ZAYD ARMAAN

LOVE WAS’NT ENOUGH

by @jiddaahbarkum


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER FORTY TWO:42*

*LOVE WASN’T ENOUGH*

*JIDDAAH BARKUM*

—————

Washegari da safe...
Inno ta iso garin Kaduna, all the way from Yola, kai tsaye ta nufi Armaan Mansion ba tare da ta tsaya ko ina ba.

Da ta isa, ta sauka daga motar cikin nutsuwa, sannan ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan ya ƙaraso ya ɗauki jakar da ta zo da ita.

A lokacin kuwa, Suhaila da Seeyama suna zaune a lounge, Suhaila tana gyarawa Seeyama gashin kanta, tana ɗan magana da ita lokaci-lokaci, yayin da Seeyama ke zaune cikin nutsuwa.
Sai suka ga ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan ya shigo, ɗauke da jakar Inno a hannu, ita kuma tana biye da shi a baya.

Inno...
Mace ce mai ƙa’ida, mai dokoki, komai nata yana da tsari, tsayyiyar mace ce wadda idan ta yi magana, ba kasafai ake samun wanda zai tsaya yana tambayar me yasa? ba.

Ba ta cikin matan da suke yawan magana, ba ta kuma son hayaniya, kawai kaɗan daga kalamanta ya isa ya sa kowa ya fahimci abin da take nufi.
Ko irin wasan nan na jika da kaka ma, Inno ba ta cika yinsa ba, ba ta raini jikokinta, amma ba ta kuma san wani irin shagwaɓa da ake yi wa jikoki ba.
A wurinta, kowa da matsayinsa, kowa da dokarsa, kowa da abin da ya kamata ya sani.

Saboda haka, duk wanda ya san ta zai iya cewa Inno na daya daga cikin waɗanda suka fi ƙarfi a cikin iyalin Armaan.

Abin mamaki ma shi ne, duk da shekarunta, Allah Ya bata wani irin kyau da ya ƙi barin fuskar da jikinta su ɗauki shekarunta, tsayyar jikinta, nutsuwar tafiyarta da yadda take riƙe kanta yasa duk wanda ya kalleta a karon farko ba zai yi tunanin ita ce mahaifiyar Alhaji Abdulrahman, Alhaji Minzali da Mommy Hauwa ba.

Fuskarta babu alamun gajiya, babu alamun tsufa mai yawa, sai dai wataƙila hakan yana da alaƙa da irin kulawar da take samu da kuma yadda take kula da kanta.

Inno ta ƙaraso cikin lounge a hankali, matakanta ba su da sauri, ba ta shiga da hayaniya ba, kawai ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon wajen.
Idanunta suka zagaya cikin lounge ɗin, kamar wadda yau ce karo na farko da ta shigo, ko da yake ta ɗauki shekaru ba tare da ta zo Kaduna ba.

Inno ba ta cika barin Yola ba, sai idan akwai wani babban dalili, sai dai su kan je can su gaisheta lokaci-lokaci.
Saboda haka, duk lokacin da aka ga Inno ta bayyana a Armaan Mansion ba tare da an sanar da zuwanta ba... akwai dalili, ko dai wani abu ya riga ya faru, ko kuma... wani abu ne yake shirin faruwa.

Da idanunsu suka sauka kan Inno, dukansu suka mike, Seeyama kuwa ba ta nuna wani dogon mamaki ba, tun da ta kwana da sanin cewa Inno na iya zuwa a kowane lokaci.
Suhaila ce dai mamaki ya kama, ba tare da bata lokaci ba, ta kwasa da gudu ta nufi inda Inno take, ta faɗa jikinta ta kankameta sosai,
“Welcome, Granny!”

Ta sake ta, sannan ta kama kafadunta tana murmushi,
“Sannu da zuwa, kin sake fari, kin yi fresh!”
Suhaila ta ɗan yi dariya,
“Wallahi kin yi kyau.”

Inno ta ɗan harareta,
“Toh za ki bani waje na wuce, ko za ki cigaba da surutun? Na gyara tsayuwata.”

Suhaila ta fashe da dariya,
“Wane mutum na tsaida uwar masu gida? Rufamin asiri kar Ummie ta sa min gassss.”
Inno ta yi murmushi kawai tana girgiza kai.

Duk da ba ta cika wasan jika da kaka ba, Suhaila kam ba ta taɓa barin ta haka ko ya ne sai ta tayi.

