THE SMILE AFTER THE NİKAH
ZAYD ARMAAN
CHAPTER FIFTY:50
THE SMILE AFTER THE NIKAH
JIDDAAH BARKUM
——————-
Bayan fitowarsu daga masallaci, sai suka ɗan tsaya a bakin harabar masallacin, suka sake gaisawa. Ana ta godiya daga wannan gefe zuwa wancan, kowanne yana nuna farin cikinsa da yadda Allah Ya sauƙaƙa komai.
Har Baffa ya ɗan yi murmushi, “Godiya nan ta yi yawa fa…”
Alhaji Minzali ya fashe da dariya, “Ai dole mu gode.” Ya ɗan girgiza kai cikin farin ciki, “Mun zo neman a saka rana ne… Allah cikin ikonSa sai gashi mun koma da yarinya guda.”
Dukkansu suka yi murmushi.
Alhaji Minzali ya ƙara da cewa, “Mungode sosai. Allah Ya sa an kulla alheri.”
Baffa ya ɗan jinjina kai, “Ba komai.” Ya ɗan yi shiru, “Haka Allah Ya ƙaddara.”
Imraan kuwa yana can kusa da su, fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi da ya kasa ɓoyewa.
Malam Sammani da Baffa suka karasa musu rakiya zuwa wajen motocinsu. Da suka isa wajen motocinsu, sai suka sake tsayawa aka sake musafaha, suka sake yin godiya.
Alhaji Minzali ya kalli Baffa cikin girmamawa, “Allah Ya saka da alheri, Alhaji Musa.”
Baffa ya ɗan matse hannunsa, “Amin. Allah Ya sa alheri a cikin abin da muka yi.”
“Āmin.” Malam Sammani ma ya amsa.
Daga nan aka fara sallama, “Allah Ya tsare hanya.”
“Āmin.”
“A sauka lafiya.”
“In Shaa Allah.”
Motocin suka fara motsawa a hankali. Baffa da Malam Sammani suka tsaya suna kallonsu har suka fara nisa, sai Baffa ya ɗan daga hannu, su ma suka ɗaga musu hannu daga cikin motar. A ƙarshe motocin suka ɓace daga gani.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya. Malam Sammani ya dan kalleshi, sai ya ɗan yi murmushi, “Allah Ya sa alheri.”
Baffa ya jinjina kai, “Āmin.”
Sai suka juya. Har suka dawo kofar gidan, a hankali suke tafiya, suna ta ɗan tattaunawa cikin nutsuwa.
———-
Baffa yana shiga direct cikin tsakiyar gidan ya nufa. Bai ce wa kowa komai ba, kai tsaye ya wuce ya zauna a gefen tabarma, ya sauke jikinsa a hankali. Ya cire hularsa, ya ajiye ta gefensa.
Mama Sabuwa kuwa... ta zuba masa ido kamar wadda ta daɗe tana jiran wannan lokacin. Ta ɗan karkatar da kanta, “Malama wai lafiya?”
Baffa ya ɗago idanunsa ya kalleta.
“Sai shige da fice kake yi…” Ta ɗan nuna shi da hannu, “Ba ka mana bayanin komai ba. Muna tare da kai a ɗaki, aka aiko kiranka… Amma da ka shigo sai ka wuce wajen Hajara. Ka sake wuce mu…” Ta ɗan tsaya, “Ka fita.”
Sai ta ƙara kallonsa da mamaki, “Yanzu kuma ka shigo ka yi jigim.” Ta ɗan buɗe baki, “Ko mutuwa aka aiko mata, an yi ne daga can ƙasar tasu kuke ta ɓoye?”
Baffa ya ɗan kalleta, sai kawai ya girgiza kai, bai ce komai ba.
Mama Sabuwa ta ɗan matse leɓenta, “Yo meye abun boye rashi kuma Allah na tuba.”
Baffa ya sake kallonta, sai ya sauke ajiyar zuciya, bai ce komai ba.
Ita dai Mama Indo... shiru tayi, amma idanunta suna yawo daga Baffa zuwa Mama Sabuwa. Ita ma tana son jin abin da ya faru.
Sai a take akayo sallama a kofar gida, “Assalamu alaikum!”
Sallamar da ta fito daga bakin ƙofar gidan ta sake sa kowa ya ɗago kai. Baffa ya mike, kai tsaye ya nufi ƙofar.
