
“Da farko dai... bari na gabatar da kaina.”
Ta ɗan yi murmushi,
“Sunana Fateema Armaan.”
Ta ɗan dakata,
“Ni ce mahaifiyar... Zayd Armaan.”

Da kalmar ta fito daga bakinta… idanun Baffa Musa suka buɗe sosai cikin mamaki,
“Maa Shaa Allah...” ya furta a hankali,
“Allah Sarki...” ya girgiza kai cike da mamaki,
“Ashe... ke ce mahaifiyarsa?”
Ummie ta gyada kai cikin murmushi,
“Eh.”

Baffa ya sauke numfashi mai nauyi,
“Wallahi... da ba sai kin wahalar da kanki kika zo ba.”
Ya ɗora hannunsa a ƙirji,
“Mun riga mun fahimci cewa wannan duk... sharrin maƙiya ne.”
Ya girgiza kai cikin takaici,
“Wallahi ko sau ɗaya ban yarda da abin da ake yaɗawa ba.”
Raihana ta ɗaga idanunta ta kalli mahaifinta, zuciyarta tayi sanyi.

Ummie ta yi murmushi cikin natsuwa,
“Ai gara da na zo. Zuwana yana da muhimmanci.”
Ta ɗan kalli Raihana cikin tausayawa,
“A yi irin wannan babban al’amari... ace ni ban zo na ga yarinyar da aka zalunta da idona ba?”
Ta girgiza kai,
“A’a... zuciyata ba za ta bar ni ba.”

Baffa ya sauke numfashi,
“Allah Ya saka da alheri.”
“Ameen.”
Sai ya ɗan yi murmushi,
“Ni ma ai... a kamfanin Zayd nake aiki.”
Ummie ta ɗan yi mamaki,
“Da gaske?”
“Eh.”
Ya yi murmushi na girmamawa,
“Mutum ne na kirki. Mai mutunci. Mai tausayi. Wallahi ban taɓa ganin ya wulaƙanta ma’aikaci ba.”

Ummie ta yi murmushi, idanunta suka ɗan yi laushi,
“Alhamdulillah.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta juya ta kalli Suhaila da Raihana, ta yi musu murmushi,
“Suhaila...”
“Na’am Ummie.”
“Kin ga ɗakin Raihana ko?”
“Eh.”
Ta gyada kai,
“To... ku shiga ciki tare.”

Ta kalli Raihana cikin taushi,
“’Yata... ki raka Suhaila ɗakinki. Ku ɗan yi hira.”
Sai ta ƙara da murmushi mai nuni da cewa akwai abin da take son tattaunawa cikin sirri,
“Ni da Baffa... muna da wata muhimmiyar magana da za mu yi.”

Suhaila ta kalli Ummie na ɗan lokaci, ta fahimci daga yanayin muryarta cewa maganar tana da muhimmanci, ta miƙe tsaye,
“To Ummie.”
Raihana ma ta miƙe cikin ladabi, ta fara kallon Umma, sannan ta kalli Baffa, da ya yi mata alamar ta je… sai ta juya a hankali,
“Mu je.”
Suhaila ta bi bayanta zuwa ɗakin, yayin da falon ya sake yin shiru.

Ummie ta bi su da kallo har labulen ɗakin ya rufe, sannan ta maida hankalinta kan Baffa Musa, ta gyara zamanta a hankali, ta haɗe hannayenta saman cinyarta, kafin ta sauke wani numfashi mai nauyi,
“Alhaji Musa...”
“Naam Hajiya.”
“Maganar da zan yi yanzu... ba ƙarama ba ce. Kuma ba maganar da na zo da ita cikin gaggawa ba ce.”
Baffa ya gyara zamansa cikin nutsuwa,
“Ina sauraronki.”

Ummie ta yi ɗan shiru, kamar tana tsara kalmomin da za ta furta,
“Da farko... ina son na ba ka haƙuri. Na san abin da ya faru ya girgiza wannan gida. Ko da yake ba laifinmu ba ne, kuma ba laifin ku ba ne... amma sunan ɗana ya haɗu da sunan ’yarku a cikin fitinar da ba su da hannu a ciki.”

Umma ta yi saurin girgiza kai,
“Hajiya, don Allah kada ki ɗora wa ranki wannan. Mun san sarai sharrin wasu ne.”
Baffa ya amsa cikin natsuwa,
“Hakika. Tun daga ranar farko ban taɓa yarda cewa akwai wani abu tsakaninsu ba.”

Ummie ta yi murmushi mai cike da godiya,
“Allah Ya saka da alheri.”
Ta ɗan yi shiru,
“Wallahi... abin da ya sa na ƙara girmama ku ba wai saboda kun yarda da ɗana ba ne.”
Ta kalli Baffa kai tsaye,
“Abin da na gani a gidanku ne. Na ga tsafta. Na ga tarbiyya. Na ga mutunci. Na ga iyaye masu haƙuri. Na ga gidan da ake jin tsoron Allah.”
Ta yi murmushi,
“Wallahi irin wannan gida mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, kuɗi ba sa siya.”

