THE VISIT
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER THIRTY FOUR:34*
*THE VISIT*
*JIDDAAH BARKUM*
————————-
Motar ta ci gaba da zama cikin shiru.
Babu wanda ya ce uffan.
Sameer yana zaune a gaba, amma tunaninshi gaba ɗaya yana can baya.
A zuciyarsa kuwa… ya ga komai kuwa?
Bai san abin da Zayd yake tunani ba.
Shi kuwa driver ɗin ma sai ya lumshe idanunsa lokaci-lokaci, kamar wanda bacci ya ɗauke shi, duk da cewa hannuwansa suna kan steering.
Sameer ya ɗan waiga.
Zayd yana zaune a kujerar baya, idanunsa a lumshe, fuskarsa babu wani expression.
Amma wannan ne abin da ya fi ba Sameer tsoro, domin ya san Zayd.
Idan ya yi shiru haka… ba lallai ne yana lafiya ba.
Sameer ya sake maida kansa gaba.
Sai bayan ɗan lokaci, ya ga wani mutum yana tahowa daga ɗan nesa.
Ya ɗan ƙara kallonsa.
Yaya Hamza.
Sameer ya sauke numfashi a hankali, sai ya sake waigawa zuwa wajen Zayd,
“Boss...”
Zayd ya ɗan buɗe idanunsa, ya kalli Sameer.
Sameer ya haɗiye yawu,
“Uhmm...”
Ya ɗan tsaya yana neman kalmomin da suka dace,
“Dama... ga brother ɗinta zai shiga.”
Zayd bai ce komai ba.
Sameer ya ci gaba da sauri,
“Nace ko ayi masa magana ne?”
Zayd ya juya idanunsa zuwa front view na motar, ya kalli Yaya Hamza da ke ƙara matsowa wajen motar.
Bai yi magana ba, sai kawai… ya ɗan gyada kai.
Nan take Sameer ya buɗe ƙofar motar ya fito, ya rufe ƙofar a hankali, sannan ya nufi wajen Yaya Hamza.
Yaya Hamza ya tsaya.
Sameer ya ƙarasa gabansa, suka yi musabaha,
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Yaya Hamza ya kalli motar da Sameer ya fito daga ciki.
Sai Sameer ya ce,
“Mun zo wajen Raihana ne.”
Yaya Hamza ya ɗan kalli motar a karo na biyu, ya riga ya san da maganar Zayd.
Tun kafin yau, Baffa ya sanar da shi komai, saboda haka bai yi mamaki ba.
Sai ya kalli Sameer,
“Za ku shiga ku yi magana da ita ko?”
Sameer ya ɗan jinjina kai,
“Eh, muna so mu gan ta.”
Yaya Hamza ya ɗan yi murmushi kaɗan,
“Toh... ai da ya shigo.”
Ya nuna hanyar shiga gidan da hannunsa,
“Kar ya tsaya a waje haka.”
Sameer ya ɗan kalli motar, sai ya maida idanunsa kan Yaya Hamza,
“Toh.”
Ya sake jinjina kai,
“Bari na masa magana.”
Yaya Hamza ya gyada kai,
“Okay.”
Sameer ya juya, ya fara komawa wajen motar a hankali.
A nutse Sameer ya koma wajen motar, ya ɗan sunkuya, sannan ya yi knocking a glass ɗin gefen Zayd a hankali.
Zayd ya ɗago kansa, lumshashun idanunsa suka sauka kan Sameer, yana kallonsa na ƴan daƙiƙu ba tare da ya ce komai ba.
Sai ya ce cikin ƙaramar murya,
“Hmm?”
Sameer ya ɗan daidaita tsayuwarsa,
“Ya ce ko zaka shigo daga ciki?”
Zayd bai amsa nan take ba, ya juya kansa a hankali, idanunsa suka sauka kan Yaya Hamza da yake tsaye a ɗan nesa, yana jiran su.
Zayd ya ɗan yi shiru, kamar zai faɗi wani abu… amma sai kawai ya sauke idanunsa.
Ya balle murfin motar, a hankali ya zuro ƙafunsa waje, daga nan ya fito gaba ɗaya.
Sameer ya yi saurin matsawa gefe ya ba shi hanya.
