ZAYD ARMAAN

BEHIND CLOSED DOORS

by @jiddaahbarkum





*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER TWENTY-FIVE:25*

*BEHIND CLOSED DOORS*

*JIDDAAH BARKUM*

——————————

Office ɗin yayi shiru, Zayd yana zaune a kujerarsa, idanunsa a kan laptop ɗin gabansa, yana duba wasu files da aka aiko masa tun safe.
Fuskarsa a nutsu take, babu wani abu a tattare da shi da zai nuna irin abubuwan da suka faru a kwanakin baya.
Sai dai… a cikin zuciyarsa akwai wasu abubuwa da yake tunani a kai.

Ƙofar office ɗin ta buɗe a hankali, Sameer ya shigo da wasu files a hannunsa,
“Boss...”
Zayd bai ɗago kai nan take ba,
“Hmm?”
Sameer ya ƙarasa ya ajiye files ɗin a gabansa,
“Wannan shi ne updated report ɗin project ɗin da muka yi magana a kai jiya.”

Zayd ya ɗago idanunsa ya kalli file ɗin,
“Everything?”
“Yes, Boss.”
Zayd ya buɗe shi, ya fara kalla a hankali, yana juya pages ɗin ɗaya bayan ɗaya,
“Client ɗin sun amince da wannan figure din?”
Sameer ya gyada kai,
“Yes, Boss, sun amince, sai dai sun nemi mu ƙara wani clause kafin su yi sign.”
“Which clause?”
Sameer ya ɗan sunkuya ya nuna masa wani wuri a cikin document ɗin,
“This one, Boss.”

Zayd ya karanta, ya yi shiru na ƴan daƙiƙu,
“Remove it.”
Sameer ya ɗago kai,
“Boss?”
“Remove it, ba zai yi mana anfani ba.”
“Okay, Boss.”
“Then send it back to them, I want their final response before tomorrow morning.”
“Yes, Boss.”

Sameer ya ɗauki file ɗin,
“Anything else, Boss?”
Zayd ya girgiza kai,
“No.”
Sameer ya juya zai fita, amma kafin ya kai ƙofar… muryar Zayd ta dakatar da shi,
“Sameer.”
Sameer ya tsaya, ya juya ya kalle shi,
“Yes, Boss?”

Zayd ya jingina bayansa a kujerarsa, idanunsa suna kan Sameer, sai ya tambaya cikin sanyin murya,
“You took them there?”
Sameer ya tsaya cak, kamar bai fahimci tambayar ba,
“Where, Boss?”
Zayd ya kalle shi na ƴan daƙiƙu, Sameer ya fara jin wani irin pressure, ya san abin da Zayd yake tambaya, amma bai san ko Ummie ta sanar da shi ba.

Zayd ya ɗan karkatar da kansa, ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe su a kan fuskar Sameer, a hankali ya ce,
“Gidansu yarinyar can.”
Sameer ya yi shiru, ya sauke idanunsa ƙasa, sai ya yi ƙoƙarin haɗa kalmomin da zai faɗa.

Zayd ya ci gaba da kallonsa, Sameer ya haɗiye yawu, sai ya ce a hankali,
“Sorry, Boss.”
Zayd bai ce komai ba.
Sameer ya ci gaba da sauri,
“Ummie ce ta ce kada a sanar maka.”

Zayd ya ɗauke idanunsa daga kansa ya maida su kan desk ɗinsa, sai kuma ya ɗaga kansa ya kalli Sameer,
“You can go.”
Sameer ya gyada kai,
“Yes, Boss.”
Ya juya ya fita a hankali, ƙofar ta rufe, sai office ɗin ya koma shiru.

Zayd ya zauna bai motsa ba na wasu daƙiƙu, ya kalli ƙofar da Sameer ya fita, sai ya sauke idanunsa.
A hankali ya ɗauki wayarsa daga saman desk ɗin, ya buɗe screen ɗin, ya danna wani number.
Wayar ta yi ringing sau biyu… sai aka ɗaga.
Zayd bai fara magana da sauri ba, ya ɗan jingina bayansa,
“How was everything?”
Daga can aka amsa masa, ya yi shiru yana saurare,
“Everything went okay?”
Sai ya ɗan lumshe idanunsa,
“Good.”
Ya ɗan yi shiru,
“Keep trying.”
Muryarsa ta yi ƙasa,
“Don’t stop.”
Ya sake saurare, sai ya ce,
“Okay.”
Ya kashe wayar, ya ɗora ta a kan desk ɗin.

