THE UNWANTED REALITY
ZAYD ARMAAN
CHAPTER SIXTY THREE: 63
THE UNWANTED REALITY
JIDDAAH BARKUM
————
Bayan ficewar Maryam daga ɗakin Raihana, ta ja ƙafafunta a hankali, ta ƙarasa gefen gadonta ta zube a kai. Ta yi shiru tana kallon wuri guda, idanunta sun tsaya a wani wuri kamar ba ta ganin abin da ke gabanta. Ita kanta ba ta san ainihin tunanin da yake yawo a kanta ba—kalaman Maryam, da irin cin zalincin Zayd gaba ɗaya sun riƙe mata ƙwaƙwalwa in total confusion.
A hankali ta sauke gajeren numfashin, ta ɗan runtse idanunta na ƴan seconds, sannan ta miƙe tsaye. Ta sa hannunta a ƙaƙashin pillow ɗin gadonta, ta zaro ɗamin dalar da Zayd ya ɗamƙa mata ɗazun. Ta ɗan kalle ta na ƴan seconds, fuskarta babu wata alama, sai dai idanunta sun ɗan nuna wani irin tunani mai zurfi. Sannan ta juya ta tura ƙofar ɗakinta, ta fita kai tsaye zuwa ɗakin Umma.
Tana shiga ɗakin Umma cikin sanyin jiki, ta ƙarasa gefen gadon da Umma ke zaune ta zauna a hankali. Ta ɗan ja guntun mayafin rigarta tana gyara rufuwar gashinta mai masifar laushi da santsi, da aka gama gyaransa da tsara shi lami lafiya a gidan Maman Ihsan.
Umma ta ɗago kanta ta ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa. Ta ga fuskarta ba ta da ko ɗigon walwala ko alamar farin ciki. Ta ɗan ƙanƙance idanunta, kamar tana ƙoƙarin karanta abin da ke ranta. Amma sanin cewa a ƴan kwanakin nan dama Raihana ba ta cika sakin fuska ko yin fara’a ba gaba ɗaya, ya sa Umma ba ta bi ta kan tambayarta the reason behind her bad mood ba.
A hankali, Raihana ta ɗago hannunta, kai tsaye ta ajiye kuɗin da ya bar mata a gaban Umma a kan shimfiɗa. Hannunta ya ɗan tsaya a kan kuɗin na ɗan second kafin ta janye shi da sauri.
Umma ta kafe kuɗin da kallo na ƴan seconds, girarta ɗaya ta ɗan ɗaga, sannan ta ɗago tana kallon Raihana fuskarta cike da tambaya, waiting for an explanation.
Raihana ta saukar da kanta ƙasa, hannayenta biyu suna ta murza gefen rigarta, gaba ɗaya ta kasa haɗa eye contact da Umma. Yatsuntsa suna ɗan karkarwa, ta haɗiye yawu a hankali kafin muryarta ta fito a hankali, cike da nauyi da ɗan rawar murya:
“Wajensa ne… Shi ne ya ba ni. Na ƙi karɓa wallahi Umma, amma ya matsa ya ce dole sai na karɓa…”
Umma ta ci gaba da kafe ta da idanu ba tare da ta ce uffan ba, fuskarta completely expressionless. Ta ɗan karkatar da kanta gefe, idanunta har yanzu a kan Raihana, kamar tana jiran ƙarin bayani.
Irin wannan zurfaffen kallon da Umma ke yi mata ne ya sa gaban Raihana ya yanke ya faɗi masifaffan faɗuwa kuwa. Nan take ta soma jin wani irin zafi yana taso mata daga tafin ƙafafunta har zuwa kanta, wata azababbar kunya da fargaba suka mamaye ta. Ta ɗan motsa a zaune, ta haɗe hannayenta biyu a kan cinyarta, idanunta suka ƙara sauka ƙasa.
A ranta, ji take yi kamar Umma ta riga ta fuskanci ainihin abin da ya faru tsakaninta da Zayd a falon Baffa—daga azababben matse lips ɗin da ya yi mata, dominant hold ɗin da ya yi mata, har zuwa matsattsen saƙon da ya bar mata a jiki.
Ta sake sunkuyar da kanta sosai ƙasa, yatsunta na karkarwa yayin da take murza gefen rigar jikinta cikin tsantsar matsuwa. Numfashinta ya ɗan yi nauyi, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin ɓoye rikicewar da ke bayyana a fuskarta.
