ZAYD ARMAAN

THE SILENT ARRIVAL

by @jiddaahbarkum



*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER SEVENTY FOUR:74*

*THE SILENT ARRIVAL*

*JIDDAAH BARKUM*

————

Ana dawowa Jumu’ah, Inna tayi sallama da kowa aka rabu lafiya. Yaya Hamza ya dauketa ya kai ta Tasha, inda ta hau motar Makarfi.

Baffa ya riga ya sanar da Mama Indo cewa idan ta fita a girki ta bawa Mama Sabuwa. Mama Indo ta saki baki hangangan, idanunta suka kafe a kofar da Baffa ya fita. Ta ɗan yi shiru tana kallon wajen, kamar har yanzu tana processing abin da ya faɗa mata, sai ta ɗaga hannunta sama tana girgiza kai a hankali, snn tayi kwafa, “huuuu!” Ta fesar da numfashi cikin mamaki, sannan ta dafe kirjinta, “Namiji munafiki ne Wlh!” Ta sake kallon kofar, ta rufe bakin, sannan ta girgiza kai cike da haushin abin.

Mama Sabuwa kuwa kawai ta fito tsakar gida, ba tare da ta ce komai ba, ta hau aikace-aikace na ba gaira babu dalili. Ta ɗauki abu ɗaya, ta ajiye, ta koma wani aikin, tana ta wake-wake a hankali kamar babu abin da ya dameta da al’amarin duniya. Mama Indo dake wanke wanke ta juya ta kalleta, tana aika mata da wata uwar harara. Mama Sabuwa kuwa sai ƙara wake-waken ta yi, hannuwanta na ci gaba da aiki, fuskarta kuma babu ko alamar damuwa.

Mama Indo ta ja wani uban tsaki, ta ɗaga kai sama tana sauke numfashi da ƙarfi, “Allah ka rabamu da cusa kai, kafafar banza da wofi! Yo da ba a san asalin balbelaa ba sai tace daga Misira tazo.” Mama Sabuwa da ke aikin ta dago kai a hankali, ta kalleta, sannan ta ajiye abin da ke hannunta, ta ɗan runtse idanu kafin ta amsa cikin wata izzah, “Indo, idan kinada magana ki bude baki kiyi, ba wai ki dinga sakin habaicin ba. Ai kowa ya san habaicin kura na me kare ne.”

Mama Indo ta yi tsit na ɗan lokaci, sai ta mike da sauri, ta kankance idanu tana kallon Mama Sabuwa kai tsaye, “Dake nake, naji duka! Dan Allah! Yo Allah na tuba! Uban wa zaki dagawa kai ki hurawa hanci? Bayan kaff ba wanda baisan cusawa Malam ke akayi ba, tun daga fari kawo yanzu sanin kanki ne! Ba dan Inna ba, wlh saidai ki kare rayuwarki a bazawara!” Ta ɗan qara matsowa gaba, tana nuna Mama Sabuwa da yatsa, “Toh dake shi mai biyayya ne, yaji maganarta ya dawo dake, abinda mun riga mun san ba wai wani uban capacity ke gareki a wajensa ba, bare ki ce ya ga ba hazaaa ne ya dawo dake!”

Mama Sabuwa ta zabura kamar an kunna mata wuta, ta saki abin da ke hannunta, ta juya gaba ɗaya tana nufar Mama Indo, bakinta na zuba mata ashariya. Mama Indo kuwa nan take ta fincike dankwalin kanta ta ci uwar damara dashi snn ta cigaba, “Billahillazi kika karaso nan sai na sauke miki kai da kujerar nan! Ke kinsan ba tsoronki nake ba, kawai daga miki kafa nake. Amma idan kin haifu cikin uwa da uba, dan Allah karaso!”

Mama Sabuwa ta ja birki a inda take, kirjinta na hawa da sauka, tana huci, idanuwanta a kan Mama Indo, “Wlh sa’arki daya! Ni ba karya bace, da wallahi sai kin gane Allah da girma yake! Ni nan Sabuwa na zame muku kadangaren bakin tulu, a tabani a kar tulu a barni. Kuma na bata ruwa! Ko shi mijin naki haka zai ganni ya kyale bare wata ke!”

