BOUND BY A VOW
ZAYD ARMAAN
CHAPTER FIFTY FOUR:54
BOUND BY A VOW
JIDDAAH BARKUM
—————-
Suhaila ta ɗan miƙe tsaye, idanunta suna kan wayarta wadda ta fara haske, alamun kira ya shigo.
Inno ta ɗago kai ta kalleta.
“Ina kuma za ki je?”
Suhaila ta ɗan juyo tana kallonta, wayar har yanzu a hannunta.
“Akhi ne yake kirana. Ko wani abu zan masa.”
Kafin Inno ta sake cewa komai, Baffa ya buɗe baki.
“Yana waje ne dama?”
Suhaila ta ɗan jinjina kai.
“Eh, Baffa. Tare muke.”
Baffa ya ɗan dafe kansa, ya kalli hanyar ƙofar gidan kamar wanda yanzu ya tuna cewa tun zuwansu Zayd yake tsaye a wajen.
“Yanzu duk wannan lokacin yana tsaye a ƙofar gida?” Ya girgiza kai a hankali. “Haba… ai ya zama ɗan gida.” Sai ya ɗan kalli Raihana. “Tashi ki je ki shigo da shi ɗakina mana.”
Kalaman suka faɗa wa Raihana kamar wani abu mai nauyi ya sauka a ƙirjinta. Zuciyarta ta buga da ƙarfi, kamar an buga mata guduma a tsakiyar ƙirji. Ta ɗan kalli Baffa, sai ta kalli Inno da ke zaune kusa da ita. Ba ta ce komai ba. A hankali ta miƙe. Hannunta ya ɗan gyara gefen hijabinta, sannan ta nufi inda Suhaila take, suka fita daga ɗakin tare.
A daidai lokacin da Raihana ta wuce ƙofar falon, Mommy Hauwa ta sauke idanunta daga kanta. Ta ɗauki dogon numfashi, ta ɗan jingina da kujerarta. Amma wani irin feeling ɗin da ta kasa fahimta ya ci gaba da kasancewa a cikin zuciyarta. Ba ta san me yake damunta ba, sai dai tun lokacin da idanunta suka sauka kan Raihana, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa.
A ɗakin kuwa, Baffa ya sake duban Inno. Ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Toh, Hajiya…” Ya ɗan gyara zamansa. “Yaushe yake buƙatar ta tare?” Ya ɗan dakata. “Ni kam, tunda an riga an ɗaura aure, ba na son wata bidi’a.” Ya kalli Inno kai tsaye. “Ba sai an yi wani taro ba. Musamman ma akwai wani biki nan da kwana uku, idan muna da rai. Ina ganin tsayawa wani biki ba shi da wani amfani yanzu. Saboda haka, gwara a saka rana. Idan ya so, sai a je a yi mata jere kafin ranar.”
Umma ta ɗago idanunta ta kalli Baffa. A fili ta so ta yi magana, amma ta san halinta—ba ta saba musu da Baffa ba, ko da su biyu ne kawai, bare kuma a gaban mutane. Sai ta yi shiru. Itama ba wai tana son a yi wani biki ba ne, amma ta so dai a bari ta shirya ɗyarta da kyau, musamman yanzu da ta ji cewa akwai wata matar. Amma sai ba ta ce komai ba, kawai ta yi shiru tana sauraronsu.
Inno kuwa ta zauna tana kallonsa, sai ta saki murmushi.
“Wallahi na ji daɗin wannan magana, Malam Musa.” Ta ɗan gyara mayafinta. “Dama wannan yana cikin alfarmar da zan roƙe ka kenan.” Ta ɗan sunkuyar da kanta cikin girmamawa. “Zan so ta tare kafin a ɗaura masa wancan auren. Tunda ita ce uwargida, ina ganin ya dace ta kasance a cikin ɗakinta tukunna kafin a sake ɗaura masa aure.” Sai ta ɗan sauke ajiyar zuciya. “Na gode sosai da ka fahimci abin da nake nufi.”
