A BRIDE IN THE MAKING
ZAYD ARMAAN
CHAPTER FIFTY SEVEN:57
A BRIDE IN THE MAKING
JIDDAAH BARKUM
——-
Daga ɗakin Ummie, Zayd kai tsaye ɗakinsa ya nufa. Ba tare da ya cire ko takalminsa ba, ya kwanta rigingine a kan gadon, ƙafafunsa a ƙasa, ya ɗora hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa. Ya yi shiru na tsawon lokaci, amma a cikin shirun nasa, akwai wani irin aura da kowa ke kallo zai sani sarai cewa it was definitely not a pleasant mood. Idanunsa suna lumshe, Allah kaɗai ya san irin nauyayan tunanin da yake saƙawa a ransa.
Yatsunsa suka ɗan motsa a hankali a kan ƙirjinsa, kamar yana ƙoƙarin daidaita bugun zuciyarsa. Ya sauke dogon numfashi, amma har yanzu fuskar tasa ta ƙi sakin wannan tsaurin da ya lullube ta. Ya bude idanunshi a hankali ya kalli sama. Kallon ceiling ɗin kawai yake yi, amma a zahiri hankalinsa yana can wani wuri daban.
He stayed like that for a long time, completely immersed in his thoughts, kafin daga ƙarshe ya miƙe a nutse ya wuce bathroom. Ya yi wanka da ruwan ɗumi don ya rage wa kansa wannan heavy tension ɗin, sannan ya sako a simple, normal house outfit ya fito ya nufi masallaci.
Lokacin da ya dawo daga masallacin, Inno da Suhaila suna zaune a falo. Without giving them a single glance, Zayd ya yi hanyar stairs, kamar bai san Allah yayi ruwansu a wajen ba.
Takunsa bai yi sauri ba, amma yana ɗauke da wani irin ƙarfi da ya nuna sarai cewa ba ya son a tsayar da shi. Hannunsa ɗaya yana cikin aljihun wandonsa.
“Kai Zayd!” Inno ta kwala masa kira.
Zayd ya tsaya cak.
Na ɗan lokaci, falon ya yi shiru.
A hankali ya juyo tare da zuba mata waɗancan zurfafa idanunsa, amma bai ce mata ko uffan ba; kawai ya dawo ya tsaya a gefe yana kallonta ƙasa-ƙasa.
Fuskarsa babu murmushi. Babu fushi a fili. Sai dai wannan irin nutsuwar da idan mutum ya san Zayd, zai fahimci cewa akwai abubuwa da yawa da yake riƙe da su a ransa.
Inno ta ɗaga murya tare da buɗe baki: “Yanzu na kiraka kazo ka tsaya min tsage-tsage kamar nonon budurwa yar shekara sha uku? Sai ka zauna, magana nake so mu yi!”
Suhaila ta ɗan sunkuyar da kanta, tana ɓoye murmushin da ya fara bayyana a gefen bakinta.
Daga yanda Inno ta fara maganar, ta fahimci dai yan jarabarta sun motsa, ko tana zaton Zayd zai mata bori ne, shine ta ga gwara ta zo masa da zafi-zafi ne oho!
Without saying a word, Zayd ya ƙarasa ya zauna a gefen Suhaila, still maintaining his intense composure.
Ya zauna a hankali, ya ɗora hannayensa biyu a kan cinyarsa, sannan ya ɗago idanunsa zuwa ga Inno.
Inno ta gyara zamanta ta fara magana cikin ikonta: “Yanzu dai mun gama magana da baban matarka. Za ta tare ranar Alhamis, saboda ni kaina ina da buƙatar a ɗaura aurenka da Seeyama ranar Juma’a. Ba ni da masaniyar maganar ita uwargidan naka a baya, sabida haka na riga na haɗa zancen Seeyama, kuma yarinyar ta riga ta sa rai. Kaga kuwa ba zan fasa ba! Tunda dai addinin Musulunci ya amince ka auri mace har hudu, so there is nothing to argue about!”
Yayin da take magana, fuskarta cike take da tabbacin cewa ita ce ta riga ta yanke hukunci, kuma ba ta shirya sauraron wata gardama ba.