Na wasu daƙiƙu… kawai ya zauna yana kallon screen ɗin laptop ɗinsa ba tare da yana ganin abin da ke ciki ba, sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya.
Ya jingina bayansa sosai da kujerar, kansa ya ɗan koma baya, idanunsa suka lumshe.

——————-

Hajiya Hauwa ta dubi Seeyama da ta ga yadda idanunta su ka yi ja saboda kuka, ta matso kusa da ita, ta zauna a gefenta, sannan ta ɗora hannunta a kafadarta,
“Stop worrying yourself, daughter.”
Seeyama ta ɗaga idanunta ta kalleta, amma ba ta ce komai ba.

Mommy Hauwa ta ci gaba cikin murya mai sanyaya zuciya,
“Indai kinga baki auri Zayd ba, toh ba ni ce uwarki ba kamar baki san ni ba. Ki kwantar da hankalinki, aure fa… dole ne sai an yi.”
Seeyama ta ɗago kanta gaba ɗaya, ta kalli Mommy ɗinta na wasu daƙiƙu, kamar tana ƙoƙarin fahimtar kalamanta, sai ta yi murmushi mai ɗaci,
“Mommy...”
“Hmm?”
“Ai kullum dai haka kike cewa.”
Muryarta ta fara rawa,
“Shekaru nawa kenan kina faɗa min haka? ‘Ki kwantar da hankalinki... zan yi... Zayd zai aure ki...’”
Ta share hawayen da suka zubo mata,
“Amma har yanzu baki yi komai ba.”

Mommy ta yi shiru, Seeyama ta girgiza kai,
“Ni, Mommy, na gaji da wannan maganganun naki kawai, ki kyale ni da abin da yake damuna.”
“Sweetheart...”
“A’a, Mommy.”
Seeyama ta juya fuskarta gefe,
“Don Allah ki bar ni.”

Nan da nan sai Mommy ta rikice, nan take ta sake rungume ta, ta matse ta a jikinta,
“Haba, sweetheart... kar ki ce haka mana.”
Ta shafa bayanta a hankali,
“Ba ki ganin duk ƙoƙarin da nake yi?”
Seeyama ta yi shiru.

Mommy Hauwa ta ɗan janye jikinta, ta kalli fuskarta, sannan ta yi wani ƙaramin murmushi mai cike da tabbaci,
“I promise you...” ta riƙe hannunta sosai,
“Ko da zan rasa komai, sai kin auri Zayd.”
Seeyama ta kalleta,
“Just calm down, okay?”
Seeyama ta sauke ajiyar zuciya, sai ta sake janye jikinta daga gare ta,
“Toh, na ji.”
Ta share fuskarta,
“Ni dai ki tafi kawai, I need some space, ina son in huta.”

Mommy ta ɗan tsaya tana kallonta, ta san zuciyar yarinyar ta yi nauyi, a hankali ta miƙe,
“Okay, my darling. Zan tafi, amma ki daina kuka, kin ji?”
Seeyama ba ta amsa ba.
Mommy ta kalle ta na ɗan lokaci, sannan ta ce a hankali,
“Please... ki kwantar da hankalinki.”
Seeyama ta ɗan jinjina kai,
“Na ji.”
Mommy ta yi murmushi kaɗan, sai ta nufi ƙofa.

Amma da ta kai bakin ƙofar… murmushin da ke fuskarta ya gushe, ta tsaya na ɗan lokaci, hannunta a kan handle ɗin ƙofar.
A zuciyarta kuwa… tambaya guda ɗaya ce take yawo, ta yaya za ta samo wa ɗiyarta mafita?
Domin wannan karon… ta fara jin cewa maganar Zayd ba za ta kasance da sauƙi kamar yadda ta yi tsammani ba.

——————

*MALALI BAYAN SALLAR MAGRIB…*

Kamar yadda ya ce zai zo, Haris ya zo.
Bayan ya shigo, suka zauna a varanda wajen dakin yaya Hamza cikin nutsuwa, ba wani hayaniya, ba kuma wani yawan magana, sai iskar da ke ratsa wajen ta bayan sallar Magrib.

