THE TURNING POINT
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER FORTY FOUR:44*
*THE TURNING POINT*
*JIDDAAH BARKUM*
———————-
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar,
ƙofar ta buɗe,
Zayd ya shiga.
A falon kuwa mutane ne zaune,
Inno, Ummie, Seeyama, Suhaila, har ma da Mommy Hauwa.
Kusan lokaci guda, kowa ya ɗago kai,
idanuwansu suka sauka kansa,
babu wanda ya yi tsammanin ganinsa a wannan lokacin.
Zayd ya tsaya na ɗan lokaci a bakin ƙofar,
amma kafin ya kalli kowa sosai, idanunsa suka fara neman mutum ɗaya,
Ummie.
A gefe guda kuma…
Seeyama ta zuba masa ido, zuciyarta ta fara bugawa da wani irin mahaukacin sauri,
wani abu ya matse mata ƙirji.
Soyayyar da take masa…
da kuma kishin da har yanzu take ji duk lokacin da ta tuna da Felicia,
kamar brain ɗinta ya zaɓi lokaci mafi muni da zai tuna mata da hotunan da ta gani.
Felicia tana rungume da Zayd,
tana dariya,
tana manne da shi,
tana manna masa peck a kumatu.
Seeyama ta ɗan ja tsaki a hankali,
ta ɗauke idanunta daga kansa.
Amma Zayd… hankalinsa bai ma kai gare ta ba, ko ɗaya.
Idanunsa suka sauka kai tsaye kan Ummie, wadda ke zaune kusa da Inno tana ɗan gyara mata nails.
Ummie kuwa sarai ta ji shigowarsa,
ta ji motsin ƙofar, ta kuma san sautin takun sawunsa,
amma da ta ɗago kai… idanunta suka sauka kansa na ɗan lokaci,
kawai na ɗan lokaci, sai ta maida kanta kan abin da take yi,
kamar bai shigo ba, kamar ba ta gan shi ba.
Wannan ne ya fi komai daskarar da gwiwar Zayd.
Ya tsaya cak, kamar kalaman Ummie na daren jiya sun dawo masa a lokaci guda.
Ya yi tsammanin ko da kuwa tana fushi ne… za ta kalle shi, za ta ce wani abu, ko ta nuna masa cewa ta ji daɗin ganinsa.
Amma ba komai.
Zayd ya haɗiye yawu, gabansa ya sake faɗuwa.
A hankali ya ɗauki wani mataki zuwa cikin falon,
amma idanunsa har yanzu suna kan Ummie.
Inno ta buɗe baki tana kallonsa,
“Kai, kuma daga ina da daren nan? Kamar dai wanda aka kore ka daga inda kake?”
Ta dan sake kallon fuskarsa ta da dan rame na yini daya.
“ A ka ce sai ka yi kusan sati guda a can inda kake,”
ta sake kallonsa daga sama har kasa, “ji yanda kayi wani zuru zuru kamar mai fama da amai da gudawa kalau kake kuwa Ahmad?”
Ta ɗan yi murmushi, tana kallonsa daga sama har ƙasa,
“ba dai jin da kika yi nazo ne ya sa ka bar duk abin da kake ka dawo ba?”
Suhaila ta fashe da dariya,
“Toh yanzu sai ya bar duk uzurinsa saboda kin zo, Inno?”
Inno ta zabga mata harara,
“Toh ba gashi ba dai ya dawo?”
Ta sake kallon Zayd, tana ɗan girgiza kai.
Zayd kuwa bai damu da tsokanar da take masa ba,
a hankali ya ƙarasa gabansu, sai ya ɗan zube kan gwiwowinsa, ya fara da gaishe da Inno cikin girmamawa.
“Barka da dare.”
“Barka ka dai.”
Inno ta amsa masa tana kallonsa da murmushi.
Zayd bai ƙara cewa komai ba,
kai tsaye ya juya wajen Mommy Hauwa.
Tun shigowarsa take kallonsa, idanunta suna yawo tsakanin shi da uwarsa,
tana nazarin yanayin da ke tsakaninsu, saboda ta san sarai… ba haka suke ba.
Ko a gaban waye ne, Zayd baya jin kunyar zuwa wajen uwarsa,
itama Ummie ba ta taɓa ɓoye irin kulawar da take masa ba.
Amma yau… akwai wani abu daban.
Gaisuwar da Zayd ya jefo mata ta katse mata tunanin,
“Barka da dare, Mommy.”
