THE DECISION BEHIND THE SILENCE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER FORTY SIX:46*
*THE DECISION BEHIND THE SILENCE*
*JIDDAAH BARKUM*
—————-
Zayd ya zauna a wurin, idanunsa a kan Raihana har ta gama fadin duk abin da ke ranta.
Bai katse ta ba, kawai ya bar ta ta faɗi komai,
har ta juya ta fita daga ɗakin, sai ƙofar ta rufe a bayanta.
Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye falon.
ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ajiye wayarsa a gefensa, ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya shafa fuskarshi daga goshinsa zuwa haɓarsa.
Ya yi shiru na wasu seconds,
kalaman Raihana suna ta maimaituwa a cikin kansa.
Ya runtse idanunsa.
“Hmm…”
Ya furta ƙasa-ƙasa.
A ƙarshe ya mike, ya ɗauki wayarsa ya saka a aljihunsa, sannan ya nufi ƙofar.
Da ya fito, sai ya tadda Baffa tare da wani maƙocinsa suna tsaye a gefen gidan suna magana cikin nutsuwa.
Sai ya ɗa rage tafiyarsa, da ya ƙaraso wajensu, sai ya ɗan risina.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Suka amsa kusan lokaci guda.
Maƙocin Baffa ya ɗan kalli Zayd, sannan ya yi wa Baffa sallama,
“toh sai mun sake magana.”
“toh toh ba laifi Allah ya bamu alkhairi.”
Mutumin ya juya ya wuce.
Baffa kuwa ya mayar da kallonsa kan Zayd.
“Har ka fito?”
ya ɗan shafa kansa, yana sunkuyar da kai,
“Eh, baba, zan wuce ne.”
Baffa ya yi murmushi kaɗan,
“Toh shikenan, Allah Ya tsare hanya ka gaida hajiyar do Allah.”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“In Shaa Allah.”
Sai ya yi shiru,
amma… bai tafi ba.
Baffa ya lura, kallon da yake yi masa ya nuna masa sarai cewa akwai wata magana da ke bakinsa.
Sai ya ɗan kalli bencin da ke gefen gidan.
“Ko akwai wata magana ne?”
Ya nuna bencin da hannunsa,
“Mu ƙarasa can mu zauna.”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Toh, baba.”
Baffa ya fara tafiya, Zayd ya bi bayansa.
Da suka isa bencin, Baffa ya zauna, Zayd kuma ya ɗan risina kafin ya dan durkusa a gefensa.
Ya sake shafa kansa, idanunsa suna ƙasa.
Baffa ya kalleshi na ƴan seconds,
sai ya ce cikin nutsuwa,
“Toh… ina sauraronka.”
Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana neman kalaman da suka dace.
“Uhm… Baba…”
“Hmm?”
“Dama… tace wai na turo.”
Baffa ya ɗan daga gira.
Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ƙara sunkuyar da kansa.
Baffa ya tsaya yana kallonsa,
kamar yana son tabbatar da abin da kunnensa ya ji.
“Raihana ce ta ce ka turo?”
Zayd ya ɗan gyada kai,
“Eh, baba.”
Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskar Baffa,
ba wai murmushin farin ciki kai tsaye ba ne, a’a,
murmushin wanda ya fahimci cewa akwai wani abu da ke faruwa a bayan maganar.
“Babu laifi,”
ya ɗan gyara zamansa,
“ka sanar da magabatan naka,”
ya kalli Zayd,
“Idan sun samu lokaci, sai su zo.”
Zayd ya ɗan ɗaga kai,
“In Shaa Allah, baba,”
ya sauke ajiyar zuciya,
“Nagode.”
Baffa ya ɗan gyada kai,
“Madallah.”
Zayd ya mike a hankali,
“Ka gaida jama’ar gidan.”
Zayd ya sake sunkuyar da kai cikin girmamawa,
“za su ji, baba.”
Sai ya juya ya nufi motarsa.
Baffa bai motsa ba, kawai ya tsaya yana kallonsa.
