INTO HER NEW HOME
ZAYD ARMAAN
CHAPTER SIXTY SEVEN :67
INTO HER NEW HOME
JIDDAAH BARKUM
————
Raihana ta yi saurin ɗauke kanta, ta shagwabe fuska tare da ɗan jan tsaki ƙasa-ƙasa, duk da dai ta yi ƙoƙarin sautin ya fito ƙarami domin Maman Ihsan kada ta ji. Maman Ihsan ta ɗan taɓe baki, sannan ta girgiza kanta a hankali. Ta ajiye turaren da ke hannunta a kan madubi, kafin ta juyo da kyau ta fuskanci Raihana. Fuskarta a haɗe take, tana bin ta da wani irin kallo mai cike da faɗa da gargadi. “Ke kuma wai wacce irin yarinya ce? Shi ne za ki dinga sakin wa mijinki magana haka kina kashe masa waya?” ta faɗa da muryar da ke nuna tsananin ɓacin rai. “Kin manta cewa wata duniya za ki shiga yau? Kina da kishiya a gidan nan, amma kin kasa nutsuwa ki gane irin shirmen da kike yi!” Raihana ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta, amma babu abin da ta ce. Maman Ihsan ta ɗora hannayenta a hips ɗinta, ta ɗan matsa gaba. “Wallahi idan kin je gidan nan da wannan taurin kan naki da rashin yaƙini, za ki zama ‘yar kallo! Auren zamani ba irin na kauye bane. Dole ne ki koyi kissa, ki iya magana mai daɗi, ki zama mai tarairayar miji.” Ta ɗan daga gira. “Kar ki yarda ki nuna masa gadara ko tuntuɓe a duk abin da ya shafi danginsa musamman mahaifiyarsa. Dole ne ki girmama ta, ki so ‘yan uwansa ko da ba su so ki ba, ta yadda za ki mallaki zuciyar mijinki.” Ta ja wani dogon numfashi, tana kallon yadda Raihana ke ta lafe a wajen. “Idan har kika ce za ki je da halin nan naki na faɗa da ko-in-kula, wallahi za ki yi kuka da idanunki, kuma ba wanda zai tausaya miki. Ki fara canza wannan halin naki tun yanzu kafin lokaci ya ƙure miki!”
Maman Ihsan ta sauke numfashi mai nauyi, ta dawo ta zauna kusa da ita a gefen kujrar. A wannan karon, harshenta ya yi sanyi, ta taɓo kan Raihana a hankali cikin wani irin yanayi na tausayi da nasiha. “Ki saurare ni da kyau, Raihana. Aure ba wuri bane na nuna isa ko girman kai. Miji ba ya son mace mai taurin kai, musamman ma wanda yake da matsayi irin na Zayd.” Ta ɗan yi murmushi. “Namiji kamar ƙwai yake a hannun mace; idan kin san yadda za ki juya shi da laushi da magana mai daɗi, zai ba ki komai nashi Wlh sai yanda kikayi dashi. Amma ki je da rigima, za ki ga yadda zai juya miki baya ba tare da ya kalle ki ba.” Ta ci gaba da shafa man da ke hannunta a jikin fatar Raihana, tana cigaba da kintsata cikin nutsuwa. “Ki zama mai lallami. Idan ya yi fushi, ke ki kasance mai saukar da kai. Kar ki zama wacce duk abin da ya faɗa sai kin bi shi gida-gida da musu kina mayar masa da Martani.” Ta ɗan dakata, sannan ta kalli Raihana ta cikin mirror. “Wajen zama da kishiya kuma, sirrin zama yana cikin haƙuri da basira. Kar ki taɓa bari ta gano raunin ki ko inda kika fi zafi. Ki nuna mata girmamawa da mutuntawa, amma ki riƙe naki gurbin da iya taku.” “Shi mutum, idan ya ga kina girmama mutanen gidansa da mahaifiyarsa, shi kansa zai ƙara ɗaukaka ki a idanunsa.”