Da ya isa, Imraan ne tsaye. Gefensa jibge da carton ɗin alawa goro da kuma wani uban dabino.
Baffa ya ɗan tsaya, idanunsa suka sauka kan kayan. Sai ya ɗan buɗe baki, “Haba…” Ya ɗan girgiza kai, “Ai da duk ba ayi wannan ba.”
Imraan ya danyi dariya, “Baba…” Ya ɗan ɗaga carton ɗin, “Ai ba a daura aure ba goro ba.”
Baffa ya ɗan yi murmushi.
Imraan ya shigo kaɗan, ya ajiye kayan, sai ya sake komawa ya ɗebo sauran. Da ya dawo, ya ɗora su gefe. Daga nan ya dubi Baffa da ɗan murmushi, “Zan wuce, Baba.”
Baffa ya gyada kai, “Toh, Madallah.”
Imraan ya yi murmushi, “Na gode sosai.”
“Ba komai.”
Imraan ya juya, ya nufi motarsa, ya shiga, ya bar layin.
Baffa kuwa ya tsaya yana kallonsa na ƴan seconds, sai ya juya ya koma cikin gida niki-niki da kayan da aka kawo. Ya ajiye su, sai ya sake komawa ya ɗebo sauran.
Mama Sabuwa tana kallonsa, ta kasa ƙara jurewa. A hankali ta mike, ta ɗan tsaya, “Malam…”
Baffa ya kalleta.
Ta matsa kaɗan gaba, “Ka yi wa darajar Allah da Manzonsa…” Muryarta ta ɗan ɗauki nauyi, “Ka faɗa mana abin da ke faruwa.” Ta nuna kayan, “Wallahi ka bar mu cikin duhu. Wannan alawar da kayan daurin auren…” Ta kalli Baffa kai tsaye, “…na meye kuma?”
Baffa ya ɗan tsaya, ya kalleta sama da ƙasa, sai ya sauke idanunsa kan kayan, kamar yana jin daɗin ganin yadda ta kasa haƙuri. Daga ƙarshe ya ce cikin nutsuwa, “An daura auren Raihana ne da Zayd.”
Shiru.
Mama Sabuwa ta tsaya cak, idanunta suka ƙara buɗewa, sai ta ɗan ja numfashi kamar kalmar ta buge ta a kirji, “Raihana…?” Ta maimaita a hankali, sai kuma ta ɗago kai, “Wacce Raihana kuma? Raihana ta Hajara?”
Baffa ya ɗan gyada kai, “Eh.”
“Haba!” Ta ɗan yi wata irin dariya, dariyar mamaki ce mai ɗauke da kasa yarda da abinda taji, “Wanne irin aure?” Ta girgiza kai, “Kamar kuma wasan yara! Shi kuma waye Zayd ɗin?” Ta ɗan matsa gaba, “Ko Haris dai?”
Baffa ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, kamar ya kasa yarda da tambayar, sai ya buɗe su ya kalli Mama Sabuwa, “Zayd.” Ya faɗa a nutsuwa, “Zayd Armaan.”
Mama Sabuwa ta yi shiru, kamar yanzu ne sunan ya fara shiga kanta. Sai idanunta suka koma kan kayan da Imraan ya kawo, daga nan ta koma kan Baffa, sai ta sake bude ido cike da hassada, “Zayd Armaan…?” Ta furta ƙasa-ƙasa.
Mama Indo kuwa har yanzu shiru tayi saboda ita ta fara fahimtar inda zancen ya dosa.
Mama Sabuwa ta sake zabura, idanunta suka sauka kan Baffa, “Wanda kake aiki a kamfaninsa…” Ta ɗan dakata, “Kuma wanda aka ga hotunanshi da Raihana suna yawo a duniya…” Ta ɗan kankance idanunta, “Shine ya aure ta?”
Baffa ya zuba mata ido, bai ce komai ba.
Sai Mama Indo ta ɗan girgiza kai, “Toh, banda abinki Sabuwa…” Ta ɗan yi murmushi, “Tunda kika ji haka, ai hakan ne mana.”
Mama Sabuwa ta zabga mata wata uwar harara, “Kingaaa…” Ta ɗaga hannu, “Ba dake nake magana ba.” Sai ta maida kallonta kan Baffa, “Shine ko, Malam?”
Baffa ya ɗan gyada mata kai, kawai, amma kamar wanda yake jiran abin da zai biyo baya domin ya san Mama Sabuwa, idan ta fara da wannan yanayin ba za ta tsaya a nan ba.