Zayd ya isa motar, ya buɗe ƙofar ya shiga,
motar ta tashi, a hankali ta fara barin layin.
Baffa ya ci gaba da kallonta har sai da ta ɓace daga ganinsa,
sai kawai ya sauke ajiyar zuciya mai zurfi.
Ya tsaya na wasu seconds yana kallon hanyar da motar ta bi,
kamar tunaninsa ya tsaya can.
Daga ƙarshe ya girgiza kai a hankali,
sai ya juya ya koma cikin gidan.
———————
Motar ta fara barin unguwar a hankali.
Zayd ya jingina kansa da kujerar baya, idanunsa suna kallon window yayin da fitilun gidaje suke wucewa ɗaya bayan ɗaya.
Bayan wasu seconds, sai ya ɗan juya kansa zuwa ga Sameer da ke tuƙi,
“Marafa zamu nufa.”
Muryarsa ta fito a takaice.
Sameer ya ɗan kalleshi ta mirror,
“Okay, Boss,”
ya sake mayar da hankalinsa kan hanya.
Tun da ya ji Marafa, ya san inda suke nufi,
gidan Alhaji Munzali ne, ƙanin mahaifin Zayd.
Motar ta sake yin shiru, Zayd ya koma kallon window,
hankalinsa yana can wani wuri.
Bayan kusan mintuna goma sha biyar, motar ta fara shiga cikin unguwar Marafa.
Lokacin ya kusa ƙarfe tara na dare,
fitilun titi suna haskawa a hankali, yayin da gidaje suke jere gwanin sha’awa a gefen hanya.
Daga nesa, Sameer ya hango babban gate ɗin gidan Alhaji Munzali,
ya rage gudun motar, yana shirin yin horn dan ya samu shigar da motar.
Amma kafin ya danna, Zayd ya ɗan daga hannu,
“A’a.”
Sameer ya kalleshi.
Zayd ya ci gaba da kallon gidan,
“ba daɗewa za mu yi ba,”
ya ɗan dakata,
“Park outside, I’ll go in.”
“Okay, Boss.”
Sameer ya rage gudun motar, sannan ya yi parking a gefen gidan.
Zayd ya buɗe murfin motar, ya fito, sannan ya kalli gate ɗin gidan na ƴan seconds,
kamar yana tattara tunaninsa kafin ya shiga, ya rufe murfin motar a hankali.
Sai ya nufi ƙofar gate ɗin,
a lokacin ne maigadin da ke bakin gate ya hango shi.
Da ya gane shi, sai ya miƙe da sauri ya buɗe gate ɗin.
“Barka da dare, Alhaji.”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Barka.”
Sai ya shiga.
Sameer kuwa ya jira har Zayd ya wuce, sannan ya shiga motar ya nemo wajen da ya fi kyau ya yi parking, dan inda ya ajiye motar da farko yayi hanya.
Ya ci gaba da tafiya shi kaɗai zuwa cikin gidan.
Fitilun compound ɗin suna haskawa cikin tsari,
daga cikin gidan kuwa, ana iya hango hasken falon yana fitowa ta manyan windows.
Ya ɗan tsaya na ɗan lokaci,
sai ya sauke ajiyar zuciya,
ya san abin da ya zo yi,
amma duk da haka… wani abu a zuciyarsa ya sake bugawa.
Sai ya ci gaba da tafiya zuwa entrance ɗin gidan.
Kai tsaye ya nufi falon Alhaji Munzali.
Da ya shiga, sai ya same shi shi kaɗai, yana zaune cikin nutsuwa yana karanta jarida.
Haske mai laushi na cikin falon ya sauka kan fuskar Alhaji Munzali, yayin da yake juyar da shafukan jaridar ɗaya bayan ɗaya.
Zayd ya ƙarasa cikin nutsuwa,
“Assalamu alaikum.”
Alhaji Munzali ya ɗago kai,
“Wa alaikumus salam.”