Zayd ya miƙe tsaye, ya zura wayarshi a aljihunsa, sannan Sameer ya rufe masa ƙofar motar a hankali.
Zayd bai jira shi ba, ya nufi wajen Yaya Hamza.
Da ya ƙarasa, suka yi musabaha,
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Yaya Hamza ya ɗan yi murmushi,
“Bismillah.”
Ya juya ya fara tafiya zuwa cikin gidan.
Zayd ya bi bayansa a hankali, ba ya gaggawa, kawai yana tafiya ne cikin nutsuwa, hannunsa ɗaya a aljihun wando, fuskarsa a rufe kamar yadda ya saba.
A baya kuma… Sameer ya tsaya yana kallonsu har suka ɗan yi nisa, sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya,
“Haa...”
Ya ɗan girgiza kansa, daga nan ya koma motar, ya buɗe ƙofar gaba ya shiga, ya zauna ya jingina bayansa da kujerar.
Yaya Hamza ya raka Zayd har bakin ƙofar falon Baffa da yake can a bayan gidan.
Da suka isa, sai Yaya Hamza ya tsaya ya kalli Zayd,
“Bari na yi maka magana da ita.”
Zayd ya ɗan gyada kai,
“Okay.”
Ba tare da ya ƙara cewa komai ba, sai ya shiga falon ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ke gefen falon.
Yaya Hamza kuma ya juya ya nufi cikin gidan.
A ɗayan ɓangaren gidan kuwa… Maryam da Raihana suna zaune a gefe, yayin da Umma take zaune kusa da su tana kallon yadda Raihana ke ware kitsonta.
Umma ta sauke ajiyar zuciya,
“Wallahi na gaji da miki magana akan wannan kitson.”
Raihana ta ɗago idanunta kaɗan.
Umma ta ci gaba da faɗa tana kallon gashin nata,
“Inaga zan bi dare na kwashe wannan gashin da almakashi, kinga bakina ya huta ko?”
Maryam ta kasa riƙe dariyarta, ta fashe da dariya,
“Ummaaa!”
Raihana ta kalle ta ta zuba mata uwar harara,
“Ke kuma me kike dariya?”
Maryam ta ɗan rufe bakinta tana ƙoƙarin tsayar da dariyar.
Umma ta nuna Raihana da yatsa,
“Ki ga dai! Har yanzu kin tsaya kina kallon mutane maimakon ki yi abinda ke gabanki.”
Maryam ta sake dariya,
“Umma, idan kika aske mata fa...”
Ta ɗan yi shiru kamar mai tunani,
“Zan siyo Super Glue ni, ki manna min gashin a kaina.”
Maryam ta sake fashewa da dariya.
Raihana ta wani kalle ta,
“Maryam!”
A dai-dai lokacin ne Yaya Hamza ya ƙaraso wajen, ya tsaya a bakin ƙofar, sannan ya dubi Umma,
“Umma...”
Umma ta ɗago kai,
“Hmm?”
Yaya Hamza ya maida kallonsa kan Raihana,
“Kinada baƙo a falon Baffa.”
Raihana ta ɗago kai da sauri,
“Baƙo kuma Yaya?”
“Eh.”
Ya ɗan yi murmushi,
“Ki yi sauri, ya daɗe.”
Umma ta ɗan kalle shi da mamaki,
“Yaya, waye kuma?”
Sai ta ɗan kalli Raihana,
“Ba dai haris din kika bari a tsaye a waje ba kika shigo?”
Yaya Hamza ya girgiza kai,
“Umma, ba Haris ba ne.”
Ya ɗan dakata, sai ya faɗi sunan a hankali,
“Zayd ne.”
Shiru, kamar an kashe duk wani sauti a ɗakin.
Umma ta ɗaga gira,
“Zayd?”
Sai idanunta suka nufi Raihana.
Raihana kuwa… ta tsaya cak, idanunta suka ɗan buɗe cikin mamaki,
“Zayd...?”
Kalmar ta fito daga bakinta kamar ba ita ce ta faɗe ta ba.
Maryam kuwa da jin sunan… sai ta kalli Raihana, ta kalli Yaya Hamza, sannan ta sake kallon Raihana, sai murmushi ya fara bayyana a fuskarta,
“E toh...”
Maryam ta cije leɓenta tana ƙoƙarin hana kanta dariya.
