ZAYD ARMAAN

THE DECISION AND TGE DEFIANCE

by @jiddaahbarkum



*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER FORTY FIVE:45*

*THE DECISION & THE DEFIANCE*

*JIDDAAH BARKUM*

—————

Washegari da safe, wajen ƙarfe tara, Umma ta shiga ɗakin Raihana.
Ta same ta kwance a kan gadonta, hijab ɗinta har yanzu a jikinta.
Tun bayan da ta idar da sallar Asuba, ba ta cire hijabin ba, kawai ta koma kan gadon ta kudundune cikin bargo, kamar wadda ba ta san garin Allah ya waye ba.

Tun daren jiya take kiran Haris a waya, ta kirashi sau da yawa,
amma wayarsa bata shiga,
kuma rashin samun sa ya ƙara dagula mata tunani.

Ta kasa daina tunanin ko wataƙila shi ne zai iya gaya mata ainihin dalilin da ya sa aka raba aurensu,
amma har yanzu… babu amsa.

Umma ta ƙaraso kusa da gadon a hankali, ta zauna a gefensa,
ta ɗaga hannu ta taɓa goshin Raihana.
Nan take fuskarta ta sauya, jikinta yana da mugun zafi.

“Ya Allah…”
Ta furta a hankali, da sauri ta janye hannunta, sannan ta sake taɓa goshin nata kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba.

“Raihana…”
Raihana ta ɗan motsa, a hankali ta buɗe idanunta.

Kallon farko da Umma ta yi mata ya isa ya fahimtar da ita cewa ta sha kuka sosai,
idanunta sun kumbura, fuskarta ta yi jawur, kuma akwai hawaye bushe a gefen idanunta.

Umma ta kalleta da tsananin tausayi,
“Haka jikinki ya yi zafi?”
ta ɗan girgiza kai,
“amma baki zo kin faɗa min ba, da na sani da na tura Yusuf an nemo miki magani.”

Raihana ta lumshe idanunta,
kafin ta iya cewa komai, wasu hawaye suka zubo mata.

Hankalin Umma ya ƙara tashi,
“Subhanallah…”
ta ɗan matsa kusa da ita, a hankali ta ɗago Raihana, ta kwantar da kanta a kan cinyarta.
Hannunta ya fara shafa bayanta a hankali, tana patting ɗin ta kamar ƙaramin yaro.

Zuciyar Umma ta cika da damuwar ɗiyarta,
ba sai ta tambaye ta abin da ya faru ba, ta san dama dole abin ya ci mata zuciya, musamman da ba ta san dalilin raba ta da Haris ba.

“Ki daina kuka, kin ji?”
Muryarta ta kasance a hankali, cike da tausayi,
“kin san mahaifinki ba zai yi abinda zai cutar da ke ba,”
ta ci gaba da shafa bayanta,
“tunda kika ga haka, tabbas yana da nasa dalilin.”

Raihana ta yi shiru, hawayenta suna ci gaba da zubowa a hankali.

“Ki yi haƙuri,”
Umma ta ɗan sauke ajiyar zuciya,
“sau da yawa muna son abu, amma ba lallai ne ya zama alheri a gare mu ba,”
ta ɗan dakata,
“haka kuma muna iya ƙin wani abu, alhali alherinmu yana tare da shi.”

Hannunta ya ci gaba da yawo a bayanta,
“ki bar wa Allah ikonsa, kin ji? shi kaɗai ya san abin da yake gaba, shi ne zai shige miki gaba, kuma shi zai musanya miki da mafi alkhairi.”

Raihana ta yi luff a kan cinyar uwarta,
a hankali, kamar kalaman Umma suna fara rage mata zafin da ke ƙirjinta.

Umma ta ɗan ci gaba da shafa kanta,
sai bayan wasu seconds ta ɗago kanta a hankali,
“yanzu tashi ki yi wanka,” ta ɗan gyara hijab ɗin da ke kanta,
“ki ji daɗin jikinki, sai ki zo ki karya, kin ji ko?”

Raihana ta gyada kai a hankali,
hannunta ya tafi gefen idonta tana share sauran hawayen.

Umma ta kalleta na ƴan seconds,
kamar har yanzu zuciyarta ba ta gamsu da barin ta ita kaɗai ba,
sai ta ɗan taɓa kumatunta,
“ki yi haƙuri, Raihana.”
Raihana ta sake gyada kai.

Umma ta sauke ajiyar zuciya, sai ta mike a hankali,
ta sake kallon Raihana na ƴan seconds, sannan ta juya ta nufi ƙofar.

Raihana ta bita da kallo har Umma ta fita,
sai ta sake kwantar da kanta kan pillow, idanunta suka rufe.
Amma wannan karon… kukan nata ya yi shiru.

—————-

A safiyar kuwa, a ARMAAN MANSION, Inno ce tare da Ummie a ɗakin da Inno ta sauka.
Duk da cewa sun riga sun gaisa da asuba, yanzu da gari ya waye, Ummie ta sake dawowa wajenta, suka sake gaisawa cikin girmamawa.