Zayd ya juyo ya watsa mata wani irin cold gaze, sai kawai ya miƙe tsaye a hankali, ba tare da gaggawa ba, ya gyara gefen rigarsa.
“Na ji,” ya furta a takaice, sannan ya fara takawa zai bar wajen.
Inno ta saki baki da hanci cikin tsantsar takaici. “Yau na ji lalacewa! Toh ce maka na yi na gama magana da zaka kwashi tsayi kamar daren baƙin ciki ka yi gaba!”
Zayd ya sake tsayawa.
A wannan karon, bai juyo nan take ba.
Ya sauke numfashi a hankali, sannan ya juya kansa kaɗan kafin daga ƙarshe ya fuskanci Inno gaba ɗaya.
Ya sake zuba mata idanunsa cike da wani irin indifferent look.
“Toh me zan ce miki? Tunda dai kin riga kin shirya abinki ba tare da yardata ba.”
Muryarsa ba ta da ƙarfi, amma kowane kalma ta fito a sarari, cikin wannan nutsuwar da ta fi ihu nauyi.
Inno ta miƙe tsaye da sauri cikin masifa. “Toh daga abun arziki uban wa yake auren mata biyu a tare a lokaci guda? Daga na yi maka abun ƙirƙi shine zaka tsaya ka riƙa yi min fitsara?!”
Ta ɗaga hannunta cikin zafin rai, fuskarta ta cika da mamaki da haushi. Suhaila kuwa ta ɗan buɗe baki, tana kallon Inno sannan ta kalli Zayd, kamar wadda ta riga ta san wannan maganar za ta ƙara rikitar da komai.
Zayd ya yi shiru kawai, yana kallonta ba tare da wata damuwa a fuskarsa ba.
Bai yi ƙoƙarin kare kansa ba.
Bai yi ƙoƙarin yin gardama ba.
Kawai ya tsaya ne, hannunsa ɗaya cikin aljihunsa, yana kallon Inno cikin wannan calmness ɗinsa mai tayar da hankali.
Seeing that he was not responding, Inno ta ci gaba da cewa: “Yanzu ka zo ka bada ƙudade za a haɗa musu lefe gaba ɗaya matan naka! Kuma ita uwargidan, biyu zaka mata—na aurenta da kuma na faɗar ƙishiya. Ka tura ƙudin a account ɗin Suhaila yanzu domin ta yi lissafi, idan da ciko sai ka ciko.”
Suhaila ta ɗan ɗago gira.
Ta kalli Inno, sannan ta kalli Zayd.
A wannan lokacin ma, Zayd bai motsa ba.
Sai kawai ya ɗan karkatar da kansa, kamar yana auna kalmomin da zai faɗa.
Zayd ya kalle ta kai tsaye, muryarsa ta fito tsaf cikin wata irin sanyi amma mai ɗauke da tsantsar kwarjini:
“Iya wacce na aura da yardata zan yi wa lefe… Ita wacce kike shirin liƙa min, ke sai ki yi mata.”
Shiru ya sauka a falon.
Kamar an kashe duk wata magana a cikin falon.
Suhaila ta zaro idanu, tana rike dariyarta.
Inno kuwa ta tsaya cak, bakinta ya ɗan buɗe, kamar har yanzu kwakwalwarta na ƙoƙarin processing ɗin abin da kunnenta suka ji.
Zayd kuwa ko ƙifta ido bai yi ba.
From that moment, he didn’t utter another word. Ya wuce abinsa zuwa matakala, ya bar falon cikin takunsa mai nutsuwa.
Takunsa ɗaya bayan ɗaya yake hawa, babu sauri, babu waiwaye.
Inno ta tsaya a tsakiyar falon baki buɗe, completely stunned by his audacity!
Ta ɗaga hannu ɗaya zuwa kirjinta, sannan ta girgiza kai a hankali kamar ba ta yarda da abin da ya faɗa ba.
Suhaila kuwa, dariya ta ƙube mata har sai da ta faɗo daga kan sofa ɗin da take zaune, tana riƙe cikinta saboda tsananin dariya.
Ta kasa zaune daidai. Ta sunkuya, tana bugun sofa da tafin hannunta, hawaye har sun fara fitowa a gefen idanunta saboda dariyar.