Yaya Hamza ya ɗan gyara tsayuwarsa,
“Ki tashi ki fito, yana falon baffa, na faɗa miki ya daɗe.”
Ya juya ya fita.
Sai Maryam ta miƙe, ta ƙarasa wajen Raihana,
“Ki tashi dai, ki daure kan nan muje, na raka ki.”
Raihana ta yi shiru, idanunta suka sauka kan hannunta, zuciyarta kuwa ta fara bugawa da wani irin sauri da ita kanta ta kasa fahimta.
Umma ta kalle ta,
“Ki tashi mana, ana magana kin tsaya kina ta raba ido.”
Sai Raihana ta dan mike a hankali, ta dauki hijab ɗinta tana ƙoƙarin gyara shi ta maida kanta, amma kafin ta gama sawa, Umma ta sake kallonta daga sama har ƙasa,
“A haka za ki je?”
Raihana ta ɗan tsaya, ta kalli Umma,
“Eh, Umma.”
Umma ta saki baki,
“Ke dai!”
Ta ɗan gyara zamanta, sannan ta nuna kanta da hannu,
“Kalli kanki gefe ɗaya, a tsefe... ya yi tudu, gefe ɗaya kuma a kitse, sai ki kama hanya ki je wajensa a haka?”
Raihana ta ɗan turo baki,
“Umma...”
“Me?”
“Yanzu fa na dawo daga wajen Haris, ba abinda hijabina ya yi...”
Umma ba ta bari ta ƙarasa ba,
“Wuce daga gabana ki je ki kintsa kanki, kalleki dan Allah.”
Raihana ta ɗan yi shiru.
Maryam kuwa tuni ta fahimci inda maganar Umma ta dosa, ta finciko hannun Raihana, ta ja ta zuwa ɗakin.
Raihana tana biye da ita kamar wata yar’ta.
Da suka shiga ɗakin, Maryam ta rufe ƙofar a bayansu, sai ta juya ta kalli Raihana,
“Wallahi sai kin canja kayan nan.”
Raihana ta zaro ido,
“Sabida me toh?”
“Sabida me?”
Maryam ta maimaita cikin mamaki,
“Gaskiya ray, wani lokacin kamar baki da saiti, kin san kalar mutumin da yazo wajenki shine zaki debi kafa ki tafi da wannan gantalalliyar rigar taki?”
“Kalleki fa, ga wani uban gashi a gefe kamar bararojii.”
Raihana ta kalli doguwar rigar da take jikinta,
“Me ya same ta?”
“Nothing.”
Maryam ta girgiza kai,
“Amma ki canja.”
Sai ta ƙarasa wajen wardrobe ta buɗe shi,
“Amma idan mutum ya zo gidanku, musamman irin wannan mutumin...”
Ta ɗan waiga ta kalleta,
“…ba za ki je ki tarbe shi kamar kin tashi daga bacci ba.”
Raihana ta yi shiru, ta sauke idanunta kan rigar ta,
“Naje wajen Haris ma a haka balle wani kuma...”
Maryam ta ɗan ɗaga gira,
“Ke dai kika sani.”
Ta ci gaba da duba kayan.
Raihana kuwa ta tsaya a wurin tana bin Maryam da ido dake kokarin nemo mata kaya a wardrobe, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci,
“Me ya zo yi yau kumaaaa?”
Maryam ta ɗauko black plain abaya wadda babu wani irin ƙawanya a jikinta, ta miƙa wa Raihana,
“Sa wannan.”
Raihana ba ta yi gardama ba, ta karɓa ta saka.
Maryam kuma ta ƙarasa wajen gashinta, ta tattara gashin da ta riga ta tsefe, ta haɗa shi da sauran wanda ba a ware ba, sannan ta yi mata simple packing ɗinsa.
Bayan ta gama, sai ta ɗauko veil din abayar ta ɗan nada mata shi a kai, ta gyara gefensa yadda ya zauna da kyau.
Sai ta ɗauko turare,
“Juya.”
Ta fesa mata kaɗan.
Raihana ta lumshe idanunta saboda ƙamshin, yayin da Maryam ta kalle ta ta yi ɗan murmushi.
Raihana kuwa kawai kallonta take yi,
“Me?”
Maryam ta ɗaga gira,
“Nothing, kin yi kyau.”