Umma ta sauke numfashi kafin a hankali ta ce:
“Ki ajiye. Idan Baffanki ya shigo, sai a kai masa.”
Raihana ta gyaɗa kanta a hankali, tana sauke gajeren relief breath. Kamar dai wannan amsar ita ce kawai take jira domin ta samu damar tashi daga wurin. A hankali ta miƙe tsaye, ta isa gefen mudubin Umma ta ajiye ɗamin kuɗin a kai cikin nutsuwa. Ta ɗan tsaya na ƴan seconds tana kallon kuɗin, sannan ta juya ta koma inda Umma take.
A ranar, wajen ƙarfe biyar na yamma, Baffa ya shigo gidan. Su Yaya Hamza da wasu maza biyu ne biye da shi, suna ta shigar da kaya da ke cikin kwali an yi sealing cikin gidan, suna ajiyewa a gefe ɗaya. A lokacin, dukkan jama’ar gidan suna tsakar gida zaune, ciki har da Mama Sabuwa da Bintu.
Hayaniyar ajiye cartons da motsin mutane ta cika tsakar gidan. Wasu daga cikin mutan gidan suka ɗan juyo suna kallon kayan da ake shigarwa, yayin da Raihana ta zauna cikin nutsuwa, gabanta na faɗuwa, idanunta a ƙasa.
Bayan sun gama shigar da komai, Baffa ya fita waje ya sallami mazan. Sannan ya sake shigowa gidan tare da Yaya Hamza. Ya dubi Umma, ya ce:
“Ga kayan ɗakin Raihana nan… gado ne set biyu, sai kujeru. Kayan kitchen ɗin kuwa, gobe da wuri sai ku fita ku je kasuwa ku siya. Idan akwai sauran ƙananan abubuwa waɗanda ni tunanina bai kawo kai ba, sai ki yi tunani zuwa anjima ki sanar min dan na bayar da kuɗi.”
Ya miƙa mata ledar hannunsa:
“Gashi, kuɗin kitchen items ɗin ne. Ba sai an yi wani abu na musamman ba, kawai a tabbatar an siya mata abubuwa masu muhimmanci kaɗai.”
Umma ta sa hannu biyu ta karɓa cike da girmamawa, ta ɗan sunkuyar da kanta:
“Toh, Allah ya saka da alheri. An gode, Baffa.”
Baffa ya gyaɗa kai kawai, babu wani dogon bayani a fuskarsa. Ya juya ya nufi ɗakinsa cikin nutsuwa.
Raihana kuwa ta sauke idanunta ƙasa, tana haɗiye wani abu mai masifar nauyi da ƙyar daga makogwaronta sakamakon emotional heaviness ɗin da ke maƙale a ƙirjinta. Ta ɗan matse yatsunta a kan cinyarta, numfashi na sauka a hankali.
Yaya Hamza ma ya juya ya koma ƙofar gida.
Directly, Maryam ta yi murmushi tana kallon Umma bayan tafiyar Baffa:
“Umma, amma fa ni za a je da ni! Wallahi I know all the trendy and essential items da za a siya mata!”
Ta ɗaga gira sama cikin wasa, kamar wadda ta riga ta yanke shawarar cewa ita ce za ta jagoranci wannan siyayyar.
Umma ta ɗan yi ƙaramin dariya, tana girgiza kanta:
“Toh Maryam, dama ai ke da ita za ku je. Ku je tare, ai da hankalinku ku biyu kun san abin da ya kamata.”
Mama Indo ta yi ƙaraff ta tare maganar, tana ɗan gyara zamanta:
“Haba Hajara! Sai a aika yara kasuwa su kaɗai? Banda shiririta, me za su yi? Kina jin Malam ya ce iya abubuwa masu muhimmanci kawai. Ai gwara yanzu a aikawa Maman Ihsan… idan goben ba ta yin komai sai mu je ni da ita in sha Allahu a siyo. Amma yaushe za a bar Raihana da Maryam su yi wani siyayyan kayan aure?”
Umma ta yi ɗan murmushi, ta ɗan ɗaga cikin sanyin hali:
“Babu komai… toh, Allah ya kaimu.”
“Amin,” Mama Indo ta amsa.
Mama Sabuwa, wadda ke binsu da kallo tun ɗazu da wani azababben eye-roll, ta ɗan yatsine fuskarta. Ta ja wani riƙaƙƙen tsaki mai sauti, tana ɗan juyar da kanta gefe kamar abin da suke faɗa ya ɓata mata rai sosai.