Inno ta juyo baki buɗe tana kallon Suhaila da kanta ke shirin faɗuwa ƙasa saboda dariya:
“Ke! Kin ji abin da yaron nan ya faɗa kuwa?!”
Amma Suhaila ta kasa ko buɗe idonta balle ta iya bawa Inno amsa, kawai ci gaba da yin dariya take yi son ranta!
Ta yi ƙoƙarin magana, amma dariyar ta sake kubuce mata.
Da ƙyar Suhaila ta samu ta tsaita dariyarta, ta goge hawayen da suka zuba. Ta ɗan ja numfashi mai zurfi, tana ƙoƙarin dawo da nutsuwarta, amma har yanzu gefen bakinta yana ɗauke da murmushin da ta kasa ɓoyewa.
Inno kuwa tana tsaye a tsakiyar falon kamar wata mutum-mutumi. Fuskarta hade saboda ɓacin rai da kuma irin wulaƙancin da Zayd ya yi mata. Ta dafe ƙugunta na ɗan lokaci, sannan ta ɗaga kanta a hankali tana kallon Suhaila da wani irin kallo mai ɗauke da gargaɗi.
“Wato Suhaila maganar ma dariya take ba ki ko?” Inno ta faɗa tana jefa mata wani irin mugun kallo.
Ta ɗan ɗaga hannayenta sama cikin takaici, sannan ta sauke su da ƙarfi a gefenta.
Suhaila ta tashi tsaye tana gyara rigarta, trying so hard to keep a serious face. Ta matse leɓɓanta waje guda, ta share gefen idonta, amma kallon Inno ya sa ta ƙara jin wata dariyar.
“Inno, ƙe ma fa kin san Akhie ba za a taɓa yi masa abu dole ya ƙyale ba. You pushed him too far, and honestly, he made his point crystal clear. Ya ce wadda ya aura da yardarsa ita kaɗai zai yi wa lefe!”
Ta faɗi maganar cikin nutsuwa, tana ɗan ɗaga hannunta kamar wadda take ƙoƙarin yi wa Inno bayanin abin da ya faru cikin hankali.
“Wallahi ƙarya yake!” Inno ta daka tsawa cikin fushi.
Ta matso gaba kaɗan, idanunta suka ƙanƙance cikin tsantsar masifa.
“Dolensa ne ya yi! Shi da kansa zai fitar da ƙudin lefen nan ya yi mata dole babu fashi! Za mu gani idan shi ya isa ya yi min taurin kai a gidan nan!”
Ta ƙare maganar tana nuna hanyar da Zayd ya bi, kamar yana nan a gabanta.
Daga haka Inno ta juya ta nufi dakinta tana mita da masifa a tsaye, tana saƙa yadda za ta bi da Zayd. Takunta ya kasance cikin sauri, hannayenta suna motsi lokaci-lokaci yayin da take ta furta kalmomin takaici a ƙasa-ƙasa.
Suhaila ta bi ta da kallo tana girgiza kai tare da guntun murmushi a fuskarta.
Ta san Inno sosai.
Idan ta fara wannan irin mita da masifar, kuma shikenan an shiga uku.
Ta ɗan karkata kanta gefe, tana kallon Inno wadda har yanzu take ta faman magana ita kaɗai.
Knowing very well that the real drama was just getting started.
A daren ranar, around 9:00 PM, Raihana tana tsaye a gaban mirror ɗinta. Fuskarta har yanzu babu alamar walwala; tsantsar damuwa ce kawai ke ɗauke a tattare da ita.
Ta gama shirin kwanciya bacci tsaf. Ta haɗe tsawon gashinta waje guda, sannan ta ɗauki bun ɗinta ta ɗaure shi sosai. Tana shirin saka hularta ke nan, sai Umma ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama.
Raihana ta ɗago kanta a hankali ta kalle ta, muryarta na fitar da amsar sallamar cikin sanyi:
“Wa’alaikumussalam…”
Umma ta ƙaraso ciki, ta zauna a gefen gadon Raihana, amma idanunta har yanzu suna kanta, carrying a deep, motherly concern.
Raihana ta ƙarasa saka hularta a kanta, sannan ta ƙaraso a nutse ta zauna a gefen Umma. Ta haɗa hannayenta a cinyarta, tana ƙoƙarin riƙe kanta da ƙarfi, but she was trying so hard to hold back the heavy tears that were threatening to spill from her eyes.
