THE VOW OF REVENGE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER SEVENTY SEVEN:77*
*THE VOW OF REVENGE 🔥*
*JIDDAAH BARKUM*
————
Seeyama ta tsaya a wajen gate ɗin tana kallon motar Zayd har sai da ta ɓace daga ganinta. Fuskarta ta cika da mamaki da ɓacin rai, tana riƙe da ledojin naman da ya jibga mata kamar wata mayya, ashe wai nufinshi ita kadai zataci kenan. Sai ta juyo a hankali ta kalli mai gadin da wani shegen kallo kaamr shine Zayd din, shi kuwa yana tsaye ne kawai, yana kallonta da wani irin shiru, kamar shi ma bai san me zai ce ba.
Seeyama ta ɗan zaro idanu, “Open the gate!” Mai gadin ya ɗan motsa, amma kafin ya kai ga yin komai, sai ta sake ɗaga murya a hasale, “I said open the damn gate!” Mai gadin ya yi saurin nufar ƙofar, amma Seeyama ta bi bayansa tana ta masifa, “Look at you! Standing there like you don’t understand simple English! Open the gate!” Ya yi saurin buɗe mata ƙofar, yana matsawa gefe don ta wuce. Amma sai ta tsaya tana jan numfashi da ƙarfi, sannan ta juyo ta kalle shi daga sama har ƙasa, “You people are unbelievable! What exactly were you staring at?!” Mai gadin ya buɗe baki, amma bai samu damar cewa komai ba. Seeyama ta ɗaga hannu, “Don’t even answer me!”
Ta juya tana nufar cikin gidan, amma bayan ta yi ƴan steps sai ta sake waiwayowa, “And next time, whenever I gives you an instruction, you don’t stand there looking stupid! You open the gate and keep your mouth shut!” Mai gadin ya sunkuyar da kai, “Yes, ma.” Ta juya ta shige ciki da sauri tana wuce tana ci gaba da zage-zage, “You people better learn how to behave around me. I am not one of your maids or some random woman you can stare at!” Mutumin bai sake magana ba, kawai ya zuba mata idanu. Seeyama kuwa ta wuce cikin fushi, tana dan jan ledojin da handbag ɗinta, ta kusa isa entrance din kenan sai ta tsaya, ta buɗe handbag ɗinta cikin sauri, ta fara neman wayarta, ta ciro ta ta kunna screen ɗin, sai ta fara dialing.
Washegari, gidan ya tashi kamar wani abu bai faru ba; kowa ya cigaba da sabgar gabansa, as if last night’s drama never happened. Gidan ya koma normal, kowa na harkarsa kamar babu komai. Ummie ta dubi Suhaila, sannan tace ta shirya ita da Raihana su wuce wajen matar da ta riga tayi booking zatayi ma Raihana gyaran jiki. Raihana da ke ɗaki kam bata san me ake yi ba, sai da Suhaila ta shigo ta kalleta da murmushi tana zama a gefenta, “Anty Rayy, ki shirya zamu fita, Ummie ce ta aike mu.” Ta faɗa cikin cheerful tone, murmushi na ƙara bayyana a fuskarta.
Ba musu ta tashi, Suhaila ta ɗauko mata simple black abaya da veil ɗinta ta saka, ta shirya tsaff gwanin sha’awa, Suhaila ma ta shirya, ta kamo hannun Raihana suka fito. Lokacin da suka sauko falon, Ummie ce kaɗai a kan sofa tana zaune, calm and composed, kamar yadda ta saba. Suka karaso, Raihana ta durƙusa cikin girmamawa tana gaishe da ita, Ummie ta ɗago ta tana murmushi, “Nace miki ki daina wannan zubewar mana, haba! Zauna a nan.” Ta faɗa tana girgiza kai da ɗan murmushi, sannan ta zaunar da ita a gefenta, sai ta ɗauki wani ɗa box mai kyau ta mikawa Suhaila, “Ki faɗa mata da wannan nake so tayi mata amfani.”
Suhaila ta karɓa, tana kallon box ɗin na ɗan lokaci kafin ta ɗago idonta zuwa Ummie, “Zamu tafi, amma Ummie dan Allah ni zan yi driving da kaina mu tafi mu kaɗai. Ai dai yanzu ba ni ɗaya na fita ba, akwai Anty Rayy, in sha Allah zamu tafi lafiya mu dawo lafiya.” Ta faɗa cikin ɗan shagwaɓa, tana kallon Ummie da pleading eyes. Ummie ta kalli Suhaila sannan ta kalli Raihana, “Toh shikenan, make sure you drive safe. Suhaila, karki yi min ganganci da yarinya a mota!” Suhaila ta yi ƴar dariya tana turo baki da ɗan shagwaɓa, “Ni yanzu Ummie shikenan! Tunda Anty Rayy ta zo gidan nan an daina so na? Kin ji fa kince wai kar na miƙi ganganci da yarinya! Toh Ummie ni fa…” Ta tsaya da gangan, tana kallon Ummie da innocent face, kamar wadda aka doka.