“Yauwa welcome son.”
Ta amsa a hankali, idanunta har yanzu a kansa,
“Lafiya dai??”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Lafiya.”
Ya haɗiye yawu, sai ya ɗan kalli Mommy Hauwa kafin ya juya.
A hankali ya ƙarasa wajen Ummie.
Ummie kuwa tana zaune kusa da Inno, hannunta a kan nail care set din tana maida su yanda suke.
Zayd ya durƙusa gabanta, ya kamo hannunta cikin girmamawa,
“Assalamu alaikum, Ummie.”
“Wa alaikumus salam.”
Muryarta ta fito a sanyaye.
Zayd ya ɗan sunkuyar da kansa, sai ya sumbaci hannunta a hankali.
Ko da yake fushin da take yi bai ɓoye ba… a cikin zuciyarta, ta ji daɗin ganinsa, ya dawo, abin da ta fi so kenan tun daren jiya,
amma ba za ta bari ya gane hakan da wuri ba.
Sai kawai ta ɗaga ɗayan hannunta ta shafa kansa kamar yadda ta saba yi a duk lokacin da suka yi wannan musabahar.
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, wani irin ajiyar zuciya ya kuɓuce masa,
kamar duk nauyin da ya ɗauko daga New York ya ɗan sauka masa daga ƙirji.
Ya ɗan ɗaga kai ya kalleta,
amma Ummie ta riga ta maida hannunta, fuskarta har yanzu babu murmushi.
Zayd ya yi shiru, aƙalla… taɓa kansa, kuma a wannan lokacin, hakan ya ishe shi.
Inno ma ta ɗan kalli Ummie, sannan ta mayar da idanunta kan Zayd, a fili ta lura da cewa akwai wani abu da ba ta saba gani ba,
ta ɗan fuskanci akwai dai abin da ya faru, domin ganin yadda Ummie ta yi watsi da Zayd haka, ba ƙaramin sabon abu ba ne a gare ta.
Seeyama da Suhaila kuwa sun san komai,
sun san abin da ya faru, amma babu ɗayansu da ya ce komai,
kawai suka baza ido suna kallon Ummie da Zayd, suna jiran ganin abin da zai biyo baya.
Inno ce ta katse wannan shirun,
ta kalli Zayd ɗin da har yanzu yake durƙushe a gaban Ummie,
“Ahmad…” muryarta ta fito cikin nutsuwa,
“ka sha hanya, ga dare, ka ƙarasa ɗakinka mana ka ɗan huta.”
Zayd ya ɗan ɗago kai,
sai ta maida kallonta ya koma kan Seeyama,
“ki tashi ki ɗan samo masa wani abu da zai ci,”
ta sake kallon Zayd daga sama har ƙasa,
“daga ganin sa, ba wani abin kirki yake ci ba, ni dai duk sai na ga ya ƙare ma a idanuna.”
Suhaila ta danyi murmushi, inno na son tsokanar Zayd duk da bata wasa da kowa amma a kan Zayd tana dan yi kadan.
Seeyama kuwa ta dan mike a hankali,
“Okay, Inno.”
Amma kafin ta wuce, idanunta suka sake komawa kan Zayd.
Shi kuwa ya ɗan sauke ajiyar zuciya,
a wannan lokacin ne kawai ya fahimci cewa Inno ta lura da yanayin da yake ciki.
Sai ya kalli Ummie na ɗan lokaci,
amma ita har yanzu hankalinta yana kan abinda ke gabanta.
Zayd ya ɗan haɗiye yawu, ya mike a hankali.
“Okay, Inno,” sai ya ɗan sunkuyar da kansa cikin ladabi,
“Good night.”
Inno ta ɗaga masa kai,
“Allah ya bamu alkhairi.”
Zayd ya juya a hankali ya nufi hanyar stairs,
Suhaila da Mommy Hauwa suka bi shi da kallo.
———————
*MALALI*
Bayan an idar da sallar Isha’i, Baffa ya nufi ɗakin Umma.
Da ya shiga, sai ya tarar da ita zaune a inda ta yi sallar, ba ta tashi ba tukuna, Qur’ani ne a hannunta, tana karatun wasu ayoyi cikin nutsuwa.
Baffa bai katse ta ba,
ya ƙaraso cikin shiru, ya nemi kujera ya zauna a kusa da ita,
kawai ya zauna yana jiran ta gama.
