ZAYD ARMAAN

THE UNFORESEEN VOW

by @jiddaahbarkum



ZAYD ARMAAN

CHAPTER FIFTY ONE:51

THE UNFORESEEN VOW

JIDDAAH BARKUM

————-
Raihana da Maryam ba su dawo gidan ba sai wajen ƙarfe shida na yamma, lokacin ana gab da kiran magariba. Da suka isa bakin ƙofar gidan, sai suka tarar da Baffa ya idar da alwala kenan. Nan take suka durƙusa har ƙasa cikin girmamawa suka gaishe shi.
Baffa ya kallesu ɗaya bayan ɗaya, “Ya kuka bar Fauziyya? Jikinta da sauƙi?”
Raihana ta ɗan gyada kanta kafin ta amsa, “Eh, Baffa. Da farko ma kwana za mu yi, amma sai muka ga gwara mu dawo. Muka ce gobe da safe sai mu koma.”
Baffa ya ɗan jinjina kai, fuskarsa babu wani canji na musamman, “Toh, ba laifi. Ku shiga gida. Allah Ya sauketa lafiya.”
“Amin.”
Suka mike a hankali suka nufi ƙofar gidan. Amma da suka shiga tsakar gida, Raihana ta tsaya na ɗan lokaci.
Wani irin shiru ne ya mamaye gidan, ba shiru na yau da kullum ba. Shiru ne mai nauyi, wanda yake sa mutum jin kamar akwai wani abu da ya faru, amma babu wanda ya furta shi. Tun bayan abin da ya faru da rana, gidan ya sauya, babu dariyar da aka saba ji, babu hayaniyar gidan zaman tsakar gida ma da akeyi da daddare yau baayi ba, babu motsin mutane kamar yadda ya kamata. Komai ya yi tsit.
Maryam ta ɗan kalli Raihana, sannan ta nufi ɗakinsu, “Rayy, bari na yi sallah sai na zo.”
Raihana ta ɗan gyada kai, “Toh.”
Ita kuma kai tsaye ta nufi ɗakin Umma. Da ta shiga falon, sai ta sake tsayawa, babu kowa, komai yana a gyare tsaf. An share falon, kayan daki suna nan yadda aka saba, sannan ƙamshin turaren wuta ya cika wajen, yana yawo a hankali kamar yana ƙoƙarin rufe wani abu da ba a iya gani.
Raihana ta ɗan ja numfashi, wani abu ya faɗa mata cewa akwai abin da ya faru yau a gidan nan. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Umma, ta same ta zaune a kan sallayarta, carbi yana yawo a hankali tsakanin yatsunta. Fuskarta a sake take, amma idan aka duba sosai, idanunta ba sa nan, kamar tana wani wuri daban gaba ɗaya, tana cikin zurfin tunani.
Raihana ta ƙaraso, ta zauna kusa da ita. Umma ba ta sani ba. Raihana ta kalleta na ƴan seconds, “Umma…”
Babu amsa.
Ta ɗan taɓa hannunta, sai Umma ta ɗago kai kamar wadda aka tashe daga wani irin tunani mai nisa. Idanunta suka sauka kan Raihana, “Kun dawo?”
Raihana ta ɗan murmusa, “Eh, Umma. Mun dawo.” Sai ta ƙara kallonta da kyau, “Amma… akwai wani abu ne?”
Umma ta ɗan kalleta, “Me ya sa kika ce haka?”
Raihana ta ɗan karkatar da kanta, “Na yi ta sallama baki ji ba.” Ta ɗan yi murmushi, “Har na shigo na zauna kusa da ke baki sani ba.” Ta ƙara kallon fuskarta, “Wani abu ya faru ne, Umma?”
Umma ta yi shiru. Na ɗan lokaci, carbin da ke hannunta kaɗai ne ake jin sautin ƙananan beads ɗinsa suna bugun juna. Sai ta kakalo murmushi, murmushi ne mai rauni, “Babu abin da ya faru.”
Raihana ta zuba mata ido. Ta san Umma, kuma wannan ba fuskar mutumin da babu abin da ya faru ba ce.
“Ya Fauziyya fa?” Umma ta tambaya a hankali, “Ya jikinta?”