Raihana ta ɗan ɗago idanunta. Sun cika da ƙwalla kaɗan, ta kalli Maman Ihsan ta cikin mirror. Maganganun sun shiga ranta. Duk da tana da taurin kai, tasan maganganun gaskiya ne tsantsa. Maman Ihsan ta ɗan yi murmushi tana share mata wani ɗigon hawaye da ya fito. “Ki daina ɗaukar komai da zafi, kinji?” Raihana ta yi shiru, ta ɗan lumshe idanunta. “Ba na cewa ki zama wacce za ta rasa kanta saboda miji. A’a. Ki san darajarki, ki san iyakarki. Amma akwai bambanci tsakanin mace mai sanin darajarta da mace mai taurin kai.” Ta ɗan ɗaga haɓar Raihana sama a hankali, ta sa ta kalle ta. “Ki shiga gidan nan da hankali, not with anger. Kar ki fara rayuwarki da mijinki da faɗa. Ba kowa ne yake fahimtar zuciyar mutum ba, kuma ba kowa ne zai zauna ya binciki dalilin fushinki ba.” Raihana ta haɗiye yawu. Maman Ihsan ta cigaba da shafa gefen fuskarta a hankali. “Ki koyi kallon mutum ki gane lokacin da ya kamata ki yi magana da lokacin da ya kamata ki yi shiru. Silence ba rauni bane, Raihana. Wani lokaci shiru shi ne mafi girman hikima.” Raihana ta sauke idanunta. “Amma Maman…” Ta fara magana cikin rauni, sai Maman Ihsan ta ɗaga hannu a hankali ta dakatar da ita. “Ki saurare ni tukuna.” Ta ɗan yi murmushi. “Zayd ba ƙaramin mutum bane. Kin san haka. Kuma da gani zaiyi tsauri, I can see how difficult he can be to read. So don’t make things harder for yourself.” Raihana ta yi nodding a hankali. “Idan ya yi miki magana da zafi, kar ki rama da zafi. Idan ya yi shiru, kar ki fara neman faɗa saboda kin ji shiru ya dame ki. Ki bar shi. Idan yana son magana, zai yi.” Ta ɗan tsaya, kafin ta sauke numfashi. “Kuma game da kishiyarki…” Nan take Raihana ta ɗago idanunta. Maman Ihsan ta lura da hakan, sai ta yi ɗan murmushi. “Eh. Kishiyarki.” Raihana ta lumshe idanunta, ta ɗan juya fuskarta gefe. “Kar ki bari kasancewarta ta sa ki manta da ke wace ce. Kada ki yi ƙoƙarin yin gasa da ita. Kada ki yi ƙoƙarin nuna cewa kin fi ta. Just be yourself, amma ki zama yourself ɗin da ta fi sanin lokacin da za ta yi magana da lokacin da za ta yi shiru.” Mutane da yawa zaki gansu kamar masu hankali amma da zarar sun buɗe baki sunyi magana zaki ga ashe ba hankali a tare da su, ki daure shirunki yafi maganarki yawa. Ta ɗan dafa kafaɗar Raihana. “Kin fahimta?” Raihana ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai ta gyada kai a hankali. Maman Ihsan ta yi murmushi. “Good.”
“Abin da nake so kawai shi ne, ki je gidan nan da zuciya ɗaya. Kar ki shiga da tsoro. Kar ki shiga da tunanin cewa dole ne ki yaƙi kowa saboda akwai wata mace.” Ta ɗan kalleta cikin ido. “Ki shiga da mutunci. Ki shiga da haƙuri. Ki shiga da hankali.” Raihana ta ɗan lumshe idanunta, ƙwalla ta sake taruwa a idanunta. Maman Ihsan ta share mata kafin hawaye su sauka. “Komai zai yi kyau, In Shaa Allah.” Raihana ta yi murmushi kaɗan, duk da zuciyarta har yanzu cike take da tsoro. “Yanzu bari Saleema tayi miki kunshin.” “Toh,” Raihana ta amsa a hankali. Haka suka gama abinda za su yi a dare, dan Raihana sai kwana tayi a gidan. Ta kwanta, zuciyarta cike da maganganun Maman Ihsan. Ta yi ta juyawa cikin gadon na ɗan lokaci, tana kallon duhun ɗakin, har bacci ya fara satar idanunta. Ba ta ma san lokacin da bacci barawo ya yi gaba da ita ba.