Baffa ya ɗan jinjina kai.
Inno ta ci gaba cikin ladabi, “Amma tunda wannan bikin nan ba ku shirya masa wani babban abu ba kuma ya zo ne ba shiri…” Ta ɗan yi shiru. “Ni ma ina roƙonka kada ka damu da komai, ba sai kun shirya komai ba. Duk abin da take buƙata, daga ɓangarenmu za mu yi.” Ta ɗan kalli Baffa cikin murmushi. “Lefenta ma zai kasance gaba ɗaya, tare da na abokiyar zamanta, in sha Allah. Ba mu son mu ƙara muku wani nauyi.”
Baffa ya ɗan yi murmushi, ya girgiza kai a hankali.
“Hajiya, Allah Ya saka da alheri.” Ya ɗan ɗaga hannu kamar yana nuna ba haka yake so ba. “Amma ki bar wannan. Na gode ƙwarai da irin wannan niyya.” Ya kalli Umma na ɗan lokaci, sai ya koma kan Inno. “Amma ni ma a matsayina na mahaifinta, yana da kyau na yi mata dukkan abin da uba ke wa ɗyarsa a lokacin aure. Dukkan abin da ya kamata a yi, zan yi mata in sha Allah. Ba don na nuna miki cewa ban yaba ba… wallahi na yaba kuma na gode.” Ya ɗan yi murmushi. “Abin da Allah Ya hore min, zan yi mata. Amma ba zan so ku ɗauki komai a kanku ku bar ni a gefe ba.”
Umma kuwa ta kalli Baffa na ɗan lokaci, murmushin da ke fuskarta ya ƙara bayyana. A ranta ta san Raihana ta samu uba, kuma a wannan ranar, ta ƙara jin alfaharin kasancewar Baffa mijinta. Sam abin duniya bai dame shi ba, ba ya ƙasƙantar da kansa a kan abu da wani yake da shi; abin da yake da shi shine abin taƙama da alfaharinsa.
Inno ta ɗan yi murmushi, ta jinjina kai cikin girmamawa.
“Na fahimce ka Malam Musa, amma ka sani bikin nan ba ku shirya masa ba, mu muka tashi da maganar nan. Yana da kyau a ce mu ne muka yi komai, ka bar maganar nan dan Allah.”
Baffa ya ɗan yi murmushi, amma wannan karon sai ya girgiza kai a hankali.
“A’a, Hajiya. Wannan ba zan yarda ba.” Ya kalli Inno. “Raihana ɗyata ce. Za ta ji daɗi idan ta juya gidanta ta ga wani abu da mahaifinta ya yi mata. Abin da zan iya yi mata, shi zan yi.”
Inno ta buɗe baki da sauri, “Malam Musa, na roƙe ka ka bar mana wannan.”
Baffa ya ɗan yi murmushi, “Hajiya, ba na jin daɗin gardama da ke.”
Inno ta yi murmushi cikin ladabi, “Ba wai mu muna son mu zo mu ɗauke maka nauyin da ya rataya a wuyanka ba ne. Kar ka manta fa, ƙa’ida ma miji ne ya kamata ya yi wa matarsa komai, duk abin da ya kamata a yi za mu yi.”
Baffa ya girgiza kai, ya buɗe baki zai saki magana, sai Ummie—wadda tun farko take shiru—ta ɗan matsa gaba.
“Wallahi Malam Musa, abin da Hajiya ta faɗa gaskiya ne. Dan Allah ka bar mana komai, dan Allah.” Ta ɗan yi murmushi. “Ba don muna ganin ba za ka iya ba ne, a’a, mun dai so mu ɗauki nauyinmu.”
Baffa bai ce komai ba. Kawai ya zauna yana murmushi, idanunsa suka riƙa bin Inno, sai Ummie, sai ya sake komawa kan Inno, kamar yana kallonsu ne yana mamakin yadda mata biyu suka haɗa kai suka ƙi barinsa ya yi wa ɗyarsa komai.
