ZAYD ARMAAN

WHEN FATE TAKES THE LEAD

by @jiddaahbarkum



*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER-TWENTY FOUR:24*

*WHEN FATE TAKES THE LEAD*

*JIDDAAH BARKUM*
——————————

Ummie ta fito daga ɗakin Zayd a hankali, da ta rufe ƙofar bayanta, hannunta ya zauna a kan handle ɗin na wasu daƙiƙu.
Ta kasa matsawa nan take, idanunta suka lumshe, sai ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya wadda ta fito daga zurfin zuciyarta.

Fuskarta kuwa… ta cika da wani irin farin ciki mai nutsuwa, ta ɗaga hannayenta biyu zuwa kirjinta, ta furta a hankali,
“Alhamdulillah…”
Hawaye kaɗan suka cika idanunta, ta ɗaga fuskarta sama, muryarta ta yi rauni saboda tsananin farin ciki,
“Ya Allah… idan wannan shi ne alkhairin ɗana, Ka sauƙaƙa masa.”
Ta ɗan yi shiru,
“Ka sanya masa albarka a cikin wannan shawarar, Ka haɗa shi da matar da za ta zama nutsuwarsa, farin cikinsa da mafakarsa.”

Sai ta share gefen idonta da yatsa,
“Ya Allah, kada Ka bar shi ya yi nadama, kada Ka bar zuciyarsa ta taɓa jin cewa ya yi wani zaɓi ba daidai ba.”
Ta sake yin murmushi,
“Ka sanya alkhairi a tsakanin Zayd da Raihana… idan wannan shi ne abin da Ka rubuta musu.”

Ta sauke hannayenta a hankali, sai ta kalli ƙofar ɗakin Zayd da murmushi mai cike da tsantsar farinciki,
“Alhamdulillah...” ta sake furtawa.

A zuciyarta kuwa… ta ji kamar an ɗauke wani babban nauyi daga kanta, shekara nawa tana addu’a Allah Ya nuna mata ranar da Zayd zai yarda ya yi aure, kullum ta kawo maganar sai ya zille, har ta hakura, ta zuba masa ido kawai.
Amma yau ya amince ba tare da jayayya ba, Zayd baya jayayya da ita akan komai sai akan maganar aure, yau kam ba wani dogon zance, ya amince.

D’anta  ta san ba ya saurin yanke hukunci… a yau ya ce mata:
“Na amince, Ummie.”

Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci,
“Allah Ya sa na yi maka abin da ya fi dacewa, Habibi...”
Sai ta juya a hankali, ta fara tafiya down the corridor.

Amma wannan karon… takunta ba su da nauyin da suka kasance da shi lokacin da ta hau wannan corridor ɗin, fuskarta cike take da farin ciki, kamar mace da ta samu labarin da ta daɗe tana jira.
Kuma a cikin zuciyarta… ta riga ta fara ganin wani sabon babi yana buɗewa a rayuwar ɗanta.

————

*MALALI*

Bayan sallar La’asar… Raihana na zaune a kan sallayar da ta gama sallah, bayanta a jingine da jikin mirror ɗin ɗakinta, idanunta a lumshe suke.
Amma zuciyarta… ta yi nisa sosai cikin tunani.

Tun daga zuwan su Ummie… maganganun da aka yi a gidan… da yadda Baffa ya yi shiru yana sauraron komai… sai yadda Ummie ta zauna da ita cikin wannan irin nutsuwar da har yanzu take ji a zuciyarta.

Raihana ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe idanunta a hankali, amma kallonta bai tsaya kan komai ba, a zuciyarta ne kawai take sake maimaita abubuwan da suka faru.
Me ya sa duk wannan lamarin yake kama da wani abu da ya fi ƙarfin fahimtarta?
Ta girgiza kai a hankali.

Sai ba zato ba tsammani… tunaninta ya koma ga wani abu daban, Zayd.
Ta yi ƙoƙarin tuna fuskarsa daga ranar da suka fara haɗuwa, wannan irin kallon da ya yi mata ta window din motarsa kafin convoy ɗin ya wuce…
Ta ɗan lumshe idanunta, ba ta san dalilin da ya sa wannan ƙaramin memory ɗin ya dawo mata a wannan lokacin ba, amma ta tuna sosai.

