ZAYD ARMAAN

A CALL IN THE NIGHT

by @jiddaahbarkum


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER FORTY SEVEN:47*

*A CALL IN THE NIGHT*

*JIDDAAH BARKUM*

————————

Seeyama ta ɗan leƙo da kanta kaɗan.
Idanunta suka koma kan window ɗin ɗakin Ummie.
Ta tsaya tana kallon wajen na wasu seconds, tana tabbatar da cewa ba ta hango Ummie ba.

Sai ta fara rarrafawa a hankali.
Ta sake kallon window ɗin, babu kowa.
Sai ta ci gaba da rarrafawa har ta zo daidai gate din garden din, sannan ta mike ta fice daga da mugun sauri.

Da ta isa bakin entrance ɗin lounge, sai ta ɗan leƙa cikin window,
tana fatan Ummie ba ta a falon.
Allah ya taimake ta kuwa, bata nan.

Inno ce kaɗai a zaune, sai kubura a durkushe a gefe tana zuba mata kunu a cikin kofi.

Seeyama ta sauke ajiyar zuciya.
Ta buɗe ƙofar ta shiga.

Inno ta ɗago kai ta kalleta,
“Ke kuma daga ina?”

Seeyama ta ɗan tsaya,
sai ta yi ƙoƙarin ɓoye yanayin da ke fuskarta.

“Uhmm…”
ta ɗan sosa kunnenta kama munafuka.

“Na leka wajen Garzali ne, na faɗa masa ya wanke min mota gobe, ina son zuwa gidanmu.”

Inno ta ɗan jinjina kai,
“toh.”
Sai ta koma sipping kununta, kamar maganar ba ta da wani muhimmanci.

Seeyama ta ɗan tsaya tana kallonta.
Ganin Inno ta ci gaba da abin da take yi, sai ta wuce a hankali.

Ta haura sama, kai tsaye ta nufi ɗakin Suhaila.

Amma hankalinta… yana can akan kalaman da ta ji.
Ba ta ji komai duka ba, amma abin da ta ji ya isa ya dasa mata wani irin shakku.

Har zuwa yanzu, zuciyarta ta fara yarda da abu ɗaya,
Ummie ce ba ta son Zayd ya aure ta.

Ta so ta kira Mommy, ta so ta faɗa mata duk abin da ta ji,
amma ba za ta iya yin hakan ba a yanzu.
Amma ba zai yuwu ba, sabida waje daya suke kwana da Suhaila, falo kuma Inno tana nan kuma Inno is very observant, yanzu sai ta fahimci wani abu.

Saboda haka kawai ta yanke shawara.
Da safe za ta je gida, za ta zauna da Mommy ido da ido.
Ta faɗa mata komai, ba ta son sake yin hasashe.

Wannan karon… duk da Inno ta tabbatar da aurenta da Zayd har kuma ta furtawa Ummie kuma bata Musa ba,
yanzu lokacine da ita da mahaifiyarta za su san abinyi, idan ba haka ba Ummie ba zata barta ta zauna lafiya da Zayd ba.

⸻

*ZAYD*

Wajen ƙarfe 9:45 na dare, motarsu ta yi parking a ARMAAN MANSION.
Da Zayd ya fito, kai tsaye ya nufi entrance ɗin.
Sameer kuwa ya ɗauki kayansa ya nufi BQ.

Da sallama a bakinsa, ya shiga gidan.
Babu kowa a falon, sai hasken chandeliers ɗin da ya mamaye wajen, yana sa falon ya yi shiru fiye da yadda ya saba.

Zayd ya ɗan tsaya, ya kalli wajen na wasu seconds.
Sai a hankali ya nufi ɗaya daga cikin sofas ɗin ya zauna.
Ya yi crossing legs ɗinsa ya dago.

Yatsansa ɗaya ya fara zagaye lips ɗinsa.
Ya yi shiru, idanunsa suka tsaya a wuri ɗaya,
kamar mutum ne da tunaninsa ya kai shi wani wuri mai nisa.

Sai wani ɗan murmushi ya subuce masa,
ya ɗan girgiza kai, kamar shi kansa bai yarda da tunanin da ya zo masa ba.