Inno ta sake ɗora magana, “Wallahi, Malam Musa, duk abin da Raihana za ta buƙata, za mu tanada. Komai.”
Ummie ta ɗan gyaɗa kai, “In sha Allah.”
Baffa ya yi shiru, sai dai murmushin da ke fuskarsa ya ƙara faɗaɗa.
A ƙarshe, Mommy Hauwa—wadda take zaune tana sauraron duk abin da suke faɗa—ta ɗan gyara zamanta.
“Malam…” Baffa ya kalleta. Ta ɗan yi murmushi. “Tunda sun ce ka bar shi…” Ta ɗan kalli Inno da Ummie. “Ai ka bar shi.” Ta ɗan ɗaga kafaɗarta. “In dai ba raina wanda za su yi ka yi ba.”
Baffa ya sake kallonsu. Kafin ya yi magana, Mama Indo ta shigo da nata.
“Gaskiya dai, Malam…” Ta zauna tana kallonsu. “Tunda sun dage haka, ai yanzu an zama ɗaya.” Ta ɗan yi dariya. “Yanzu ai sun tashi daga baƙi an zama ɗaya, tunda ana shirin haɗa zuri’a.”
Ƙaramar dariya ta tashi a falon. Baffa ya girgiza kai yana murmushi.
“Ku mata kam…” Ya ɗan kalli Inno, sannan ya kalli Ummie. “Kun haɗa kai a kaina.”
Inno ta yi dariya, “Ba a kanka ba ne, Malam Musa.”
Baffa ya sauke ajiyar zuciya. “Allah Ya saka da alheri. Amma duk da haka dai, zan ɗan yi mata wani abu ko yaya ne, dan Allah Hajiya kar ki ce a’a.”
“Toh shikenan,” Inno ta faɗa tana murmushi. “Ba mai yawa ba dai, za ka yi koma menene.”
Aka ɗan yi dariya. Baffa ya sake yin shiru, amma wannan karon murmushin da ke fuskarsa ya kasance na wani uba da ya fara jin cewa ɗyar da Allah Ya ba shi ta samu wata sabuwar rayuwa da mutanen da suka riga suka fara ɗaukarta tamkar tasu.
Baffa ya yi murmushi a hankali, “Toh, babu laifi. Ina ganin ranar Alhamis, idan muna da rai, sai ta tare.” Ya ɗan sauke ajiyar zuciya. “Allah Ya ba su zaman lafiya da zuri’a masu albarka, Ya kuma haɗa kawunansu.”
“Amin. Amin,” muryoyin jama’ar falon suka haɗu kusan a lokaci guda, har da Mommy Hauwa—wadda tun farko take bin kowa da idanu. Ta ɗan sunkuyar da kanta, amma idanunta suka ci gaba da yawo daga kan wannan zuwa wannan.
—————-
Suhaila ce ta fara fitowa ƙofar gidan, Raihana na biye da ita a baya. Da ƙafafunta suka taka ƙofar gida, zuciyarta ta fara wani irin mugun bugu. Ta ji bugun zuciyarta har cikin kunnuwanta, numfashinta kuwa kamar tana ƙokawa da shi—kowane numfashi sai ta ji kamar yana buƙatar ƙoƙari kafin ya shiga huhunta. Tun lokacin da aka ce mata za ta fito ta same shi, ta kasa samun nutsuwa. Mutumin da aka ɗaura mata aure da shi jiya, a yau ne karo na farko za su tsaya fuska da fuska tun bayan auren.
Ta ɗan matse gefen hijabinta da hannunta, ta riƙe shi gam, kamar hijabin ne kaɗai zai iya ba ta ƙarfin gwiwa. Wallahi… ba don Suhaila ce a gabanta ba, da ba ta san ko ƙafafunta za su iya kai ta inda yake ba. A lokacin da suka ƙaraso kusa da motar, ta ji kamar duk jama’ar unguwar sun fito suna kallonta. Ta ƙara sunkuyar da kanta, ta ƙi ta kalli direction ɗinsa.