Wancan fuskar mai nutsuwa, idanuwan nan masu haske, da yadda ya kalle ta ba tare da ya ce komai ba,
“Zayd...” sunan ya fito daga bakinta a hankali, sai ta girgiza kai.

The convoy guy, shi ne kawai abin da ta sani game da shi, mutumin da ta samu sabani da shi a ranar saboda yaron nan.
Mutumin da bai yi mata gardama ba, bai yi mata ihu ba, bai kuma fito ya tambaye ta komai ba, sai dai ya kalle ta… sannan ya bar convoy ɗinsa ya wuce ta.

Ta sauke kanta a hankali, sai tunaninta ya koma ga Haris.
Haris… mutumin kirki ne, ba wai tana cewa tana tsananin son sa ba, a’a, amma akwai wasu halaye nasa da suke burge ta.
Baya hayaniya, baya takura mutum, komai nasa yana gudanar da shi cikin nutsuwa, kuma akwai wata irin kwanciyar hankali da take ji idan tana magana da shi.

Raihana ta ɗan yi murmushi, sai a hankali wayarta da ke gefenta ta katse mata tunanin.
Ta ɗan juyar da kanta, kallonta ya sauka kan wayar, Haris.

Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta miƙa hannu ta ɗauka, ta ɗaga wayar a kunnenta,
“Assalamu Alaikum...”
Daga can ya amsa da wannan nutsuwarsa,
“Wa’alaikumussalam Warahmatullahi...”
A hankali ta ce,
“Ina yini?”
“Lafiya lau. Ya kike? Ya kika yini?”
“Alhamdulillah.”

Sai ta ɗan yi shiru kafin ta tambaya,
“Ya aiki?”
Sai ta ji murmushinsa a ɗaya gefen wayar,
“Aiki Alhamdulillah...” ya ɗan dakata,
“Amma tunaninki ya hanani yin wani abu na arziki.”
Raihana ta yi shiru, idanunta suka sauka ƙasa.

Haris ya fahimci shirun nata,
“Kinyi shiru ko?”
Ta ɗan yi murmushi, amma ba ta ce komai ba, sai ya yi ƙaramar dariya,
“Na san ba za ki ce komai ba.”
Sai ya canja maganar cikin nutsuwa,
“Kin ci abinci?”
Raihana ta ɗan jinjina kai,
“Eh.”
“Me kika ci?”
Ta ɗan yi murmushi,
“Rice.”
“Hmm...” ya yi shiru kaɗan,
“Toh kin ci da yawa ko?”
Ta ɗan ɗaga gira,
“Me ya sa?”
“Saboda kwana biyu nan kin rame.”
Muryarsa ta ƙara laushi,
“Ina so ki dawo yadda kike kafin aurenmu.”

Kalmar aurenmu ta sauka a zuciyarta, Raihana ta yi shiru, sai wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta, ba ta ce komai ba.
Haris ya san ba za ta ce komai ba, don haka bai matsa mata ba, sai ya tambaya,
“Yau kina da wasu schedules ne?”
Ta girgiza kai,
“A’a.”
Ya sauke ajiyar zuciya,
“Toh... ina neman izini.”
“Wane izini?”
“Anjima da Magrib zan zo...” ya ɗan dakata,
“Naga gimbiyata.”

Raihana ta lumshe idanunta,
“Zuciyata ta kasa samun sukuni, kwana biyu idanuna ba su ga kyakkyawar fuskarki ba.”
Ta yi murmushi mai kyau, a hankali ta amsa,
“Toh... Allah Ya kaimu. Allah Ya kawo ka lafiya.”
“Ameen, Rayhaan... nagode.”
Sai ya yi ɗan dariya,
“Sai anjima ko?”
“Hmm.”
“Kar na dame ki da surutu.”
Raihana ta yi murmushi,
“A’a... ba za ka dameni ba.”
Haris ya yi murmushi a ɗaya gefen wayar,
“Toh shikenan... sai anjima.”
“Toh. Allah Ya kaimu.”
“Ameen.”
Wayar ta katse.