Washegari, da safe. Raihana tana zaune a ɗakin Maman Ihsan, fuskarta ɗauke da wani irin sanyi, amma a ƙarƙashin wannan sanyin akwai fargaba mai girma. Gaban madubi ta ke zaune, yayin da Maman Ihsan da Khausar suke ta faman gyara mata kaya da kuma fesheta da turaruka masu daɗin ƙamshi. Khausar ta kalleta ta cikin mirror tana murmushi. “Amaryar Zayd Armaan!” Ta ɗan ɗaga gira cikin wasa. “Wallahi kin yi kyau sosai. Amma ki rage wannan fargabar taki, ba wani abin tsoro bane a gidan miji.” Raihana ta yi wani irin murmushi mara sauti. Ta kalli kanta a mirror na ƴan seconds, kafin ta ɗan sauke idanunta. A ranta kuwa, tunaninta yayi nisa bata gane komai ba ganin abinda take gani da wasa. Gashi ya zama gaske. Ba mafarki bane.
Daga nan suka ƙarasa gidan Baffa, ba laifi. Mutane na kusa da makota duk sun zo, duk da ba wani babban taro aka yi ba, amma Alhamdulillah an cika gidan. Mama Sabuwa kuwa da Bintu, dama ficewa suka yi ba su wuni a gidan ba. Amma yaran Mama Sabuwa kaf sun zo, kuma da su aka yi dukkan abinda aka yi. Da yamma, wajen ƙarfe biyar, sai ga motocin ɗaukar amarya sun iso bisa jagorancin Imraan, tare da wasu daga cikin kannen Ummi sai kuma Hajiya Hauwa, waɗanda su ne masu karɓar amarya. A lokacin Baffa yana zaune da abokinsa Malam Sammani a ƙofar gida. Da Imraan ya ƙaraso, sai ya tsugunna ya gaishe su cikin mutunci, sannan ya sanar da Baffa cewa sun zo ɗaukar amarya ne. Baffa ya ɗaga kai ya kalli motocin da suke jere a wajen gidan. Gasu nan, rerass tamkar an zo ɗaukar wani presidential candidate sun fi guda talatin! Ya ɗan kalli motar farko, sannan ta biyu, sai ya sake kallon jerin motocin da suka cika layin gaba ɗaya. Sai ya dawo da kallonsa kan Imraan, murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Imraan, wannan duk motocin ɗaukar Raihana ne?” Imraan ma ya yi murmushi, ya ɗan sunkuyar da kansa cikin girmamawa. “Eh Baffa. An zo da su ne saboda masu rakiyar amarya kowa ya samu waje.”
Baffa ya jinjina kai a hankali, har murmushin da ke fuskarsa ya ƙara bayyana. “To, ma sha Allah. Amma ina ganin za ku koma ne, saboda da kai na nake so na kawo ta. Sauran masu son ganin ɗakinta za su iya zuwa daga baya.” Ya ɗan dakata, kafin ya ƙara da cewa: “Yanzu kam, da mun idar da sallar Magariba, In Shaa Allah zan kawo ta. Ka maida su gida. Ba wani abu, an gode sosai da ƙoƙari.” Imraan ya gyada kai cike da gamsuwa. A ransa kuwa, yana jin wani irin girman Baffa da mutuncinsa sun sake ƙara shiga ransa. Cikin girmamawa ya amsa: “To Baffa, ba komai. Yadda kace, In Shaa Allah. Mun gode da karramawa.” Baffa ya ɗan ɗaga masa hannu cikin fara’a. “Allah ya kaiku lafiya.” “Ameen,” Imraan ya amsa. Daga nan ya miƙe ya nufi wajen motar da matan suke. Ya sanar musu da abinda Baffa ya ce, sannan ya juya ya koma motarsa. Dama shi ne zai ɗauki Raihana da kansa cikin motarshi. Motocin suka fara barin layin a hankali, ɗaya bayan ɗaya, cike da burgewa. Baffa ya na zaune yana kallon su har sai da jerin motocin ya fara ɓacewa daga gabansa. Ya sauke numfashi a hankali, sannan ya juya wajen Malam Sammani. A wannan karon, babu wani abu da ya fi bayyana a fuskarsa sama da natsuwa da kuma tunanin cewa In Shaa Allah yarinyar shi ta samu gidan mutunci.
