THE UNWANTED BOND
ZAYD ARMAAN
CHAPTER SIXTY:60
THE UNWANTED BOND
JIDDAAH BARKUM
————-
Wannan mugun kusancin da kuma yadda ya zuba mata idanu gaba ɗaya ya firgita Raihana. Ta haɗiye wani uban yawu, idanunta suka firfita kaɗan tana kifta su da sauri kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya, amma maimakon ta yi shiru ta ba shi amsa cikin sauƙi, sai ta murguɗa baki tana janye idanunta daga nashi. Tsoron da ya datsa a ranta ya juye zuwa wata irin tsantsar rashin kunya da masifa.
Ta ɗaga kai tana kallon cikin idanunsa direct, duk da yadda zuciyarta ke dukan uku-uku saboda kusancin da ke tsakaninsu.
“Toh ni na san kai ne ka kira? Da ka kira ai ba cewa ka yi kai ne ba!” Muryarta ta fito cikin rawar tsiwa. “Balle ma dai har yanzu ina gidanmu! Ba ka da haƙƙin da za ka ce wai dan zan fita sai na tambaye ka! Ka jira na dawo gabanka mana kafin ka fara ba ni wadannan zaɓaɓɓun rules ɗin naka… And for your information, ni ban fara ganin kaina a matsayin wata matar aure taka ba tukunna!”
Raihana ta ƙarasa rufe bakinta tana ƙawarda kanta gefe, sai ta ji Zayd ya sake ƙara ƙarfin riƙon da ya yi mata—his patience was completely pushed over the edge, leaving no room for her defiance.
Zayd bai sake ba ta damar yin wata tsiwar ba. Ya matse jikinsa gaba ɗaya da nata a bango, pinning her completely with his broad frame and allowing no space between them. Raihana ta ji yadda tudun ƙirjinta ya sauka a kan nasa ƙirjin mai ƙarfi, wani irin zafi da shock suka bi ta jikinta a lokaci guda.
Kafin ta ankara, Zayd ya sa hannunsa ɗaya ya ƙanƙame bayan kanta, ya ɗaga fuskarta sama, sannan cikin wani slow motion ya fara sauke kansa. Ba zato ya ɗora bakinsa kan lips ɗinta, ya yi grabbing ɗinta with intense dominance, ya cafki leɓenta na ƙasa da bakinsa ya fara aika mata wani irin mashahurin kiss mai cike da mugun zafi!
Ya kamo leɓenta yana wani irin tsotsarsa da kyau. Daga yadda yake tsotsar ka san da niyyar mugunta ne, ɗan ba ƙaramin deep sucking yake mata ba; tabbas ya nuna mata matsayinsa a matsayin mijinta da ba ta gama yarda da shi ba. Raihana ta zaro idanu waje cikin tsantsar firgici, girar ta suka ɗago, numfashinta ya rikice saboda tsananin mamaki da tsoro. Tana ƙoƙarin haɗe leɓunanta tamau tana wani irin mutsu-mutsu da ƙoƙarin juyar da kanta gefe, amma jikin Zayd ya fi ƙarfinta gaba ɗaya. Hannayenta biyu da ke ƙirjinsa sun gaza tura shi ko da da rabin inch ne, sai ma hannunsa ɗaya da ya ɗago ya sake dawo da shi kan cheeks ɗinta, ya ƙama kanta da kyau a cikin tafin hannunsa, giving his mouth total control and full access to her soft lips.
Sautin numfashin Zayd ya rikiɗe ya zama mai nauyi yayin da yake ƙara shiga cikin bakinta, overpowering her senses and sucking her lip deeply, fiye da yadda ya zaci zai yi. Raihana ta ji duk wata tsiwa da rashin kunya sun warware sun zama ruwa. Tsoro tsantsa ya kama ta; idanunta suka cika da ƙwallar firgici, fuskarta ta yi sanyi saboda firgicin da ya mamaye ta, ganin yadda yake sarrafa bakinta ba tare da tausayi ba.
Ganin yanayin jikinsa ya fara canjawa ya sanya a hankali ya zare lips ɗin bakinsa a nata, pulling back slowly while locking his dark eyes on her face with a intense, unblinking glare.