Ba ta jira amsarta ba, ta kama hannun Raihana,
“Muje.”
Da suka fito falo Umma ta bi su da kallo kawai.
Ta ja ta har bakin ƙofar falon Baffa.
Maryam ta fara shiga bakinta dauke da sallama,
“Assalamu alaikum.”
Zayd da yake zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon, yana danna wayarsa, ya ɗan ɗago kai, idanunsa suka sauka kansu.
Da ya ga Maryam, sai ya amsa sallamar,
“Wa alaikumus salam.”
Maryam ta shiga gaba, ta zauna a kujerar da ke facing ɗinsa, hannunta har yanzu a rike da na Raihana, sai ta ja Raihana ta zaunar da ita a gefenta.
Fuskarta ɗauke da murmushi, ta gaishe shi,
“Barka da zuwa, ina yini?”
“Lafiya lau, ya kike.”
Zayd ya amsa cikin nutsuwa, yana ƙoƙarin mayar da ɗan murmushi.
Maryam ta ɗan gyara zamanta,
“Sorry da muka bar ka kana jira.”
Ta kalli Raihana,
“Ka ga hannun nata ne har yanzu yana ciwo, sai da na tsaya na ɗan taimaka mata ta shirya.”
Raihana ta mintsini Maryam a cinya, ta kalle ta da gefen ido, wai ta shirya?
Kamar zata sa Zayd ya ɗauka cewa sai da ta yi wani irin shiri na musamman kafin ta zo wajensa.
Maryam kuwa ta yi kamar ba ta ji komai ba.
Zayd kuwa… idanunsa suka sauka kan hannun Raihana da take mintsinin Maryam, ya ɗan tsaya yana kallon hannun, sai ya ɗaga idanunsa zuwa fuskarta, amma bai ce komai ba, kamar bai ga abin da yake faruwa ba, sai kawai ya maida hankalinsa kan Maryam,
“Ya School fa?”
Maryam ta ɗan yi murmushi,
“Alhamdulillah.”
Sai ya tambaya,
“Kin kusa gamawa kenan?”
Maryam ta yi ɗan dariya,
“Wallahi ina Level 3.”
Sai ta ɗan juya ta kalli Raihana,
“Ray ce dai take final year.”
Muryarta ta ɗan sauka,
“Amma tun bayan abinda ya faru... incident ɗin nan, Baffa ya hanata zuwa school, har yau bata koma ba.”
Zayd ya ɗan ɗaga kai, idanunsa suka koma kan Raihana.
Raihana kuwa ta ji kamar kawai ta rufe Maryam da duka saboda takaici, me ya sa sai ta faɗa masa?
Ta sauke kanta.
Zayd ya kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ya ɗan ɗauke idanunsa gefe, ya jinjina kai a hankali,
“Toh...”
Sai ya ƙara cikin sanyin murya,
“Allah ya ba da sa’a.”
“Amin.”
Maryam ta amsa tana murmushi.
Ta kuma ta mike tsaye,
“Laa... ban kawo maka ruwa ba.”
Ta kalli ƙofar,
“Bari na kawo maka.”
Zayd ya ɗan yi ƙaramar dariya,
“Ki barshi, kada ki damu.”
Ya ɗan gyara zamansa,
“Ina azumi yau.”
Maryam ta tsaya,
“Azumi?”
“Eh.”
Zayd ya kalli agogon hannunsa na ɗan lokaci,
“Yau Thursday.”
Maryam ta gyada kai,
“Ahh, okay.”
Ta sake zama.
Raihana kuwa tana zaune shiru a gefenta, hannunta a hankali tana riƙe da gefen abayar, yayin da zuciyarta ke ta tambayar kanta abu ɗaya kawai…
Me ya kawo shi kuma yau?
Maryam ta ɗan zauna na ƴan daƙiƙu, sannan sai ta mike tsaye tana dariya a hankali,
“Bari na ba ku waje ko?”
Raihana ta ɗago kai da sauri ta kalleta,
“Ina za ki je?”
Maryam ta ɗan tsaya, sai ta kalli Zayd.
Zayd kuwa ya ɗan ɗauke kansa gefe, kamar bai ji komai ba.
Maryam ta sake kallon Raihana, sai ta yi wani murmushi,
“Ina ni?”