Seeyama kuwa, tun shigowar Inno take tsaye gefe, a hankali ta matso,
“Sannu da zuwa.”
Ta faɗa tana murmushi.

Inno ta kalleta, sannan ta koma ta zauna a kan kujera,
“Yauwa, nan kika taho kenan?”
Seeyama ta ɗaga kai,
“Eh.”
“Toh, yayi, madallah.”

Sai Suhaila ta yi saurin cewa,
“Bari na maza na faɗawa Ummie, ta zo ta ga wani abin mamaki a falon nan.”
Ba ta jira amsar kowa ba, ta juya da gudu ta nufi stairs.

Sai Inno ta girgiza kai a hankali,
“Wannan yarinyar...”
Seeyama kuwa ta ɗan yi murmushi tana kallonta.

Sai Inno ta ɗago idanunta zuwa kan Seeyama, ta kalle ta daga sama har ƙasa, ba tare da ta ce komai ba.
Daga ƙarshe ta ɗan rage murya,
“Ba dai wani haukan kika zo kina musu a gidan nan ba?”
Seeyama ta ɗan buɗe baki, amma Inno ta kafeta da idanunta.

Ta ɗan gyara zamanta,
“Ki sani, ko da gidan ƴan uwanki ne, toh nan gidansu mijin da kike so ne, kuma yanada kyau ki sani akwai uwarsa a nan.”
Ta kalleta sosai,
“Saboda haka ki dinga kintsa kanki, duk wani lalaci da shagwaɓe-shagwaɓen da kike yi wa uwarki a can , toh a nan gidan, ki ajiye su.”
Ta ɗan dakata,
“Ahto, na dai faɗa miki.”

Seeyama ta turo baki gaba, ta ji maganar ba ta yi mata daɗi ba sam, amma ta san Inno ba irin mutanen da ake musu gardama ba ce, saboda haka ta yi shiru kawai.

Ummie ta sauko daga upstairs, Suhaila na biye da ita a baya, da idanunta suka sauka kan Inno, sai ta tsaya cak, baki ta ya ɗan buɗe cikin tsantsar mamaki da farin ciki, sabida ko jiya da dare sun yi waya, Inno ba ta gaya mata cewa za ta zo ba, da a ce ta sani, da tuni ta shirya komai tun kafin saukarta.

Ummie ta ƙarasa kusa da ita, sannan ta risina a gabanta cikin matuƙar girmamawa, tana murmushi,
“Barka da zuwa, Hajiya Inno, an zo lafiya?”
Inno ta amsa mata da murmushi,
“Alhamdulillah.”
“Ya muka same ku?”
“Lafiya kalau, Alhamdulillah.”

Ummie ta gyada kai, kafin ta ɗan kalleta da murmushi,
“Amma baki sanar da ni za ki zo ba, da yanzu an riga an haɗa miki abincinki na musamman, musamman da na san ba komai kike ci ba.”
Inno ta ɗan yi dariya,
“Haba, Hajja Fati, idan zan zo sai na sanar da ke kamar wata baƙuwa? Wane irin shiri kuma za a yi min na daban saboda zan zo?”
Ta girgiza kai,
“A’a wallahi, duk na hutar da ku.”

Ummie ta yi murmushi,
“Ai ba abun wahala ba ne, Hajiya,” ta ɗan dakata, sannan ta mike a hankali,
“ko da yake dai, ko yaya ne... bari na je na samo miki wani abu da za ki ci.”
Ba ta jira Inno ta amsa ba, kai tsaye ta nufi kitchen.

Inno ta bita da kallo, idanunta suka bi Ummie har sai da ta ɓace daga lounge ɗin.
A zuciyarta kuwa, ta ji wani irin daɗi, domin Ummie tun kafin ta zama matar danta, tana girmama Inno sosai, bayan aurenta ma, girmamawar ta ƙara zurfi.
Har yanzu Ummie ta na matukar yi mata ladabi da biyayya tun lokacin yana raye, shiyasa itama ba taɓa ɗaukar ta matsayin matar ɗan ta ba, ya ta dauketa sabida duk inda take, ladabinta gare ta ba ya canzawa.

Yanzu da ya rasu... haka nan Ummie ta ci gaba da riƙe wannan girmamawar, ba don yana nan yana gani ba, ba don wani zai yaba mata ba, sai don kawai ta ɗauki Inno a matsayin uwar mijinta, wadda darajarta ba ta ƙare da mutuwar mijinta ba.