Umma ta miƙa hannu ta shafa fuskarta a hankali.
“Kukan ne har yanzu, Raihana?”
Kamar wadda take jira kawai a taɓa, Raihana ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Ta rufe fuskarta gaba ɗaya da tafin hannayenta biyu, kafadunta suna rawa a hankali saboda tsananin kuka.
Umma ta yi shiru, tana kallonta cike da tausayawa. Suka yi kusan mintuna biyar a haka—Raihana na shessheƙar kuka mai ban tausayi, yayin da ɗakin ya kaɗaita da sautin kukanta.
Daga ƙarshe, Umma ta kama hannayenta ta sauke su daga fuskarta. Ta sake shafa kumatun Raihana, tana goge mata hawayen da suka jika fuskarta.
Sai kuma ta janyo ta a hankali, ta kwantar da kanta a saman cinyarta.
Hannunta ya fara shafar bayanta cikin lallashi, causing Raihana to slowly let out long, shaky breaths.
Umma ta fara magana a hankali, her voice dripping with warmth and wisdom:
“Kiyi haƙuri, Raihana. Kowacce mace a duniya, akwai kalar yadda ƙaddarar aure ke zuwar mata. Ba kowacce mace ke samun fari da aminci a karon farko ba.”
Ta ɗan yi shiru na dakika kalilan, tana ci gaba da shafa bayanta a hankali, kafin ta ci gaba:
“Ba ki gani yadda ni kaina na yi nawa auren ba? Na bar mahaifata, na zo wani sabon gari… wata ƙasa ma daban da ban da kowa, ban kuma san kowa ba. But I endured, because marriage requires sacrifice.”
Umma ta sauke numfashin a hankali, sannan ta sake shafa hannun Raihana.
“Kinsan mahaifinki ba zai taɓa yi miki abin da zai cutar da ke ba a rayuwa. Balle ma ai kina son mijinki, tunda ƙe ce da kanki kika yarda ya turo gidan nan da amincewarki…”
Hearing those words, Raihana ta runtse idanunta gam, yayin da sabbin hawaye masu zafi suka sake zubo mata. Leɓɓanta suka ɗan motsa kamar za ta yi magana, amma babu wata kalma da ta fito.
Ya Allah… ta furta a cikin zuciyarta cike da tsantsar takaici.
Wallahi Zayd ya cuceta! Ya kulleta a wajen iyayenta gabaki ɗaya. Kowa yanzu zato yake ita ce da kanta ta aiko shi da amincewarta, alhalin shi da kansa ya haɗa wannan abun ba tare da ta sani ba!
Kafin tunaninta ya yi nisa, Umma ta katse mata hanzari:
“Idan kuma sabida auren da zai yi ne na biyu kike wannan damuwar, ki kwantar da hankalinki. Kowacce mace akwai matsayinta a wajen mijinta, kuma kowacce da irin halinta za ta zauna a gidanta. Ni dai abin da nake so da ke… karki yarda ki cutar da ita ko da a magana ne. Ki zauna da ita da zuciya ɗaya, ba ma ita kaɗai ba, har da kowa da kika tarar a danginsa. Idan kika yi hakan, za ki ga yadda Allah zai tsare ki daga sharrin kowa.”
Raihana lay flat on Umma’s lap, totally speechless. Idanunta a lumshe suke, hawayen kuma suna zuba a hankali daga gefen idanunta, suna bin gefen fuskarta. Ba ta furta ko kalma ɗaya ba, nor did she attempt to clear the misconception.
Kawai ta bar idanunta a lumshe, letting her silence speak for the intense emotional turmoil within her.
A hankali ta ɗaga hannunta ta riƙe gefen rigar Umma, kamar ƙaramin yaro da yake neman mafaka. Ta yi shiru, tana sauraron kowace kalma, amma a cikin zuciyarta, wani irin yaƙi ne ke ci gaba da gudana.
Daga ƙarshe, Umma ta gyara mata kanta a saman matashin kai, ta yi mata addu’o’in tsari da fatan alkairi, sannan ta rufa mata katoton duvet ɗinta.
Ta tsaya na ƴan seconds tana kallon Raihana, kafin ta shafa kanta a hankali.