Sai Mama Sabuwa ta ɗan yi shiru, kamar yanzu ne ta haɗa komai a kanta, sai ta buɗe baki a hankali, “Ahaaa…” Ta ɗan yi dariya, “Ko da na ji…” Ta ɗan kankance ido, “…biri ai ya yi kama da mutum.” Ta sake yin wata ƙaramar dariya mai cike da hassada, “Ashe dai kowa yana son abin duniya. Ake ganin ni kadai ce mai son abin duniya a gidan nan.”
Baffa ya ɗaga idanunsa zuwa gare ta, amma bai ce komai ba.
“Sabida anga Allah Ya daga Bintu ya bata farinjini tana juya kudi yanda take so samarin ta kaff ba na yada wa kuma cikinsu kowa bajinta yake mata…” Ta ɗan juya kai, sai ta sake kallon Baffa daga sama har ƙasa, ta yi wata dariya, “Ashe kai ma uban nasu haka kake? Toh son abin duniya mana!” Muryarta ta ƙara ɗaukar zafi, “Tunda gashi kiri-kiri mai zuwa wajenta ka hana, ka ba wani saboda shi yana da kuɗi.” Ta ɗan ja tsaki, “Ko dai babban sirrinsu kuke son rufewa? Wanda aka riga aka gani a duniya?” Ta ɗan yi wata dariya, “Shine aka yi wa kura lullubi da fatar akuya?”
Shiru. Baffa yana nan, yana kallonta. Fuskarsa ta fara sauyawa a hankali, amma bai katse ta ba.
Mama Indo kuwa ta yi shiru, babu abin da ta ce.
Sai Bintu wadda take cikin ɗakinta ta ji hayaniyar muryar Mama Sabuwa, a hankali ta fito ta tsaya bakin ƙofar, idanunta suka sauka kan mutanen. Mama Sabuwa kuwa ba ta ma lura da ita ba, ta cigaba, “Wannan gagarumin abun kunya da girma yake.”
Baffa ya yi shiru. Umma ma dake falo ta dan leko kawai ta tsaya a kofar dakin.
Mama Sabuwa ta ci gaba da zuba kalamai, “Daga ji…” Ta ɗan juya kai, “Raihana halin Hajara ta ɗauko. Yo matar da ta bar iyayenta da danginta…” Ta girgiza kai, “Ta zaɓi saurayi ta taho har wata duniya.” Ta ɗan yi dariya, “Meye kuma abin da ta haifa ba zai aikata ba? Wato kun rufe wancan abinda suka aikata da wannan aure?” Ta yi wani irin ihu na raini, “Na gane!” Ta ɗan dafe kirjinta, “Aure kenan? Huuhuu…” Ta yi wani irin dariya mai cike da baƙin ciki da hassada, “Munafurcin gidan nan…” Ta kalli Baffa kai tsaye, “…ba babba ba, yaro!”
A nan ne Baffa ya sauke ajiyar zuciya a hankali. Ya ɗaga idanunsa ya kalleta, fuskarsa ta riga ta daina ɗaukar ko wanne irin reaction. Muryarsa ta fito ƙasa, amma ta yi nauyi, “Sabuwa…”
Ta tsaya tana wani kalkınsa cike da rashin mutunchi.
Baffa ya sake maimaitawa, “Sabuwa.”
Ta kalleshi.
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya faɗa cikin cikakkiyar nutsuwa, “Na sake ki saki ɗaya.”
…
Shiru. Mama Sabuwa ta daskare, Mama Indo ta ɗago kai, Bintu kuwa ta tsaya bakin ƙofa, idonta a buɗe. Umma ta dan bude baki kamar kowa a gidan ya manta da abin da yake yi.
Baffa kuwa bai ƙara cewa komai ba. Kawai ya ɗauki hularsa daga gefensa, ya miƙe a hankali, sai ya kalli Mama Sabuwa na ƴan seconds—kallon da ya fi kowace magana nauyi. Daga nan ya juya, ya bar su a wajen.
Mama Sabuwa kuwa ta tsaya cak. A wannan karon, ba ta sami kalmar da za ta fito da ita ba.
Sai Mama Indo ta ɗan sauke ajiyar zuciya, Bintu kuma ta kalli Mama Sabuwa, sai ta haɗiye yawu domin duk abin da ta ji, ya wuce yadda ta zata.