Sai ya saka hannu cikin aljihunsa ya ɗauko wayarsa.
Ya kalleta na wasu seconds, kamar yana nazarin wanda zai kira.
Daga ƙarshe ya danna number da yake son kora.

Wayar ta fara ringing…
har ta gama ringing, ba a ɗaga ba.

Sai ya cire wayar daga kunnensa, ya kalleta.
Unusual, ba kasafai ake kiran wannan number ba a rasa ɗagawa.

Sai ya sake kira.
A wannan karon ma… shiru.

Zayd ya yi shiru na wasu seconds, idanunsa suka sauka ƙasa,
kamar yana nazarin abin da ya hana mai wayar dauka.

Daga ƙarshe kawai ya mike, ya saka wayar a aljihunsa.
Kai tsaye ya haura sama, ya nufi ɗakin Ummie.

Da ya isa bakin ƙofar, ya yi knocking a hankali.
“Come in.”
Muryar Ummie ta fito daga ciki.

Zayd ya buɗe ƙofar, ya shiga.
Ummie tana zaune a kan gadonta, ƙafunta a miƙe, bayanta jingine da headboard.
Da ta hango shi, sai idanunta suka sauka kansa.

Zayd ya ƙarasa gabanta, sai ya zube a kan gwiwowinsa.
Ya kama hannunta da girmamawa, ya sumbace shi.

“Barka da dare, Ummie.”
Murmushi ya bayyana a fuskar Ummie,
“Barka da zuwa.”
Sai ta ɗan zame hannunta daga cikin nasa, ta ɗora shi kan kansa tana shafawa a hankali.

“Sannu da zuwa, har ka dawo?”
Zayd ya ɗan gyada kai,
“eh, na dawo.”

Idanunta suka fara yawo a fuskarshi, ta nazarce shi na ƴan seconds.
Sai ta tambaya,
“toh, ya ka bar min yarinyar? Tana lafiya ko?”

Zayd ya yi shiru,
kwakwalwarsa ta haska masa uban rashin kunyar da Raihana ta zuba masa.

Sai wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen bakinsa.
Ummie ta lura, amma ba ta ce komai ba, kawai ta tsaya tana nazarinsa.

Daga ƙarshe ta ɗan karkatar da kai,
“Habibi…”
ta ɗaga gira,
“your expression said it all.”

Zayd ya kalleta,
“me ya faru yau da ka je?”

Ya ɗan sauke idanunsa, sai ya sake kallonta.
Cikin nutsuwa ya ce,
“Baba ne yace na turo.”

Ummie ta yi shiru, ta kalleshi kamar ba ta tabbatar da abin da ta ji ba.
Da ya ga shirun ya yi yawa, sai ya ɗago kai ya kalleta.

Ummie ta ɗan buɗe idanunta,
“are you serious?”

Zayd ya ɗan gyada kai.
Ta ɗan matso gaba,
“ka aika aje a nema maka aurenta?”

Zayd ya sake gyada kai, a hankali.

Ummie ta lumshe idanunta, wani irin farin ciki ya bayyana a fuskarta.
“Alhamdulillah…”
ta furta a hankali.

Zayd kuwa ya zauna yana kallonta,
kamar ya kwana biyu bai ga wannan irin farin cikin a fuskarta ba.

Ummie ta sake kallonsa,
“kaga kenan…”
ta ɗan yi murmushi,
“gobe sai na kira Abban ka, na sanar masa ya je ya sami mahaifinta,”
ta ɗan girgiza kai cikin farin ciki,
“amma na yi farin ciki sosai.”

Zayd ya ɗan shafa kansa.
Daga ƙarshe ya mike, ya ɗan sunkuyo gabanta, ya sumbaci goshinta.
Sai cikin sanyin murya ya ce,

“Good night, my queen.”
Murmushin Ummie ya ƙara faɗaɗa,
“Good night, habibi.”
ta ɗan kalleshi,
“Allah Ya tashe mu lafiya.”

Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Amin.”

Sai ya juya, a hankali ya fara tafiya zuwa ƙofar.
Ummie ta bishi da kallo, kallon da ya ɗauki tsawon seconds.
Fuskarta cike da wani irin farin ciki da ita kanta ba ta iya ɓoye shi ba.