Cikin ɗaga murya ta ce:
“Allah ya tsinewa shishshigi a rayuwa! Mutum ya ɗinga tusa kansa inda ba a nemansa. Wannan kayan kunya da yawa yake! Ka rasa inda za ka yi shishshigi sai wajen kishiya? Kai… amma Allah wadaran naka ya lalace!”
Ta ƙare maganar da wani dogon tsaki, tana zazzare idanu kamar har yanzu akwai sauran abin da take son faɗa.
Mama Indo ta watsa mata wani mugun kallo na takaici. Ta ɗan buɗe baki, kamar za ta mayar mata da magana, amma kafin ta samu damar amsawar, Bintu ta riga ta cusa kanta cikin masifa.
Bintu ta ɗan matsa gaba, fuskarta cike da ƙarfin hali, ta ɗaga gira tana kallon Mama Sabuwa kai tsaye:
“Ke ma Mama wallahi kina da matsala! Ina ruwanki da harkar aurensu?! Ina! A kan auren ne ke kika rasa naki auren? I think whatever is being done for this wedding, bai kamata ki sa baki ba! Duk ma wanda ya cusa kansa, meye naki a ciki? Kamar ba ki san dama gidan nan akwai masu fuska biyu ba munafukai… Can matsalarsu ce su suka sani!”
Tsakar gidan ya yi shiru na ɗan second.
Mama Sabuwa ta zaro idanu gaba ɗaya, kamar ba ta yi tsammanin Bintu za ta yi mata wannan rashin kunyar a gaban mutane ba. Ƙeɓen leɓenta ya ɗan buɗe, tana kallonta yayin da fuskarta ta fara sauyawa.
Maryam kuwa ta zagayo ta jefa wa Bintu wani mugun kallo na raini da kyama. Ta ɗan matsa jikinta gaba, ta buɗe baki za ta soma magana cikin fushi, amma Mama Indo ta tare ta nan take.
“Me za ki ce mata Maryam? Ƴar da ta hayayyaƙowa uwarta tana mata magana kamar ƴar cikinta, meye abin damuwa dan ta yi wa kishiyar uwarta? A’a, wallahi ni kam ko a jikina! Mutumin da bai girmama uwarsa ba, ya kike zaton za ta girmama taki?”
Maryam ta yi shiru.
Kalaman Mama Indo sun sa ta tsaya kamar an zuba mata ruwa. Ta haɗiye kalamanta, amma har yanzu idanunta ba su daina zabga wa Bintu wancan deadly glare ɗin ba. Fuskarta cike take da takaici, yayin da Bintu ta tsaya kamar ba ta ga wani laifi a abin da ta faɗa ba.
Raihana kuwa kawai kallonsu take yi a zaune. Idanunta suna bin ɗaya bayan ɗaya, amma ba ta furta komai ba. Ita da Umma babu wanda ya tanka ko kalma ɗaya a tsakiyar hayaniyar.
Umma ma kawai ta zauna tana kallonsu cikin nutsuwa, hannunta a kan cinyarta, kamar wadda ta yanke shawarar cewa ba za ta shiga tsakiyar wannan rikicin ba.
Daga ƙarshe, Bintu ta miƙe tsaye gaba ɗaya, tana ja wani uban tsaki mai tsawon gaske, sannan ta juyo ta shige ɗakinsu ba tare da ta sake kallon kowa ba.
Da ta tafi, Maryam ta bi bayanta da idanu, har sai da ta ɓace daga gani. Ta sake sauke wani numfashi mai ƙarfi, tana girgiza kanta a hankali cikin tsananin takaici.
Bayan komai ya lafa daga dambarwar da Bintu ta tawo, Umma ta miƙe cikin nutsuwa ta shiga ɗakinta. Ta ɗan kalli ƙofar ɗakin da Bintu ta shige, sannan ta girgiza kanta a hankali kamar wadda ta gaji da irin wannan hayaniyar.
Ta ɗauko kuɗin da Raihana ta ajiye mata a kan mudubi, ta riƙe su a hannunta cikin tunani, sannan ta fito ta doshi ɗakin Baffa direct.