———-
A ARMAAN MANSION kuwa, Inno ta dubi Ummie a hankali, ta ɗan yi shiru kamar wadda take nazarin duk abin da aka faɗa mata. Sai ta sauke numfashi, “Ba laifi…” Muryarta ta fito cikin sanyin murya, “Allah Ya sanya alkhairi a wannan aure.”
Ummie ta ɗan lumshe idanunta, “Amin.”
Inno ta sake kallonta, “Wacece yarinyar kuma?” Ta ɗan dakata, “Su waye iyayenta?”
Ummie ta yi shiru na ƴan seconds kamar tana tunanin yadda za ta fara. Daga ƙarshe ta ce a nutse, “Itace yarinyar da aka haɗa hotunansu kwanakin baya.”
Inno ta ɗan kankance idanunta.
Ummie ta ci gaba, “Ni ce da kaina na je gidan iyayenta, na nemawa Zayd ita.”
Inno ta yi shiru tana kallonta.
Ummie ta ɗora, “Na yi hakan ne saboda reputation ɗin yarinyar. Kin san irin tsangwama da ƙyarar da za ta iya fuskanta…” Ta ɗan dakata, “Musamman saboda irin environment ɗin da muke.”
Inno ta yi shiru, idanunta suka sauka ƙasa kamar tana nazarin kowace kalma. Daga ƙarshe ta ɗago kai, “Kinyi daidai, Hajja Fatima.” Muryarta cike take da gamsuwa, “Ko wace uwa abinda za ta yi kenan.” Ta ɗan yi murmushi, “Allah Ya sanya an kulla alheri.”
Ummie ta sauke ajiyar zuciya. Wani irin farin ciki ya cika zuciyarta. A ƙarshe, Inno ta fahimci dalilin da ya sa ta yi abin da ta yi, ta kuma gamsu da hujjar da ta bata. Ko da ba komai, ta gode wa Allah.
Ba a daɗe ba, sai aka jiyo sallamar Alhaji Minzali a bakin ƙofar ɗakin, “Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.” Aka amsa daga ciki.
Alhaji Minzali ya shigo, fuskarsa cike da fara’a. Kai tsaye ya ƙarasa gaban Inno, ya zube yana gaisheta cikin girmamawa, “Barka da rana, Hajiya.”
“Barka da zuwa.”
Bayan ɗan lokaci, Alhaji Matawalle da Alhaji Rabiu suka shigo. Sai aka sake gaishe-gaishe. Daga nan suka fara bayyana abin da ya faru. Ana ta sambarka, ana ta yabon Baffa, ana faɗin yadda komai ya gudana cikin sauƙi fiye da yadda suka zata.
Alhaji Minzali ya yi murmushi, “Wallahi Hajiya…” Ya girgiza kai, “Mahaifinta ya girmama mu sosai. Da muka je, ya tarbe mu kamar baƙin da yake jira. Ya zaunar da mu, ya saurare mu, har ma lokacin da muka kawo maganar daurin aure…” Ya ɗan yi dariya, “…ya ce ba zai yanke hukunci shi kaɗai ba. Ya ce dole ya ji ra’ayin mahaifiyar yarinyar.”
Inno ta ɗan gyara zamanta.
Alhaji Minzali ya ci gaba, “Amma gaskiya…” Ya ɗan yi murmushi, “Zayd ya samu yarinya daga gidan manyan mutane. Malam Musa fa mutum ne mai mutunci. Ko da muka shiga gidansu, tabbas nan ake cewa gidan mutanen arziki.” Ya ɗan kalli sauran, “Amma abin da ya fi bani mamaki… mahaifiyarta.”
Ummie ta ɗago gira, Alhaji Minzali ya kalleta, “Wallahi Hajiya, ba mu daɗe ba. Ya shiga, ya sanar da ita, ba ta yi wata doguwar magana ba.” Ya ɗan yi dariya, “Ko mintuna ashirin baiyi da shiga ba ya fito yace ta amince.” Ya girgiza kai cikin farinciki, “Wallahi Hajiya, na ga mutunci sosai a wannan gidan.”
Inno ta dubesu ɗaya bayan ɗaya, sai ta gyara murya, “Toh… tunda Allah Ya nufa an daura masa wannan aure, ina mai matuƙar farin ciki. Allah Ya sa mutuwa ce kawai za ta raba su.”
“Amin.”