Raihana ta dauke wayar daga kunnenta a hankali, ta kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu, sai ta sauke ajiyar zuciya.
Haris yana ƙaunar ta, haka take ji, amma ita… har yanzu ba ta san irin matsayin da yake cikin zuciyarta ba.

Ta ɗora wayar gefenta, kamar ba da gangan ba… fuskar Zayd ta sake faɗowa cikin tunaninta, wancan kallon, wancan ranar, wancan incident ɗin.
Ta ɗan dafe goshinta,
“Me ya sa nake tunawa da wannan mutumin haka?”
Sai ta girgiza kai da sauri,
“Ai ban ma san shi ba.”
Ta ɗauki dogon numfashi, amma duk da ta faɗi haka… memory ɗin kallon Zayd bai bar zuciyarta ba.

Maryam ta turo ƙofar ɗakin a hankali ta shigo, fuskarta ɗauke da wani irin excitement da ya sa tun kafin ta yi magana Raihana ta ɗago kai ta kalle ta,
“Ray...”
Raihana ta ɗan ɗaga gira.
Maryam ta ƙarasa cikin ɗakin, ta zauna kusa da ita ba tare da ɓata lokaci ba,
“Su waye suka zo?”
Raihana ta buɗe baki za ta amsa, amma kafin ta samu damar cewa komai, Maryam ta sake cewa cikin doki,
“Ray, kin gane yarinyar nan da suka zo da mamanta?”
Raihana ta ɗan karkatar da kai,
“A’a...”
Maryam ta zaro ido kamar wanda aka faɗa wa wani abu mai ban mamaki,
“Itace fa!”
Raihana ta kalle ta,
“Wacece?”
Maryam ta matsa kusa da ita, muryarta cike da farin ciki,
“Itace fa wacce ta baki gate pass a bikin Asieeya!”
Raihana ta ɗan buɗe ido,
“Really?”
Maryam ta gyada kai da sauri,
“Wallahi! Itace!”

Raihana ta ɗan yi shiru, tana ƙoƙarin haɗa fuskar yarinyar da memory ɗin bikin,
“Ni ma da ƙyar na gane ta... amma wallahi itace.”
Ta ɗan yi murmushi, sai Maryam ta kasa ɓoye farin cikinta,
“Wai me suka ce da suka zo?”
Nan take murmushin da ke fuskar Raihana ya ɗan gushe, ta sauke kanta ƙasa.

Maryam ta lura da sauyin fuskarta,
“Ray?”
Raihana ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta fara gaya mata komai, ta gaya mata yadda Ummie ta zauna da ita, yadda ta yi mata magana cikin tausayi, yadda ta ce ta san ba ta da laifi, yadda ta gaya mata cewa bai kamata duniya ta ci gaba da hukunta ta saboda abin da ba ta aikata ba, har zuwa lokacin da ta ambaci maganar da ta zo da ita a yau...

Maryam ta yi shiru tana saurare, da Raihana ta gama… Maryam ta zaro ido,
“Dan Allah, da gaske?!”
Raihana kawai ta ɗaga idanunta ta kalle ta.
Maryam kuwa ta yi wata irin ƙara da ƙarfi,
“Aaaaaah!”
Raihana ta firgita kaɗan,
“Maryam!”
Amma kafin ta sake cewa komai, Maryam ta fashe da dariya, ta dafe kirjinta,
“Kaiii! Wallahi na yi farin ciki! Oh my God!”
Raihana ta girgiza kai tana kallonta,
“Me ya sa kike farin ciki haka?”
Maryam ta kasa zama lafiya, ta miƙe, ta sake zama, sannan ta kamo hannun Raihana,
“Ray, kin san me wannan yake nufi kuwa?”
Raihana ta ɗan daure fuska,
“Me?”
Maryam ta kalleta da wani irin murmushi mai cike da ma’ana,
“Allah Ya kawo miki mafita daga inda ba ki zata ba.”
Raihana ta sauke idanunta,
“Maryam...”
“Ki bari na gama!”
Maryam ta yi dariya,
“Dan Allah ki sallami Haris ɗin nan!”
Raihana ta ɗago kai da sauri,
“Maryam!”
“Me?”
“Ki daina mana.”
Maryam ta yi dariya sosai,
“Wallahi ina magana ne da gaske! Ki sallami Haris.”