Inno tana zaune a kan carpet, ta jingina da jikin gadon, Ummie kuma tana zaune a gefenta.
Sun ɗan yi hira na wasu mintuna, kafin Inno ta maida hankalinta gaba ɗaya kan Ummie.

Ta ɗan gyara zamanta,
“ni kam, Ahmad, haka zai ta zama kina zuba masa ido ba zai yi aure ba?”
ta ɗan girgiza kai,
“kullum fa ƙara girma yake, ba wai yaro yake dawowa ba, zuwa yanzu, idan ba mantawa nayi ba, ai ya yi shekaru talatin da shida a duniya.”

Ta ɗan dakata, sannan ta ɗaga gira,
“amma ace ba zai yi aure ba? toh ko dai ba shi da lafiya ne?”

Ummie ta ɗan buɗe baki, amma Inno ta ci gaba kafin ta samu damar magana,
“na san dai ba zai rasa wacce ke son shi ba, idan ma shi ba ya son kowa…”

Ta yi shiru na ɗan mintina, idanunta suka koma gefe kamar tana nazarin abin da za ta faɗa,
sai ta dawo da kallonta kan Ummie.

“Hajja Fati…”
Ummie ta ɗan gyara zamanta, tana sauraronta cikin nutsuwa.

Inno ta ɗan yi murmushi,
“na yanke shawara,” ta ɗan dakata,
“wannan Juma’ar mai zuwa za a daura wa Zaydu aure da Seeyama.”

Ummie ta ɗago kai da sauri,
“idan an daura ai zai hakura, ko?”

Ummie ta yi shiru na ƴan seconds,
a fuskar Inno ta ga cewa maganar ba shawara bace kawai, hukunci ne,
kuma ta san ba ta da ikon tambayarta ko ƙalubalantar hukuncin da ta yanke.

Saboda haka kawai ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan yi murmushi,
“toh, ba komai, Allah Ya sa haka ya fi alkhairi,”
ta ɗan dakata,
“saida kuma akwai yarinyar da yake nema… har Alhaji Munzali ya je ya nema masa izinin zuwa wajenta.”

Inno ta kankance idanunta,
“ba fa wata yarinya ku dai?”
ta ɗan girgiza kai,
“Zaydu dai ya raina ku wallahi daga ke har Minzalin, wasa da hankalinku kawai yake yi, shi ya ma maida ku kamar ba ku da wayo.”

Ummie ta yi shiru.

Inno ta ci gaba,
“yo idan ba haka ba, idan zuwa wajen yarinyar yake, me ya hana shi zuwa yanzu ace sun fahimci juna har an fara maganar biki?”
ta ɗan yi shiru, sannan ta ja tsaki,
“ko dai maganar ta yi nisa ne.”

Ta sake kallon Ummie,
“share wannan soki-buturtun nashi kawai, Juma’ar nan a daura masa aure,”
ta ɗan ɗaga yatsa,
“kuma kar ma ki sanar masa, ku bar min komai a hannuna.”

Ummie ta yi murmushi,
murmushin da bai kai ko bakinta ba, iyakar lips ɗinta kawai,
“toh, shikenan Hajiya, yanda kika ce, In Shaa Allah.”

“Yauwa.”
Inno ta gyara mayafinta, sannan a hankali ta miƙar da kafafunta bayan dogon zama, sai kuma ta mike tsaye,
ta kalli Ummie na ƴan seconds,
“bari na watsa ruwa.”

Sai ta juya a hankali ta nufi hanyar ƙofar toilet,
Ummie kuwa ta bita da kallo.

—————-

*6:00 PM — MALALI, KADUNA*

A hankali wata black Range Rover Autobiography ta yi parking a gaban gidan Baffa.
Zayd yana zaune a kujerar baya, ya jingina da kujerar cikin nutsuwa.

Yau ma traditional outfit ne a jikinsa — blue-black kaftan wanda ya matuƙar karɓar fatarsa,
rigar ta zarce cinyoyinsa kaɗan, amma ba ta kai gwiwa ba.
A kansa babu hula, sai gashinsa da yayi luff lufff a gyare amma ba shi da yawa sosai, sai kuma agogon da ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa.

Fuskarsa babu wani expression sosai,
kamar tunaninsa yana wani wuri dabam.

Sameer, wanda ke zaune a gaba, ya ɗan juya ya kalleshi,
“Boss…”
Zayd ya ɗago idanunsa ya kalleshi na ƴan seconds, amma bai ce komai ba.

Sameer ya ɗan gyara zamansa,
“ga Baba nan yana zuwa.”
Zayd bai amsa ba, kawai ya maida kallonsa gaban glass din motar.

A dai-dai lokacin Baffa yana ragowa daga kofar gidan,
yana gyara hannun rigarsa a hankali, kamar wanda ya yi alwala yanzu-yanzu, sannan ya nufi inda motar take.