“Eh da sauki.” Raihana ta amsa.
Ta yi shiru, amma zuciyarta ta ƙi yarda da amsar Umma. Wani abu ya faru, ta tabbata, sai dai Umma ba ta son faɗa mata. A zuciyarta sai tunani ya fara zagaye, ko dai sun samu saɓani da Baffa ne? Ko kuma matan gidan sun sake sakar mata wata magana? Ta san yadda wasu daga cikinsu suke, ta san irin maganganun da suke iya jefawa idan sun samu dama.
Raihana ta buɗe baki za ta sake tambaya, amma Umma ta riga ta ɗago kai, “Ki tashi ki yi sallah.” Ta ɗan nuna mata gefe, “Idan kina jin yunwa, ga abinci ki ci.”
Raihana ta ɗan kalli Umma. Ta gane, ba za ta sami komai daga gare ta yanzu ba, sai ta sauke numfashi a hankali ta mike, “Toh, Umma.” Ta cire hijab ɗinta, “Bari na yi sallah.” Ta ɗan yi murmushi, “Abinci ma mun ci a can, ba na jin yunwa.”
Umma ta ɗan jinjina kai, “Toh.”
Raihana ta juya ta nufi ƙofar banɗakin. Amma kafin ta shiga, ta sake waiwayowa. Umma tana nan zaune, carbi a hannunta, idanunta a ƙasa. Raihana ta ɗan tsaya, sai ta sake kallonta, amma ba ta ce komai ba, ta juya ta shige toilet din.
Umma kuwa ta ɗago idanunta a hankali tana kallon inda Raihana ta ɓace, sai ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Carbin ya sake yawo tsakanin yatsunta, babu wata kalma da ta fito daga bakinta. Ta lumshe idanunta, sai ta fara ambaton Allah a hankali, kamar addu’a ce kaɗai za ta iya kwantar da wannan zuciyar tata.
————
Mama Sabuwa ta sake duban Bintu, ba karo na farko ba, ba na biyu ba, a karo na ba adadi, sai ta sake kwafa, “Ni, Malam zai saka sakin wulakanci irin wannan kawai saboda na faɗi gaskiya a tsakiyar gida, a gaban kishiyoyi.” Ta ɗan ja numfashi, kirjinta yana hawa yana sauka, “Ba don komai ba sai saboda na faɗi abin da yake a zuciyata.”
Ta sake kwafa, “Ba dai saboda auren Raihana ya datse igiyar aurena ba! Billahil-lazi…” Muryarta ta ɗan yi rawa, “Na rantse da Allah, ita ma ba za ta zauna lafiya a gidan aurenta ba.”
Sai ta cigaba cikin zafi, “Ba ita kaɗai ba.” Idanunta suka kaɗa, “Har uwarta, Hajara Buzuwa.” Ta furta sunan da wani irin ƙiyayya, “Ba zan sake daga mata kafa ba. Dama na saurara ne saboda wani dalilina.” Ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, amma sai ta sake girgiza kai, “Amma wallahi tallahi… yanzu za su san cewa a kansu aka kaskantar da ni. A kansu aka wulakanta ni.” Ta ɗan taɓa kirjinta, “Akansu aka sake ni.”
Ta yi wani irin dariya mai ɗauke da ɗaci, “Saki ma na cin mutunci…”
Bintu da ke zaune kusa da ita ta tabe baki, ta kalli Mama Sabuwa da gajiyawa, “Wlh Mama, kin cika mita.”
Mama Sabuwa ta juyo da sauri, “Me kika ce?”
Bintu ta ɗan ɗaga kafaɗa, “Eh mana. Tundazu kike maganar nan. Saboda Baffa ya sake ki…” Ta ɗan yi shiru.
Mama Sabuwa ta zuba mata ido.
Bintu ta ci gaba, “Shi fa Baffan nan ba wani uban kuɗi ne da shi ba balle ki ce idan kika fita za ki rasa wani abu. Kin ci gida.” Ta ɗan nuna gidan, “Tun da kin haifa.” Sai ta ƙara da ɗan haushi a muryarta, “Shima ai bai ce ki tafi ba. Ba sai ki musu banza ba? Ganin ki kawai a gidan nan ya ishe su bakinciki.” Ta ɗan karkatar da kanta, “Musamman tunda suna tunanin Baffa zai iya korar ki.”