Raihana ta kawo masa ruwa a cikin glass, ta miƙa masa a nutse,
“Ga shi.”
Ya karɓa,
“Thank you.”
Ya ɗan sha kaɗan, sannan ya ajiye glass ɗin a hankali a gabansa.

Na ɗan lokaci ya yi shiru, Raihana kuwa tana zaune cikin natsuwa, idanunta a ƙasa.
Sai Haris ya ɗago kansa ya kalle ta,
“Rayhaan...”
Muryarsa ta fito a hankali.
Raihana ta ɗago idanunta, idanunsu suka haɗu, sai kamar yadda ta saba, ta sauke nata idanun a hankali.

Haris ya yi murmushi, amma murmushin nasa wannan karon ya kasance mai ɗauke da wani abu daban, ya ɗan sauke ajiyar zuciya,
“Ina jin tsoro.”
Raihana ta ɗago idanunta kaɗan,
“Tsoron me?”
Haris ya yi shiru, ya kalli hannayensa, kamar yana neman kalmomin da suka dace.
Bayan ƴan daƙiƙu sai ya ɗago idanunsa ya kalleta,
“Tsoro nake...” ya ɗan dakata,
“Kar na rasa ki.”

Raihana ta yi shiru, Haris ya ci gaba cikin murya mai laushi,
“Kin san ke ba kalar matar talaka ba ce.”
Raihana ta ɗan daure fuska kaɗan, ya yi saurin gyara maganarsa,
“Ba wai ina nufin ki da dukiya nake aunawa ba.”
Ya yi murmushi mai rauni,
“Amma kina da ilimi, kina karatun likita, kina da makoma a gabanki.”
Ya sauke numfashi,
“Ni kuma... iya abin da nake da shi diploma ne da na yi a Shari’a.”
Ya ɗan yi shiru,
“Wani lokaci idan na kalle ki, sai na ji kamar...” ya kasa ƙarasa maganar,
“Ko zan iya baki abin da ya dace da ke?”

Raihana ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai ta ɗan yi murmushi, ta ɗaga idanunta ta kalle shi, kafin cikin nutsuwarta ta ce,
“Ni ba na neman miji saboda degree ko dukiya.”
Muryarta ta kasance mai sanyi, nutsuwa, ta ɗan sauke idanunta kafin ta ci gaba,
“Ba na neman wanda zai zo ya bani jin daɗin rayuwar da ba lalle na samu farinciki a cikinta ba.”

Haris ya yi shiru yana kallonta,
“Abin da nake so...” ta ɗan dakata,
“Shi ne mutum mai tsoron Allah.”
Ta ɗaga idanunta,
“Mutumin da zai mutunta ni. Ya mutunta iyayena. Ya mutunta ’yan uwana.”
Ta sauke numfashi a hankali,
“Kuma...” muryarta ta yi laushi sosai,
“Ya so ni.”

Haris bai motsa ba, kawai ya ci gaba kallonta.
Raihana ta ci gaba,
“Ba wai saboda ina da kyau ba, ba wai saboda ina karatun likita ba, ba wai saboda abin da nake da shi ba.”
Ta ɗan yi murmushi,
“Ya so ni saboda ni ce ni.”

Haris ya sauke idanunsa, wani irin shauƙi ya mamaye zuciyarsa, sai ya ɗago idanunsa ya sake kallonta, a wannan karon… kallon nasa ya cika da wani irin so da ya kasa ɓoyewa,
“Rayhaan...”
“Hmm?”
“Dan Allah...” ya ɗan matsa gaba kaɗan, amma har yanzu cikin mutuntawa,
“Ki bani dama.”

Raihana ta yi shiru,
“Dama na turo iyayena.”
Ya haɗiye yawu,
“Wallahi...” muryarsa ta ɗan yi rawa,
“Ba zan iya rasaki ba.”

Raihana ta sauke idanunta, Haris kuwa ya ci gaba da kallonta cikin shauƙi,
“Na daɗe ina kallon ki daga nesa, Rayhaan.”
Ya yi murmushi,
“Ban san ranar da kika zama wani abu mai muhimmanci a zuciyata ba.”
Ya ɗan sauke ajiyar zuciya,
“Amma yanzu...” ya girgiza kai a hankali,
“Ba na son in sake yin shiru har wani ya zo ya ɗauke ki daga gare ni.”

Raihana ta ɗago idanunta a hankali, kalaman nasa suka tsaya mata a zuciya, amma… ba ta samu damar cewa komai ba.