Baffa ya ɗago kansa daga takardun da yake dubawa lokacin da Umma ta shigo yana kallonta, sannan ya aje abin da yake riƙe da shi gefe. Umma ta ƙarasa ta durƙusa cikin ladabi sannan ta miƙa masa kuɗin, tana bayyana masa cewa daga wajen Zayd suke.
Baffa ya kafe ɗamin dalar da kallo cikin gajeren al’ajabi. Yatsunsa suka ɗan motsa kamar zai karɓa, amma bai yi hakan nan take ba. Fuskarsa cike da nazari kafin ya ɗaga kai ya kalli Umma:
“Wannan kuɗin fa da yawa sosai… It’s too much. Ina ganin a siya mata wani abun da za ta amfana da shi nan gaba, ko fili ko dai wani abun na ƙaruwa.”
Umma ta gyara zamanta, ta ɗan jingina bayanta da kujerar, sannan ta fara magana cikin sanyinta:
“Gaskiya ne. Ko za a ɗauka a ciki a yi siyayyar kayan kitchen ɗin ne kawai?”
Baffa ya girgiza kansa nan take. Fuskarsa ta ɗan ƙara tsuke wa, muryarsa ta ƙarfafa:
“A’a. I prefer that every single essential item da za ta yi amfani da shi a gidanta ya zamana ni ne na siya mata da kaina. Don haka, a yi yadda na faɗa ɗin kawai.”
Umma ta ɗan yi shiru na ƴan seconds, sannan ta amsa cikin girmamawa da biyayya:
“Toh, Allah ya ƙara buɗi mai albarka. Ga kuɗin sai ka ajiye a wajenka kafin a samu abin yi da su.”
“A’a, ki ajiye kawai,” Baffa ya ce yana maida kansa kan abin da yake yi. “Tunda dai a wajenki suke, idan an samu ainihin abin siyan sai a fitar a siya.”
Umma ta gyaɗa kanta a hankali.
“Toh.”
Haka Umma ta amshi kuɗin ta koma ɗakinta. Ta buɗe wani wuri na musamman ta musu kyakkyawar ajiya a wurin da ya dace, tana tabbatar da cewa komai yana cikin tsari kafin ta rufe wurin.
Bayan ta ajiye ta dawo gefen gadonta, ta ɗauki wayarta ta ƙira Maman Ihsan. Wayar ta ɗan yi ringing na ƴan seconds kafin aka ɗauka.
Ta sanar mata da batun zuwa kasuwar gobe domin siyo kayan kitchen ɗin Raihana.
Maman Ihsan ta amsa cike da farin ciki, muryarta ɗauke da annashuwa:
“Babu damuwa wallahi, Maman Aminu. Allah ya kaimu goben! Idan yaso idan mun dawo daga kasuwar, sai a ƙarasa sauran gyaran jikin da za a ƙarasa mata na ƙarshe.”
Umma ta yi murmushi a hankali, tana jin wani irin farin ciki a ranta saboda yadda Maman Ihsan ke ɗaukar al’amuransu ita da ƴaƴanta da muhimmanci.
A ranar washegari da safe, shirye-shirye suka yi nisa. Mama Indo, Maman Ihsan, da kuma Maryam suka amshi kuɗin siyayyar daga hannun Umma.
Maman Ihsan ta so a tafi kasuwar da Raihana gaba ɗaya domin ta zaɓi abubuwan da ke yi mata preference, amma Raihana ta lafke gaba ɗaya a katifa. Ta kwanta a gefe, ta ɗan ja bargon jikinta, fuskarta babu walwala ko kaɗan. Ta nuna jikinta ba ya yi mata daɗi.
“Ɗan Allah ku je… ba na jin daɗin jikina.”
Muryarta ta fito a hankali, kamar wadda ko magana kanta take mata wahala.
Maman Ihsan ta kalle ta da damuwa, ta ɗan matsa kusa da ita.
“Ki huta kawai, Raihana. Ba sai kin wahalar da kanki ba.”
Maryam ma ta ɗan kalli Raihana, ita dai ta san wallahi ƙalau take, amma ganin halin da take ciki da rashin walwalarta ya sa ba su tilasta mata ba, suka ƙyale ta ta huta.
Daga ƙarshe, suka fita daga gidan, Maryam na biye da su fuskarta fal da excitement kamar ita ce amaryar.
A haka suka fice daga gidan, suka bar Raihana a kwance ita kaɗai, cikin wani irin yanayi wanda zuwa yanzu ya riga ya fahimci abin da ke damunta…
Not edited