Sai ta sauke ajiyar zuciya.
A wannan daren… ta ji kamar komai ya fara komawa inda ya kamata.

(Jama’a ya naga Ummie na Neman mantawa da maganar auren Seemaa ne 🥺🫩)

——————

*MALALI*

Baffa bai shigo gidan ba sai wajen karfe goma na dare.
Kai tsaye da ya shigo gidan, ya nufi ɗakin Umma.

A lokacin, Raihana na kwance a kan doguwar kujera, jikinta a ɗan dunƙule, yayin da Umma ke zaune a ƙasa kusa da Aminu da Yusuf.
Hirar suke yi a hankali, suna dan dariya jefi-jefi.

Baffa ya ɗaga labulen ƙofar,
“Assalamu alaikum.”

Nan take Raihana ta ɗan motsa.
Ta tashi daga kwancen da take, sannan ta sauko ƙasa a hankali, tana ba Baffa waje.

Baffa ya shigo ya zauna.
Idanunsa suka sauka kan Aminu da Yusuf,
“har yanzu ba ku yi bacci ba?”

Aminu ya ɗan gyara zamansa,
“Baffa, yanzu za mu kwanta.”

Umma ta kallesu,
“toh ku je ku kwanta ko? ku yi fitsari kafin ku kwanta, sannan ku yi addu’a.”
“Tohm, Umma.”
Suka amsa kusan lokaci guda, sai suka mike suka nufi ɗakin Umma.

Raihana ma ta ɗan miƙe, za ta wuce zuwa ɗakinta, tana so ta ba su waje.
Amma kafin ta kai ƙofa, muryar Baffa ta dakatar da ita.

“Raihana…”
Ta tsaya,
“dawo ki zauna, magana za mu yi.”

Gabanta ya faɗi, nan take zuciyarta ta fara buguwa.
Allah Ya sa mutumin nan bai je ya faɗa wa Baffa abin da na ce masa ba…

Ta haɗiye wani irin yawu mai nauyi wanda ba ta san lokacin da ya taru a bakinta ba.
Sai ta dawo a hankali, ta tsuguna a gefen Umma.

Baffa ya ɗan kalleta, sai ya kalli Umma.
Daga nan idanunsa suka dawo kan Raihana.
Ya yi shiru na ƴan seconds, kamar yana neman hanyar da zai fara maganar.

Sai cikin nutsuwa ya buɗe baki,
“Raihana…”

Ta ɗago idanunta kaɗan,
“Zayd ya ce min kin amince ya turo.”

Kafin Baffa ya gama maganar —
Raihana ta zaro ido, ta ɗago kai da sauri.
Idanunta suka sauka kan fuskar Baffa cikin wani irin rashin fahimta.

Amma Baffa ya ci gaba kamar bai lura da yanayin da ta shiga ba,
“saboda haka na ba shi dama ya turo da magabatansa,”
ya ɗan dakata,
“duk lokacin da suka zo, za a tsaida ranar bikinku.”

Raihana ta daskare,
kamar an kashe duk wani motsi a jikinta.
Ta zauna cak, idanunta sun tsaya wuri guda.
Kwakwalwarta kuwa… ta kasa fahimtar abin da kunnenta suka ji.

Zayd?
Ta amince?
Yaushe?

Ta so ta buɗe bakinta, ta ce masa —
“Baffa, karya yake.”
“ba haka muka yi ba.”
“ban amince ba.”

Amma… babu ko ɗaya daga cikin kalaman da suka iya wuce harshenta.
Kamar wani katon dutse aka ɗora mata a kan harshe.
Ta kasa magana, ta kasa ko motsawa.
Sai kawai ta ji numfashinta yana fita a hankali.

Baffa kam ya dan jingina da jikin kujerar,
“shikenan, abinda zan sanar dake zaki iya tafiya.”

Ta danyi shiru kamar bata gane me yace ba.

A ƙarshe, ta miƙe.
Ta kasa kallon kowa a cikinsu, kawai ta juya.
A hankali ta nufi ɗakinta, kamar wadda ba ta san inda take zuwa ba.
Burinta ɗaya kawai — ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofar, ta samu wuri inda ba za a tambayeta komai ba.