Lokacin da ya sake ta a hankali, Raihana ta tafi luuuu zata faɗi saboda yadda jikinta ke mugun rawa. Cikin sauri ya riƙo ta, pulling her flush against the wall once more. Ta saki wani ƙaramin numfashin mai fita da sauri-sauri, bakinta yana wani irin rawa. Lips ɗinta sun riga sun kumbura, sun yi jawur saboda yadda ya tattare su ya matsa su da tsotsa mai ƙarfi. Zayd ya ci gaba da kallon fuskarta duk da ta lumshe idanunta, ya bar fuskarsa daf da nata, yana shakar daddaɗan ƙamshin da ke fita daga jikinta na gyaran jikin da aka yi mata.
“Open your eyes,” ya faɗa can ƙasa in a low, dangerous whisper, don ba dan tana daf da shi ba ba za ta ji abin da ya faɗa ba saboda yadda muryarsa ta yi sanyi. Kamar wadda aka yi wa remote, ta buɗe idanunta a hankali, ta sauke su fesss a kan fuskarsa.
Idanun Zayd suka haɗe da nata direct, babu alamun wasa ko ɗan sassauci a ciki. Yana kallon tsantsar tsoron da ke ɗauke a cikin idanunta. Ya sunkuyo da kansa, muryarsa ta fito tsakiyar bakinta tana fitar da ɗumi a tsakanin lips ɗinta da suka kumbura:
“Ina tambayarki… waye mutumin nan? And why did you go out without my permission?”
A daidai lokacin, Raihana ta riƙe numfashinta da ƙyar. Duk da yadda take jin jikinta na rawa saboda tsoro, sai tsiwar tata ta sake motsawa a fakaice. Ta ɗan lafe a bangon tana harararsa ta ƙasan ido, tana son ta sake ba shi amsa cikin tsiwa, amma tana tsoron kusancinsu.
Zayd ya lura da yadda take son ta sake kawo masa taurin kai. Ya lumshe idanunsa kaɗan, sannan ya buɗe su a kanta.
Cikin wata irin muryarsa da ta fara dusashewa sosai—mai cike da nauyi—ya ce: “Since you are not ready to talk… bari na ci gaba da abin da kike so.”
Kafin ta ankara, ya sake haɗe ɗan gap ɗin da ya rage, closing every single inch between them and pressing his heavy chest against hers, completely allowing no space between them! Raihana ta saki wani ƙaramin numfashi na firgici, idanunta suka sake buɗewa sosai, ta ji tamkar zuciyarta za ta fito daga ƙirjinta saboda tsananin tashin hankali da mamaki da suka mamaye ta.
Tsoro da mamakin wannan miskilin ya gama kashe mata jiki. Ta zaro idanunta waje sosai, ta ji tamkar ruhi zai fice daga jikinta.
“Wallahi zan faɗa maka! Tsaya… tsaya na faɗa maka!” ta furta cikin sauri da rawar murya, tana rufe idanunta da ƙarfi saboda yadda hannunsa ya sauka a kan bombom ɗinta ya matsa da ƙarfi.
Zayd ya ɗan dakata da yawon hannunsa a jikinta, amma ko ɗaya bai sake ta ba. Hannunsa na nan inda yake, holding her firmly, idanunsa masu nauyi suna ta faman yawo a kan fuskarta, kafin ya sauke su kan swollen lips ɗinta.
“Ina kika je?” ya tambaya a tsanake, muryarsa a ƙasa amma tana ɗauke da wani irin umarni da ya sa Raihana ta haɗiye yawu da ƙyar.
Cikin sauri ta fara ba shi amsa tana rawar baki: “Gidan… gidan Maman Ihsan na je… gyaran jiki aka yi min.”
Zayd ya ɗan ɗage giransa ɗaya sama yana kallonta tun daga sama har ƙasa, cike da wani irin kallo na iskanci. “Gyaran jiki aka yi miki a hakan?” ya faɗa idanunsa na ƙara shiga cikin nata, yana jin yadda jikinta ke ɗan rawa a tsakanin hannayensa.
Raihana ta ɗan murguɗa bakinta, ta sa hannu tana ɗan zame hannunsa daga duwawunta, ta furta ƙasa-ƙasa a makogwaronta: “Ohoo…”
Zayd ya haɗe ransa lokaci guda, ya sake matse ta a bango: “Me kika ce?”