Zayd kuwa yana jingine da motarsa, hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonshi, ɗayan kuma riƙe da wayar da ke kunnensa yana magana—a hankali, cikin nutsuwarsa irin wadda ta saba kasancewa tare da shi. Amma da idanunsa suka hango Raihana tana takowa a bayan Suhaila, maganar da yake yi ta ci gaba, amma hankalinsa ya sauka kanta.
Raihana kuwa, idanunta a ƙasa, tafiyarta a hankali, hannunta ya matse gefen hijabinta. Zayd ya ƙafe ta da idanu, kamar yau ne karo na farko da ya fara ganinta, kamar duk abin da ke gabansa ya ɗan tsaya na wasu seconds.
Suhaila ce ta fara lura. Ta kalli Zayd, ta kalli Raihana, sai ta sake kallon Zayd. Murmushi ya fara bayyana a fuskarta, saboda gaskiya… irin kallon da yake yi wa Raihana bai yi kama da kallon da yake yi wa kowa ba. Kuma abin da ya fi ba ta dariya? Kamar dai ita ma kanta bai san da ita a wajen ba! Ta yi murmushi tana ci gaba da tafiya.
Raihana kuwa har yanzu idanunta a ƙasa suke, ta kasa ɗagowa ko second ɗaya ne har suka ƙaraso gabansa. Suhaila ta ɗan tsaya, ta ɗaga hannunta, ta ɗan janyo Raihana ta matso gefenta. Amma Zayd har yanzu idanunsa suna kanta. Sai Suhaila ta yi murmushi mai cike da tsokana, ta ɗan taɓa hannunsa. A take Zayd ya janye idanunsa daga Raihana, ya kalleta. Suhaila ta ɗaga masa gira tana masa nuni da Raihana ta gefen ido.
Zayd ya sake kallonta, sai ya ɗauke kansa kamar bai fahimci komai ba, ya ci gaba da maganar da yake yi a waya. Suhaila ta cije leɓenta tana danne dariya har ta kasa cewa komai.
Raihana kuwa ta ji zuciyarta ta ƙara bugu, ta kasa sanin ko saboda kallon da ya yi mata ne, ko saboda tunanin cewa mutumin da yake tsaye a gabanta yanzu wai shi ne mijinta.
Suhaila ta ɗan matsa kusa da ita, ta janyo hannunta a hankali. A lokacin ne Raihana ta ɗago idanunta—kallo ɗaya kawai, idanunta suka sauka kansa, nan take ta sake sauke idanunta. Amma wannan kallo ɗaya ya isa ta ga fuskarsa sosai. Kuma yanzu, shi ne mutumin da za ta calling mijinta.
Suhaila ta sake janyo ta gaba. Zayd kuwa ya kashe wayar, ya sauke wayar daga kunnensa, ya kalli Suhaila. Sai muryarsa ta fito cikin nutsuwa.
“Sai yanzu kika ga damar zuwa?”
Suhaila ta saki ƙaramar dariya, “Baffa ne ya ce na tsaya na taho maka da matarka.” Ta juya ta nuna Raihana da ido, “Ga ta.”
Zayd bai kalleta ba, sai ya yi kamar bai ji ta ba. “Ba ni number Mahfouz.”
Suhaila ta zaro ido, ta turo baki. “Yanzu dan Allah? Number tashi ce kawai zan ba ka, sai na fito?” Ta girgiza kai. “Gwara ka ce in tura maka ta SMS, ba?”
Zayd bai kalleta ba, muryarsa ta kasance a sanyaye. “Haka na ga dama.”
Suhaila ta lumshe ido, “Hmm.” Ta buɗe wayarta, ta fara karanta masa number ɗin. Zayd ya saka a wayarsa ba tare da gaggawa ba, sai da ta gama karantawa.
Raihana kuwa ta tsaya a gefe, kanta a ƙasa, hannunta har yanzu a kan hijabinta. Ta yi ƙoƙarin samun ƙarfin gwiwa. A ƙarshe, muryarta ta fito a hankali, “Ina yini.”