Zayd ya ɗan risina cikin girmamawa, sannan ya samu gefe ya zauna,
“Barka da dare, Abba.”
“Yauwa, Zayd.”
Alhaji Munzali ya ɗan ajiye jaridar a cinyarsa,
“ya gida? ya su Hajiyan?”
“Suna lafiya, Abba.”
“Ma sha Allah.”
Alhaji Munzali ya jingina bayansa da kujerar, yana kallon Zayd da nutsuwa.
Zayd kuwa ya ɗan gyara zamansa, ya miƙa ƙafarsa ɗaya gaba, sannan ya fara shafa kansa a hankali,
kamar yana neman kalmomin da suka dace.
“Uhmm Abba…”
Alhaji Munzali ya ɗan ɗaga gira,
“Hmm?”
“Dama… gidansu ne aka ce na turo.”
Ya ɗan yi shiru,
“shi ya sa nace bari na zo na sanar maka.”
Alhaji Munzali ya zuba masa ido na wasu seconds,
kamar yana son tabbatar da abin da ya ji.
“Su wa kenan?”
Muryarsa ta fito cikin nutsuwa,
“can gidan da kake neman auren?”
Zayd ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci,
sai ya ɗan jinjina kai,
“Eh.”
Alhaji Munzali ya yi shiru,
sai wani irin murmushi ya bazu a fuskarsa.
“Finally…”
ya ɗan girgiza kai,
“Allah Ya nufa kenan.”
Zayd bai ce komai ba, kansa har yanzu a ɗan sunkuye.
Alhaji Munzali ya sake kallonsa, murmushin bai bar fuskarsa ba.
“Toh shikenan, babu komai,”
ya ɗan gyara zamansa,
“Gobe idan Allah ya sa muna cikin rayayyu, ni da Matawalle za mu je,”
ya ɗan dakata,
“duk abin da ake ciki, za ka ji.”
Zayd ya ɗan ɗago kai,
“Toh, Abba.”
Sai ya sake risinawa,
“Allah Ya kaimu,Allah Ya ƙara girma.”
“Amin.”
Alhaji Munzali ya amsa, har yanzu fuskarsa a washe da murmushi.
Zayd ya ɗan yi shiru na ƴan seconds, sai ya miƙe a hankali.
“Abba, zan wuce.”
Alhaji Munzali ya ɗaga masa kai,
“Toh, madallah.”
Zayd ya ɗan risina,
“ka gaida jama’ar gidan.”
“In Shaa Allah.”
Sai ya juya, a hankali ya fara fita daga falon.
Alhaji Munzali ya bishi da kallo har ya kai bakin ƙofa.
A fuskar Alhaji Munzali kuwa…
murmushin da ke kan fuskarsa ya ƙara faɗaɗa,
kamar mutumin da ya ji labarin da ya daɗe yana jira.
————-
*ARMAAN MANSION*
Ummie na tsaye a gefen wardrobe ɗinta, wayarta manne a kunnenta.
Idanunta suna kan window ɗin ɗakin,
daga can, hasken garden ya ratsa cikin labulen da aka ɗan ja gefe, yana zana wani irin haske mai laushi a cikin ɗakin.
Ummie ta sauke ajiyar zuciya,
“Falmata… ba za ki gane ba,”
muryarta ta fito a hankali,
“wallahi ban taɓa ƙin Seeyama ba, ban taɓa kim Zayd ya aureta ba.”
Ta ɗan yi shiru, idanunta suka sauka ƙasa,
“amma…”
ta sake jan numfashi,
“yanayin tarbiyyarta ne yake damuna.”
Ta ɗan matsa daga wardrobe ɗin, ta jingina da gefenta,
“kin san Zayd, ba mutum ne mai hayaniya ba,” Seeyama kuma akwai rawar kai.
Ta ɗan lumshe idanunta,
“ba kowane irin hali ne zai dace da shi ba,”
sai ta ɗan girgiza kai.
“Wannan yarinyar… ba ita ce irin matar da nake ganin za ta iya jure Zayd ba.”