Zayd bai ce komai ba,
kawai ya buɗe murfin motar ya fito,
Sameer ma ya kashe motar, sannan ya sauko.

Da Baffa ya hango Zayd, sai fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi,
da ya ƙarasa inda suke sai ya musu sallama.

“Assalamu alaikum.”
Ya miƙa hannunsa,
“Assalamu alaikum, Baffa.”

Amma maimakon ya kama hannun Baffa, sai Zayd ya durƙusa a gabansa cikin girmamawa,
Sameer ma, ganin Boss ɗinsa ya durƙusa, bai yi wata-wata ba ya bi bayansa.
Su biyun suka gaishe shi cikin ladabi.

Baffa ya washe baki, yana kallonsu cikin farin ciki,
“Wa alaikumus salam,” ya ɗan girgiza kai,
“Bismillah, ku taso,”
ya kalli Zayd, sannan ya kalli Sameer,
“mu ƙarasa masallaci mu yi sallah, na ji kamar an kusa shiga.”

Zayd ya ɗan jinjina kai, sai ya miƙe.
Baffa ya juya ya fara tafiya a gaba,
Zayd da Sameer suka bi shi a baya,
a hankali suke tafiya zuwa masallacin, Baffa a gaba, Zayd da Sameer a bayansa.

Bayan sun dawo daga masallaci, Baffa ya dubesu,
“ku shigo daga ciki mana, bari na yi mata magana.”
Zayd ya ɗan jinjina kai, ya bi bayansa, yayin da Sameer kuwa ya koma cikin motar.

Baffa har bakin ƙofar falonsa ya raka Zayd kafin ya juya,
cikin gidan dan yi wa Raihana magana.

Lokacin kuwa, Raihana tana zaune a gefen Umma, sun idar da sallar Magariba.
Baffa ya ɗaga labulen ƙofar falon.

“Raihana, ki fito, kinada baƙo.”
Gabanta ya faɗi nan take, ta fara yin addu’a a cikin zuciyarta.
Allah Ya sa Haris ne… Allah Ya sa sun daidaita da Baffa.

Kamar wadda aka zabura, sai ta miƙe da sauri,
Baffa ya riga ya juya, saboda haka ta ɗan kalli Umma.
A sanyaye ta ce,
“Umma, bari na je.”
Umma ta gyada mata kai kawai.

Ita kam Raihana, ta nufi falon Baffa.
A lokacin ma, kwakwalwarta ba ta hasko mata ta canja kaya ba, ko ta gyara fuskarta, ko kuma ta fesa wani turare,
babu abin da ya dame ta, burinta kawai shi ne idanunta su sauka kan Haris, kai tsaye.

Ta isa ƙofar ɗakin Baffa, ta tura ƙofar bayan ta yi sallama,
“Assalamu alaikum.”

Mutumin yana zaune a kan kujera, ƙafa ɗaya a kan ɗaya, wayarsa manne a kunnensa,
yana magana ƙasa-ƙasa, dama direction ɗin ƙofar yake kallo.

Saboda haka da Raihana ta shigo, idanunsa fesss suka sauka kanta,
ya kalleta na wasu seconds, sai ya ɗauke kansa,
kamar bai ga kowa a wajen ba.

Raihana ta tsaya cak,
wani irin takaici ya cika mata zuciya, wani abu ya makale mata a maƙogwaro.
Ta kasa ƙarasawa gabansa, sai ta tsaya a wajen.

Shi kam gogan, yana nan yana magana a waya,
bai ce mata komai ba, har ya gama wayar.

Da ya kashe wayar, maimakon ya kalleta, kawai ya fara latsa wayarsa.
Raihana ta kalleshi, ta sake kallonsa.

Take ta ji a zuciyarta, wato sabida shi Baffa ya sallami Haris?

Ba tare da ta tsaya wani dogon tunani ba kawai sai ta buɗe baki,
“Idan dai a kanka Baffa ya fasa ba wa wanda nake so aurena…”
ta ɗan tsaya, muryarta tana rawa kaɗan, amma babu shakka a cikinta.

“…toh ka sani wallahi billahi, ka tafka babban kuskure.”
Ta ɗan ja numfashi,
“ni da kai kamar ruwa da wuta ne, kuma sanin kanka ne ba sa haɗuwa.”

Ta ɗan kalleshi kai tsaye,
“don haka zaman lafiyarka… ka koma wajen mahaifina ka sanar da shi ka janye zuwa wajena da kake,”
“tunda dama ba zuwan kanka ba ne, yanda aka tursasa maka.”

Muryarta ta fara dan rawa,
“nima tursasamin aka yi,”
“ka barni na auri wanda nake so.”

“Domin duk wanda ya aureni…” ta yi ɗan shiru,
sai ta furta kalaman a sarari, ba tare da ta kau da idanunta daga kansa ba.

“…idan ba Haris ba, toh tabbas gangar jikina ya aura!”





Not edited