Inno ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ta kalli hanyar kitchen ɗin da Ummie ta bi, sai ta ɗan murmusa,
“Allah ya ƙara miki daraja, Hajja Fati...”
Ta furta a hankali.

Suhaila dake tsaye gefe ta ji maganar, sai ta ɗan yi murmushi, ta san Inno tana da tsauri, amma duk wanda ya san Inno sosai ya san abu ɗaya, Ummie tana da matsayi na musamman a zuciyarta.

—————

*MALALI*

Kamar yadda Haris ya faɗa mata, Raihana ta sanar da Baffa tun da sassafe, bayan sun gaisa, Baffa ya saurare ta cikin nutsuwa, sannan ya amsa mata da cewa ya ji.

Daga baya ya sanar da ita cewa ta gaya masa cewa yana jiransu zuwa bayan La’asar, saboda haka, da rana ta ja... Baffa yana zaune a kan tabarmar da aka shimfiɗa a tsakar gida, yana cikin nutsuwa.

Sai Yaya Hamza ya fito ya ƙaraso gabansa,
“Baffa...”
Baffa ya ɗago kai,
“Hm?”
“Haris ne yake son magana da kai.”

Baffa ya ɗan tsaya, sai ya mike daga kan tabarmar, yana gyara babbar rigarsa a hankali, ya kalli Yaya Hamza,
“Da ka shigo da su falona mana, abin da nake jira kenan.”
Yaya Hamza ya gyada kai,
“Toh, Baffa.”
Ya juya ya yi gaba, Baffa kuma ya biyo bayansa.

Suna isa bakin ƙofar gidan, sai suka tarar da Haris tsaye shi kaɗai a jikin motarsa, Baffa ya tsaya, idanunsa suka sauka kan Haris.

A fili ya yi tsammanin zai ga shi tare da iyayensa, musamman da yake maganar zuwan nasu ce, Haris kuwa da ya hango Baffa, nan take ya cire jikinsa daga jikin motar, ya gyara tsayuwarsa.

Baffa ya ɗan ƙara kallonsa, yana nazarin abin da ya kawo shi kaɗai, Haris ya ƙaraso gare shi cikin matuƙar girmamawa.
Da ya isa gabansa, sai ya durƙusa a hankali ya gaida shi,
“Assalamu alaikum, Baffa.”
“Wa alaikumus salam.”
Baffa ya amsa cikin nutsuwa.

Ya ɗan kalli fuskarsa, daga fuskar sa dai akwai abin da yake son faɗa,
“Bismillah, shigo ciki.”
Ya juya ya fara tafiya.

Haris bai ce komai ba, kawai ya bi shi, kai tsaye Baffa ya jagorance shi har zuwa falonsa.

Ya shiga ya zauna, sannan ya nuna masa ɗaya daga cikin kujerun,
“Zauna.”
Haris ya ɗan kalli kujerar, sai ya girgiza kai a hankali,
“Nan ma ya isa Baffa.”
Ya zauna a ƙasa, ya durƙusa yana sunkuyar da kansa cikin ladabi.

Baffa ya ɗan kalle shi, bai yi magana nan take ba, kawai ya yi shiru yana nazarin Haris ɗin, yadda ya zo shi kaɗai, yadda yake zaune a ƙasa, da kuma wannan irin nutsuwar da ke fuskarsa wadda ke nuna cewa ba zuwan gaisuwa kawai ya kawo shi ba.

Baffa ya ɗan gyara zamansa amma dai bai ce komai ba.

Haris ya ɗago idanunsa a hankali,
“Baffa...” sai kuma ya runtse idanunsa na ƴan daƙiƙu, ya yi wani irin dogon numfashi, kamar yana ƙoƙarin tara courage ɗin da zai ba shi damar furta abin da ya zo da shi.

Sai ya ɗago idanunsa zuwa kan Baffa,
“Baffa...” muryarsa ta fito a hankali,
“Na maka laifi.”

Baffa bai ce komai ba, kawai ya zuba masa ido.

Haris ya sunkuyar da kansa,
“Abubuwan da na taɓa faɗa muku a baya game da kaina... ba gaskiya ba ne,” ya ɗan ja numfashi,
“inda na ce nan ne gidanmu... ba nan ba ne,” ya ɗaga idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya sake sunkuyar da su,
“inda na ce nan nake aiki... ba nan nake aiki ba.”

Ya yi shiru,
“da sauran abubuwan da na faɗa muku game da kaina...” muryarsa ta fara rauni,
“ba gaskiya ba ne.”