Wata fitilar waya ta haske su kwatsam, hasken ya sauka kai tsaye kan fuskokinsu, dukkansu suka ɗago hannu lokaci guda, suka kare idanunsu daga hasken.
Raihana ta ɗan runtse idanunta, Haris ma ya juya fuskarsa gefe, sai kuma… a hankali aka ɗauke fitilar.

Mutumin ya wuce kawai, babu wata magana, babu sallama, babu ko neman afuwa.
Sai Raihana ta sauke hannunta a hankali, sannan ta maida idanunta ƙasa, ta san wannan hali, ta san ko waye, Bintu ce.

Kamar dai za ta yi mata wata magana, amma ta san Haris yana zaune a gabanta, sai ta yi shiru, dan ta san tsafff sai su raba hali a wajen.
Raihana ta ɗan kalli Haris,
“Kayi haƙuri.”
Haris ya yi murmushi cikin natsuwa,
“Ba komai.”
Ya ɗan kalli inda Bintu ta wuce, sannan ya maida idanunsa kan Raihana,
“Maybe ba ta san akwai mutane a wajen ba.”
Raihana ta ɗan jinjina kai, ba ta ce komai ba.

Amma a cikin zuciyarta… ta san Bintu sosai, ba yau ta fara ganin irin wannan hali nata ba, ta sani sarai.
Ta san akwai mutane a wajen, ta san ita da Haris suna zaune a nan, wulakancine kawai irin na Bintu, wanda ba sai an tambaye ta dalilinsa ba.

Bintu ta shiga ɗakin a hankali, tana ɗauke da wasu ledoji a hannunta, da ta shigo, ta ajiye ledojin a gefe, sannan ta fashe da dariya,
“Mamaaa!”
Mama Sabuwa ta ɗago kai da sauri, tun daga lokacin da ta ga Bintu da wannan farin cikin a fuskarta, zuciyarta ta yi haske, ta yi murmushi,
“Na’am, Bintoto... sannu da zuwa.”

Bintu ta cire mayafinta,
“Yar arziki irin albarka!”
Mama Sabuwa ta faɗa tana dariya tana jan ledojin da Bintu ta ajiye.
Bintu ta zauna, ta cire mayafinta ta ajiye a gefenta.

Mama Sabuwa ta fara buɗe ledojin, sai ta ɗago kai ta kalli Bintu,
“Wai dama wannan ne wanda yake zuwa wajen Raihana?”
Bintu ta sake fashewa da dariya, Mama Sabuwa ta ɗan dakata da abin da take yi,
“Kin san shi ne?”
Bintu taɓe baki,
“Ban san shi ba wallahi, kawai dai mamaki na yi da na gan shi.”
Ta sake dariya,
“Na ga dai kamar ba laima a jikinsa ne! Aljihunsa a bushe yake, ban ga alamun zai yi wani abin arziki ba.”

Mama Sabuwa ta kalli Bintu, sannan ita ma ta saka dariya,
“Ke dai!”
Bintu ta ci gaba da dariya,
“Duk kafafar da ake mana a nan aka kare!”
Mama Sabuwa ta sake dariya,
“Ni kaina fa, duk da ban gan shi ba, na san ba za a yi wani abin arziki ba.”
Ta sake janyo wata leda tana dubawa,
“Wai meye a cikin wannan?”
Bintu ta ɗaga hannu,
“Yan kayan ciye-ciye ne dana kawo miki.”
“Laaa! Mamaa.”

Mama Sabuwa ta yi murmushi, ta ɗago ta kalli Bintu,
“Ki ga ni zan manta ma Hajiya fa...”
Bintu ta ɗan tsaya,
“Hajiya ta ce tana so zan raka ta can foundation ɗinta na Abuja.”
Mama Sabuwa ta ɗago kai,
“Foundation?”
“Eh, za a gudanar da wani taro, tana son ta je da ni, kusan duk ’yan can sun san ’yarta da ta rasu...”
Murmushin Bintu ya ɗan canza,
“Wacce muke kama.”
Ta ɗan gyara zamanta,
“Tana son su ganni.”
Mama Sabuwa ta ɗago kai da sauri,
“Ke... Dan Allah Abuja faa, can birnin tarayya!”
Bintu ta yi murmushi,
“Wallahi mama”



Not edited