WHEN DESIRES COLLIDE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER THIRTY NINE:39*
*WHEN DESIRES COLLIDE*
*JIDDAAH BARKUM*
—————-
A hankali Raihana ta wuce ta gaban Maryam dake zaune a tsakar gida. Maryam ta bi ta da kallo har ta shige ɗakin Umma.
Sai ta rufe littafinta a hankali ta miƙe, ta bi bayanta.
A kwance ta sameta a kan gadon, ta yi rubda ciki, idanunta a lumshe.
Maryam ta zauna a gefenta, tana leken fuskarta na ƴan daƙiƙu kafin cikin sanyin murya ta ce,
“Rayyy...”
Raihana ta ɗan buɗe idanunta ta kalleta, amma ba ta ce komai ba.
Maryam ta ɗan matso, sai ta hawo gadon gaba ɗaya ta kama hannun Raihana.
“Me Baffa yace miki? Akwai wani abu ne? Na ga kin wuce ni kamar ba kya jin daɗi, bayan ba a haka kike ba kafin ya kiraki.
Me ya faru?”
Raihana ta ɗan lumshe idanunta, kamar tana ƙoƙarin tara ƙarfin da za ta faɗi abin da ke ranta.
Sai ta buɗe su a hankali, ta sauke kallonta kan Maryam.
Ta ɗan buɗe baki cikin sanyin murya,
“Baffa aure zai yi min.”
Maryam ta yi shiru.
Raihana ma ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta ci gaba,
“Yace na faɗa wa Haris ya turo magabatansa.”
Maryam ta zaro ido.
Nan take ta saki hannunta, ta kankance idanunta,
“Karki ce min ya tambayeki wa kike so, kika ce masa Haris?”
Raihana ma ta harare ta,
“Toh wa zan ce idan ba shi ba?”
Maryam ta saki baki da uban takaici tana kallon Raihana,
“Wallahi Rayy, karki zama mara rabo!”
Ta ɗan daga hannu tana nuna ta,
“Banda rashin rabo! Ace mutum kamar Mr. Armaan ya zo neman aurenki, amma saboda lalacewa ki gantale a zaben wani miskini Haris!”
Raihana ta wani tashi ta zauna, ta kalli Maryam da kyau, idanunta suka cika da ɗan haushi,
“Toh ni shi nake so mana! Shine wanda zuciyata take muradi, ba wancan uban girman kan ba.”
Maryam ta yi wata dariya, ta ɗan girgiza kai kafin ta kalli Raihana,
“Wallahi Rayy, ƙarya kike.”
Raihana ta ɗan daure fuska.
Maryam ta matso kusa,
“Idan kina son Haris ɗin, me yasa da Baffa yace ki faɗa masa ya turo, kika wuce ni kina bata rai?”
Ta ɗan daga gira,
“Ya kamata ki zo ki rungume ni kina cewa, ‘Maryam, I’m getting married!’”
Ta faɗa tana kwaikwayon muryarta, sannan ta fara dariya.
Raihana ta zuba mata uwar harara,
“Sai aka ce miki kuma saboda an ce ya turo ne?”
Ta kauda kai gefe, ta yi shiru na ƴan daƙiƙu.
Sai ta sauke numfashi a hankali,
“Kawai...”
Muryarta ta yi sanyi,
“Damuwata shi ne... zan yi aure ban karasa karatuna baaa.”
Maryam ta saki baki kawai tana kallonta...
————-
Driver ya yi parking a ƙofar gidan Baffa.
Hajiya Balaraba ta kama hannun Bintu, tana sakar mata wani irin makirin murmushi. Bintu kuwa idanunta suna kanta, tana mayar mata da murmushin a hankali.
Hajiya Balaraba ta ɗago ɗayan hannunta, ta shafa fuskar Bintu a hankali, kafin ta matso kusa da ita.