A lokacin Umma ta ɗan leko daga ɗakin, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsu, fuskarta a nutse, sai ta girgiza kai a hankali, kamar wadda ta riga ta san ba za ta iya dakatar da su da ƙarfi ba, “Dan Allah kuyi hakuri, makota duk suna ji yanzu, sai ku ga labari ya je wajen Malam idan ya dawo.” Mama Sabuwa ta katseta nan take, ta jefa mata wata uwar harara kamar idanunta zasu zubo, “Ke dallah rufewa mutane baki, munafuka kawai! Ba dake nake ba da uwar dakinki nake! Ke baki kai na kalli inda kike ba ma bare nayi dake!” Mama Indo ta yo wata uwar shewa, “Hehehehe! Toh ni uwar dakinta nace! Ki karaso amma kin kasa!”

Umma ta kalli Mama Indo, ta sauke numfashi a hankali sannan ta ɗan girgiza kai, “Dan Allah kiyi shiru.” Mama Indo ta yi kwafa tana zubawa Mama Sabuwa harara snn ta juya kawai ta yiwa Mama Sabuwa banza, daga nan kuwa ta cigaba da sabgoginta, tana jan numfashi lokaci-lokaci saboda har yanzu zuciyarta cike take da haushi. Umma ma ta koma ɗaki ta kyale su. Mama Sabuwa kuwa ta buɗe sabon babin zage-zage da maganganu, ba kai ba kafafuwa.

Wasa-wasa fa har after Magrib babu Zayd, babu labarinsa. Shi dama ba wai yana da friends bane, balle ace aje a neme shi a inda suke. Ummie duk ta damu, tana zaune tana riƙe da wayarta, lokaci-lokaci ta kalli screen ɗin, ta sake sauke numfashi cikin damuwa.

Inno ta kalleta, ta ɗan girgiza kai, “Ki kwantar da hankalinki, Hajja Fatee, duk inda Zaydu yake, dama yayi aniyar maida mu ’yan iska ne, shiyasa yaje ya boye. Duk dai boye-boyenshi, an riga an daura aure, me ya rage kuma? Zai ma fito daga duk inda yake yanzu.” Ta ɗan yi shiru, sannan ta cigaba, “Yanzu kawai kira Sameer, ya haɗa mota, a je a ɗauko amarya, ya kawo ta nan, na haɗasu da Raihana, na ɗan yi musu magana, daga nan sai a wuce da ita gidanta.” Ummie ta kalleta, tana sauraron ta cikin nutsuwa, “Kuma itama uwargidan, yana da kyau ki gaggauta abinda zakiyi, dan ta samu ta tare a ɗakinta, har yanzu kwanakin uwargidan ne, ko?”

Ummie ta ɗan jinjina kai kafin tace, “Ehh, yau kwananta ɗaya ai.” Inno ta gyara zamanta, ta ɗaga hannunta tana ƙirga da yatsunta, “Kuma kwana bakwai zaiyi mata kenan kafin ya koma ɗakin Seeyama.” Ta kalli Ummie da wani irin kallo mai ma’ana, “Toh a kwanaki shidan nan, duk abinda zakiyi kiyi.” Ummie ta amsa da ƙananan murmushi, “In Shaa Allah.” “Yauwa.” Inno ta ɗan gyada kai, kamar an gama shirya komai, “Toh yanzu ki kira Sameer, ya wuce a je a ɗauko Seeyama.”

Ummie ta ɗauki wayarta nan take, ta danna sunan Sameer, ba a ɗau lokaci ba ta same shi, ta sanar da shi abin da za a yi. Haka kuwa akayi, Sameer ya tashi nan take, ya haɗa motoci, aka tafi unguwar su Haj Hauwa ɗaukar amarya Seeyama. Ko da ya je, sai da Mommy Hauwa tayi zage-zage, wai an raina mata hankali, “Idan banda haka, sai a rasa wa za a aika a dauko yarta sai wadanann ma’aikatan?” Ta na tsaye tana ta magana, tana nuna ɓacin ranta, yayin da guards ɗin Zayd suka tsaya a gefe, tare da Sameer personal assistant ɗinsa, kowa ya yi shiru yana jiran ta gama.