Raihana ta yi shiru, Maryam ta ci gaba, wannan karon cikin wani irin excitement:
“Ray, ba wai saboda kuɗinsa nake cewa haka ba, a’a, ki duba situation ɗin gaba ɗaya.”
Ta fara ƙirga da yatsunta,
“Babban mutum ne, family ɗinsa suna da mutunci, yana da matsayi, kuma ga shi yanzu... mutane irin su waɗannan suna shigowa gidanku da kansu.”
Ke kalleni, ko a musulunchi ana aure sabida nasaba.

Ta ɗan matsa kusa da Raihana,
“Kin san me zai fi bani daɗi?”
Raihana ta kalleta,
“Me?”
Maryam ta yi murmushi mai cike da shauƙi,
“Makiya da ’yan media nan su mutu!”
Raihana ta buɗe baki cikin mamaki,
“Maryam!”
“Wallahi!” ta fashe da dariya,
“Ki imagine kawai... bayan duk abin da aka yi miki, sai labari ya fito cewa Raihana ta yi aure...” ta ɗaga hannunta sama kamar mai bada sanarwar breaking news,
“…kuma ba wai kawai ta yi aure ba, ta auri babban mutum daga gidan da kowa ya sani!”
Ta dafe bakinta tana dariya,
“Wallahi social media za ta ƙone!”

Raihana ta kasa daurewa, ta ɗan yi murmushi, amma nan da nan murmushin ya dusashe,
“Maryam...”
“Na’am?”
Raihana ta sauke kanta,
“Ba haka nake kallon abin ba.”
Maryam ta yi shiru.
Raihana ta ɗaga idanunta a hankali,
“Ni ma ban san Zayd ba. Shi ma bai san ni ba.”
Maryam ta kalle ta,
“Amma kin san abin da Ummie ta gani a jikinki.”
Raihana ta yi shiru.
Maryam ta kamo hannunta,
“Ba ta zo da maganar aure saboda ta ji tausayinki kawai ba, Ray. Daga abinda kika faɗamin yanzu na fahimta.”
Ta yi murmushi a hankali,
“Ta zo ne saboda a ɗan zuwan da tayi... ta gane ke wacece.”

Raihana ta sauke idanunta kan hannayensu, amma cikin zuciyarta… wani suna ya sake bayyana a hankali, Zayd.
Mutumin da ba ta san shi ba, mutumin da ita da shi ba su taɓa samun wata magana ta gaskiya ba, mutumin da haduwarsu ta farko ta kasance cike da fushi, hayaniya da rashin fahimta.
Kuma yanzu… sunansa ya fara shiga cikin rayuwarta ta wata hanyar da ba taɓa tsammani ba.

*BAYAN SALLAR MAGRIB…*

Falon gidan Alhaji Munzali ya yi shiru mai nutsuwa, duhun Magrib ya riga ya ɗan yi nisa, yayin da kamshin turaren da aka kunna a falon ya cika wajen da wani irin natsuwa.
Ummie tana zaune a kan kujera mai laushi, hannayenta haɗe a kan cinyarta, a gefenta kuwa… Alhaji Munzali.

Ƙanin marigayi mahaifin Zayd, mutum ne mai shekaru, nutsuwa da hangen nesa, ba ya yawan magana, amma idan ya yi magana… kalmarsa tana zuwa ne bayan ya auna komai a zuciyarsa.

Ummie ta gama ba shi labarin komai.. ziyararta gidan Raihana, abin da ta gani a yarinyar, da kuma dalilin da ya sa zuciyarta ta fara ganin cewa wataƙila Raihana ce za ta iya zama matar Zayd.