Cikin muryar rada ta ce,
“Zan yi kewarki, baby, ki kula da kanki, kin ji? Duk wani abu da kike so, just chat me up ko ki kira ni. Don’t hesitate to call me, kina jina?”
Bintu ta sake murmushi cikin shagwaɓa,
“Toh... ai Mommy, wannan uban kuɗin da kike bani fa?”
Ta nuna jakarta, wadda ke cike da dollars,
“Kuma kin turo min wasu a account ɗina, ai bazan nemi komai ba.”
Ta kalli bakin Bintu, sannan ta girgiza kai tana murmushi,
“Wannan ai ba komai bane, ke dai duk abin da kike so, kawai ki faɗa min. Kina ji na?”
Bintu ta gyada kai tana murmushi,
“Yes, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta ƙara kallonta na ƴan seconds, kamar tana ƙoƙarin haddace fuskarta, kafin ta janyo ta jikinta,
“I will miss you.”
Bintu ma ta rungumeta sosai,
“Same, Mommy.”
Bayan ƴan seconds, Hajiya Balaraba ta sake ta a hankali.
“Go.”
Bintu ta jinjina kai, ta buɗe ƙofar motar ta fito.
Driver ɗin da ke jingine da motar ya miƙe nan take, ya zagaya zuwa bayan motar ya buɗe boot.
Bintu ta kwashi uban ledodin da ke ciki ɗaya bayan ɗaya.
Ta ɗan gyara su a hannunta, sannan ta kalli Hajiya Balaraba.
Ta ɗaga mata hannu tana murmushi.
Hajiya Balaraba ma ta ɗaga mata hannu.
Bintu ta juya, ta nufi cikin gidan tana jan ledodin, yayin da Hajiya Balaraba ta bita da kallo har sai da ta ɓace wa ganinta.
Kai tsaye Bintu ta shiga cikin gidan.
Idanunta suka fara yawo a wajen.
Babu kowa a tsakar gidan.
Karfe huɗu na yamma ne.
Tun da suka dawo daga Abuja, sai da suka tsaya a gidan Hajiya Balaraba, suka baje suka huta gajiyar tafiyar, a cewarsu kafin daga baya Hajiya Balaraba ta kawo Bintu gida.
Bintu ta tsaya a tsakiyar gidan tana kallon komai, sai ta ja tsaki a hankali.
A idanunta, gidan ya yi mata ƙarami.
Yanzu kamar rayuwarta ta riga ta girma fiye da zama a irin wannan gida.
Babu guards, babu air conditioning, babu manyan lounges, babu expensive furniture, babu wani abu da yake tunasar da ita irin duniyar luxury da ta ɗan ɗanɗana a Abuja.
Ta ɗan murguda baki,
“Hmm...”
Sai ta sake kankame ledodin hannunta ta nufi ɗakin Mama Sabuwar.
Da ta shiga, Mama Sabuwar na zaune a kan sallaya, ta idar da La’asar kenan, ta jingina kaɗan, tana ɗan gyangyadi.
Sai kawai ta ji sallamar Bintu,
“Assalamu alaikum.”
Nan take Mama Sabuwar ta wartsake, ta buɗe idanunta da sauri, ta murza su kamar wadda ba ta gama yarda da abin da kunnuwanta suka ji ba.
Sai ta miƙe,
“Bintotooo!”
Ta ƙarasa wajenta ta kama hannunta da farin ciki,
“Kin dawo! Kai, Masha Allah!”
Ta ja Bintu kusa da ita, tana kallonta daga sama har ƙasa.
Idanunta suka tsaya kan kayan jikinta.
Bintu ta saka wata arniyar Yasmeen abaya, wadda ta zauna a jikinta cikin tsari mai kyau. Hannunta cike yake da gold bracelets, a yatsunta kuma akwai zobuna masu sheƙi.
Sai kuma wani uban tafkeken glasses da ta manna a idanunta.