“Amin.” Kowa ya amsa.
Inno ta yi ɗan shiru, sai ta sake magana, “Amma…” Fuskarta ta ɗan sauya, “Duk da haka…” Ta kalli Ummie kai tsaye, “Har yanzu ina nan a kan bakata.”
Ummie ta tsaya cak.
Inno ta ci gaba cikin cikakkiyar nutsuwa, “Zayd ya auri Seeyama.” Ta ɗan dakata, “Ban janye ba. Aurensa da wannan yarinyar…” Ta yi ɗan shiru, “…ba zai hana auren Seeyama ba.”
Kowa ya yi shiru. Alhaji Minzali ya kalli Alhaji Matawalle, Alhaji Matawalle ya kalli Alhaji Rabiu, kowa yana neman wanda zai fara magana.
Ummie kuwa, zuciyarta ta yi wani irin tsalle sabida a zuciyarta tana tunanin tunda Zayd ya yi aure, Inno za ta janye maganar Seeyama, musamman ganin ba ta sanar da kowa ba. Amma yanzu ta ji maganar kai tsaye daga bakinta, sai dole ta yi murmushi, ta jinjina kai, “Ai yadda kika zartar haka za a yi. Allah Ya sanya alkhairi, Ya haɗa kawunansu.”
“Amin.” Aka sake amsawa.
Shiru ya sake sauka. Alhaji Minzali ya kalli Alhaji Matawalle, Alhaji Matawalle ya kalli Alhaji Rabiu, sai suka yi shiru kamar kowannensu yana jiran ɗayan ya fara. Amma cikin ikon Allah, ba wanda Allah Ya ba damar magana a lokacin.
—————
Kasancewar yau Lahadi ce, gidan ya ɗan yi wani irin shiru na ƙarshen mako. Tun bayan da Zayd ya tashi da safe, ya yi breakfast wajen ƙarfe goma sha ɗaya, daga nan ya koma ɗakinsa ya ɗan kwanta. Wajen ƙarfe ɗaya ya tashi, ya yi sallah. Bayan ya gama, kai tsaye ya nufi gym ɗinsa.
Gym ɗin yana ɗaya daga cikin manyan rooms ɗin ARMAAN Mansion, an tsara shi cikin wani irin salon da ya dace da halin Zayd—simple, clean, amma cike da kayan motsa jiki na zamani. Manyan mirrors ne suka mamaye bango ɗaya, a gefe kuma akwai dumbbells da aka jera cikin tsari, bench press, cable machines da sauran kayan motsa jiki. Hasken rana yana shigowa ta manyan glass windows, yana haskaka wajen ba tare da ya yi yawa ba.
Zayd kuwa yana cikin nashi world din. Black fitted T-shirt ne a jikinsa, wanda ya manne da upper body ɗinsa ba tare da ya yi yawa ba, black joggers, white sneakers, a kunnensa kuwa akwai EarPods. Yana tsaye a kan treadmill, yana tafiya da wani steady pace, hannunsa ɗaya yana riƙe da bottle ɗin ruwa. Fuskarsa babu ko alamun wasa, cikakkiyar nutsuwa, idanunsa suna kallon gaba.
Amma duk da haka, tunani ɗaya yana ta dawo masa lokaci-lokaci. Malali. Yanzu da ya tuna da abin da ya faru jiya, yadda Raihana ta kira shi da kanta, yadda ta fara magana ba tare da shakkar komai ba, yadda ta zuba masa lecture har kusan ta manta da numfashinta, sai murmushi ya subuce masa. Ƙarami, ba tare da ya shirya ba. Ya ɗan girgiza kai kamar yana ƙoƙarin korar tunanin, sai ya ƙara saurin treadmill ɗin, amma bai yi nisa ba tunanin ya dawo.
“Wallahi ba na sonka.”
Ya ɗan lumshe idanunsa, wani murmushi ya sake bayyana a gefen bakinsa kamar shi kansa ya kasa gane dalilin da ya sa abin yake ba shi nishaɗi.
A dai-dai lokacin, Imraan ya fito daga corridor din study room din Zayd, ya fara neman shi. Ya fara ɗuba ɗakin Zayd, babu shi. Ya sake kallon study room, shima babu shi. Ya ɗan dafe haɓarsa, “Hmm…” Sai ya ɗan yi murmushi. Ya san Zayd, idan ba bedroom ba, study room, idan ba biyun nan ba, to gym.