Raihana ta firgita, ta yi saurin ƙawarda fuskarta gefe: “Ba da kai nake ba…”
“Ohhh!” Ya furta a hankali. Fuskarsa ta ƙara haɗewa tightly, idanunsa suka rine cikin wani irin tsanani da bai ba ta damar wasa ba ko kaɗan. “Waye wanda ya tare ki?”
Raihana ta ɗan ƙawarda kanta gefe, tana ƙoƙarin ɓoye yadda bakinta ke rawa, kafin a hankali ta fara faɗa masa: “Abokin Haris ne…”
Zayd ya haɗe ransa sosai, girarsa ta tsuke. Muryarsa ta ƙara yin ƙasa tare da nauyi: “Waye hakaaa?”
Raihana ta ɗan ɗago ta kalle shi direct, sai ta sauke idanunta ta zabga masa wata uwar harara ta ƙasan ido: “Saurayina mana! Wanda ka raba mu, ka—”
Babu ko ɗigon sauran haƙuri a tare da shi! Raihana ba ta ƙarasa rufe bakinta ba, Zayd ya ɗago hannunsa, ya sa yatsansa guda biyu ya dalle mata lips ɗinta da ƙarfi!
“Wayyooo!” Raihana ta saki wani ƙaramin ihu mai fitar da tsantsar shagwaɓa da radadin zafi, har sai da ta lumshe idanunta tana juya fuskarta gefe!
Zayd ba tare da ya ɗaga kansa ba ko ya sake ta daga jikin bangon ba, ya tsare fuskarta da kallo, fuskarsa ba ta da ko ɗigon wasa. Ya ƙara matse ta a bango gaba ɗaya, muryarsa ta fito da wata irin amsa mai nauyi da tsanani da ta ratsa cikin kunnen Raihana:
“Kina ɗaukar auren abin wasa ne da za ki riƙa kiran wani ‘saurayinki’ da aurena a kanki? Me ma ya kai ki tsayawa da shi? Ki sani, faɗar hakan da aurena a kanki babban laifi ne! Ko ni an ce miki sonki nake yi? Do you think I’m madly in love with you?”
Kalaman nasa gaba ɗaya suka doki zuciyarta, ga kuma wani masifar zafi da lips ɗinta ke yi mata saboda yadda ya dalle mata leɓen da ya riga ya kumbura. A take wani zafaffen hawaye ya wanke fuskarta, ya zubo har kan leɓenta.
Ta ɗaga idanunta da suka rine suka kuma cika da hawaye, tana kallonsa cikin tsantsar radadi da jin haushinsa. Muryarta ta fito a shaƙe, cike da shagwaɓa da kuka: “Tunda ba ka so na… toh ka sake ni mana! Meye zai sa ka nace sai da ka aure ni?!”
Hawayen suka ci gaba da zuba a fuskarta gaba ɗaya, bakinta yana wani irin rawa saboda zafin dukan da ya yi mata da kuma haushin kalaman da ya jefa mata.
Zayd ya tsaya tsam yana kallon hawayen da ke bin fuskarta, idanunsa suna yawo tsakanin ƙwallar da ke sauka a kumatunta da kuma lips ɗinta da ke rawa.
Sai ya ƙara tsuke fuska, idanunsa suka rine yayin da kalaman Raihana suka ratsa shi. Maimakon ya ba ta amsa cikin sauri, sai ya sake matso da fuskarsa daf da nata, har yana jin dumin numfashinta mai cike da rawar kuka.
“Na sake ki?” ya faɗa a tsanake, muryarsa a matukar ƙasa amma tana ɗauke da wani irin barazana da masifa. “Za ki ci gaba da mafarkin samun saki ne a hannuna. Mutu ka raba, shine kaɗai abin da zai raba mu… So get that useless thought out of your head.”
Ya sa yatsansa guda biyu ya kama habarta ya riƙe fuskarta tamau don kar ta juyar da kanta gefe. Yana kallon tsantsar haushin sa da tsoron da ke ɗauke a cikin idanunta, ya buɗe bakinsa a hankali:
“An ce miki ana sakin mace don kawai ta buƙata? Da aurena a kanki, ba ki da wani ikon zaɓi. I own you now… and you will stay right here and endure every single thing I throw at you.”
Raihana ta sake fashewa da kuka sosai, kumatunta na karkarwa a cikin tafin hannunsa. Zafaffen hawayen da ke zuba daga idanunta ya jika yatsunsa, amma ko ɗaya bai saki fuskarta ba.