Kamshin turarenta kuwa... da ta shiga ɗakin, kamar atmosphere ɗin ɗakin ya canja.
Mama Sabuwar ta ɗan buɗe baki,
“Subhanallah...”
Ta sake kallonta,
“Bintu, ke ce kuwa?”
Bintu ta yi murmushi tana ɗan gyara hannun abayarta,
“Ni ce mana, Mama.”
Mama Sabuwar ta riƙe hannunta sosai,
“Wannan yaushe kika koma haka?”
Ta sake kallonta daga sama har ƙasa, sannan ta ɗan taɓa hannun Bintu tana kallon gold ɗin da ke jikinta,
“Wallahi kamar ba ke ba ce kika fita daga wannan gidan.”
Bintu ta yi wata ƙaramar dariya.
Mama Sabuwar ta zaunar da ita kusa da ita, tana kallonta cike da sha’awa,
“Zauna ki bani labari, yaya aka yi? Ina kika je? Me kika gani?”
Bintu ta gyara zamanta, ta ɗan cire glasses ɗin ta riƙe su a hannunta, sai murmushi ya bayyana a fuskarta,
“A Abuja?”
Mama Sabuwar ta gyada kai da sauri,
“Eh.”
Bintu ta ɗan kalli kayan jikinta kamar tana tuna inda komai ya fito,
“Kin san Mama... rayuwar da na gani can ba kamar wadda muka sani ba ce.”
Mama Sabuwar ta ɗan matsa kusa,
“Yaya?”
Bintu ta ɗan sauke murya,
“People there are living differently.”
Ta ɗan ɗaga gira.
Ta ɗaga hannunta tana nuna gold ɗin da ke jikinta,
“Wannan ma fa? Ba komai bane compared to what I saw there.”
Mama Sabuwar ta sake kallon zobenta,
“Subhanallah...”
Bintu ta yi murmushi,
“Na ga wata mace da handbag ɗinta kaɗai ya fi abin da wasu suke kashewa a shekara.”
Mama Sabuwar ta dafe ƙirji,
“Ita jakar?”
“Wallahi.”
Bintu ta fashe da ƙaramin dariya,
“Kuma babu wanda yake kallon farashi kamar yadda muke yi.”
Ta ɗan karkatar da kanta,
“Abu kawai suke so shi ne su samu abin da suke so.”
Mama Sabuwar ta yi shiru tana saurare.
Bintu ta ci gaba, yanzu muryarta cike da excitement,
“Na kuma ga yadda suke tafiya... yadda ake kula da su... guards, drivers, ma’aikata, kowa yana da wanda yake yi masa wani abu.”
Ta ɗan kalli tsakar ɗakin,
“Life ɗin can is just... different.”
Mama Sabuwar ta saki baki tana kallonta,
“Amma ke kin shiga wannan duniyar?”
Bintu ta yi murmushi,
“Na ɗan shiga.”
Ta ɗan yi shiru, sai ta ƙara da murmushi mai ɗan nuna alfahari,
“Kuma Mama... na ji daɗinsa.”
Sai ta ɗan matsa kusa da Mama Sabuwar, kamar wadda take son ta tabbatar ta fahimci abin da take faɗa,
“Mama... da na shiga gidan nan fa, sai na ji kamar na shiga wata duniya daban.”
Mama Sabuwar ta kalleta sosai,
“Gidan?”
Bintu ta gyada kai, murmushi ya fara bayyana a fuskarta,
“Wallahi Mama, gidan ba gida kawai bane... inda kuɗi da iko ke magana ne.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ci gaba da wani irin sha’awa a muryarta,
“Babban gate ne tun daga waje, akwai guards a ko’ina, da ka shiga, sai ka ga garden ɗin nan babba, komai green, komai clean. Motoci kuwa... Mama, motoci ne da sai kin tsaya kina kallonsu.”
Mama Sabuwar ta ɗan buɗe baki.