Muryarta ta ƙara laushi,
“Da Seeyama nutsattsiyar yarinya ce, Falmata, wallahi da na yi farin ciki da wannan maganar.”
Ta ɗan yi shiru,
“amma…”
Kafin ta ƙarasa, sai wani motsi ya kama gefen idanunta.
Ummie ta ɗago kai, ta kalli window ɗin,
wani abu ya gifta a wajen.
Ta ɗan daure fuska.
“Falmata…”
ta sauke wayar daga kunnenta kaɗan,
“I’ll get back to you.”
Ta katse kiran, a hankali ta ajiye wayar a gefen wardrobe,
sai ta nufi wajen window.
⸻
A wajen kuwa…
Seeyama ta tsaya cak.
Tun lokacin da ta ga Ummie ta taho daga falon tana magana a waya, wani irin rashin nutsuwa ya shige ta.
Dama suna zaune a falon ne lokacin da aka kira Ummie,
da Ummie ta miƙe ta nemi excuse, ta nufi ɗakinta, sai Seeyama ta ɗan jira.
Amma zuciyarta ta kasa barin ta,
daga karshe ta tashi ta fita compound.
Tun da Inno ta sanar da Mommy Hauwa maganar da ta yi da Ummie…
ita kuma Seeyama tunda uwarta ta fesa ma ta wannan gagarumin albishirin din,
Seeyama ta riga ta fara ganin komai ya kusa kammala.
Auren Zayd, auren da take ganin kamar ya kusa zama gaskiya.
Saboda haka da ta ga Ummie ta tashi ta shige ɗakinta tana magana cikin wata irin murya mai nauyi, sai zuciyarta ta fara bugawa,
domin Ummie kowacce irin waya zatayi a gabansu takeyi, yanzu kuma ta tashi.
Dan haka da taje compound din sai ta zaga zuwa garden din gidan dai ta gefen window Ummie ta kasa kunne.
Ko dai akwai wani abu?
Ta ɗan kusanci window ɗin, sai ta ji muryar Ummie daga cikin ɗakin.
Ba ta ji komai sosai ba,
amma kalmar…
“Seeyama…”
ta isa ta sa jikinta ya ɗauki wani irin sanyi.
Seeyama ta tsaya tana saurare,
sai kawai ta ji Ummie tana cewa,
“…ba ita ce irin matar da ta dace da Zayd ba.”
Idanun Seeyama suka buɗe, zuciyarta ta buga,
me?
Ta yi saurin kallon ƙofar wajen garden din,
kamar ana iya kama ta.
Sai ta sake jin muryar Ummie,
“da Seeyama nutsattsiyar yarinya ce…”
sauran kalaman ba su fito sarai ba.
Seeyama ta haɗiye yawu,
a wannan lokacin ta fahimci abu ɗaya,
Ummie ba ta goyon bayan auren.
Tsoro ya ratsa ta, ta waiga, babu kowa.
Sai kawai ta ja baya a hankali.
Amma kafin ta iya komawa falon, sai ta ga motsi a ɗakin Ummie,
ana yowa wajen window.
Ummie na shirin lekowa.
Seeyama ta tsure, ta kasa tunanin inda za ta shiga.
Sai idanunta suka sauka kan wani babban drum da yake gefe a cikin compound ɗin.
Ba tare da ta sake tunani ba, ta yi saurin nufarsa,
ta shiga bayansa, ta matse jikinta da bango, tana ƙoƙarin yin shiru.
Ta ɗora hannunta a ƙirjinta,
numfashinta ya fara hawa da sauka da sauri.
“Ya Allah…”
Ta furta ƙasa-ƙasa.
A wannan lokacin…
abin da ta ɗauka a matsayin albishir na aure ya fara zama kamar wani abu da zai iya kuɓuce mata a kowane lokaci,
kuma abin da ya fi tsorata ta shi ne…
Ummie ta riga ta fara shakkar dacewarta da Zayd.
Not edited