Kafin Baffa ya tafi sallar Magariba, ya leka cikin gida, kai tsaye ɗakin Umma ya nufa. Akwai mata a ciki, ba dai yawa. Ya ɗaga labulen, Umma ta ɗago tana kallonshi. “Ku shirya Raihana. Idan na dawo daga masallaci zan kai ta. Masu ɗaukarta daga can sun zo, amma na ce su tafi. Zan kawo ta da kaina.” Daga nan ya saki labulen ya juya ya koma. Umma kuwa, da jin haka, her heart sank. Jikinta ya yi sanyi, ta kalli Maman Ihsan wadda ita ma ta fahimci nauyin maganar. Maman Ihsan ta miƙe ba tare da bata lokaci ba, ta nufi ɗakin Raihana. Tun da aka yi La’asar, zazzabi ya kama Raihana sosai—ba irin wanda za a yi wasa da shi ba. Tana kwance a kan gadonta, completely covered in a heavy blanket. Maryam, Khausar da wasu daga cikin ƙawayenta suna baje a ƙasa, ana ta shan hira, wasu kuma suna tsokanarta. Khausar ta fashe da dariya. “Duk fa wannan abun da take yi ko? Wallahi idan aka kaita can, luff za ta yi a ɗakinta! Maybe idan muka zo ma tace mu yi mu tafi mu bata waje. Allah na tuba! Dubu nawa akayi irin wannan? Kai Rayy, idan kin je kin jike a daula, karki manta da mu fa!” Sauran suka fashe da dariya. Raihana kam sam hankalinta baya tare da su. Tana kwance ne kawai, idanunta a rufe, numfashinta na fita a hankali.
Sallamar Maman Ihsan ce ta katse hirar. Duk suka juyo lokaci guda suna kallon ƙofar da ta shigo. Kai tsaye wajen Raihana ta wuce. Ta janye blanket ɗin da ta rufe ta da shi, sannan ta ɗora tafin hannunta a goshinta. Nan take ta janye hannunta. “Subhanallah! Zazzabi kuma?!” Ta kalli Raihana da sauri, kafin ta ɗan sunkuya kusa da ita. “Kai, a’a! Jikin yayi zafi sosai. Da zan ce ki yi wanka ne, amma a yammannan ga zazzabi. Idan kika yi wankan, zaki sake kwanciya ne.” Ta taimaka mata ta zauna, tana riƙe da kafaɗarta. A lokacin ne kawayen Raihana suka yi shiru. Wasu suka fara aika mata da “Sannu,” domin da farko sun ɗauka kawai iskancin Rayy ne. Maman Ihsan ta kalli Maryam. “Ɗauko min ɗan bawo da ruwa, ki haɗo da ɗan towel ko ɗankwali.” “To,” Maryam ta amsa, ta fice. Ba daɗewa ta dawo da kayan, ta miƙa wa Maman Ihsan. Maman Ihsan ta karɓi ruwan da towel ɗin, ta fara goge wa Raihana jiki a hankali, tana ta yi mata nasiha cewa ta daina jefa kanta cikin damuwa. Amma ina! Tunanin yadda za ta fuskanci sabuwar rayuwar da ke jiranta ya riga ya gama taɓa lafiyar jikinta. The fever was hitting her hard, ga shi kuma lokaci ya ja sosai.