Amma ta kasa hakuri, nan take ta kira Inno. Da Inno ta ɗauka, sai Mommy Hauwa ta fara mata korafi, Inno kuwa ta mata “Tassss!” “Idan ba zaki basu ita ba, toh ta sha zamanta a gidan ubanta!” Daga nan ta kashe wayar. “Hmm!” Mommy Hauwa tayi kwafa, ta zurawa wayar da ke hannunta ido.

Ita kuwa Seeyama, ko a jikinta, burinta kawai ta shiga gidan Zayd, a ganinta, kamar auren ma bai dauru ba tukuna, amma idan ta ganta a ɗakinta, hankalinta zai fi kwanciya. Dan haka, ba tare da wani dogon bata lokaci ba, ta fito da ƙawarta Safina kawai, domin ita kaɗai ta rage a cikin friends ɗinta. Sai Haj Balaraba da wasu mutum biyu a cikin friends ɗin Haj Hauwa, sai kuma Bintu wacce ta dage sai ta ga kwakwafff.

Haj Balaraba tayi tayi da Haj Hauwa kan tayi zamanta, su zasu wakilce ta, amma tace samm, sai taje ta kai Seeyama ɗakin mijinta. Ko da motoci suka ɗauki saiti a kan kwalta, Seeyama wacce ke kallon hanya fesss kamar ba amarya ba, sai ta dubi Sameer da ke driving, daga ita sai Safina, sai kuma Sameer ɗin, “Wai gidan uwar wa zaka kaini? Naga ka ɗauki wata hanyar!” Sameer ya ɗan kalli mirror, idanunsa suka sauka kan Seeyama na ƴan seconds, kafin a nutse ya ce, “Zamu je can gidan ne, Hajiya Inno tace can za a kai ki.” Seeyama ta ɗan bude baki, tana jefa masa wani mugun kallo, sai ta hantare shi, “Dallah rufemin baki! Ita Inno ɗin uwata ce? Malam, ka mike ka kaini gidan mijina! Kar ka bata min rai na sa ya kwace wannan aikin da kake ji dashi, har kake kokarin yiwa mutane rainin hankali sabida shi!” Sameer bai sake cewa komai ba, ya yi shiru kawai, hannunsa a kan steering, fuskarsa babu wani expression na gardama, sai ya juya akalar motar zuwa gidan Zayd. Nan take sauran motocin ma suka bi bayansa dodarrrrrr… 


har after 10, babu amarya, babu ’yan ɗauko amarya. Inno da Ummie na zaune a parlour suna jiransu, amma shiru, kowa ya yi tsit, sai lokaci-lokaci Ummie ta kalli agogo sannan ta sake kallon ƙofar. Daga ƙarshe, sai suka ji karar shigowar motoci. Ummie ta ɗan motsa a kujerarta, ta miƙe tana sauraron karar, “Ina ganin gasu nan, bari na sauko da Raihana.” Daga haka ta wuce sama.

A lokacin, Raihana har tayi shirin bacci, tana kwance a kan gado, jikinta a lullube, idanunta a rufe. Suhaila kuma tana bathroom tana wanka. Ummie ta karaso kusa da ita, ta ɗan taba goshinta a hankali. Raihana ta buɗe idanunta a hankali, da ta ga Ummie, sai ta fara ƙoƙarin miƙewa. Ummie ta yi mata ɗan murmushi, “Daughter, saka hijab, mu je ƙasa, ko?” Ba tare da wata musu ba, Raihana ta miƙa hannu ta ɗauki hijab ɗin ta saka. Ummie ta kamo hannunta, suka fito tare.

Sai dai suna saukowa, Sameer ma ya shigo, kai tsaye ya karaso wajen Inno ya ɗan risina. Inno ta ɗaga kai, ganin Sameer kadai sai ta buɗe baki, “Ina Amaryar?” Sameer ya sake sunkuyar da kansa kaɗan, “Dama cewa tayi na kai ta gidanta kawai.” Inno ta saki baki, idanunta suka zaro. Ummie kuwa ko mamaki ɗaya babu a fuskarta, har ta zauna sannan ta zaunar da Raihana a gefenta.

