A PLAN IN DISGUISE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER- TWENTY SIX:26*
*A PLAN IN DISGUISE*
*JIDDAAH BARKUM*
———————
Raihana ta shiga ɗakin Umma a hankali, tana ɗauke da wani irin murmushi a fuskarta.
Da ta shigo ta yi sallama cikin ladabi,
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Muryar Umma ta amsa mata daga can cikin ɗakin.
Raihana ta ƙara matsowa, Umma tana zaune a gefen gadonta, wasu kayan Ameenah da Yusuf suna gabanta, tana ɗaukar kaya ɗaya bayan ɗaya tana gyara su, tana naɗe su da kyau kafin ta saka su cikin wardrobe.
A ɗayan gefen kuma, Ameenu da Yusuf suna zaune a ƙasa, Yusuf yana riƙe da littafin assignment, yana nuna wa Ameen abin da yake rubutawa,
“Wannan nan ka fara da shi… sai ka yi carry ɗin nan zuwa nan.”
Ameenu ya sunkuya sosai yana kallon littafin.
Raihana ta yi murmushi ganin yadda suka nutsu, ta ƙarasa ta zauna a gefen Umma,
“Umma, sannu da aiki.”
Umma ta ɗago kai ta kalle ta,
“Yauwa, sannu. Har ya tafi ne?”
Raihana ta jinjina kai,
“Eh.”
Ta ɗan gyara zamanta, sannan idanunta suka koma kan yaran,
“Wato kun bar min Umma na gyara muku kaya ku?”
Ta yi dariya kaɗan,
“Yanzu ma ba ku kai ku dinga gyaran kayanku da kanku ba? Komai sai an yi muku.”
Ameenu da Yusuf suka kalli juna, sai suka yi dariya,
“Anty Rayy...”
Yusuf ya ɗago kansa,
“Ai Umma ba ta son mu sha wahala.”
Umma ta ɗan saci kallon Yusuf, sai ta yi murmushi.
Raihana ta girgiza kai tana dariya,
“Umma, dan Allah ki kyaleshi, Yusuf fa zai iya gyaran kayansu, ki dinga hutawa ke ma.”
Umma ta danyi dariya,
“Kyalesu, nawa suke? Idan ma na barsu, ai ba za su yi shi da kyau yadda zan yi ba.”
Raihana ta kalli Umma,
“Hmm...”
Sai ta matso kusa,
“Toh ni kawo, ni na yi.”
Umma ta ɗaga hannu,
“Barshi.”
Amma Raihana ta riga ta miƙa hannu,
“Umma, kawo mana.”
Umma ta kalleta na ƴan daƙiƙu, daga ƙarshe ta miƙa mata kayan.
Raihana ta karɓa, ta fara jera su ɗaya bayan ɗaya, tana gyara kowanne kafin ta saka shi cikin wardrobe.
Umma kuwa tana kallonta ne kawai, akwai wani irin nutsuwa a fuskarta.
Sai ta juya ta kalli yaran,
“Toh ku je falo ku ƙarasa assignment ɗinku.”
Yusuf ya kalli Ameenu,
“Mu tafi.”
Ameenu ya ɗauki littafinsa,
“Toh.”
Dukkansu suka miƙe suka fita,
“Anty Rayy sai mun dawo.”
“Okay.”
Ƙofar ta rufe a bayansu, sai ɗakin ya yi shiru.
Umma ta dawo da hankalinta gaba ɗaya kan Raihana, Raihana kuwa har yanzu tana jere kayan, ba ta lura da canjin kallon Umma ba.
Sai Umma ta ce a hankali,
“Raihana...”
Raihana ta ɗago kai,
“Hmm, Umma?”
Umma ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Ya maganar da kukayi da Baffanki... akan zuwan baiwar Allah nan?”
Raihana ta tsaya, hannunta da ke riƙe da wata riga ya yi sanyi, ta kalli Umma, sai ta maida idanunta ƙasa,
“Da kuma maganar Haris?”
Raihana ta ɗan ɗago idanunta, ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sai a hankali ta ce,
“Umma...”
“Hmm?”
“Yace... dan Allah yana so ma ya turo a zo wajen Baffa ayi magana.”
Umma ta kalleta sosai, hannunta ya tsaya kan kayan da take gyarawa,
“… waye kenan?”
Raihana ta ɗan ɗago kai, sai kuma kamar wacce kalmar ta yi mata nauyi, ta maida kanta ƙasa, muryarta ta fito a hankali,
“… Haris.”
Wajen ya danyi shiru, Umma ta kalleta, ba ta ce komai ba.
Kallon da ta yi mata ya ɗauki wasu mintuna kaɗan, kamar tana ƙoƙarin karanta abin da ke zuciyar ɗiyarta ba tare da ta tambaye ta da yawa ba.
Raihana kuwa ta ci gaba da jere kayan, amma wannan karon… hannunta ba ya tafiya da sauri.