Baffa ya bita da kallo har ta shige, sai ya dawo da kallonsa kan Umma,
“kin ji dai abin da ya faru.”
Umma ta ɗan jinjina kai,
“na ji.”
ta yi shiru na ƴan seconds, sai ta kalli Baffa da tambaya a idanunta.

“Toh, Malam…”
ta ɗan dakata,
“shi Haris ɗin nan me ya faru ne?”

Baffa bai amsa nan take ba, kawai ya yi shiru yana kallon gabansa.
Umma ta ci gaba a hankali,
“naga sai da ka yi bincikensa kafin ka bashi damar zuwa,”
“daga baya kuma sai ka ce ka fasa,”
ta ɗan karkatar da kanta,
“me ya faru?”

Baffa ya sauke ajiyar zuciya.
Ya yi shiru na ƴan seconds kafin ya ɗago idanunsa zuwa gare ta.

“Hajara…”
muryarsa ta fito cikin nutsuwa,
“wani abu ne da ba ya bukatar mu riƙa yin magana a kansa.”

Umma ta yi shiru.
Baffa ya ci gaba,
“na fasa ba da auren Raihana ne saboda wani babban dalili,”
ya ɗan dakata,
“amma yanzu ba lokacin yin bayaninsa ba ne.”

Umma ta kalleshi na ɗan lokaci,
ta san Baffa, idan ya rufe magana haka, babu abin da za ta iya tilasta masa ya faɗa.

Saboda haka ta ɗan sauke idanunta.
Baffa ya ƙara da cewa,
“ki yi ta addu’a kawai,”
“Allah Ya sa abin da muka yanke ya zama alheri a gare ta.”

Umma ta ɗan jinjina kai,
“In Shaa Allah.”

Baffa ya sauke ajiyar zuciya.

A ɗayan ɓangaren gidan kuwa…
Raihana ta rufe ƙofar ɗakinta, ta jingina bayanta da ita.
Sai ta lumshe idanunta.

A wannan karon… abin da ta kasa faɗa a gaban Baffa ya fara dawowa mata da ƙarfi a zuciya.

Zayd ya ce ta amince.
Amma ita… yaushe ta amince?

Kamar wadda aka zabura,
da sauri ta ƙarasa wajen study table ɗinta, kamar wani sabon tunani ne ya faɗo mata a take.

Idanunta suka fara yawo a kan teburin,
sai ta hango wani magazine da aka ba su a lokacin da suka yi wancan babban school event ɗin —
wanda aka yi collaboration tsakanin makarantar tasu da ARMAAN Group.

A lokacin ne Zayd ya zo makarantar,
a lokacin ne ita ma ta yi speech,
a lokacin ne komai ya fara ɗaukar wani irin sabon salo a tsakaninsu.

Raihana ta miƙa hannu da sauri, ta ɗauki magazine ɗin,
“Ya Allah…”
ta furta ƙasa-ƙasa.

Ta fara buɗe shafuka ɗaya bayan ɗaya, hannunta na rawa.
Ta wuce wani page, ta dawo, ta sake buɗewa.

“Where is it…?”
ta furta cikin tashin hankali.

Ta san akwai contact numbers a cikin magazine ɗin,
tun da event ɗin collaboration ne tsakanin makarantar tasu da ARMAAN, an saka bayanan kamfanin da wasu lambobin sadarwa.
Kuma a yanzu… ita ce kaɗai hanyar da take da ita.

Ta fara laluben pages ɗin da sauri, idanunta suna yawo kan rubuce-rubucen da suke cike da shafukan.
Sai ta tsaya, wasu numbers suka bayyana a gabanta, guda hudu.

Ta kankance idanunta, ta sake dubansu.
Zuciyarta ta ƙara bugawa, ba ta san wanne ne na Zayd ba.
Amma ba ta da lokacin tunani.

Ta ɗauko wayarta da sauri, hannunta yana rawa sosai.
Ta buɗe contacts, sai ta fara kwashe lambobin ɗaya bayan ɗaya.
Numfashinta yana fita da sauri.