Maman Ihsan ta ɗan kama hannunta. “Raihana, look at me. Wannan ba lokacin zazzabi bane. Yi haƙuri, ki daure kin ji ko?” Da ƙyar Raihana ta buɗe idanunta waɗanda suka yi wani irin ja. Her strength was completely drained. Ta yi ƙoƙarin gyara zamanta da kyau saboda taimakon Maman Ihsan da Maryam, amma still, she looked so fragile. Jikinta na rawa a ƙarƙashin heavy fabric ɗin da ta rufa da shi. Maman Ihsan ta goge mata jiki da ruwan ɗumi a hankali, tana ƙoƙarin rage mata zafin jikinta, sannan ta taimaka mata ta cire kayan jikinta. Ta ɗauko wata atamfa mai launin sky blue da gold color, wadda aka ɗinka ta zama doguwar riga, ta haɗa da wata kyakkyawar lafayya mai laushi sosai, ta ajiye su a gefen gadon. A daidai lokacin ne Maman Khausar ta shigo ɗakin, ɗauke da kwalaben turarukan da Maman Ihsan ta bata ajiya. Dama tun farko ta tanade su ne popularen su zama na musamman a irin wannan lokaci. Maman Ihsan ta karɓa, ta fara shafa wa Raihana turarukan a hankali, tana tabbatar da ƙamshin ya ratsa jikinta da gashin kanta, making sure every inch of her smelled divine. Bayan nan, suka taimaka mata ta saka kayan. Lokacin da aka naɗa mata lafayyar a jikinta, she looked stunningly gorgeous, duk da cewa zazzabin ya riga ya gama raunana ta. Hawaye ya fara taruwa a idanunta. Maman Ihsan ta kamo hannunta a hankali, tana mata wani irin kallo mai cike da ƙarfin gwiwa da encouragement. “Ki daure, Raihana. Kin ji?” Raihana ta yi nodding a hankali, tana ƙoƙarin danne hawayen. Maman Ihsan ta sake matse hannunta. “Come on, mu je. Kar Baffa ya dawo ya same ki ba ki shirya ba.” Raihana ta ɗan goge gefen idanunta, sannan ta miƙe a hankali. Maman Ihsan ta kama hannunta sosai, tana supporting her weight. Haka suka fara tafiya a hankali zuwa ɗakin Umma, yayin da sauran suka bi su da kallo cikin shiru. A wannan karon, babu wacce ta sake tsokana. Saboda duk sun fahimci cewa wannan ba wasa bane kuma. Raihana was finally leaving home.
Da suka ƙarasa ɗakin Umma, Raihana ta tsaya bakin ƙofa na ɗan lokaci. Umma kuwa tana zaune, idanunta suka sauka a kanta. Na ɗan lokaci babu wacce ta ce komai. Umma ta kalli ɗiyarta daga sama har ƙasa, tana kallon yadda aka shirya ta cikin kayan amarya. Her little girl… wadda tun ranar da ta haife ta, ba ta taɓa zuwa wani wuri ta yi kwana biyu ba. Amma yau… aure rai raba su. Zuciyar Umma tayi mata wani iri. Ta ɗan juya fuskarta gefe, tana ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata maƙogwaro. Amma ƙwalla ta riga ta cika idanunta. Maman Ihsan ta kama hannun Raihana a hankali, suka ƙarasa gaban Umma. Raihana ta ƙarasa wajenta. Da ta zauna kusa da ita, ta rungume Umma da ƙarfi. “Ummaa…” Muryarta ta karye. Nan take ta fashe da kuka. Umma ma ta rungume ta, ta ɗora hannunta a bayanta tana shafa ta a hankali. “Shhh… Raihana.” Muryar Umma ta fito a raunane, cike da emotion da take ƙoƙarin ɓoyewa. Ta sumbaci kanta, sannan ta share mata hawaye. “Allah ya ba ku zaman lafiya.” Ta ɗan ja numfashi, kafin ta ƙara da ƙaramar murya: “Allah ya baku hakurin zama da juna… ya sa zaman ya zama alheri.” Raihana ta ƙara matse ta, kukan nata ya ƙara tsananta. Umma ta lumshe idanunta. Hawayen da ta yi ta ƙoƙarin riƙewa suka zubo mata a hankali. Ba ta son ta nuna mata irin ciwon da ke zuciyarta. Ta sake shafa bayanta. “Ki yi haƙuri, Raihana.” Ta sumbaci goshinta. “Ki kasance mai haƙuri… ki kasance mai kauda kai. Fi Amanillah.” Raihana ta ɗago fuskarta daga kafaɗarta, fuskarta jike da hawaye. “Umma…” Umma ta share mata hawayen da ke gefen kumatunta. “Go, my baby.” Ta yi murmushi. “Tashi kuje.” Raihana ta sake rungume ta. A wannan karon, Umma ba ta ce komai ba. Ta dai riƙe ɗiyarta sosai. Domin wasu lokuta, babu wata magana da za ta iya faɗin abin da zuciyar uwa ke ji a lokacin da aure ya zo ya ɗauki ɗiyarta daga hannunta.