Umma ta ci gaba da karatunta har ta kai ƙarshen ayar da take kai,
sai ta rufe Qur’anin a hankali, ta ɗora shi gefe, sannan ta ɗago kai ta kalli Baffa.
“Sannu da shigowa.”
Baffa ya ɗan gyara zamansa,
“Yauwa.”
Ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, kamar yana tsara kalaman da zai faɗa,
sai ya kalli Umma,
“Ki kira min Raihana.”
Umma ta ɗan kalleshi na ƴan seconds, ta ɗan gyada kai, kafin ta miƙe.
Ta nufi ɗakin Raihana.
Bayan ɗan lokaci kaɗan, Raihana ta fito tare da ita,
da ta shiga ɗakin ta hango Baffa zaune, sai ta ƙaraso ta zauna.
Umma ma ta dawo ta zauna a gefensu.
Baffa ya kalli Raihana,
kallonsa ya kasance cikin natsuwa, amma akwai wani abu a cikin idanunsa da ya sa zuciyar Raihana yin wani mahaukacin tsalle.
“Raihana…”
“Na’am, Baffa.”
Baffa ya ɗan yi shiru,
“kin san na kira ki ne saboda maganar Haris.”
Zuciyar Raihana ta buga da sauri, ta sunkuyar da kanta kaɗan.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya,
“na san kin riga kin fara tunanin yadda komai zai kasance.”
Raihana ta ɗago idanunta.
“Amma akwai abu ɗaya da nake son ki fahimta,”
ya ɗan dakata,
“wani lokaci, abin da muke so ba shi ne abin da ya fi dacewa da mu ba.”
Raihana ta fara jin wani irin nauyi a ƙirjinta,
Umma kuwa ta kalli Baffa, ta lura da yadda muryarsa ta sauya.
Baffa ya ci gaba,
“na yi tunani sosai, na saurari abin da ya kamata na saurara, na kuma duba abin da zai iya zama alheri gare ki,”
ya ɗan yi shiru, sai ya kalli Raihana kai tsaye.
“Saboda haka…” muryarsa ta yi sanyi,
“na fasa ba da auranki ga Haris.”
Raihana ta daskare,
kamar kalaman sun sauka mata ne ba tare da ta shirya ba.
Idanunta suka sauka ƙasa, ba ta ce komai ba,
kawai yatsun hannunta suka fara murɗewa a hankali cikin cinyarta.
Umma ma ta yi shiru,
a fili ta nuna mamaki, amma ba ta tambayi Baffa komai ba,
ta kalli Raihana kawai.
Raihana ta haɗiye wani irin yawu mai nauyi,
a zuciyarta kuwa, kalmar “na fasa” ta maimaita kanta sau da yawa.
Haris, aure, duk abin da ta yi tunani a kai tun safe…
yanzu kamar an kwashe shi ne gaba ɗaya daga gabanta.
Ta ji wani irin zafi ya taso mata a ƙirji,
amma ba ta iya cewa komai ba,
ba za ta iya zama a gaban Baffa tana tambayar sa me ya sa? ba.
Baffa ne, mahaifinta, wanda maganarsa ba ta saba yi wa gardama ba.
Saboda haka kawai ta sunkuyar da kai.
Baffa ya ɗan sunkuyar da kansa,
“Raihana,” muryarsa ta kasance mai laushi, amma babu damar gardama a cikinta,
“ki amince da ni.”
Ta haɗiye yawu,
Baffa ya ɗan matsa kusa da ita,
“na san za ki ji zafi, na san wataƙila ba wannan amsar kika yi tsammani ba,
amma ina son ki fahimci abu ɗaya…” ya ɗan dafa kanta,
“duk abin da nake yi, saboda ina son in ga kin samu rayuwar da za ta zama alheri a gare ki.”
Raihana ta sunkuyar da kanta, idanunta suka fara cika da hawaye.
Umma ta kalleta, zuciyarta ta yi nauyi,
amma ba ta tambayi Baffa dalilin da ya sa ya canza hukuncinsa ba,
ta san Baffa, ta san idan yana son ta san dalilin, zai gaya mata da kansa idan lokacin ya yi.
Saboda haka ta yi shiru.
Baffa ya kalli Raihana,
“ki yi haƙuri kinji.”
Raihana ta goge gefen idonta da sauri, sai ta gyada kai.
“Toh Baffa…” muryarta ta fito ƙasa-ƙasa.
Baffa ya ɗan gyada kai,
“Allah ya zaɓa miki mafi alheri.”