Zayd ya ɗago kai, idanunsa suka sauka kanta. A hankali ya kalleta, daga sama zuwa ƙasa, ba wai da wani obvious expression ba. Raihana tana sanye da doguwar rigar atamfa wadda ta zauna mata da kyau, sannan hijabinta ya rufe kanta da jikinta cikin nutsuwa. Fuskarta kuwa fresh, fes, akwai wani irin haske na halitta a fuskarta da ya fito sosai saboda rashin yawan kwalliya.
Zayd ya tsaya na ɗan lokaci, sai ya ɗan taɓe baki, ya maida kansa gefe. Bai amsa gaisuwar ba, kawai ya ɗauke idanunsa daga kanta.
Raihana ta ji wani malolon ɓaƙin ciki ya takure mata wuya, kamar an zuba mata wani abu mai ɗaci a cikin zuciya. Ta haɗiye abin da ya taso mata, ta kasa sanin me ya fi mata zafi—ko kallon da ya yi mata, ko rashin amsar gaisuwarta. Amma ba ta bari komai ya bayyana a fuskarta ba.
Suhaila kuwa ta tsaya tana kallonsu, murmushi ya bayyana a fuskarta. Ta kalli Raihana, ta kalli Zayd.
“Uhmm…” Ta janyo hannun Raihana. “Ni dai wannan kallon soyayyar ba da ni ba.”
Raihana ta ɗan kalleta. Suhaila ta danne dariyarta, ta sake janyo ta, sai ta kalli Zayd.
“Ka shigo ciki. Baffa ya ce daga yau ka daina tsayawa a waje, ka taho mu shiga ciki.”
Suhaila ta riga ta fara tafiya, hannunta har yanzu riƙe da na Raihana, Raihana tana bin ta kamar jela. Zayd ya tsaya yana kallonsu, idanunsa suka bi Raihana har lokacin da ta ɓace daga ganinsa, ba ko ƙiftawa. Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ya ɗan gyara tsayuwarsa. Daga nan ya juya, ya rufe murfin motar, sai ya kalli ƙofar gidan na ɗan lokaci kafin ya juya ya bi bayansu cikin nutsuwa.
—————-
Suhaila ta kalli Raihana da suka shiga gidan, “Ina ne ɗakin da za mu kai shi?”
Raihana ta ɗan ɗaga hannu ta nuna mata ɗakin Baffa, “Can.”
Suhaila ta juya za ta nufi wajen, amma kafin ta kai ga yin wani abu, sai ga Zayd ya shigo. Ya wuce su kawai, bai tsaya ba, bai kallesu ba, kawai ya wuce ya shige ɗakin Baffa kamar wanda gidan nasa ne.
Raihana ta bi shi da kallo, sai ta zabga masa wata uwar harara ta ƙarƙashin ido, ta ɗauke kanta da sauri. Suhaila kuwa da ba ta lura da komai ba, ta ci gaba da tafiya. A hankali suka ƙarasa bakin ƙofar ɗakin. Suhaila ta buɗe ƙofar, Raihana ta shiga, ita kuwa ta tsaya a bakin ƙofar tana kallonta. Sai ta kalli Raihana, ta kalli Zayd. Murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta, wani irin murmushi ne da ya ɗauki ma’ana fiye da magana.
“Byeee…” ta furta a hankali, sai ta juya ta fita, ta bar su.
Raihana ta tsaya a tsakiyar ɗakin. Zayd kuwa yana can yana kallonta—babu magana, babu ko ɗan motsi, kawai idanunsa ne suke yawo a kanta kamar zai cinyeta. Raihana ta ɗan motsa ƙafarta, ya ci gaba da kallonta. Ta ƙarasa ta zauna a kujerar da ke gefe ɗaya, amma Zayd har yanzu yana kallonta. Ta ɗan juya kanta gefe, ya ci gaba.