“Ina zama tsakanin masoya...”
Ta kalli Raihana tana kanne ido ɗaya,
“…wata magana ai ba za a yi idan ina nan ba.”
Raihana ta zaro ido,
“Maryam!”
Maryam ta fashe da dariya ƙasa-ƙasa,
“Me na ce?”
Ta juya ta nufi ƙofar.
Raihana ta bita da kallo cikin uban takaicin da ya isheta, Maryam ba ta saurare ta ba, ta ci gaba da tafiya tana dariya ƙasa-ƙasa, sannan kafin ta fita ta sake juyowa ta kalli Raihana, wani irin murmushi take yi wanda ya ƙara bata ran Raihana, ta ji kamar ta bi ta da dukaaaa.
Raihana ta ɗan ja numfashi, ta kalli ƙofar da Maryam ta fita, sai ta maida idanunta ƙasa.
A gefe guda kuma… Zayd yana zaune shiru, wayarsa tana hannunsa, amma yanzu bai sake kallonta ba.
Sai ya ɗago idanunsa a hankali, idanunsa suka sauka kan Raihana.
Raihana ta ji kallon yanda idanunsa ke bin ta, amma ta kasa ɗago kanta.
Shiru ya mamaye falon.
Zayd ya ɗan kalli hannun nata, wanda ya ji ciwon, amma yanzu babu kumburi, babu wani abu da ya nuna cewa ciwon yana damunta sosai.
Sai ya ɗan maida idanunsa kan fuskarta.
Raihana kam tunaninta ya riga ya fara rikicewa, me ya kawo shi? Me ya zo yi? Me yake so?
Ta ɗan gyara zamanta a hankali, tana ƙoƙarin ta daina tunanin komai, sai ta ɗan ɗago kai,
“Ina yini?”
Zayd ya yi mata banza kamar bai ji ba, bai ce komai ba sai kawai ma ya fara danna waya.
Sai ta sake kallonsa a gefe, har yanzu babu amsa.
Ta ɗan tabe baki, sannan ta juya kanta gefe cikin kasa da murya ta fara magana,
“Wlh ba za ka yi min wannan baƙin halin naka ba, mu kwana a nan idan ka ga dama.”
Ta ɗan gyara zaman abayar ta, sannan ta ɗauke kanta gaba ɗaya,
“Kar Allah ya sa ka amsa ma.”
Zayd kuwa yana kallonta ta gefen ido, ya lura da yadda ta ɗauke kanta take magana kasa kasa, ya ɗan lumshe idanunsa, kamar yana ƙoƙarin ɓoye wani abu a fuskarsa.
Raihana ta sake kallon gabanta,
“Ai shi ne ya zo... ba ni na kira shi ba.”
Falon ya sake yin shiru, sai ƙar agogon bango kawai ke ɗan fitowa a hankali.
Raihana ta ƙara ɗan tabe baki.
A dai-dai lokacin ne wayar Zayd ta yi ƙara, ya ɗan kalli screen ɗin.
Ummie naa💕
Sunan da ya bayyana kenan.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ya danna receive ya kai wayar kunnensa,
“Barka da yamma, Ummie.”
Muryarsa ta fito a hankali.
Raihana wacce take zaune tana kallon gefe, sai ta ɗan ɗago kai, jin yadda muryar Zayd ta sauya… sai ta ɗan tsaya,
“Ashe yana iya sakin murya haka?”
Ta ɗan tabe baki,
“Ji shi, ashe ya iya magana haka... sai ya zo nan yana wani shegen kafirin iyayi.”
Ta sake ɗauke kanta gefe, tana ƙoƙarin kada ya lura da yadda take sauraron muryarsa.
Daga ɗayan ɓangaren Ummie ta sake magana, Zayd ya saurara cikin nutsuwa.
Sai a hankali ya waiwayo ya kalli Raihana, idanunsa suka tsaya a kanta na ƴan daƙiƙu,
“Okay, Ummie.”
Ya sauke wayar daga kunnensa, sai ya miƙe tsaye.
Raihana ta lura da motsinsa daga gefen ido, amma ba ta kalleshi ba, ta yi kamar tana kallon wani wuri daban.
Sai ta ji takunsa, ɗaya bayan ɗaya, yana ƙara kusantowa.