Mama Sabuwa ta ɗan buɗe baki, amma Bintu ta riga ta ci gaba, “Don Allah… ki bar wannan maganar. Raihana fa… saboda ta yi aure a can? Wani abu ne?” Ta ɗan yi dariya ƙasa-ƙasa, “Su masu kuɗi fa… akwai wanda ya kaisu gori da wulakanta mutane? Wallahi sai ta yi nadamar auren ma.” Ta ɗan yi shiru, “Danginsa kawai sun ishe ta.”
Mama Sabuwa ta kalleta sosai.
Bintu ta ɗan matsa gaba, “Karki manta hotunanta ne fa suke yawo a duniya, tsirara.”
Mama Sabuwa ta ɗan ja numfashi.
“Me yasa za ki wahalar da kuɗinki da kanki? Ki je wajen wani boka ya miki wani aiki…” Ta ɗan yi dariya, “tana kwanciya akan kujera.”
Mama Sabuwa ta zuba mata ido.
Bintu kuwa ta ɗan gyara gashin kanta, “Ni fa… wanda ta aura din, tun da farko ni na fara saninsa.”
Mama Sabuwa ta ɗago gira, “Ke kika fara saninsa?”
Bintu ta amsa ba tare da ko shakku ba, “Eh mana.” Sai wayarta ta fara ringing. Ta kalli screen ɗin, ta ɗauki wayar, sai ta mike, “Bari na ɗauka.” Ta juya ta nufi ɗakinta.
Mama Sabuwa ta bita da kallo, ba ta ce komai ba. Amma kalmar Bintu ta ƙarshe ta tsaya mata a zuciya. Ta ɗan runtse idanunta, sai wani sabon tunani ya fara tasowa a zuciyarta. A hankali… sake-sake suka fara cika mata zuciya.
Mama Sabuwa ta ɗan gyara zamanta. Wannan karon, maganar sakin da aka yi mata ba ita ce yanzu kuma a gabanta ba, sai wannan sabon sirrin da Bintu ta bar mata. Kuma kamar yadda ta san kanta, ba za ta samu nutsuwa ba har sai ta gano gaskiyar abin.
—————-
ARMAAN MANSION
Suhaila ta shigo ɗakin Ummie da mugun sauri. Ummie kuwa tana tsaye gaban wardrobe, tana gyara wasu kaya. Kafin Ummie ta maida hankali kan shigowarta, Suhaila ta ƙaraso ta rungumeta ta baya.
“Ummieee!” Muryarta cike take da farin ciki, “I’m so happy wallahi!” Ta ƙara matse Ummie, “Finally! Akhi tied the knot!” Ta yi dariya, “Wai Raihana! Wallahi har yanzu na kasa yarda!” Ta saki wata irin dariyar farin ciki, “Farin cikin nan kamar ya kashe ni, Ummieeeee! Wayyo Allah…” Ta sake rungumeta, “Akhi yayi aure! Aure faaa! Alhamdulillah!”
Ummie ta ɗan yi murmushi, sai ta juyo a hankali ta kalli Suhaila. Ta ɗan girgiza kai, “Yarinyar nan…” Ta kama hannun Suhaila ta janye shi daga jikinta, “Toh, yadda ni za ki yi ne saboda kawai yayanki yayi aure?”
Suhaila ta fashe da dariya, “Wallahi Ummie!” Ta ɗan buɗe hannayenta, “Farin ciki ne kawai! Na rasa inda zan je na sauke murna ta.” Ta sake yin dariya, “Shi ya sa kai tsaye na zo nan.”
Ummie ta ɗan girgiza kai tana kallonta, amma murmushin da ke fuskarta bai kai irin wanda Suhaila take tsammani ba.
Suhaila ta lura, nan take dariyarta ta ɗan ragu. Ta tsaya tana kallon Ummie, “Ummie…”
Ummie ta ɗaga gira, “Hmm?”