Raihana dake zaune a gefen Ummie kanta a ƙasa ta ɗanyi murmushi amma ba tace komai ba, she tried to hide it, but the little smile escaped. Ummie ma murmushin tayi tana hararar Suhaila kafin tace, “Ni dai na faɗa miki.” Sai ta kalli Raihana, muryarta ta yi laushi, “Tashi ku je, daughter, sai kun dawo.” “Toh,” ta amsa a hankali, sannan ta miƙe. Suhaila tayi gaba, Raihana na biye da ita har compound, su biyu suna tafiya tare, Suhaila tana ɗan juyawa lokaci-lokaci tana kallon Raihana da ƙaramin murmushi, yayin da Raihana kuwa take biye da ita cikin nutsuwa, hannunta riƙe da ƙaramin handbag ɗin da Suhaila ta dauko. A simple morning, a peaceful outing, at least, for now.
Lokacin da suka fito, Zayd na tsaye a gefen parking lot ɗin shi da Sameer, yana nuna masa wasu document yana masa bayaninsu a hankali. Sameer ya riƙe folder ɗin da hannu biyu yana saurare sosai, lokaci-lokaci yana ɗaga ido zuwa document ɗin da Zayd ke nunawa, “Here,” Zayd ya nuna wani paragraph da finger ɗinsa, “This figure is not matching the previous report. I want you to cross-check it with the original file before it goes to finance.” Sameer ya duba takardar sosai, “Yes, boss. I noticed the difference too. I’ll have the accounts team verify it and send you the corrected version before close of business.” Zayd ya ɗan gyada kai, “Good. And the contract?” “The final draft is ready. I’ve already sent it to the legal team for their last review. Once they clear it, I’ll put it on your desk.” “Make sure they don’t rush it. I want every clause checked properly. No assumptions.” “Yes, boss.”
Suna cikin wannan hirar ne Suhaila da Raihana suka zo suka gifta ta gefensu. Suhaila tana sane ta ƙi kallonsa dan ta san kadan a aikinshi yace ba zata fita ba tare da driver ba. Ita kam ta san halinshi sosai; idan ya ce ba za a fita ba, ba za a fita ba, so she deliberately kept her eyes ahead, pretending he wasn’t even standing there. Raihana dama ta kalleshi ta masa me? Ita da kawai from nowhere ta ke jin wani bala’in haushinsa kuma idan yankata za’ayi batasan meye dalili ba, duk da zuciyarta na wani mahaukacin bugu, still ta wuce taqi ta kalli direction ɗinshi, kawai da tafiya kanta a ƙasa, ta ƙara matsa takunta tana bin Suhaila a baya har wajen da motar da za su hau take.
Zayd ya dubi Sameer yana rufe folder ɗin hannunsa, “Okay, you can proceed. Just make sure everything goes as planned.” “Yes, boss,” Sameer ya amsa yana ɗan risinawa, “Keep me updated.” “I will.” Sameer ya juya ya nufi BQ a hankali. Zayd kuwa ya tsaya na ƴan seconds, idanunsa suka bi direction ɗin Suhaila da Raihana, sannan ya fara takawa zuwa inda suke.
Suhaila har ta shige driver seat tana warming motar, Raihana kuma ta fara takawa zuwa dayan side ɗin motar. Zayd ya karaso, fuskar nan a haɗe tsaf, ya kalli Raihana da bata riga ta shiga ba, tana kallonshi ta gefen ido kuma each step da yake taking zuwa inda take zuciyarta haka take mahaukacin bugu amma ta dake kamar bata san yana wajen ba, “Hey, where do you think you’re going with that so called mayafi?” Raihana ta wani haɗe rai ta sake ɗauke kai, kamar Allah bai yi ruwanshi a wajen ba, ta yi kamar ba ta ji shi ba. Suhaila da bata ma ganshi ba ta sauke glass ɗin motar tana ɗan kallon Raihana, “Anty Rayy, come in, let’s go.” Raihana ta buɗe ƙofar ta shiga, ta fara ƙoƙarin saka seat belt. Zayd kawai ya tsaya yana kallonta kamar an dasa shi a wajen har ta shige ta rufe kofar yana tsaye yana bin ta da kallo.
Sai kawai ya zagaya ta side ɗin Suhaila, ya buɗe car seat ɗin ya zuba mata, idanun nasa a kanta, calmly yace, “Come down.” Suhaila ta zaro ido, “Akhie, na fito kuma Ummie ce fa ta aike mu. Don Allah, kabar ni. Wallahi bazan yi gudu da ita ba. I promise to drive gently.” Ta yi maganar cikin pleading tone, tana kallonsa da fuskar wadda take son a tausaya mata, amma Zayd bai sake magana ba, kawai ya tsaya yana kallonta. Suhaila ta sani idan yayi haka, toh yana nufin ta fito ɗin kenan, dan ita duk tunaninta yana nufin bazasu fita su kaɗai bane ba tare da driver ba, ta sauke numfashi a hankali, ta na turo baki, “Fine…” Ta zuro kafafuwanta duka, sai kuma ta fito ta ja gefe, ta haɗe hannayenta a chest ɗinta tana kallonsa, fuskarta a haɗe.