Kai tsaye ya nufi gym ɗin. Da ya isa bakin ƙofar, sai ya tsaya, ya leƙa ciki. Nan take murmushi ya bazu a fuskarsa domin abin da ya gani ya isa ya ba shi dariya. Zayd a kan treadmill, EarPods a kunnensa, cikin serious expression ɗinsa.
Imraan ya ɗan girgiza kai, sai ya jingina da door frame, ya kalli Zayd na wasu seconds, sai wata dariya ta kubce masa, “Hmm…” Ya furta ƙasa-ƙasa, “Yanzu fa…” Ya sake kallon Zayd, “wannan guy din ya samu mace.” Ya ɗan cije lips ɗinsa yana ƙoƙarin hana dariya, “Ba wacce ake cewa tana crushing ɗinsa ba… matarshi.” Sai ya sake yin wata dariya, “Allah…” Ya girgiza kai, “Zaydu kana cikin alkhairi.”
Ya ƙara kallonsa. Zayd kuwa ko gezau, bai san yana nan ba.
Imraan ya shigo cikin gym ɗin a hankali, ya ci gaba da kallonsa yana murmushi har ya ƙarasa kusa da treadmill ɗin. Zayd yana nan cikin natsuwarsa, waƙa tana playing a kunnensa, tunaninsa kuma har yanzu yana can wani waje daban.
Imraan ya tsaya kusa da shi, ya jira. Babu reaction. Ya ɗan ƙara matsowa, still nothing. Sai ya ɗan daki kafadar Zayd.
Zayd ya ɗan karkata kai da sauri, idanunsa suka sauka kan Imraan.
Imraan ya ɗaga gira, sai ya nuna kunnen Zayd da yatsa, “EarPods.” Ya motsa hannunsa yana nuna masa ya cire su.
Zayd ya kalle shi na ƴan seconds, fuskarsa babu komai, sai ya ɗaga hannu ya cire ɗaya daga cikin EarPods ɗin, “Me?” Muryarsa ta fito cikin nutsuwa.
Imraan ya yi murmushi, “Me?” Ya maimaita, sai ya kalli Zayd daga sama har ƙasa, “Na zo ne in ga ko da gaske ka fara zama husband.”
Zayd ya ɗan kalleshi.
Imraan ya ƙara murmushi, “Amma na ga alamun sun fara bayyana.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira, “Imraan.” Muryarsa kaɗai ta isa.
Imraan ya ɗan yi dariya, “Okay, okay…” Ya ɗaga hannayensa sama kamar wanda aka kama, “Mr. Serious.” Sai ya ɗan kalli treadmill ɗin, “Amma gaskiya…” Ya sake kallon Zayd, “…matar ka ta sa ka fara murmushi kai kaɗai a gym.”
Zayd ya yi shiru.
Imraan ya ƙara dariya, “Wallahi na gani.”
Zayd ya sauke idanuwansa, sai ya ɗauki bottle ɗin ruwansa, “Ka zo ka yi magana ne?”
Imraan ya yi murmushi, “A’a.” Ya ɗan karkatar da kai, “Na zo ne in ga sabon married man ɗinmu.”
Zayd ya ɗan kalleshi, sai ya sake saka EarPod ɗin, “Get out.”
Imraan ya fashe da dariya, “Ahhh! Wai duk wannan attitude din I hope ka sani ba zaka shiga dakin amarya da wannan ba?”
Zayd ya ci gaba da tafiyarsa a kan treadmill kamar bai ji shi ba.
Imraan ya tsaya yana kallonsa, sai ya girgiza kai da murmushi, “Allah Ya taimake ka, Zaydu. Wannan aure…” Ya ɗan yi shiru, sai ya ƙara da murmushi, “Kai, dallah, rascal…”
Imraan ya ɗan matsa kusa da shi, “Look here.”
Zayd ya yi masa banza, kawai ya ci gaba da abin da yake yi.
Imraan ya ɗan kalli fuskarsa, sai ya yi murmushi, “Mun je mun nema maka aure… kuma guess what?”
Zayd bai ko kalleshi ba, kamar maganar ba ita yake ji ba.
Imraan ya fashe da wata ƙaramar dariya, “Okay.” Bai sake cewa komai ba, kawai ya saka hannunsa cikin pocket ɗinsa, ya ciro wayarsa, ya buɗe wani video. Imraan ya ɗaga volume ɗin wayar sosai, sai ya dawo gaban Zayd, ya ɗaga screen ɗin wayar daidai gaban fuskarsa.