Suhaila ta kalli fuskarta da kyau, “Akwai matsala ne? Na lura ba kya farin cikin da na zata za ki yi idan Akhi yayi aure.”
Ummie ba ta amsa nan take ba, ta ɗan sauke numfashi, sai ta nufi gefen gadonta ta zauna.
Suhaila ma ta bi bayanta, ta zauna kusa da ita. Ta zuba mata ido, wannan karon babu wasa a fuskarta. Ta san Ummie, kuma ta san idan ta yi irin wannan shiru… akwai wani abu.
Ummie ta ɗan kalleta, “Ina farin ciki da wannan auren sosai.” Ta yi murmushi kaɗan, “Wallahi ina farin ciki.” Sai murmushin ya ɗan gushe, “Amma…” Ta ɗan yi shiru, “Yadda Inno ta dage akan sai Zayd ya auri Seeyama…” Ta sauke idanunta, “…shi ne damuwata.”
Suhaila ta yi shiru.
Ummie ta ci gaba a hankali, “Ba wai ina ƙin Seeyama ba.” Ta girgiza kai, “A’a. Amma akwai wasu abubuwa a cikin halayenta da ban cika so ba.” Ta ɗan ja numfashi, “Kuma ban san yadda zamansu zai kasance ba.” Ta kalli Suhaila, “Ban san wanne irin yanayi za su samu kansu a ciki ba. Sannan…” Muryarta ta ƙara laushi, “Ban san wanne irin tarbiyya za ta ba yaran da za ta haifa masa ba.”
Suhaila ta ɗan gyara zamanta.
Ummie ta sauke numfashi, “Wannan shi ne abin da yake damuna. Sannan kuma…” Ta ɗan dakata, “Raihana da aka aura yau… ba a sanar mata cewa akwai wata magana a kan Seeyama ba.” Ta ɗan kalli Suhaila, “Na san ba dole ba ne, amma ina ganin ya fi kyau iyayenta su san da hakan, kar su taɓa tunanin mun yaudare su, kar su zaci mun yi musu munafurci.”
Suhaila ta yi shiru. A gaskiya, maganar ta zo mata a bazata, domin ita ba ta ma san cewa akwai wani shirin auren Zayd da Seeyama ba. Ta kalli Ummie na ƴan seconds, sai ta yi magana cikin sanyin murya, “Ummie…” Ta ɗan matsa kusa da ita, “Ki kwantar da hankalinki, ki cigaba da yi wa Akhi addu’a.” Ta yi murmushi, “Duk abin da yake alheri a tare da shi… Allah Ya tabbatar masa da shi.” Ta ɗan taɓa hannun Ummie, “Kin ji? Ki daina damuwa, babu abin da zai faru.”
Ummie ta ɗan jinjina kai, “Amin.” Sai ta sauke numfashi.
Amma Suhaila ta san… wannan “Amin” ɗin ba yana nufin damuwar ta ƙare ba, kuma Ummie ma ta san hakan. Domin zuciyarta har yanzu tana cike da tambayoyin da babu wanda ya iya ba ta amsarsu. Auren Zayd da Raihana ya kasance a yau, amma a can gaba, akwai wata magana da Inno ta riga ta ƙulla, kuma ta sani cewa ba yadda za ta iya hana wannan kasancewa ba.
Bayan Suhaila ta fice daga ɗakin, Ummie ta ɗan zauna na ƴan daƙiƙu, amma hankalinta duk yana wajen Zayd. Tun bayan da aka sanar da shi daurin auren, bai zo wajenta ba. Shi ma kuma ta san halinsa, Zayd ba mutum ne mai iya nuna abinda ke ransa cikin sauƙi ba.
Ta miƙe, kai tsaye ta nufi ɗakinsa. Da ta isa bakin ƙofar, ta tsaya. Ta ɗan ɗaga hannu, tayi knocking a hankali. Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba sai ta ji motsin bude ƙofa.
Zayd ya ƙaraso ya buɗe. Da ya ga Ummie, sai ya buɗe ƙofar gaba ɗaya, “Ummie…” Muryarsa ta fito ƙasa-ƙasa.
Ummie ta kalleshi, sai murmushi ya bayyana a fuskarta.