Zuciyarta ta fara bugawa a hankali, ta ɗan haɗiye yawu,
“Ina kuma zai je?”
Takun ya ƙara kusantotaa, sai ya tsaya.
Raihana ta kasa jurewa, a hankali ta ɗago kai, sai kawai ta gan shi… tsaye a gabanta.
Nan take idanunta suka zaro kaɗan.
Zayd yana kallonta kai tsaye, babu wani expression mai yawa a fuskarsa, sai dai natsuwarsa wacce ta sa Raihana ta manta da abin da take shirin faɗa.
Zayd ya miƙa mata wayarsa,
“Take.”
Muryarsa ta yi ƙasa.
Raihana ta kalli wayar, sai ta ɗago idanunta zuwa fuskarsa, idanuwansu suka dan hadu.
Na ƴan daƙiƙu… babu wanda ya motsa.
Raihana ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, da sauri ta sauke idanunta kasa, sai ta ji kamar sararin falon ya yi musu kadan.
Ta ɗan turo baki, tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin da ya fara bayyana a fuskarta.
Zayd bai ce komai ba, har yanzu yana riƙe da wayar, hannunsa yana miƙa mata.
Raihana ta ɗan sauke idanunta, sai a hankali ta miƙa hannu ta karɓi wayar, yatsunta suka taɓa wayar… sai zuciyarta ta ƙara bugawa.
Ta kalli screen ɗin na ɗan lokaci,
Ummie naa💕
Sai ta kai wayar kunnenta.
Bayan Raihana ta karɓi wayar, Zayd ya koma kujerarsa a hankali.
Raihana ta ɗan gyara zamanta, sannan ta kai wayar kunnenta,
“Assalamu alaikum, Ummie.”
Muryarta ta fito cikin ladabi.
Daga ɗayan ɓangaren, Ummie ta amsa cikin fara’a,
“Wa alaikumus salam, Raihana, ya kike?”
“Alhamdulillah, Ummie.”
Raihana ta ci gaba da magana cikin girmamawa, kamar yadda ta saba, ta dan risina kamar Ummie na gabanta,
“Barka da yamma.”
“Barka da yamma, ya hannunki?”
Nan take Raihana ta ɗan kalli hannunta,
“Alhamdulillah, Ummie, na ji sauƙi.”
“Da gaske? Har yanzu yana ciwo?”
“A’ah, ya daina, dama targade ne.”
Ta yi magana cikin nutsuwa.
Ummie ta danyi murmushi,
“Toh Alhamdulillah, Allah Ya ƙara sauƙi.”
“Amin, Ummie.”
Sai Ummie ta sake magana cikin kulawa,
“Kin daina amfani da shi sosai toh, har sai ya gama warkewa gabaɗaya.”
Raihana ta ɗan yi murmushi,
“Tohm ummie, in Shaa Allah.”
“Good, kada ki wahalar da kanki, ki bari ya warke sosai.”
“In Shaa Allah.”
Zayd ya ɗan karkatar da kansa, ya kalleta daga gefen ido, a duk lokacin da take amsawa… yanda take magana da Ummie cikin girmamawa, yadda take riƙe wayar, yadda take ɗan risinawa, yadda muryarta take sauyawa idan tana magana da Ummie.
Da Ummie ta tambaye ta wani abu, Raihana ta amsa cikin ladabi, sai ya ɗauke idanunsa kamar bai damu da komai ba, sai ɗan murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Okay, Ummie.”
Ta ɗan yi shiru tana sauraro,
“Eh... yana nan.”
Zayd ya ɗan ɗago gira.
Raihana kuwa ba ta lura ba, sai muryar Ummie ta sake shigowa daga ɗayan ɓangaren.
Raihana ta amsa,
“Tohm.”
Ta ɗan kalli Zayd, sai ta mike a hankali da wayar.
Zayd kuwa ya ɗan lumshe idanunsa, kamar babu abin da ya faru, ta ƙarasa gabanshi ta Mika masa wayar, bai kalleta ba kawai ya amsa ta, juya ta koma wajenta, ya sa a kunnensa, “okay Ummie” kawai yace ya kashe wayar.
Zayd ya kalle ta na ɗan lokaci, sai a nutse ya ce,
“AI kin warke ma.”