A daidai lokacin da Raihana ke manne da Umma, sai suka ji muryar Baffa daga tsakar gida. “Wai me akeyi yanzu baku fito ba.” Raihana ta ɗago kanta da sauri. Jin maganar Baffa kaɗai ya isa ya sake karya mata zuciya. Ta sake juyawa ta rungume Umma, wannan karon da ƙarfi fiye da farko. “Ummaa…” Ta fashe da kuka sosai. Muryarta ta shake, ta kasa ƙarasa maganar. Umma ta riƙe ta sosai, ita ma hawaye na bin fuskarta, tana ta shafa bayanta. “Raihana… go tashi ku je.” Amma Raihana ta ƙara manne mata kamar ba za ta sake ta ba. Maman Ihsan da Maman Khausar suka kalli juna. A hankali suka ƙaraso. “Raihana, my dear…” Maman Ihsan ta kama hannunta. Amma Raihana ta girgiza kai, tana ƙara kuka. “Ummaa taa…” Maman Ihsan ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, zuciyarta ta karye. Amma lokaci ya riga ya kure. Tare da Maman Khausar, suka fara ƙoƙarin bambare Raihana daga jikin Umma. “Ki yi haƙuri, Raihana. Come on…” Da ƙyar suka raba ta da Umma. Raihana ta miƙa wa Umma hannunta tana kuka kamar ranta zai fita. “Umma!” Umma ta ɗaga hannunta tana share hawaye fuskarta. Maman Ihsan ta kama Raihana sosai, yayin da Maman Khausar ta ɗan riƙe kafaɗarta. A haka suka fitar da ita zuwa tsakar gida. Baffa yana tsaye yana jiransu. Da idonsa ya sauka kan Raihana, ya yi shiru na ɗan lokaci. Ya ga yadda take kuka, ya sauke numfashi a hankali, amma bai ce komai ba. Maman Ihsan ta kai Raihana ɗakin Mama Indo. Mama Indo tana ciki, sai Maman Ihsan ta kalleta. “Toh, ga Raihana. Zaman da aka yi, idan ta saba miki ko ta yi miki wani abu, ki yi haƙuri.” Mama Indo ta kalli Raihana, wadda take kuka sosai. Sai ta girgiza kai a hankali. “Ni me Raihana za ta yi min?” Ta ɗan yi murmushi. “Wallahi bata min komai ba. Allah ya ba ku zaman lafiya da zuriyya masu albarka.” Raihana ta sauke idanunta, hawaye na sake zuba kamar an buɗe famfo. “Ameen,” Maman Ihsan ta amsa a hankali. Daga nan suka fito. Baffa yana tsaye a tsakar gida. Ya kalli Inna da ta fito daga daki. Inna ce, Maman Khausar, Maman Ihsan sai Maryam. “Ku kaɗai kun isa ku rakata.” Ya ƙarasa yana kallon sauran mutanen da suka taru. Inna ta gyada kai. A hankali suka fara tafiya. Maman Ihsan tana riƙe da Raihana a gefe ɗaya, Maman Khausar tana kusa da su, yayin da Maryam da Inna suke biye. Raihana kuwa har yanzu tana kuka. Kukan da ke fitowa daga zuciyar da har yanzu ba ta gama yarda cewa wannan gaskiya ce ba. Suka ƙarasa ƙofar gida. Mota na gefe tana jiransu. Maman Ihsan ta buɗe ƙofar baya, sannan ta taimaka wa Raihana ta shiga, ita ma ta shiga tare da Maman Khausar. Inna da Maryam suka shiga gidan tsakiya. Baffa ya shiga gefen driver, kusa da Malam Sammani, abokinsa. A hankali motar ta fara motsawa. And just like that… Raihana was leaving the only home she had ever known. The home she had called hers all her life. And now, she was heading to a new house a place she would have to learn to call home from this day forward.
The longest chapter 😟