Zayd kuwa ya ɗan shafa kansa. Gaskiya, kunya ce kawai ta hana shi zuwa wajenta. Tun bayan da aka ce an daura aurensa, ya ji kamar ya kasa fuskantar kowa. Har Alhaji Minzali da sauran su suka kirashi falo suka sanar masa, ya zauna yana saurare, ya kasa cewa komai, kansa a ƙasa. Bayan sun gama suka tafi, har yanzu bai iya motsawa ba.
Ummie ta wuce ta gefensa tana shiga ɗakin.
Zayd ya ɗan shafa kansa kuma, sai ya rufe ƙofar ya biyo bayanta.
Ummie ta zauna a gefen sofa, idanunta a kansa, murmushi har yanzu bai gushe daga fuskarta ba.
Zayd ya ƙaraso gabanta, ya durƙusa, ya kama hannunta. Suka yi musabaha, daga nan ya ɗan sunkuya ya sumbaci hannunta.
Ummie ta ɗaga hannunta ta shafa kansa, murmushinta ya ƙara faɗaɗa, “Habibi…” Ta ɗan karkatar da kanta, “Yau saboda ka yi aure ne kake guduna?”
Zayd ya ɗan langwabe kai, “Ummie…” Muryarsa cike da shagwaɓa, “Ba guduwa nake ba, bacci nake yi fa…”
Ta ɗan shafa gefen fuskarsa, “Har yanzu wannan shagwaɓar taka, an gama yi min ta wa sauran ta yarinya ta ce.”
Zayd bai amsa ba, kawai ya ɗan yi murmushi. Sai kuma… kamar yaron da ya gaji da komai, ya kifa kansa a kan cinyar Ummie.
Ummie ta sake yin dariya, hannunta ya sauka kan gashin kansa, ta fara shafawa a hankali. Sai murmushin da ke fuskarta ya ɗan sauya, wani irin ƙaunar ɗa da wani irin tausayinsa ya sake cika zuciyarta. Ta kalli fuskarsa.
Zayd ya rufe idanunsa, yana kwance a kan cinyarta, shiru.
Ummie ta sauke ajiyar zuciya, “Habibi…”
Zayd bai motsa ba.
Ta ci gaba da shafa kansa, “Yanzu fa…” Muryarta ta yi laushi, “ba kamar da bane.” Ta ɗan yi shiru, “Yanzu kai mijin Raihana ne.”
Zayd ya buɗe idanunsa kaɗan, amma bai ɗago kansa ba.
Ummie ta ci gaba, “Kuma wannan yana nufin akwai wani sabon nauyi da Allah Ya ɗora maka. Daga yau… ba kai kaɗai kake tunani ba, ba kai kaɗai kake yanke hukunci ba.” Ta sake shafa kansa, “Ka samu mace, mace wadda aka ba ka amanarta.”
Zayd ya yi shiru, kunnuwansa suna gare ta.
Ummie ta ɗan yi murmushi, “Yanzu nauyin Raihana ya dawo kanka. Abin da iyayenta suke yi mata, abin da suke kula da shi a kanta, daga yau kai ma kana da wani ɓangare na wannan nauyin, bangare mafi girma.” Ta ɗan sauke numfashi, “Ka kula da ita, ka mutunta ta, ka ji tsoron Allah a kanta.”
Zayd ya lumshe idanunsa, hannunsa ya ɗan motsa a gefen sofa, amma bai ce komai ba.
Ummie ta ci gaba da magana cikin natsuwa, “Ka sani, habibi… aure ba wai kawai samun mace ba ne, ba wai kawai ka ce wannan matata ce ba.” Ta ɗan dakata, “Aure amana ne, haƙƙi ne, juriya ne, kuma adalci ne.” Ta sake shafa kansa, “Raihana yanzu tana da kai. Idan ta ji tsoro, kai za ta kalla. Idan ta yi farin ciki, kai ne za ka fi kusa da ita. Idan ta yi kuskure…” Ta ɗan yi shiru, “ka koya mata cikin tausayi. Kar ka wulakanta ta, kar ka yi amfani da ƙarfinka ko matsayinka wajen karya mata zuciya.”
Zayd ya buɗe idanunsa, ya kalli Ummie daga inda yake kwance.