Ya ɗan yi shiru, idanunsa har yanzu a kanta,
“Ban ga amfanin zuwan nawa ba.”
Raihana ta ɗan ɗago gira.
Zayd ya ɗauke idanunsa gefe, kafin ya ƙara cikin wata irin murya mai sanyi, kamar maganar ba daga bakinsa ta fito ba,
“Tun da dama ba ni na saka ki dambe a waje ba... har aka miki duka.”
Ya ƙarasa maganar a hankali.
Raihana ta juyo gun sa gaba ɗaya, ta zuba masa wata uwar harara,
“Duka?”
Ta maimaita kalmar a hankali, kamar ba ta yarda da abin da ya faɗa ba.
Zayd ya kalleta.
Raihana ta ɗan tabe baki,
“To ai dama...?”
Ta ɗan gyara zamanta,
“Ni ma dama nace ka zo ka duba ni ne?”
Zayd bai amsa ba.
Ta ɗan kalleshi,
“Ka dai ka san abinda ya kawo ka ai.”
Ta ɗan tsaya, sannan ta ƙara cikin sautin da ke ɗauke da ɗan haushi,
“Da kanka ai naga ka faɗa wa Baffa cewa hannun ya warke.”
Ta ɗan ɗaga hannunta kaɗan,
“Yanzu kuma kar ka wani makale kana cewa ka zo dubani.”
Ta ɗauke kanta gefe,
“Ni ban ce ka zo ba.”
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, sai wani ɗan murmushi ya kusan bayyana a gefen leɓensa.
A zuciyarsa kuwa… nasan ai ba za ta yi shiru ba, dole sai ta maida martani.
Sai dai a zahiri… fuskarsa ta kasance cikin cikakkiyar nutsuwa, babu wani abu da zai nuna irin tunanin da ke gudana a zuciyarsa.
Ya ɗan miƙe a hankali,
“Uhmm...”
Muryarsa ta katse shirun falon.
Raihana ta ɗago kai ta kalleshi.
Zayd ya tsaya gabanta, ya ɗan karkatar da kansa,
“Kin gama bazawa a duniya cewa ba ki da lafiya?”
Raihana ta ɗan daure fuska.
Ya ɗan ɗaga gira,
“Ba ki da lafiya, kowa sai ya taso ya zo dubiya.”
Ya yi ɗan shiru, idanunsa suka sauka kan hannunta na ɗan lokaci, sai ya sake ɗago su zuwa fuskarta,
“Bayan ke kika jawo abin da aka yi miki.”
Raihana ta zuba masa ido,
“Ni na jawo?”
Muryarta ta fito da mamaki da ɗan haushi.
Zayd bai amsa ba, sai kawai ya ɗauki wayarsa daga inda ya ajiye ta, ya zura ta cikin aljihun wandonsa a hankali.
Raihana har yanzu tana kallonsa da mugun mamaki, jin yanda yake zaro zance kamar ba daga bakinsa ba.
Ya ɗan kalleta, wannan kallon nasa ya sa ta yi shiru na ɗan daƙiƙa.
Sai idanunsa suka sake sauka kan hannun nata, ya yi shiru kamar yana nazarin wani abu, sai ya ce cikin sanyin murya,
“Idan kin ga dama...”
Ya ɗan dakata,
“…gobe ma ki je.”
Zayd ya ɗan karkatar da kansa,
“Sai a karya ɗayan hannun.”
Raihana ta buɗe baki, idanunta suka zaro, amma shi… ya riga ya juya, kamar bai yi komai ba.
Ya nufi ƙofa cikin nutsuwa, takunsa ɗaya bayan ɗaya, ba gaggawa, ba wai yana gudu daga amsar da za ta biyo baya ba, a’a, kamar dai ya faɗi abin da yake so ya faɗa ne kawai.
Raihana ta bishi da kallo, ta ɗan miƙe kamar za ta bi shi, amma sai ta tsaya.
Zayd ya kai ƙofar, hannunsa ya kai kan handle ɗin, ya buɗe ƙofar.
Kafin ya fita… sai ya ɗan tsaya na ɗan daƙiƙa, bai waiwayo ba, amma kamar ya san har yanzu idanunta suna kansa, sai ya fita.
Ƙofar ta rufe a hankali.
Raihana ta tsaya cak, tana kallon kofar
Not edited