Inno ta juyo ta dubi Ummie, sannan ta sake kallon Sameer da ke tsaye gabanta, “Kuma ka ce mata nace nan zaka kawota?” Sameer ya ɗan jinjina kai, “Ehh, na sanar da ita.” Inno ta ci gaba, “Amma tace maka ka kai ta gidanta?” “Ehh, haka tace.” “Hooooo!” Inno ta cije yatsa ɗaya, ta nuna masa hanyar fita, “Je ka abinka, kai kam ka gama naka, Allah maka albarka!” Sameer ya ɗan risina cikin ladabi, “Assalamu alaikum.” Daga nan ya juya ya fice gently, yana barin Inno da Ummie a parlour.

Inno ta juya ta kalli Ummie, fuskarta cike da ɓacin rai, ta ɗan dafe cinyarta, tana girgiza kai kamar har yanzu abin da ya faru yana bata mata rai, “Yanzu ni Hauwa ta mayar mutumiyar banza a garin nan? Zan sa doka! Yar ta ta karya amma ta bi son ran yarta!” Ta sake girgiza kai, idanunta cike da fushi, “Hauwa zata gane ni ce na haifeta, ba itace ta haife ni ba!” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana sauke numfashi da ƙarfi, sannan ta ƙara da ɗan daga murya, “Wannan karon dai sai ta gane cewa ba komai ake yi da sunan son rai ba, zan ɗauki mataki, kuma wallahi zan ɗauka.”

Ummie kuwa bata ce komai ba, kawai ta zauna shiru, idanunta akan Inno, tana kallonta cikin nutsuwa, fuskar ta babu ko alamar mamaki ko gardama, ta bar Inno ta gama fitar da haushinta. Bayan ɗan lokaci, Inno ta sauke numfashi, sai idanunta suka koma kan Raihana da ke zaune a gefen Ummie, shiru tana sauraron su. Fuskar Inno ta ɗan yi sanyi, “Raihana, tafi kiyi kwanciyarki yar nan.” Ta ɗan yi murmushi kaɗan, “Allah ya tashe mu lafiya.” Raihana ta jinjina kai a hankali, sannan ta miƙe.

Bintu bata dawo gida ba sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na dare, Baffa yana zaune a tsakar gida, kansa a sunkuye yana sauraron radio. Da jin ƙarar buɗewar ƙofa, ya ɗago kai. Bintu ta shigo a hankali, tana ɗauke da ledojin da ta siyo, da ganinsa, ta tsaya a tsaye ba ko risinawa, “Sannu da gida, Baffa,” ta faɗa a hankali, tana ƙoƙarin wucewa zuwa ɗakinsu.

Baffa ya ɗago kansa ya kalleta daga sama har ƙasa, fuskarsa ta sauya nan take, ya ajiye radio hannunsa gefe, idanunsa suka ƙanƙance, “Ke!” Tsawar da ya daka mata ta sa Bintu ta firgita, jikinta ya ɗanyi rawa ta zube a ƙasa cikin firgici, ledojin da ke hannunta suka watse a wajen.

Baffa ya miƙe a fusace, ya tsaya yana kallonta da wani irin tsayayyen kallo, fuskarshi ta nuna fushi, “Daga gidan uban wa kike kika shigomin gida a wannan lokacin nan?!” “Wlh Baffa—” “Shiru!” Ya ɗaga hannu sama da ɗan ƙaramin yatsa yana nuna ta, muryarsa cike da tsawa, “Ki saurare ni da kyau!” Bintu ta sunkuyar da kanta, amma duk da haka ta cigaba da magana, “Hajiyar da nake mata aiki ne ake biki a gidanta… shine ta gayyace ni, kuma na tambayi Mama kafin na tafi…”

Baffa ya harbeta da kafa ta dafe wajen, tana fashewa da kuka, “Ina cewa ki min shiru kina min wata maganar banza.” “Kin tambayi Mama?” Ya yi wani ɗan murmushi mara daɗi, kafin fuskarsa ta sake komawa cikin tsananin fushi, “Shi ke nan? Saboda Mama ta ce ki tafi, sai ki ga dama ki dawo gida ƙarfe goma sha ɗaya na dare?” Ya taka mataki ɗaya zuwa gabanta, Bintu ta ja baya kaɗan. Baffa ya goya hannayensa a bayansa, ya tsaya cak a gabanta yana tsare ta da kallo, “Wallahi billahi, Bintu…” Ya ɗan dakata, yana kallonta kai tsaye cikin idanunsa, “Idan kika sake taka ƙafarki ko da bakin ƙofar gidan nan ne ba tare da izinina ba, sai na maida ke ƙauye!”