Sai ɗakin ya sake yin shiru,
Umma ta ɗan kalli Baffa, a idanunta akwai tambaya mai yawa,
amma ba ta furta ko ɗaya daga cikinsu ba.
Baffa ya ɗan yi shiru, yana kallon yadda Raihana ta sunkuyar da kanta,
sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali,
“ki tashi ki je, Allah Ya yi miki albarka.”
Raihana ta ɗaga idanunta a hankali,
“Amin, Baffa.”
Ta miƙe cikin nutsuwa, sannan ta ɗan kalli Umma kafin ta sunkuyar da kai,
sannan ta juya.
A hankali ta nufi ƙofar ɗakin,
Baffa da Umma suka bita da kallo, ba wanda ya ce komai,
kawai suka kalli bayanta har ta fice daga ɗakin.
Raihana ta bar falon cikin nutsuwa,
amma da ta isa ƙofar ɗakinta, sai ta buɗe ta shiga a hankali,
ta rufe ƙofar bayanta, sai a nan… ta tsaya cak.
Ta lumshe idanunta, ta yi ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata maƙogwaro,
amma zuciyarta ta kasa yin shiru,
kawai sai ta dafe kirjinta ta fashe da kuka…
——————
*ARMAAN MANSION*
A Armaan Mansion kuwa, ƙarfe 11:45 na dare.
Zayd yana kwance a kan gadonsa, amma duk ƙoƙarinsa na samun barci ya ci tura.
Bai iya rufe idanunsa na wasu seconds ba tare da fuskar Ummie ta dawo masa a rai ba.
Yadda ta yi watsi da shi,
yadda ta yi kamar ba ta gan shi ba,
yanda tayi kamar dawowar shi ma batada wani mahimmanci,
har gaisuwar da ya je mata da dukkan girmamawa ta kasa kallonsa a yadda ta saba.
Ya sake juyawa a kan gadon, sai ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Ya san Ummie sosai, kuma ya san cewa idan da babu mutane a falon a lokacin da ya shiga,
da wataƙila ma ba za ta kalleshi ba.
A hankali ya tashi ya zauna a bakin gadon,
ya shafa fuskarsa da tafin hannunsa, sannan ya yi shiru na ƴan seconds.
“Damn…” ya furta ƙasa-ƙasa, ya sauke numfashi.
A ƙarshe ya mike, ya zura slippers ɗinsa, sannan ya nufi ƙofar ɗakin.
Maybe I should just talk to her,
gaskiya ba zai iya kwana da wannan abu a zuciyarsa ba.
Duk da yadda ƙirjinsa ke bugawa da wani irin sauri, ya fita daga ɗakinsa,
a hankali ya nufi corridor ɗin da zai kai shi ɗakin Ummie.
Matakansa ba su da sauri, amma duk matakin da ya ɗauka sai gabansa ya ƙara faɗuwa.
Da ya isa bakin ƙofar ɗakin Ummie, sai ya tsaya,
ya kalli ƙofar, ya sake sauke numfashi,
kamar wanda yake shirin fuskantar wani abu da bai san yadda zai kasance ba.
Ya ɗaga hannunsa, sai ya yi knock ɗin a hankali,
kamar yana tausayawa ƙofar ma.
A cikin ɗakin kuwa, Ummie tana kwance a kan gadonta, ta riga ta shirya bacci tsaf.
Da ta ji knocking, sai ta ɗan buɗe idanunta,
ta yi shiru na ɗan lokaci, maybe kunnenta ne kawai yaudare ta.
Sai aka sake yin knocking,
a wannan karon ta tabbatar.
Ummie ta ɗan zauna a kan gadon,
ta sauko daga gadon, ta dauki mayafinta a gefen sofa, sannan ta ƙarasa bakin ƙofa.
Ta buɗe, idanunta suka sauka kai tsaye kan fuskar Zayd.
Ya tsaya a gabanta kamar kazar da aka tsamo daga ruwa,
kamar duk confidence ɗin da ya saba zuwa da shi ya tsaya a corridor ɗin kafin ya isa ƙofar.
Ummie ta kalleshi daga sama har ƙasa,
sai ta hade rai a taƙaice, ta ce,
“Lafiya?”
Zayd ya ɗan hadiye yawu, ya ɗaga kansa kaɗan, sannan ya langwabe shi gefe,
muryarsa ta fito a hankali, cike da sanyin murya.
“Ummie…”
Ta kalleshi, batace komai ba.
Ya sake haɗiye yawu,
“Please… na shigo?”