Alhaji Munzali ya yi shiru, bai ce komai ba, ya jingina bayansa da kujera, ya haɗa yatsunsa biyu a gabansa, yana tunani.
Ummie ma ba ta matsa masa ba, ta san halinsa, idan ya yi shiru haka… yana tunani ne.

Bayan wasu daƙiƙu masu tsawo, ya ɗaga kansa ya kalli Ummie,
“Hajja Fateema...”
“Na’am.”
“Kin tabbatar wannan shi ne mafita? Kin ga yarinyar, kin zauna da ita, kin san halinta. Amma... Zayd fa?”
Ya ɗan dakata,
“Kin san halinsa fiye da kowa, ba mutum ne da za a tura masa mace kawai ya karɓa ba.”

Ummie ta yi murmushi kaɗan,
“Na sani.”
“Shin ya nuna wani abu da ya sa kika ga yana da sha’awar wannan lamarin?”
Ummie ta girgiza kai a hankali,
“A’a.”
Alhaji Munzali ya ɗaga gira,
“Toh?”
Ummie ta sauke numfashi,
“Shi ya sa ban ce masa ya aure ta ba. Abin da na ce masa shi ne... ya yi tunani, ya yi istikhara, ya san ta. Idan zuciyarsa ta amince, sai ya zo da maganar.”
Ta ɗan yi shiru,
“Ba na son Zayd ya auri Raihana saboda ni, ina son ya aure ta ne idan shi da kansa ya ga cewa akwai alkhairi a ciki.”
Sai tayi murmushi kuma ya tabbatar min ya amince.

Alhaji Munzali ya gyada kai a hankali, Ummie ta ci gaba,
“Amma ka san abin da na gani?”
“Me?”
Muryarta ta yi sanyi,
“Na zauna da ita, na ga yadda take magana, na ga yadda take kallon iyayenta, na ga yadda take ƙoƙarin ɓoye ciwon da ke zuciyarta.”
Ta sauke idanunta,
“Wallahi... zuciyata ta kwanta a kanta.”

Alhaji Munzali ya yi shiru, Ummie ta ɗaga idanunta ta kalle shi,
“Shi ya sa nake son kai ma ka shiga lamarin. Ka je ka yi magana da mahaifinta, a matsayinka na baban Zayd.”
Ta yi murmushi kaɗan,
“Ka nemi izinin fara zuwa neman yarinyar, ba wai aure kai tsaye ba.”
Alhaji Munzali ya ɗan gyara zamansa,
“Wato mu fara neman su fahimci juna?”
“Exactly.”
Ummie ta yi saurin amsawa,
“Su san juna, su yi magana, iyaye su san abin da ake ciki. Idan suka ga akwai fahimta tsakanin su, idan Allah Ya nufa da aure a tsakaninsu... sai ayi.”
Ta ɗan yi shiru,
“Ba na son mu yi komai da gaggawa.”

Alhaji Munzali ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya danyi murmushi, daga ƙarshe ya gyada kai,
“Toh. Wannan magana ce mai kyau.”
Ummie ta ɗago idanunta,
“In Sha Allah. Zan je, zan yi magana da mahaifinta, zan nemi izinin fara zuwa neman yarinyar, sannan mu ga yadda lamarin zai kasance.”
Ummie ta sauke ajiyar zuciya,
“Allah Ya saka maka da alkhairi.”
“Ameen.”

Amma sai Ummie ta yi shiru, murmushin da ke fuskarta ya ɗan gushe, Alhaji Munzali ya lura,
“Me ya faru?”
Ummie ta sauke idanunta,
“Akwai abu ɗaya da yake sa jikina ya yi sanyi.”
“Menene?”
Ta ɗan yi jinkiri kafin ta ce,
“Seeyama.”
Alhaji Munzali bai yi mamaki ba, ya dai ci gaba da kallonta.