Bintu ta ɗago kai a firgice, “Baffa…” “Ba na son na sake jin wannan ‘Baffa’ ɗin!” Ya ɗan sunkuyar da kansa zuwa gare ta, muryarsa ta sauka amma ta ƙara tsauri, “Kuma a can zan samu wanda zan aurar masa da ke, shashasha! Wacce bata son ciwon kanta ba ta san darajar gidan da take ciki ba!” Bintu ta share hawaye da bayan hannunta, jikinta har yanzu yana rawa. Baffa ya ɗaga hannu ya nuna hanyar ɗakinsu, “Kin tashi kin bani waje ko sai na taka kanki a wajen!”

Bintu bata sake cewa komai ba, ta tattara ledojinta cikin bala’in gaggawa, wasu ma ba ta kula da abin da ke cikinsu ya zube a wajen ba, ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinsu, zuciyarta tana bugawa kamar za ta fito daga ƙirjinta.

Bayan Bintu ta dawo hayayyacinta, ta samu Mama Sabuwa tana zaune, ba tare da ɓata lokaci ba ta fara bata labarin yadda sukayi da Baffa. Mama Sabuwa tana sauraron ta ne tana ɗan karkata kanta kaamr zancen n shiga ta nan yana fita ta can, har Bintu ta gama. Sai Mama Sabuwa ta ɗaga hannu kamar tana watsar da maganar, “Ke dallah! Share shi, shi ya isa ya hanaki fita ne? Rabu da shi, duk lokacin da zaki fita, ki shirya abunki, na san me zanyi.” Bintu ta kalleta, sai ta amsa a hankali, “Toh, Mama…” Amma kafin ta ƙara wata magana, sai Bintu ta juya mata da wani expression na da ya cika fuskarta ya kawar da fargabar maganganun Baffa, “Mamaa, kinga daular da muka kai Amaryar nan?”

Mama Sabuwa ta ɗan tsaya, sai ta fara bata labarin gidan, ɗaya bayan ɗaya, tana ƙara bayani kamar yadda ta gan shi. Mama Sabuwa kuwa tun kafin Bintu ta gama, sai fuskarta ta fara sauyawa, “Ke haba!” ta furta cikin mamaki, “Shi gidan?!” Ai… Mama zai yi gidan nan sau hamsin!” Everything is screaming luxury. Bintu ta ɗan yi dariya, “Iya ɗakin gateman dinsu shine gidan nan duka.” Mama Sabuwa ta zaro ido, “Ke?!” Bintu ta gyada kai tana dariya.

Mama Sabuwa ta ɗan yi shiru, kamar har yanzu tana ƙoƙarin processing ɗin abin da Bintu take faɗa, daga ƙarshe sai ta ɗauko wayarta, “Bari ki gani ai har video nayi.” Ta buɗe wayar, ta fara nunawa Mama Sabuwa videos din gidan. Mama Sabuwa ta matsa kusa, tana kallon screen ɗin da kyau sosai. Da ta ga video yayi nisa har an wuce compound an shiga cikin gidan, sai ta buɗe baki, “Ke… dawo min dashi farko.” Bintu ta sake dariya, ta dawo da shi farko. Mama Sabuwa ta ƙara kallon screen ɗin, sannan ta ɗago kai ta kalli Bintu, “Kikace wannan gidan kuka kai Amaryar?” “Ehh mana, Mama.” Bintu ta ɗan yi murmushi, “Kingani? Gida kamar ba a duniya ba ko?” Mama Sabuwa bata amsa nan take ba, ta sake kallon screen din, sai ta ɗora hannu a kirjinta, idanunta suka cika da mamaki, “Ke… wannan ai gidan muka je jeren Raihana!”