Umma ta ɗan sauke numfashi, sai ta tambaya cikin murya mai laushi,
“Zuciyarki... ta fi kwanciya da shi ko?”
Raihana ta tsaya, idanunta suka sauka kan kayan da ke hannunta, ba ta iya kallon Umma kai tsaye ba.
A hankali… ta jinjina kai, ƙaramar alamar da ta isa ta amsa komai.
Umma ta yi murmushi, ba murmushin mamaki ba, sai irin murmushin uwa wadda ta fahimci abin da ɗiyarta ba ta iya faɗa da baki ba,
“Toh...” ta gyara zamanta,
“Ba komai.”
Raihana ta ɗago idanunta.
Umma ta ci gaba,
“Zan faɗawa Baffanku.”
Sai ta ɗan yi murmushi,
“Allah Ya sa haka ne ya fi alkhairi.”
Raihana ta sauke ajiyar zuciya a hankali, a karo na farko tun bayan Haris ya yi mata maganar… zuciyarta ta ji wani irin sauƙi.
Sai ta sake maida hankalinta kan kayan da ke gabanta, amma Umma… ta ci gaba da kallonta, kamar akwai wasu abubuwa da take tunani a kansu, wasu abubuwan da wataƙila… Raihana kanta ba ta san yadda za su sauya komai ba tukuna.
——————
Hajiya Hauwa na zaune a cikin mota, tana kan hanyar zuwa gidan kawarta, Hajiya Balaraba, tuni ta iso bakin gidan, amma kafin ta shiga sai ta yi parking a waje, ta kashe injin motar, sannan ta ɗauki wayarta.
Ta danna wani number, wayar ta yi ringing na ɗan lokaci… sai aka ɗaga,
“Assalamu alaikum, Inno. Ina wuni? Ya ƙarfin jikin kuma?”
Muryarta ta fito cikin girmamawa.
Daga can bangaren, muryar matar da ta kira, Inno, ta bayyana, muryar ba irin ta tsohuwa ba ce, a’a, duk da shekarunta, har yanzu akwai wani ƙarfi a cikinta, murya ce da zarar ka ji ta, zaka san mai ita ba ta ɗaukar shirme.
Hajiya Hauwa kuwa nan take ta ɗan canja murya, ta san halin uwarta, she’s a no-nonsense woman, duk da tsufanta, ba ta yarda a yi mata wani abu da ba zai yi mata daɗi ba,
“Inno... dama maganar nan ce dai ta Seeyama akan Zayd.”
Ta ɗan sauke numfashi,
“Wallahi yarinyar nan ta ɗagawa kanta hankali, na ba ta haƙuri, nace mata indai Zayd mijinta ne, dole ta aure shi, amma kinga... bata saurarona.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Har abinci yanzu ta daina ci, ta ɗauki tashin hankalin duniya ta ɗora wa ranta.”
Muryarta ta ɗan yi ƙasa,
“Kuma tun daga lokacin da ta ga abin da Zayd ya aikata da budurwarshi a yanar gizo... yana wayo...”
Ta sake sauke numfashi,
“Nan ma ta sake rikicewa, nace mata tayi haƙuri, yanzu hankalin sa baya kanta.”
Ta ɗan kalli windshield ɗin motar, idanunta suka yi nisa kamar tana tunanin abin da ya faru,
“Tunda ya ɗauko wannan halin, abu har ya kai hotunan tsiraicinsa suna yawo a duniya, kinga ai hankalinsa ba zai kawo kan aure ba, wahala kawai zata sha.”
Ta yi ɗan shiru kafin ta ci gaba,
“Ko ta aureshi, tunda shi matan waje ke burgeshi... ba aure ba.”
Daga can kuwa… Inno ta yi shiru, ta bar Hajiya Hauwa ta gama magana, sai ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya,
“Yanzu ina Seeyama ɗin?”
Hajiya Hauwa ta gyara zamanta a cikin motar,
“Tana gida, na barta ni na fita ne yanzu.”
“Toh shikenan.”
Muryar Inno ta ɗan yi nauyi,
“Da zarar kin koma, ki kirani, zan yi magana da ita.”
Ta ɗan yi shiru,
“Shi kuma Zaidu... nasan maganinsa.”
Hajiya Hauwa ta ɗan ɗaga gira.
“Tunda uwarsa ke daure masa yana iskanci a haka dai kamar ba zai aikata ba...”
Ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Duk da dai an ce sharri aka yi masa, domin ko ni idan na duba abin, bana ganin zai aikata irin wannan abu.”
Hajiya Hauwa ta sauke idanunta,
“Amma duk da haka...”
Inno ta ci gaba,
“Da ya yi aure ai wani abu zai canja, makiya zasu hakura da bin sa da sharrin bin mata, tunda an san ya ajiye mata.”
Hajiya Hauwa ta yi shiru, sai ta ce a hankali,
“Wallahi ni, Inno, abin da nake gani kenan, dan har yaya da Hajja Fateema na Kai wa maganar bayan abun ya faru amma suka watsar.”