Ummie ta yi masa murmushi, “Ka tuna… Allah Ya halatta maka ka zama mijinta, amma wannan ba yana nufin Allah Ya halatta maka ka zalunce ta ba.”
Zayd ya sake sauke idanunsa.
Ummie ta ci gaba da shafa kansa, “Ka ba ta lokaci, ka ba ta damar fahimtar ka, kuma kai ma ka ba kanka damar fahimtar ta.” Ta ɗan yi murmushi, “Ba sai komai ya yi perfect tun daga rana ta farko ba, amma abin da nake so daga gare ka shi ne… ka kasance mai haƙuri, ka kasance mai gaskiya, kuma ka kasance mai adalci.”
Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya sake rufe idanunsa, kamar kalamanta suna sauka ne a hankali cikin zuciyarsa.
Ummie ta ɗan kalli fuskarsa, “Daga yau…” Ta furta cikin sanyin murya, “Raihana ba yarinya ce kawai da aka kawo maka ba. Matarka ce, amana ce. Ka kula da ita kamar yadda kake so wani ya kula da kai idan rayuwa ta juya maka baya.”
Zayd ya yi ajiyar zuciya a hankali, bai ce komai ba, kawai ya sake kifa kansa a kan cinyarta.
Ummie ta yi murmushi, hannunta ya ci gaba da shafa kansa. Kuma a cikin wannan shirun, Zayd ya ji nauyin wata sabuwar rayuwa yana sauka a hankali a zuciyarsa—ba nauyin aure kawai ba, amma nauyin kasancewa miji.
————-
Baffa bai dawo gida ba sai bayan an idar da sallar Isha’i. Da ya shigo gidan, bai tsaya ko’ina ba, kai tsaye ɗakin Umma ya nufa. Da ya isa, ya tarar da ita ita kaɗai a falon, Aminu da Yusuf sun riga sun yi bacci.
Umma tana zaune cikin nutsuwa, har lokacin da ta ɗago kai ta gan shi, “Barka da dare.”
Baffa ya jinjina kai, “Barka dai.” Ya ƙaraso ya zauna, sai ya ɗan yi shiru. Idanunsa suka tsaya kan Umma na ƴan daƙiƙu, kamar yana nazarin yanayinta. Daga nan ya ce a hankali, “Kira min Raihana.”
Umma ta ɗan kalleshi, sai ta gyada kai.
Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba, Raihana ta shigo. Da ta ga Baffa zaune, nan take ta ƙaraso, ta durƙusa gabansa cikin girmamawa.
Baffa ya kalleta. Na ɗan lokaci, bai ce komai ba. Sai ya saka hannu cikin aljihunsa, ya ciro kuɗi, ₦500,000, ya miƙa mata.
Raihana ta tsaya, idanunta suka sauka kan kuɗin. Ta ɗan yi jim, kamar ba ta fahimci dalilin da ya sa yake ba ta kuɗin ba. Daga ƙarshe ta miƙa hannu a hankali, ta karɓa.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya, sai ya kalleta sosai, “Raihana…”
Ta ɗago idanunta. Kallon Baffa ya tsaya a kanta, amma bakinta ya kasa furta komai.
Baffa ya ci gaba cikin nutsuwa, “Ni da mahaifiyarki… Allah Ya ba mu dama mu zama masu kula da ke. Mun ɗauki wannan amanar tun kina ƙarama, mun raine ki, mun koya miki abin da muka iya. Saboda haka…” Ya ɗan dakata, “lokacin da maganar aure ta zo, ba za mu duba kuɗi ko suna ko matsayi kawai ba. Abin da muka fi dubawa shi ne addini, tarbiya, halayya, da yadda mutum yake mu’amala da mutane, da sauran abubuwan da yakamata mu lura a mijin da zamu baki.”
Ya ɗan kalli Raihana, “Idan muka ga wanda muka yarda da tarbiyyarsa, addininsa da mu’amalarsa… ya zo ya nemi aurenki… ba za mu hana shi abin da Allah Ya halatta ba.”
Raihana ta yi shiru, hannunta yana riƙe da kuɗin.