What is wrong with this man? Ta fara jin haushin kallon, ta lura yau wani ɗan iskan kallo yake mata na ba gaira ba dalili. Tun shigowarta ɗakin yake kallonta kamar ya samu wani sabon abu da bai taɓa gani ba.
Mintuna biyu suka wuce. Shiru. Uku. Shiru. Raihana ta fara gajiya. Mintuna biyar, ta ayyana a ranta. Idan bai yi magana ba cikin mintuna biyar, wallahi zan fita. Ba za ta zauna a nan tana kallon mutum yana kallonta kamar ya samu statue ba tare da ya faɗi komai ba.
Ta ɗan juya kanta ta kalli agogon ɗakin—four minutes. Ta sake dubansa, har yanzu yana kallonta. Sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ta shirya miƙewa. A daidai lokacin… muryarsa ta katse shirun.
“Ke kuma…” Ta tsaya. Muryarsa ta fito a hankali, calm, ba hayaniya, ba ɗaga murya, amma akwai wani abu a cikin yanayin maganar nasa da ya sa ta san cewa ya shirya rainin hankalin da ya saba ne. “Haka naki salon tarbar mijin yake?”
Raihana ta daskare. A hankali ta ɗago kanta, idanunta suka sauka a kansa, sai ta zabga masa wata uwar harara.
“Shafa ka ji,” ta faɗa a taƙaice, ta ɗauke kanta gefe.
Zayd bai yi magana ba, kawai ya ci gaba da kallonta. Wannan kallon nasa ya fara ƙara ba ta haushi. Sai ya ɗan motsa kamar zai miƙe. Raihana ta wani zabura, nan take ta miƙe tsaye, ta murguda baki.
“Kar ma ka sake ɗanganta kanka da mijina!” Ta wani harare shi. “Wallahi, dan ni ba na kallonka a matsayin mijina.” Muryarta ta ƙara ɗan kauri. “Ita dai wacce za ka aura ranar Juma’a, ita ce kaɗai matarka. Sai kuma ɗayar ta US.”
Kafin ma ya samu damar cewa wani abu, ta juya da sauri tana shirin nufar ƙofa. Amma ba ta kai ga fita ba; Zayd ya miƙe cikin nutsuwa—ba gaggawa, ba hayaniya—taku ɗaya ya yi, ya isa gabanta.
Raihana ta tsaya cak, zuciyarta ta yi wani mahaukacin bugawa. Ta ɗago idanunta kaɗan. Zayd yana tsaye a gabanta, kusa, kusan ya rufe mata hanya gaba ɗaya. Ta haɗiye yawu, amma ta dake.
“Malam…” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa. “Ba ni hanya na wuce.”
Zayd bai ce komai ba, kawai ya tsaya yana kallonta. Wannan nutsuwar tasa ta fara ƙara ɓata mata rai. Ta ɗan matsa baya kaɗan.
“Wallahi zan maka ihu!” Ta ɗan ɗaga murya. “Ka ba ni hanya na ce!”
Zayd ya lumshe idanunsa a hankali, kamar wanda yake ƙoƙarin danne wani abu, amma har yanzu bai ce komai ba. Raihana ta sake ja baya, sai ta haɗe rai, ta yanke shawarar kawai ta yi wucewarta ta gefensa. Ta yi step ɗaya, sai wani, amma daidai lokacin da ta kusa wuce shi… hannunsa ya miƙe. Ya ƙama hannunta da ƙarfi, ya janyo ta, ya dawo da ita gabansa.
Ta zaro manyan idanunta, zuciyarta ta sake buguwa da ƙarfi.
“Me haka?” Ta fara magana, amma ya katse ta.
Muryarsa ta fito cikin irin nutsuwar da ta fi komai ɓata mata rai, “Ina zan shafa?” Yana faɗa yana zuba mata wannan lumshasshun idanun nasa da ya sa zuciyarta yin wani mugun zillo. Ba shiri ta runtse idanunta da bala’in sauri.
Not edited