THE SECOND TIER
by @maryam730
Nuna musu hanya yayi alamar su tafi,shiga gaba su kayi yana binsu a baya kamar mai tsoron kar su gudu.Wata ƙatuwar ƙofa ce a gurin ta azurfa ba kamar ta farko da take ta baƙin ƙarfe,sai sheƙi ta ke tana ɗaukan ido.
Nuna musu ƙofar yayi alamar su shiga,suna shiga wasu ɗirka-ɗirkan body-guards suka tsare su,sai da nan ma aka bincike su tsaf tukuna aka bar su suka shiga.
Second TIER daban take dan wannan gaba ɗaya manya- manyan mutane ne a gurin (kama daga mashahuren ƴan siyasa da manyan tycoons )gaba ɗayan su fuskarsu babu alamar rahama ko tausayi,ran mutum ba'a bakin komai yake ba a gurin su.
Tunda Maleeka da Ramlah suka gane wannan gurin yafi wancan hatsari suka ƙara kame kansu.
Ramlah ce ta kalli Maleeka tace
"Ni bari in tafi".
Saboda abinda za suyi serving daban-daban ne,gyaɗa kai Maleeka tayi tana cewa
"Ki kula da kanki".
Murmushin ƙarfin hali Ramlah tayi tana cewa "tooooh".Maleeka na juyawa itama ta nufi inda nata aikin yake .
Ƙamewa Ramlah tayi a bakin part ɗin data shiga sakamakon ganin yadda wani a gurin ya haiƙewa wata,tuni jikin ta ya ɗauki rawa kamar mazari, kuma abint takaicin ba wanda ya damu duk da dukkansu manyan mutane ne.
Hankalin ta bai gama tashi ba sai da ta fuskanci gaba ɗaya nan safarar cocaine, manya-manyan makamai,bindigogi da sauransu ake.
Haɗiye kukanta tayi tana nufar inda deserts suke ta fara rabawa.
Bayan wasu ƴan mintuna kachar-kachar ƙarar sarƙar kafar ta cike gurin kafin mamallakiyar ta bayyana.Wata zabgegiyar mace ce tasha shigar alfarma, sai baza ƙamshi take, amma sai dai kashh fuskar ta a rufe take tsaf ko kwayar idon ta ba'a gani.
HAJJAJU shine sunan da wani ya kirata dashi,wata kujera ta alfarma ta nema ta zauna,kafin wasu mata su goma suka shigo yaran HAJJAJU kenan,suma duka fuskar su rufe da baƙin ƙyalle.
Wata a cikinsu ta fito ita ɓakin ƙyallen fuskar ta haɗe da fari yake alamar tana da babban matsayi,ɗaga murya tayi tana cewa "yanxu za'a fara BIDDING",nan da nan mutane suka fara dawowa kujerun gaba da aka jera su reras dan wannan,ba ɓata lokaci matan suka fara raba musu wasu ƴan ƙananan kwalaye da mariƙi a jikin sa sai number a jiki.
Tsit gurin yayi,kafin kuma gurin ya ɗauki ƙiiiiiiiii ƙarar ana jan ƙarfe a ƙasa.Wasu mata ne samudawa ɗirka-ɗirka dasu suka taho su uku a gaba suna jan wani ƙaton abu wanda za'a fi kiranshi da keji lulluɓe da katon baƙin ƙyalle,kowanni bangare mutum uku na riqe da igiyar susu sha biyu kenan.
Sai da suka kawo shi tsakiya suna durƙusar da kansu da barin gurin alamar aikin su ya gama.
Wacce ta fito dazu ce ta ƙara fitowa,hannu tasa ta yaye wannan baƙin abin da ya rufe kejin,nan da nan ƴan matan da ke ciki suka saka ihu suna kuka.
Wata tsawa yarinyar ta daka musu nan da nan su kayi shiru.
Magana yarinya ta fara kamar haka,"za'a fara fito dasu ɗaya bayan ɗaya kowacce da farashin ta".