Zayd ya ɗan kalli wayar daga gefen ido, amma bai nuna wata alama ba, sai kawai ya ci gaba da motsa jikinsa a kan treadmill.
Imraan ya yi murmushi, “Watch.”
Zayd ya yi banza, amma kunnensa ya fara ɗaukar sautin da ke fitowa daga wayar. Muryoyin jama’a, hayaniyar masallaci, sannan muryar liman ta fara fito wa fili, “Alhaji Matawalle…”
Zayd ya ɗan rage gudun treadmill ɗin, kawai kaɗan.
Imraan ya lura, amma bai ce komai ba, ya ƙara kusantar da wayar.
Zayd ya ɗan dago kansa, idanunsa suka sauka kan screen ɗin, ya yi shiru. Sautin liman ya ƙara fitowa a sarari, “Alhaji Matawalle, ka karɓa wa Ahmad Abdulrahman…”
Ƙaramin motsi ya tsaya a fuskar Zayd. Treadmill ɗin yana ci gaba da tafiya, amma hankalinsa ya daina kasancewa a jikinsa. Kunnuwansa sun kama kowace kalma.
“Raina Musa Maiturare.”
Zayd ya ɗan ƙara kallon screen ɗin, a wannan karon ba daga gefen ido ba, kai tsaye. Idanunsa suka sauka kan mutanen da ke zaune a wajen—Alhaji Matawalle, Alhaji Minzali, Baffa, Alhaji Rabiu, da sauran jama’ar da bai ma gane su ba.
Sai muryar liman ta sake cika wajen, “Ka karɓa?”
Alhaji Matawalle ya ɗaga kansa, “Na karɓa.” Muryarsa ta fito a sarari, “Na karɓa masa.”
Wani irin shiru ya ratsa tsakanin su na ɗan seconds, sai aka jiyo muryoyin jama’a, “Alhamdulillah. Allah Ya sanya albarka.”
Zayd bai ce komai ba. Treadmill ɗin ya rage gudu sosai.
Imraan kuwa har yanzu yana tsaye a gabansa, murmushi ɗauke a fuskarshi kamar wanda yake jiran reaction ɗin da ya san zai samu.
Zayd ya ci gaba da kallon screen ɗin, kunnuwansa kuwa sun cigaba da karɓar sautin da ke fita daga wayar, “Raihana Musa Maiturare…” Sunanta ya sake ratsawa cikin kunnensa.
Sai ya yi wani irin shiru. Ba irin shirun da yake yi idan Imraan yana tsokanar sa ba, wannan wani irin shiru ne daban, kamar yanzu ne kawai yake sauraron kalmomin da aka faɗa masa. Sai ya sauke idanunsa daga screen ɗin, ya kalli gabansa. Treadmill ɗin ya tsaya.
Imraan ya ɗan ɗaga gira, amma bai ce komai ba.
Zayd ya cire EarPod ɗin ɗayan kunnen, sai ya kalli Imraan a hankali, fuskarsa har yanzu a sanyaye, “Ka gama?”
Imraan ya yi murmushi, “Ban fara ba ma.”
Zayd ya ɗan kalleshi.
Imraan ya fashe da dariya, “Congratulations, Mr. Married Man.”
Zayd ya ɗan sauke numfashi, sai ya kalli screen ɗin wayar kuma na ɗan lokaci. A cikin idanunsa, wani abu ne da Imraan bai saba gani ba—ba mamaki ba ne kawai, ba farin ciki kawai ba, akwai wani irin realization, kamar yanzu ya ji kalmar aurensa da kunnensa, ya kuma ga mutanen da suka tsaya a madadinsa, ya ji sunan matar da aka ɗaura aurensa da ita.
Wani shegen murmushi ya subuce masa, kawai sai ya juya ya ɗauki towel ɗinsa ya goge zufar da ke gefen goshinsa.
İmraan ya fashe da dariya, “Wallahi rascal kai munafiki ne! Ji fa yanda da farko ka share kamar abun bai shige ka ba amma yanzu…” Ya dan leko Zayd, “murmushi fa kakeyi.”
Zayd ya sake wani dan murmushi har hakoransa suka bayyana, daga nan kawai ya mike ya nufi kofa yana sake daga bottle din hannunsa yana zuba ruwan a bakinshi.
Not edited