Bintu ta ci gaba,
“Cikin gidan kuwa? Large lounge ne, sofas masu kyau, chandeliers suna kyalli, curtains masu tsada... komai yana da tsari. Ko ƙasa sai ka ji kamar ba za ka taka da ƙafarka ba.”
Ta yi wata ƙaramar dariya,
“Kuma mutane da suke ciki? Manyan mata ne fa.”
Ta ɗan ɗaga gira, tana kallon Mama Sabuwar,
“Ba irin taronmu na nan bane, mata ne da zaka kalla ka san kuɗi da matsayi suna magana.”
Ta ɗan daga glasses ɗinta,
“Ni ma na shiga cikinsu kamar ɗaya daga cikinsu.”
Sai ta yi wani murmushi mai cike da alfahari,
“Kin gan ni, Mama? Na shiga cikin manyan mata.”
Mama Sabuwar ta kalleta na ƴan seconds, idanunta cike da mamaki.
Bintu kuwa ta sake yin murmushi, kamar har yanzu tana can a cikin wannan duniyar.
—————
Seeyama ta fito tana jan suitcase ɗinta, wadda ta jibga mata uban kaya. Da ta shiga falon, sai ta tarar da Mommy Hauwa zaune a kan sofa, yayin da maid ɗinta ke matsa mata ƙafafu.
Tun da ta dawo da safe, Mommy Hauwa take nan, saboda a cewarta ta gaji, ko sama ba za ta iya hawa ba, komai nan aka kawo mata.
Da ta hango Seeyama, sai ta janye ƙafarta daga hannun maid ɗin ta miƙe tsaye,
“Seeyama! Ina za ki je da wannan uban akwati ɗin?”
Seeyama ta tsaya na ɗan lokaci, ta juyo ta yi mata wani kallo na raini kafin ta amsa cikin ko in kula,
“Zan je gidan su Yaya Zayd.”
Ta ɗan ja suitcase ɗin,
“Zan zauna a can, zan je nayi wa kaina farautar abin da nake so, tunda ke kin kasa yi min.”
Mommy Hauwa ta sauke ajiyar zuciya,
“Seeyama...”
Ta cigaba,
“I’m tired of this argument, I need everything to be proved factually, not logically.”
Sai Mommy Hauwa ta matso kusa da ita, ta kama kafadunta,
“Kin manta Inno gobe za ta zo ne?”
Seeyama ta kalleta ba tare da tayi magana ba.
Mommy Hauwa ta ci gaba da sauri,
“Kuma da ta zo, kin san abin da za ta fara yi, ai na riga na faɗa miki—da na dawo daga can, za ta zo. Yanzu da ta ji na dawo, gobe za ta zo.”
Ta ɗan matse kafadunta,
“Please, daughter, kar ki je yanzu, idan kika tafi can, kuma Inno ta zo Hajja Fatima za ta fahimci cewa na ƙulla wani abu.”
Seeyama ta janye jikinta daga hannunta,
“Ni wallahi, Mommy, sai na je, na gaji.”
Ta ɗan ja suitcase ɗin gaba,
“Itama Innon ai ba ta yi niyyar Zayd ɗin ya aure ni ba, da tana da niyyar haka, da tuni an yi.”
Ta ɗan yi murmushi mai ɗauke da taurin kai,
“Ni kawai zuwa zan yi, idan yana ganina a can akai-akai, watarana zai hakura... ya fara sona.”
Mommy Hauwa ta zuba mata ido,
“Seeyama—”
Amma Seeyama ta riga ta finciki trolley ɗinta,
“Wlh sai na je.”
Ta ja suitcase ɗin da ƙarfi, ta wuce ba tare da ta sake waiwayowa ba.
Mommy Hauwa ta tsaya cak, maid ɗin da ke bayanta ma ta kalli ƙofar da Seeyama ta bi.
Dukansu suka yi shiru, bakinsu a hangame.
Not edited