Baffa ya sauke kansa cikin tawali’u,
“Alhamdulillah. Allah Ya sa mu dace.”
“Ameen.”

Sai Ummie ta ɗan gyara mayafinta,
“Alhaji Musa...”
“Na’am.”
“Ba don wannan abin da ya faru ba ne na zo.”
Sai Baffa ya ɗago kai,
“Abin da ya faru ne kawai... ya sa na samu damar sanin wacece Raihana.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Sannan... bayan na san ta...” ta ɗan yi murmushi,
“…na ga irin yarinyar da kowace uwa za ta yi farin cikin ta kira suruka.”

Falón ya yi tsit, Umma ta zaro ido cikin mamaki, Baffa kuwa bai ce komai ba, sai kallon Ummie yake yi.

Ummie ta ɗora da cewa cikin natsuwa,
“Na zo ne a matsayin uwa. Ba a matsayin Hajiya Fateema Armaan ba. Ba a matsayin mai kuɗi ba. Ba kuma a matsayin mahaifiyar Zayd Armaan ba. Na zo ne da zuciyar uwa...”
Ta ɗora hannunta a ƙirji,
“…ina neman alfarmar idan Allah Ya nufa... Raihana ta zama surukata.”

Shiru... wani irin shiru mai nauyi ya mamaye falon, har Umma ta kasa motsi.
Baffa ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, kamar yana nazarin maganar da ya ji, daga ƙarshe ya buɗe idanunsa, ya kalli Ummie da murmushi mai cike da girmamawa,
“Subhanallah... wallahi Hajiya... ban taɓa tsammanin irin wannan magana za ta fito daga gare ki ba.”
Ya sauke numfashi,
“Kin ba mu girma da mutunci fiye da yadda za mu iya bayyanawa.”

Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba,
“Amma... ina ganin ya dace na faɗa miki gaskiyar halin da ake ciki.”
Ummie ta gyada kai,
“Ina sauraronka.”

Baffa ya haɗe hannayensa,
“Akwai wani saurayi da ya zo. Ba wai mun ba shi Raihana ba ne. Ko kaɗan. Ba a ɗaura komai tsakaninmu da shi ba. Amma ya zo ta ƙofar da ta dace. Ya nemi izinina. Ya bayyana manufarsa.”
Ya ci gaba cikin natsuwa,
“Na gaya masa cewa ba zan taɓa yanke irin wannan hukunci cikin gaggawa ba. Na ce masa zan yi shawara da iyalina. Sannan mafi muhimmanci... zan ji ra’ayin Raihana. Domin aure amanar Allah ne. Ba zan taɓa tilasta wa ’yata wanda ba ta so ba.”

Ummie ta yi murmushi mai faɗi,
“Alhamdulillah.”
Ummie ta ci gaba,
“Wallahi wannan ya ƙara mini kwanciyar hankali. Kuma ya tabbatar mini cewa ban yi kuskure ba wajen ganin darajar ’yarku.”
Ta ɗan yi shiru,
“Sai dai ni ma... ba na neman amsa yau. Na zo ne kawai domin in buɗe ƙofa. Ku yi shawara. Ku yi istikhara. Ku ji ra’ayin Raihana. Ni kuma... zan koma na yi magana da Zayd.”
Ta yi murmushi cikin natsuwa,
“Idan Allah Ya rubuta alkhairi, babu wanda zai hana. Idan kuma Allah Ya rubuta wani abu dabam... zan karɓi ƙaddararsa da zuciya ɗaya.”

Baffa ya yi murmushi mai cike da gamsuwa,
“Wallahi Hajiya... yau ba kawai kin zo neman ’ya ba ne... kin nuna mana irin tarbiyyar gidan da kika fito.”
Umma ma ta gyada kai cikin nutsuwa, tana jin wani irin kwanciyar hankali ya sauka a zuciyarta, duk da cewa har yanzu mamakin yadda Allah Ya juya al’amura cikin ƴan kwanaki kaɗan bai gushe ba.

*A CIKIN ƊAKIN RAIHANA…*

Raihana ta buɗe labulen ƙofar a hankali, daidai lokacin Suhaila na tsaye a bakin ƙofar, hannunta a haɗe a gabanta, fuskarta ɗauke da murmushi mai cike da nutsuwa.

Da idanunsu suka haɗu… Suhaila ta yi murmushi,
“Assalamu Alaikum.”
Raihana ta amsa cikin ladabi,
“Wa Alaikumus Salam.”
Ta matsa gefe,
“Bismillah...”
Suhaila ta shiga ɗakin a hankali… idanunta suka fara yawo a cikin ɗakin.