Ummie ta ɗora,
“Ka san Hauwa. Na san abin da take so, kuma na san yadda take kallon maganar Zayd da Seeyama.”
Ta sauke numfashi,
“Idan ta ji cewa yanzu ni ce na fara kawo wa Zayd maganar aure... za ta iya ɗauka cewa na yi ne saboda bana son Zayd ya auri Seeyama.”
Alhaji Munzali ya ɗan yi murmushi,
“Kin damu da abin da Hauwa za ta ce?”
“Ba maganarta ce kawai nake tsoro ba.”
Ummie ta kalle shi,
“Ban son ta fahimci ni ba daidai ba.”
Ta ɗan yi shiru,
“Saboda gaskiya... ba wai na hana Zayd Seeyama ba ne.”
Alhaji Munzali ya gyada kai,
“Na sani.”

Alhaji Munzali ya ƙarasa mata magana,
“Seeyama ba za ta zama matsala ba.”
Ummie ta kalle shi, sai ta ɗan yi murmushi,
“Ina ganin idan an yi wannan auren... daga baya sai ya auri Seeyaman.”
Alhaji Munzali ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sai ya girgiza kai a hankali,
“Hajja Fateema...”
“Na’am?”
“Ki daina tunanin komai kamar yadda mutane suke shirya shi.”
Ta kalle shi cikin tambaya.

Ya ci gaba,
“Mu mutane muna ganin abubuwa daga inda muke tsaye, amma Allah Shi ne Ya riga Ya tsara inda kowanne abu zai tsaya.”
Ummie ta yi shiru.
“Maganar Raihana da Zayd...” ya ɗan dakata,
“Ba ke kika kirkire ta ba.”
Ummie ta ɗaga idanunta,
“Allah ne Ya haɗa hanyoyinsu.”
Ya yi murmushi kaɗan,
“Kin tuna haduwarsu ta farko?”
Ummie ta gyada kai,
“Na sani.”
“Ba su shirya haduwa ba.”
“Eh.”
“Ba su san juna ba, event ne kawai ya hadasu, aka juya abun ya zama wani abu daban.”

Ya ɗaga hannunsa kaɗan,
“Har aka kai ga fitina, har aka bayyana gaskiya, har aka kai ga ke kika je gidan yarinyar.”
Ya kalli Ummie kai tsaye,
“Duk waɗannan abubuwan... ba wai ke kika shirya su ba.”
Ummie ta yi shiru,
“Mu kira shi abin da Allah Ya kaddara.”
Ya sauke numfashi,
“Idan Allah Ya rubuta Raihana ta zama matar Zayd, Hauwa ba zata hana ba.”
Ya ɗan yi murmushi,
“Idan kuma Allah bai rubuta ba, ko mu duka muka haɗa kai, ba za mu iya tilasta shi ba.”

Ummie ta yi murmushi a hankali,
“Gaskiya ne.”
“Saboda haka...” Alhaji Munzali ya jingina bayansa,
“Ki bar komai ga Allah.”
Ummie ta gyada kai,
“Shi ya sa nake son ka fara maganar.”
“Zan fara.”
“Ba aure kai tsaye ba.”
“Na sani.”
“Su fara fahimtar juna.”
“In Sha Allah.”

Ummie ta sauke ajiyar zuciya, wannan karon da ɗan kwanciyar hankali,
“Allah Ya sa alkhairi.”
Alhaji Munzali ya amsa,
“Ameen.”
Sai ya ɗan yi murmushi,
“Amma ki shirya.”
Ummie ta ɗaga gira,
“Me ya sa?”
“Saboda idan Hauwa ta ji labarin...” ya yi dariya kaɗan,
“Na san za ta zo da tambayoyi.”
Ummie ta yi murmushi,
“Ta zo.”
Ta ɗan gyara mayafinta,
“Ni kuma zan tsaya da gaskiyata.”
Alhaji Munzali ya gyada kai,
“Shi ne ya fi.”

Sai falon ya sake yin shiru, amma wannan karon… ba shiru ne na damuwa ba, shiru ne na mutane biyu da suka bar wani babban al’amari a hannun wanda Ya fi su sanin makomarsa, Allah.






Not edited