Cikin matsanancin kuka da rawar jiki, ta kalle shi direct cikin idanu, idanunta cike da ciwo da rashin fahimta, tana fitar da kukan da ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya:
“Toh ana so dole ne?! Da za ka ɗage dole sai na zauna da kaii, kuma ka zo har gidanmu kana cin zalina…!”
Tana ƙarasawa, sai kawai ta fashe da wani zafaffen kuka mai ban tausayi, ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta biyu. Jikinta gaba ɗaya ya soma wani irin mugun karkarwa, tana saurin shakar numfashi saboda masifar radadin kalaman nasa da kuma yadda yake wahalar da ita ta hanyar amfani da ƙarfinsa.
Zayd ya tsaya tsam a gabanta, fuskarsa ta saki gaba ɗaya, ba tare da ya bari wani motsin rai ya bayyana a fili ba, sai dai idanunsa da suka sake yin wani irin nauyi yayin da yake kallon yadda take kuka a gabansa. Ya sa hannunsa guda ɗaya ya janye hannayenta daga fuskarta. Yana riƙe da wrists ɗinta tamau a hannunsa guda, ya sunkuyo da fuskarsa daf da nata, muryarsa ta fito a hankali in a whisper:
“Auren dole ko na sa-kai… ba shi ne damuwata ba. Abin da na sani shine yanzu ke matata ce, kuma har abada ba za ki taɓa kuɓuta daga ikona ba.”
Ya sake ɗaga yatsansa ya shafa lips dinta da ya kumbura, yana jin yadda kukan nata ke ƙara tsananta a hannunsa.
Zayd ya cika hannayenta a hankali, sannan ya ɗauki step guda ɗaya baya. Ya zuba mata idanu yana kallonta kamar kukan gaba ɗaya bai damu da shi ba, fuskarsa normal ba tare da wata alamar ya damu ba. Amma can ƙasan zuciyarsa, ya matukar mamakin yadda kowace ƙwalla da ke zuba daga idanunta ke sokarsa da shiga har can cikin zuciyarshi, wanda ya kusa karya kwarjininsa.
Ya sa hannu a aljihun wandonsa, ya ciro wani bundle mai yawa na fresh $100 dollar notes. Cikin takun iko, ya kamo hannunta guda ɗaya ya danna mata kuɗaɗen a ciki.
Sake hannun da ya yi, Raihana ta so ta buɗe hannunta kuɗin su zube a ƙasa saboda masifar takaici. Amma kafin ma ta janye hannun, Zayd ya haɗe ransa sosai cikin wani strictly dangerous tone:
“Wallahi idan kika zubar, za ki sha mamaki na.”
Raihana ta runtse idanunta ruf, fuskarta ta matse saboda takaici da bacin rai, tana kuma ƙoƙarin danne kukan da har yanzu yake tasowa daga makogwaronta. Amma kalaman nasa sun tsaya mata a rai, don haka sai ta kasa zubar da su kamar yadda ta yi niyya; kawai ta riƙe kuɗin a hannunta tana cigaba da kuka.
A hankali Zayd ya koma ya sa hannunsa a aljihu, ya ciro mukullin ƙofar parlour ɗin wanda ya kulle gaba ɗaya. Ya saka mukullin ya buɗe ƙofar, sannan ya tsaya chak yana juyowa kaɗan ya kalle ta.
“Wipe those tears,” ya faɗa a tsanake, muryarsa tana ɗauke da umarni.
Raihana ta ɗago fuskarta da ke cike da hawaye, idanunta sun yi ja saboda kuka, ta zabga masa wata zafaffar harara ta ƙasan ido saboda masifar haushinsa da ke cin zuciyarta. Amma duk da hararar, ta miƙa hannu ta share fuskarta gaba ɗaya ta goge hawayen.
Ganin abin da ta yi sai ya sanya Zayd sakin wani irin ɗan murmushi na mugunta, kusurwar bakinsa ta ɗan motsa yayin da idanunsa suka tsaya kanta, kafin ya furta a hankali:
“Good girl.”
Daga haka ya juya da ƙasaitaccen takunsa, ya fice daga parlour ɗin gaba ɗaya ya barta a tsaye a wurin tana dafe da ƙirjinta da kuɗaɗen da ya bar mata a hannu.
Not edited