Wata ƙatuwar baƙar tuta ta ɗaga a hannun ta alamar an fara.Waenda suka shigo tare ne suka zo suka buɗe ƙwadon da aka rufe cagin dashi,nan da nan suka fara turmutsetseniya kamar kajin da aka zo ɗaukar ɗaya a cikin su suna haɗe kansu gurin ɗaya a lungu.
Da ƙyar aka samu aka finciko wata,doguwa ɓaƙa bata da kyau na fuska sai na jiki kamar ita tayi kanta komai yaji.
Matar wacce take host ɗin taron tace "Wannan bata da biyayya sai taurin kai amma akwai kayan aiki dan haka za'a fara wannan daga kan miliyan biyar".
Wani ne ya ɗaga kwalinsa yana cewa miliyan biyar,nan da nan wata ta ɗaga miliyan 6,haka wani ma ya ɗaga miliyan 10.
Tunda mai miliyan goma ya faɗa wani bai ƙara faɗa ba,host ɗince ta ƙara maimaita miliyan goma alamar babu wani,jin shiru yasa ta ɗaga tutar ta sama tana cewa an siyar da ita ga number 154.
Fitowa yayi da suitcase ya buɗe maƙudan kudaɗe ne maƙil a ciki.
Sauran yaran da suka shigo tare ne suka karɓa suka fara ƙirgawa,dake daloli ne sharp-sharp suka ƙirga bayan sun ga ya cika.
Haka mutumin yasa hannu ya fara jan yarinyar sai kuka take tana tirjewa da ƙyar ya ɗauke ta suka fice.
Haka aka cigaba da BIDDING ɗin har aka gama gaba ɗaya.
Kowa ya tarwatse yaran HAJJAJU suka hau layi ita ce a gaba sai su a baya niqi-niqi da mahaukatan kuɗaɗen da suka tara
Ramlah ce rakuɓe a gefe sai kuka take kamar ranta zai fita.Ganin kowa ya koma sha'anin sa yasa ta tashi tana share hawaye ta ta cigaba da aikin ta.
Wucewa tazo yi ta wani babban tebur, wainnan da ka kallesu ba abinda zai hana ka kira da ƴan ta'adda.Kiran ta babba cikin su yayi da hannun.
Nuna kanta tayi alamar ni,gyaɗa kai yayi,zuwa tayi tana durƙusawa kanta ƙasa har taune harshe take wajen faɗar "sir me za'a kawo ma".
komai ya ce mata yana mata wani matsiyacin kallo,daa sauri ta bar gurin ta je kan in da deserts ke jere ta ɗakko wani ɗan bowl me girma kusan komai akwai a ciki.
Sai da tazo wannan karan ta lura da irin manya manyan bindigogin dake kan table ɗin da kuɗaɗe alamar dai safar bindigo ake a gurin.
Wanda suke zaune alamar sune masu bindigogin ne ya ɗakko mai wata ƙarama yana cewa "Yallaɓai wannan bata da nauyi gashi duk tazara sai ta tarwatsa kan mutum ,kuma bata ƙara".
Karɓa yayi idonsa na kan Ramlah yace "Really?".Ƙara tabbatar mai yayi sai zubo bayani yake.
Kallon bindigar yayi kafin ya kalli Ramlah hannun ta ya kama ya fara janta,sai da suka kai chan ƙarshen gurin,kafin ya tsaya.
Tuni jikin ta ya fara rawa yayi sanyi ƙau,hannun sa yasa ya karɓi bowl ɗin ya ɗora a kanta,ba tsammani kawai taga ya sai ta da bindigar,tuni ta fashe da wani kuka mai cin rai.
Hannu sa ya ɗaura akan baki alamar tayi shiru yana cewa
"Bawani abu zan miki ba gwada ƙwarewa ta zanyi da kuma tabbatar da abinda aka faɗa akan bindigar gaskiya ne.In kina da sa'a bowl ɗin zan tarwatsa...,amma in baki da ita....shiru yayi yana sakin wani murmushi mugunta yayi ƙasa da muryar sa yana matso da bakin sa saitin kunnen ta cikin wata dangerous voice yace KANKI NE ZAI TARWATSE...... end of chapter 16....written by muraima Naabba ✍️✍️✍️