Ta kalli screen ɗin wayarta sai ta haɗiye yawu.
A wannan lokacin… ba ta damu da kunyar da take ji ba, ba ta damu da abin da Zayd zai ce ba.
Abu ɗaya kawai yake cikin kanta, dole ta same shi, dole ta ji daga bakinsa.
Domin ba za ta iya yarda da cewa ta amince da wani abu da ba ta taɓa cewa eh ba.

Ta sake kallon lambobin, yatsarta ta tsaya kan number.
Ta yi shiru na ƴan seconds, sai ta sauke ajiyar zuciya.

“Allah Ya sa…”
ta kasa ƙarasa maganar, kawai ta danna number ɗin.
Wayar ta fara ringing.

—————

A ɗayan ɓangaren kuwa…
Sameer yana kwance a kan gadonsa, ya riga ya yi shirin bacci.
Dakin ya yi shiru, sai hasken bedside lamp da ke kusa da shi kawai ke haskawa a gefen gadon.

Ba zato ba tsammani, wayar Zayd ta office wacce shi ke handling dinta ta fara ringing.

Sameer ya ɗan motsa, ya dan yamutsa fuska kaɗan, kamar wanda ba ya son ya ɗauki waya a wannan lokacin.
Amma ringing ɗin ya ci gaba.

A ƙarshe ya miƙa hannu ya ɗauki wayar, ya kalli screen ɗin.
Unknown Number.

Ya yi shiru na ƴan seconds, wani irin tunani ya ratsa zuciyarsa, wa zai kira wayar office yanzu?

Sai ya ɗaga wayar zuwa kunnensa,
“Assalamu alaikum.”

A ɗayan ɓangaren, Raihana ta sauke ajiyar zuciya.
Amma da ta ji muryar… ta gane, ba muryar Zayd ba ce.

Sai ta ɗan lumshe idanunta, amma ta daure.
Cikin ladabi ta ce,

“Wa alaikumus salam, dan Allah yi haƙuri…”
ta ɗan dakata,
“na kira yanzu a daren nan.”

Sameer ya ɗan gyara zamansa,
“babu matsala.”
sai ya ɗan yi shiru,
“da wa nake magana?”

Raihana ta sake haɗiye yawu,
“Raihana,”
ta ɗan dakata,
“Raihana Musa Maiturare… daga Malali.”

Sameer ya ɗan zaro ido,
“Barka da dare, Madam,”
muryarsa ta ƙara nuna girmamawa,
“an yini lafiya?”

Raihana ta ɗan yi shiru,
kamar hankalinta bai ma kan gaisuwar yake ba.
Sai ta kalli wayar da take riƙe da ita tabbatar zabga mata wata uwar harara kamar Zayd din ne yake cikin screen ɗin.

Daga ƙarshe ta daure,
“uhmm…”
ta ɗan sauke numfashi,
“dan Allah… ina son magana da shi ne? Yana kusa?”

Sameer ya ɗan yi shiru,
“Boss?”

Ta wani juya ido da takaici, ji wani rainin hankali, to da wa uban wa nake nema?
amma a zahiri sai tace,
“eh.”

Sameer ya kalli agogon gefen gadonsa, sai ya amsa kai tsaye,
“A’a, baya nan.”

Raihana ta lumshe idanunta,
ƙaramin disappointment ya bayyana a fuskarta.

Amma kafin ta ce komai, Sameer ya ƙara,
“amma bari na sanar masa,”
ya ɗan dakata,
“zan tura miki number ɗinsa right away.”

Raihana ta buɗe idanunta,
“yauwa…”
muryarta ta fito da ɗan sauri,
“na gode sosai.”
ta ɗan yi shiru,
“dan Allah… ina jira yanzu.”

“Babu komai.”
Sameer ya amsa cikin ladabi, sai kiran ya katse.

Ya sauke wayar daga kunnensa, ya ɗan kalli screen ɗin.
Raihana Musa Maiturare.

Ya ɗan yi wani murmushi,
“Raihana…?”
ya furta ƙasa-ƙasa, sai ya girgiza kai.

Bai ɓata lokaci ba, ya fara neman layin Zayd.
Amma wannan karon… har shi kansa ya fara tunanin —
me ya sa Raihana ta kira Boss da wannan lokacin?




Not edited