Ba wani ɗaki ne na alfarma ba, ba designer furniture ba ne, ba kayan da suka yi tsada ba ne, amma… komai cikin tsari yake.
Gadon an shimfiɗa shi fes, labulen window fari ne masu tsafta, a saman dressing mirror babu hayaniya, sai turare kaɗan, cream, Al-Qur’ani da wasu littattafan karatu da aka jera cikin tsari.
A gefe kuma akwai study table ɗin Raihana, cike da medical textbooks, notebooks da laptop.

Suhaila ta yi murmushi,
“Masha Allah...”
Ta juyo ta kalli Raihana,
“Ɗakinki yana da kyau sosai.”
Raihana ta ɗan yi murmushi,
“Nagode.”
Ta nuna mata kujera,
“Zauna mana.”

Suhaila ta zauna cikin nutsuwa, Raihana kuma ta zauna gefen gadonta, na ɗan lokaci… shiru ne ya mamaye ɗakin.

Raihana ta sunkuyar da kanta, Suhaila kuwa tana kallonta ne cikin tausayi, ta lura yadda idanun Raihana suka kumbura, yadda fuskarta ta rame cikin kwanaki kaɗan.
A hankali ta ce,
“Kin sha kuka sosai ko…?”
Raihana ta yi murmushin ƙarfin hali, amma batace komai ba.

Suhaila ta ɗan matsa kusa da ita,
“Wallahi... tun ranar da abin ya faru... nake ta tausayinki.”
Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba,
“Na san irin yadda ake jin ciwo idan mutane suka yanke maka hukunci ba tare da sun san gaskiya ba.”
Raihana ta lumshe idanunta,
“Wannan kwanakin...” ta kasa ƙarasa maganar.

Suhaila ta kamo hannunta a hankali,
“Ki daina damuwa. Alhamdulillah ai yanzu gaskiya ta bayyana.”
Raihana ta yi murmushi mai ciwo, cikin sanyin muryarta tace,
“Eh... amma...” ta sauke numfashi,
“Ko da an bayyana gaskiya... mutane da yawa ba su yarda ba.”

Suhaila ta girgiza kai cikin takaici,
“Haka rayuwa take. Wasu ba neman gaskiya suke ba... suna neman abin da zai tabbatar musu da abin da suka riga suka gaskata.”
Raihana ta yi shiru.

Sai Suhaila ta yi murmushi kaɗan,
“Kin san wani abu…?”
Raihana ta girgiza kai.

Suhaila ta ce cikin sanyin murya,
“Akhi ma ya damu sosai da halin da kike ciki.”
Raihana ta ɗan dago ta kalli Suhaila amma batace komai ba.

Suhaila ta gyada kai,
“Eh.”
Sai ta ɗan yi dariya,
“Wallahi kwanakin nan ba ma ya cika zama a gida. Kullum yana wajen investigations. Da hada reports. Da kansa ya dage sai an gano waɗanda suka shirya wannan abin.”

Raihana ta yi shiru, zuciyarta na bugawa.
Suhaila ta ci gaba cikin murmushi,
“Akhi ya ce...” ta ɗan tsaya,
“…‘ba zan bari a lalata sunan yarinya mara laifi ba saboda wasu mutane.’”

Idanun Raihana suka cika da ƙwalla, sai saboda ta ji akwai wanda ya tsaya domin a bayyana gaskiya, ta sauke kanta ƙasa,
“Allah Ya saka masa da alkhairi.”
“Ameen,” Suhaila ta amsa cikin sauri.

Sai ta ƙara da murmushi,
“Ki sani... ba ke kaɗai kika shiga wannan jarabawar ba. Akhi ma an yi masa mugun rauni. Mutuncinsa. Sunansa. Kasuwancinsa. Komai aka so a rusa.”
Ta girgiza kai,
“Amma Alhamdulillah... Allah Ya bayyana gaskiya.”
Raihana ta gyada kai a hankali,
“Allah ba Ya barin gaskiya ta ɓuya.”
“Wannan haka ne,” Suhaila ta amsa tana murmushi.

Sai ta ɗan kalli ƙofar ɗakin,
“Amma kin san me ya fi ba ni mamaki?”
Raihana ta girgiza kai, haryanzu tana kallonta.

Suhaila ta yi murmushi mai cike da jindadi,
“Ummie. Ta taso da kanta ta zo nan. Wallahi... ba kasafai take yin haka ba. Idan Ummie ta ɗauki lokaci ta zo gidan wani da kanta...”
Ta ɗan yi shiru,
“…to ki sani wannan mutumin yana da wani matsayi na musamman a zuciyarta.”

Raihana ta yi shiru, kalaman Suhaila suka sa zuciyarta ta cika da tambayoyi,
“Me ya sa Ummien Zayd ta zo gidanmu? Me take so?”





Not edited