“Allah Ya miki albarka, Raihana. Ya sauƙaƙa miki duk abin da ke gabanki.”
Sai ta miƙe, ta kashe fitilar ɗakin, sannan ta tura ƙofar ta fita.
Bayan fitar Umma, duhun ɗakin ya sake ƙauraye Raihana.
Ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon silin ɗin ɗakin da ba ta iya gani sosai cikin duhun.
Hawayen da ta yi ƙoƙarin dakatarwa suka sake zubo mata.
Ta juya gefe ɗaya, ta janyo duvet ɗin sama kaɗan, tana ƙoƙarin ɓoye shessheƙarta kamar Umma tana nan kusa da ita.
Ta ci gaba da yin kukanta a ɓoye cikin sanyi da takaici, har tsantsar gajiya da kuka suka rinjayeta.
Numfashinta ya fara raguwa a hankali.
Shessheƙar kukanta ta ragu.
Idanunsa suka yi nauyi.
A ƙarshe, bacci ya ɗauke ta…
Washegarin ranar, Raihana ta tashi da wani irin sauƙin ɓacin rai a zuciyarta. Duk da ta yi bacci, jikinta bai ji kamar ya samu cikakkiyar hutu ba. Tunanin abubuwan da suka faru a kwanakin ya riga ya mamaye zuciyarta tun kafin ma ta fara sabon ranar.
Ta fito tsakar gida a nutse, ta taya Umma gudanar da duk wani aikace-aikacen gida na safe. Ba ta cika magana ba, sai dai ta yi duk abin da ya kamata cikin shiru da nutsuwa, har suka kammala komai tas.
Bayan sun gama ne Umma ta kalleta cikin kulawa da muryarta mai sanyi:
“Kije kiyi wanka ki shirya, Maman Ihsan tana ta jiranki kizo. Kinsan halinta kuma… idan kika ɓata lokaci za ta iya tahowa har nan da kanta.”
Raihana ta ɗan tsaya cak, hannunta riƙe da tsintsiyar da ta gama shara. Ta ɗago idanunta zuwa ga Umma, fuskarta cike da wata irin gajiya da komai ma.
Maman Ihsan aminiyar Umma ce ta ƙud da ƙud. Tun sanda Umma ta tare a garin, amincinsu ya ƙullu har ya koma tamkar na ƴan uwan jini. Kusan duk haihuwar da Umma ta yi a ƙasar nan, Maman Ihsan ce ke tsaye a kanta, ta zama mata yar uwa, ta zama mata maƙwabciya, kuma tsayayyar amintacciyya duk abinda ya kama na Umma ita ke yin uwa tayi makarbiya.
Saboda haka, tun lokacin da Maman Ihsan ta ce tana jiranta, Umma ta san sarai cewa babu wata hanyar da Raihana za ta samu ta kauce mata.
Raihana ta ɗan langwaɓe kanta a hankali, ta sauke wani ƙaramin numfashi kamar wadda ta riga ta san ba za ta samu yadda take so ba.
“Umma… ɗan Allah ba sai na yi komai ba.”
Muryarta ta fito da wani irin roƙo mai laushi, idanunta har sun fara tara kwalla.
Amma Umma ta kalle ta kai tsaye.
Muryarta ba ta da alamar wasa:
“Kije ki shirya maza, ki wuce.”
Raihana ta ɗan goge hawayenta, ta yi shiru na ƴan seconds.
Ta san daga yanayin muryar Umma cewa babu wata gardama da za ta yi amfani da ita.
A hankali ta juya, ta nufi hanyar ɗakinta.
Ƙafafunta suna tafiya, amma zuciyarta kamar ba ta son bin su.
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya.
A lokacin, tana jin tamkar ta haɗiye zuciya ta huta, saboda yadda duk wani shiri na auren ke ƙara ɗora mata nauyi da matsin lamba a rai.
Yanzu ma ba ta san abin da za ta tarar a wajen Maman Ihsan ba.
Amma abu ɗaya ta sani…
Auren da take ƙoƙarin fahimta ne kawai yake ƙara matsowa kusa da ita, yayin da ita kanta har yanzu take ƙoƙarin fahimtar yadda rayuwarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci.
Not edited