Baffa bai motsa ba, fuskarsa ta kasance babu wani sauyi.

Haris ya haɗe hannayensa,
“Baffa, akwai dalilin da ya sa na faɗi haka,” ya ɗan yi shiru,
“amma... ba zan iya faɗa muku dalilin ba,” ya sauke idanunsa,
“ba don bana son faɗa muku ba,” ya ɗan ja numfashi,
“amma saboda akwai wasu abubuwa da ba na da ikon tona su.”

Shiru ya sake ratsa falon, Haris ya ɗan goge tafin hannunsa da ɗayan, kamar damuwar da ke jikinsa ta fara bayyana,
“Na san yanzu ba za ku ƙara yarda da ni ba,” muryarsa ta cika da nadama,
“kuma gaskiya... ba zan zarge ku ba,” ya ɗago kai,
“amma dan Allah, Baffa...” ya ɗan dakata,
“ku bani dama.”

Baffa ya ɗan karkatar da kansa, Haris ya ci gaba,
“Bani dama ta biyu,” ya haɗiye yawu,
“zan gabatar da kaina da dukkan gaskiya, ba zan sake ɓoye komai ba,” ya ɗan yi shiru,
“dan Allah, Baffa,” muryarsa ta fara rawa,
“ban ji zan iya ci gaba da rufe wannan maganar ba.”

Ya ɗaga idanunsa zuwa kan Baffa,
“saboda amincewar da kuka bani, da yadda kuka karɓe ni, da yadda kuka ba ni damar kusantar iyalinku...” ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya sauke kansa,
“ba na jin ya dace in ci gaba da yi muku ƙarya.”

Baffa ya ci gaba da kallonsa, har yanzu babu wata magana.

Haris ya lumshe idanunsa, sai ya furta kalmar da ta fi sauran nauyi,
“Baffa...” muryarsa ta sauya,
“wallahi ina son Raihana,” ya ɗan yi shiru, kamar kalmar kanta ta fito daga cikin zuciyarsa,
“ina matuƙar sonta.”

Ya ɗaga kai,
“ban zo nan yau saboda naji tsoron abin da za ku ce ba, na zo ne saboda bana son in rasa ta saboda ƙaryar da na fara tun farko,” hawaye ya yi ƙoƙarin taruwa a idanunsa, amma ya yi saurin runtse su,
“dan Allah, Baffa...” ya ɗan matsa hannayensa, muryarsa ta karye kaɗan,
“kar ku raba ni da ita.”

Ya danyi shiru,
“idan kun ga na yi laifi, ku hukunta ni, idan kun ga ban cancanci amincewarku ba, zan fahimta, amma...” ya ɗago idanunsa,
“ku bani damar gyara abin da na ɓata, ku bani damar nuna muku wanda ni ne da gaske.”

Ya yi shiru, Baffa kuwa har yanzu yana zaune yana kallonsa, ba tambaya, ba zagi, ba mamaki, kawai idanunsa ne suke kan Haris, kamar yana ƙoƙarin karanta abin da ke bayan kalamansa.

Haris ya sunkuyar da kansa, a wannan karon bai ƙara cewa komai ba, ya bar falon cikin wani irin shiru mai nauyi.

Baffa ya ɗan ɗaga gira, sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali,
“Hmm...” kawai ya furta.

Amma bai ce ya yarda da shi ba, bai ce ya ƙi yarda da shi ba, kawai ya ci gaba da kallon Haris, kamar akwai tambayoyi da yawa da suke yawo a cikin kansa, kuma wannan... ba ƙaramin bayani ba ne da za a yanke hukunci a kansa cikin mintuna kaɗan.

Shiru ya cigaba da ratsa falon na ɗan lokaci, idanunsa har yanzu suna kan Haris, ya ga nadamar da ke fuskarsa, ya ji yadda muryarsa ta canza, ya kuma fahimci cewa wannan ba maganar da Haris ya zo ya faɗa cikin sauƙi ba ce.

Sai ya ɗan karkata jikinsa a kan kujerar,
“Haris...” muryarsa ta fito cikin nutsuwa.

Haris ya ɗago kai,
“Na ji abin da ka faɗa,” ya ɗan yi shiru,
“kuma na yaba da yadda ka zo ka faɗa min gaskiya yanzu, maimakon ka ci gaba da rufe abin da ka fara.”