Baffa ya sauke numfashi, sai muryarsa ta ƙara laushi, “Saboda haka… ni yau ina mai farin cikin sanar da ke…” Ya ɗan yi shiru, “na daura aurenki.”
Raihana ta zaro ido, kamar kalmar ta buge ta a take. Ta kalli Baffa, sai ta kalli Umma, ta sake kallon Baffa.
Baffa ya ci gaba, “Na daura aurenki da Zayd.”
Numfashin Raihana ya tsaya na ɗan lokaci, idanunta suka cika da hawaye nan take, ta kasa motsawa.
Baffa ya nuna kuɗin da ke hannunta, “Wannan… shi ne sadakin aurenki. Gashi nan a hannunki.”
Raihana ta kalli kuɗin. Hawaye guda ya zubo mata, ta yi ƙoƙarin share shi da bayan hannunta, amma wani ya biyo shi.
Umma ta zuba mata ido cikin tausayi.
Baffa ya ɗan sauke murya, “Raihana…”
Ta ɗago kai a hankali.
“Na san wannan maganar ta zo miki a bazata, na san ba haka kika shirya cewa yau zai kasance ba, amma aure ba abu ne da za a ɗauka da wasa ba. Daga yau…”
Ya ɗan dakata, “Zayd ne mijinki. Ki girmama shi, ki mutunta shi, ki saurare shi a abin da ya dace, ki zauna da shi cikin gaskiya da haƙuri.” Ya ɗan yi shiru, “Amma kuma ki sani… girmama miji ba yana nufin ki rasa mutuncinki ba. Ki kasance mai hankali, ki kiyaye gidanki, ki kare sirrinsa kamar yadda kike son ya kare naki. Idan wani abu ya dame ki, kar ki yi gaggawar ɗaukar hukunci, ki fara magana da shi, ki nemi fahimta kafin fushi.”
Raihana ta sunkuyar da kanta, hawayen suka sake gangarowa.
Baffa ya kalleta da tausayi, “Daga yau kuma…” Muryarsa ta ɗan yi nauyi, “ba ki sake fita daga gidan ba sai da izinin mijinki, kuma dole ne ki fahimci cewa akwai haƙƙoƙi da nauyin da suka zo tare da wannan aure.” Ya ɗan dakata, “Har zuwa lokacin da za su shirya su zo su ɗauke ki… ki shirya zuciyarki, ki roƙi Allah Ya sa wannan auren ya zama alheri a gare ki.”
Raihana ta kasa magana, kawai ta ɗaga kai a hankali, hawayen suna gangarowa a kumatunta.
Baffa ya ɗan yi murmushi mai taushi, “Ki shiga wannan aure da Allah a gabanki, ki shiga da kyakkyawar niyya, ki girmama wanda Allah Ya sanya ya zama mijinki. Idan kuka samu matsala, ku nemi mafita, kar ku bari fushi ya zama mai magana a tsakaninku.” Ya ɗan kalli Umma, sai ya dawo da dubansa kan Raihana, “Ni dai na yi abin da na ga ya dace, yanzu abin da ya rage shi ne ki yi addu’a.”
Raihana ta runtse idanunta, sai ta ɗan gyada kai, hawaye ne kawai suka amsa masa.
Baffa ya ɗan sauke ajiyar zuciya, “Allah Ya miki albarka. Allah Ya sanya Zayd ya zama alheri a gare ki, Allah Ya sanya ke ma ki zama alheri a gare shi. Aure ya zama sutura a gare ku, ya zama rahama, ya zama nutsuwa.”
Raihana ta sake gyada kai, sai ta sunkuyar da kanta.
A wannan daren… ba ta samu kalmar da za ta iya bayyana abin da ke cikin zuciyarta ba. Aure, Zayd, sadaki, miji, komai ya zo mata a lokaci guda. Sai kawai ta ajiye kuɗin a hannunta a gefe tana zubar da hawaye a hankali.
Baffa kuwa ya kalleta na ƴan daƙiƙu. A cikin kallonsa akwai ƙauna, akwai tausayinta, amma fiye da komai… akwai wani irin tabbacin uba da ya san cewa daga wannan daren, rayuwar yarinyar da ya raina ta canza har abada.





Not edited