Ya kalleta cikin wani irin roƙo a idanunsa.
Ummie ba ta amsa ba,
kawai ta kalleshi na ƴan seconds, sai ta juya ta koma cikin ɗakin,
ba tare da ta ce eh ba, ko a’a.
Zayd ya tsaya a bakin ƙofar na ɗan lokaci,
sai ya sauke ajiyar zuciya,
At least she didn’t close the door on my face.
Ya bi ta a hankali, ya tura ƙofar ya shiga, sannan ya rufe ta bayansa.
Kallon da Ummie ta yi masa ya nuna masa abu ɗaya,
wannan ba zai zama magana mai sauƙi ba.
Ummie ta koma bakin gadonta ta zauna,
ta ɗaga idanunta zuwa kan Zayd, ta zuba masa ido ba tare da ta ce komai ba,
kamar tana jiran shi ne ya fara magana.
Zayd bai yi wata-wata ba,
ya ƙaraso gabanta, sannan ya zube a kan gwiwowinsa a ƙasa,
ya kama hannunta da hannayensa biyu, ya riƙe shi gam.
“Ummie na…” muryarsa ta fito a hankali.
Ummie ba ta amsa ba.
Zayd ya ɗan haɗiye yawu,
“Wallahi… na rabu da Felicia tun wancan lokacin,”
ya ɗan dakata, yana kallon fuskarta,
“alkawarin da na yi mata kawai shi ne zan je graduation ɗinta,”
ya ɗan sauke ajiyar zuciya,
“shi ya sa na cika alkawarin da na yi mata,”
kuma keche ki ke jaddada mana girman alkawari da muhimmancin cika shi.
Ya girgiza kai a hankali,
“amma wallahi, Ummie, bayan wannan… babu wani abu,”
ya ƙara matse hannunta,
“ki yarda da ni.”
Ummie ta yi shiru, ba ta cire hannunta daga nasa ba,
kawai ta sauke wani dogon ajiyar zuciya.
Ta san Zayd, ta san ɗanta ba ya ƙarya,
amma hakan bai hana ta jin haushin abin da ta gani ba.
Ta ɗan kalle shi,
“na san ba ka saba yi min ƙarya ba, Ahmad.”
Zayd ya ɗago idanunsa.
“Amma…” muryarta ta ƙara tsauri,
“ka je irin wannan wajen, ka yi hotuna da ita, aka saka su a media…”
ta ɗan girgiza kai,
“ka san irin maƙiyan da kake da su.”
Zayd ya yi shiru,
“me kake so mutane su ce?”
ta ɗan dakata,
“ko ka manta da abin da ya faru a baya?”
Zayd bai amsa ba, kalaman sun same shi, ya sunkuyar da kansa.
Ummie ta ci gaba cikin tsantsar nutsuwa, amma wannan karon babu wasa a muryarta,
“wannan ita ce magana ta ƙarshe da zan sake yi da kai a kan yarinyar nan.”
Zayd ya ɗago kai da sauri, ya gyada kai,
“In shaa Allah, Ummie,” ya matse hannunta a hankali,
“ba za ki sake jin wani abu a kanta daga gare ni ba.”
Ummie ta ɗan sauke ajiyar zuciya,
sai ta ɗan kalli gefe, kamar tana tunanin abin da za ta faɗa na gaba.
Shiru ya ɗan mamaye ɗakin, sai ta dawo da idanunta kan Zayd.
“Yanzu akwai abu ɗaya kawai da nake so daga gare ka.”
Zayd ya ɗago gira,
“Menene? ko meye ki fadamin Ummie na, zanyi.”
Muryarsa ta fito cike da ɗan zumudi.
Ummie ta kalleshi ido da ido,
“ka dage da maganar neman Raihana, ka yi kamar ba ni ce na saka ka ba, kayi kamar kai ne ka ga matar da kake so ka taka da kafafunka kaje nemanta,”
ta ɗan saurara,
“karka dinga jin cewa kanayin wnn ne sabida ni,” ta girgiza kai,
“kayi sabida kanka!”
Zayd ya ɗan daskare na ɗan lokaci,
kamar bai yi tsammanin wannan ne za ta faɗa ba.
Ummie ta ci gaba,
“wannan shi ne kawai abin da zai faranta min rai a yanzu,”
ta ɗan dakata, sai ta ƙara da cewa,
“ina so gobe ka shirya.”
Zayd ya zuba mata ido,
“Ka je wajenta!”
Not edited