Ta gyara wayar da ke hannunta,
“Idan ya yi aure, wani abu za a kyale mutum, ai dan an san ba shi da aure ne aka ɗauko hotunan aka yaɗa.”
Daga can Inno ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai ta ce,
“Ba komai, nasan abin da zanyi.”
Hajiya Hauwa ta yi murmushi,
“Toh Inno, bari na ƙarasa inda zan je.”
Ta kalli gate ɗin gidan Hajiya Balaraba,
“Sai anjima, Allah Ya ƙara lafiya da tsawon rai mai amfani, uwata.”
Daga can aka amsa mata,
“Amin.”
Sai ta kashe wayar, tana wani murmushi.
Ta ajiye wayar a gefenta, sannan ta ɗan kalli babban gate ɗin gidan Hajiya Balaraba, ta ja dogon numfashi, sai ta danna horn,
Piiiiiip...
Gate ɗin ya fara buɗewa a hankali, Hajiya Hauwa ta gyara mayafinta, ta kunna motar… sannan ta shige cikin gidan.
Hajiya Balaraba na zaune cikin nutsuwa a kan ɗaya daga cikin manyan luxury sofas ɗin falonta, wanda aka kawata shi da cushions masu kyau da suka dace da tsarin gidan.
Ta sha kwalliya cikin isa da ɗan ƙaramin alfahari irin nata, wayarta tana hannunta, tana dannawa a hankali, sai ƙarar buɗewar ƙofar falon ta sa ta ɗago kai.
Mommy Hauwa ce ta shigo, da ganinta, Hajiya Balaraba ta miƙe da sauri,
“Hajjaju!”
Ta ƙarasa gare ta, ta rungume ta cikin fara’a,
“Sannu da zuwa!”
Mommy Hauwa ta yi dariya, ta amsa rungumar,
“Yauwa uwardakina, ya gajiya?”
“Alhamdulillah.”
Sai Hajiya Balaraba ta ɗan janye jikinta, ta fara bin Mommy Hauwa da kallo daga sama har ƙasa, murmushi ya bayyana a fuskarta.
Mommy Hauwa ta lura da hakan, ta ɗan yi ƙaramar dariya,
“Ya ne kike kallona haka?”
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Gani nayi kin yi kyau.”
Ta ɗan karkatar da kanta,
“Kamar ba ki haifi Imraan da Seeyama ba, kullum sake dawowa yarinya kike yi.”
Mommy Hauwa ta fashe da dariya, ta miƙa mata hannu, suka tafa,
“Kinada abin dariya Hajjaju!”
Ta zauna a kan sofa,
“Tsofai tsofai da ni... na ba hamsin baya.”
Hajiya Balaraba ta zauna kusa da ita tana dariya,
“Ki dinga irin wannan maganar.”
“Dan Allah ki bari!”
Dukkansu suka sake dariya.
Bayan ɗan lokaci, Hajiya Balaraba ta gyara zamanta,
“Toh...” ta kalli Mommy Hauwa,
“Ya maganar zuwa taro Abuja?”
Mommy Hauwa ta ɗago mata ido,
“Kin san dai wannan karon ya kamata ki halarta.”
Ta ɗaga yatsa kaɗan,
“An ɗaga miki kafa daidai gwargwado, kusan taro uku ba ki je ba.”
Mommy Hauwa ta ɗan tabe baki,
“Ni wallahi ba wai zuwan ne ba...”
Ta sauke ajiyar zuciya,
“Ban samu yarinyar da zan yi presenting ɗin ba.”
Hajiya Balaraba ta ɗan kankance idanunta, ta kalle ta kamar wadda yanzu ta fahimci komai,
“Au...”
Ta ɗan matsa kusa,
“Saboda wannan ne kike ta jan kafa?”
Mommy Hauwa ta ɗan jinjina kai.
Hajiya Balaraba ta yi murmushi mai cike da dabara,
“Toh akwai mafita.”
Mommy Hauwa ta kalle ta,
“Wace mafita?”
Hajiya Balaraba ta ɗaga hannu,
“Kawo kunne ki.”
Mommy Hauwa ta ɗan matsa kusa da ita.
Hajiya Balaraba ta sunkuyo, ta rada mata wasu kalmomi a hankali, da ta gama… Mommy Hauwa ta zaro ido, sai kuma ta fashe da dariya,
“Haba dai! Dan Allah!”
Ta kalleta cike da mamaki.
Hajiya Balaraba ta yi murmushi tana girgiza kafa,
“Wallahi!”
Ta ɗaga kafada,
“Ke fa yanzu haka ake yi.”
Mommy Hauwa ta ci gaba da dariya, tana girgiza kai.
Hajiya Balaraba kuwa ta jingina bayanta cikin nutsuwa,
“Toh ki zauna ki ga zama wallahi...”
Ta ƙarasa tana murmushi.
Not edited