Haris ya sauke numfashi, amma Baffa bai gama ba,
“amma akwai abu ɗaya da ya kamata ka fahimta,” ya ɗan matsa gaba,
“maganar da kake so na yanke ba ƙaramin abu ba ce.”

Haris ya yi shiru,
“ba wai ina ba ka amanar ɗiyata ne kawai ba,” Baffa ya ɗaga idanunsa,
“ina ba ka amanar rayuwarta ne.”

Haris ya sunkuyar da kai,
“ka ce ka yi ƙarya saboda wani dalili, ban damu da jin dalilin ba,” Haris ya ɗago kai kaɗan.

Baffa ya ci gaba cikin nutsuwa,
“ba don bana son sani ba, amma saboda ko menene dalilin da ya sa ka yi ƙaryar farko, gaskiyar ita ce... ka yi ƙaryar.”

Shiru ya ratsa falon, Baffa ya sauke ajiyar zuciya,
“yanzu ka zo kana cewa in yarda da kai,” ya ɗan girgiza kai,
“ta yaya zan tabbatar wa kaina cewa wannan karon ba wata ƙaryar ba ce?”

Haris ya buɗe baki, amma Baffa ya ɗaga masa hannu a hankali,
“Bari na gama.”
Haris ya sake yin shiru.

“Yau ka ce min inda kake zaune ba gaskiya ba ne, ka ce aikin da ka faɗa min ba gaskiya ba ne, ka ce akwai abubuwan da ka ɓoye min,” Baffa ya kalle shi sosai,
“to me zai hana gobe ka sake zuwa min da wata gaskiyar da ba ita ce gaskiyar ba?”

Haris ya sauke idanunsa,
“ni ba na cewa kai mugun mutum ne,” Baffa ya faɗa a hankali,
“ba na cewa ba ka son Raihana, har ma daga yadda kake magana, na fahimci kana sonta,” ya ɗan dakata,
“amma soyayya kaɗai ba ta isa ta gina gida ba.”

Haris ya runtse idanunsa,
“akwai amana, akwai gaskiya, akwai kwanciyar hankali, idan ɗaya daga cikin waɗannan ya ɓace tun kafin a fara...” ya girgiza kai,
“yana da wuya a ce komai zai kasance lafiya.”

Haris ya ɗan matsa hannunsa,
“Baffa, dan Allah—”
Baffa ya kalle shi,
“Na ji ka,” muryarsa ba ta ɗaga ba,
“amma amsata ita ce A’AH.”

Haris ya daskare, Baffa ya ci gaba,
“ba zan ba ka Raihana ba.”

Kalaman suka sauka a tsakanin su da wani irin nauyi, Haris ya kalli Baffa kamar bai yi tsammanin wannan hukuncin ba, Baffa kuwa ya zauna cikin nutsuwa,
“ba saboda ban yarda kana sonta ba, ba saboda na ƙi ka ba, amma saboda a yanzu...” ya ɗan ja numfashi,
“ban yarda da kai ba.”

Haris ya sunkuyar da kansa, Baffa ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa,
“wataƙila wata rana abubuwa su canza, wataƙila ka samu damar nuna min cewa wannan gaskiyar da ka zo da ita yau ita ce ta ƙarshe, amma yau...” ya girgiza kai a hankali,
“ba zan iya saka Raihana a wannan haɗarin ba.”

Haris ya haɗiye yawu,
“Baffa...”
“Na san za ka ji zafi,” Baffa ya faɗa cikin sanyin murya,
“amma ni mahaifinta ne, dole ne in fi tunanin abin da zai faru da ita fiye da abin da zuciyarka take so yanzu.”

Ya ɗan kalli Haris,
“Ka ce kana sonta?”
Haris ya gyada kai a hankali,
“Ka tabbatar min da hakan da gaskiya, ba da kalamai ba, lokaci zai nuna.”

Baffa ya ɗan jingina da kujerarsa,
“amma a yanzu...” ya sauke idanunsa daga kan Haris,
“ka tafi.”

Haris ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, kamar kalmar “a’a” ɗin ta fi duk abin da ya ji nauyi, sai ya ɗaga kansa a hankali, ya gyada kai,
“Toh, Baffa.”

Ya yi ƙoƙarin miƙewa, amma kamar wanda jiri za kwashe, ya dan dafe ƙasa kafin kuma ya mike gabadaya, sai ya juya ya nufi ƙofar.

Baffa ya bishi da kallo, fuskarsa cike da natsuwa.





Not edited