Raihana ma ta fara ƙoƙarin fita, amma kafin ta fito, Zayd ya shige motar, ya kama steering ɗin, ya kunna motar sannan yayi zoom off yayi locking motar completely, ya ja wani mugun reverse sannan ya fice a gidan. Suhaila ta saki baki da mugun mamaki, ta tsaya a wajen tana kallon motar, idanunta suka bi ta har ta bar compound ɗin, for a few seconds, ta kasa ko motsawa, “Seriously?” Ta faɗa a hankali, still staring at the empty gate, sai ta juyo fuuuuu ta yi cikin gidan kamar zata fashe da kuka.
Kai tsaye ta fada falon ta zauna a gefen Ummie, tana fashewa da kukan takaici, ta zauna da ƙarfi kamar wadda aka zalunta, tana share hawayen da bayan hannunta. Ummie ta bita kallo, brows ɗinta suka ɗan haɗe cikin mamaki, “Meye ya faru?” Suhaila ta juya mata fuska, muryarta cike da takaici, “Ummie, wai kawai Akhie ne yace na fito. Ni na ɗauka ma zaice ba zamu fita mu kaɗai bane, amma ina fitowa kawai ya ja motar ya wuce ya barni a tsaye!” Ta faɗa tana sake dan fashewa da kuka, “Like, he just drove away and left me standing there!” Ummie ta zuba mata ido kamar bata gane ba, “Ya wuce ina? Ina kuma Raihana?” Suhaila ta ɗan shafa hancinta tana share ƙwallar da ta taru a idonta, “Ta na ciki ya tafi da ita.”
Ummie ta ɗan buɗe baki, surprisingly, amma kafin Ummie ta samu damar cewa komai, Inno ta sauko daga stairs, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon su, kamar tun daga sama ta ji ƙarshen maganar, “Yo, ba dole ya tafi da ita ba!” Muryarta ta fito kai tsaye, ba tare da wani hesitation ba, ta ƙaraso tana kallon Ummie kai tsaye, “Ni wallahi bansan me take a gidan nan ba. Ki tattara ta ki bashi su tafi. Idan yaso tana cikin gidan, duk ma abinda zakiyi mata sai kiyi.” Ta ɗan tsaya, sannan ta girgiza kai cike da rashin jin daɗi, “Amma a daura aure gobe Lahadi, sati ɗaya kenan kin kunshe ta a ɗaki! Ni bansan a ina ake irin wannan ba.” Ta ƙarasa maganar tana sauke numfashi da ƙarfi, kafin ta zauna a ɗaya daga cikin sofas ɗin falon.
Ummie dai kawai tayi shiru, ta kalli Inno, sannan ta kalli Suhaila, kamar tana ƙoƙarin fahimtar komai kafin ta yi magana. Suhaila ma kawai tana zaune, tana cika tana batsewa, tana share hawayen takaici lokaci-lokaci.
Seeyama da kyar tayi bacci, dan a nan falon a nan ta kwana, ko kayan jikinta bata samu sararin cirewa ba sabida takaici da bala’in bacın rai. Zuciyarta cike take da ƙuduri kala-kala akan ɗaukan fansa, ta kwana cikin tashin hankali, tana juyawa daga wannan side zuwa wancan, har bacci ya ɗauke ta da kyar. Da safe ma da kyar ta tashi, ba sallah ba, ba salati, ta miƙe kawai, ta ɗan yi stretching, sannan ta sa hannu ta janyo wayarta dake yashe a gefe, ta shiga neman Safina.
Bugu biyu Safina ta ɗauka, tana wani irin dariyar iskanci, “Kawata Amarya! Ya ne? An ji maza na san ma sai mun zo mun yi miki gashi da ruwan dumi wai don iskanci kika bar mu a watse, ni da Mommy kika yi gaba. Wai ke ga mai miji! Ai kin goge min hadda jiya.. now gist me ya abun ya kasance?” Seeyama ta ja wani shegen tsaki, fuskarta ta ƙara haɗewa, “Dallah ke! Kinsan me guy ɗin nan ya min ne?” Safina ta dakata da dariyar, muryarta ta ɗan fara zama serious, “Me ya faru?” Seeyama ta sauke numfashi mai nauyi, “Wallahi sai na koya musu hankali sai sun gane bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane, bana yafiya, wallahi.”
Safina ta katseta, “Wa? Meye ya faru? Naga kun wuce dashi kun tafi. Ko ba gidan kuka je ba ne?” Seeyama ta sake sauke numfashi, idanunta suka yi jajir saboda fushi, “Gidan muka je, amma wallahi mutum na farko da zan fara koyawa hankali itace uwarsa.” Safina ta yi shiru tana saurare, “Domin komai ya faru, itace sila. Da bata aurawa Zayd shegiyar yarinyar nan ba, da yanzu ba wannan maganar ake ba.” Ta ɗan tsaya, sannan ta taune lower lip ɗinta cikin wani mugun murmushi, “I promise to divert their ways. Uwarsa sai ta zama ita da Zayd, wallahi sai kallo. Ita kuma shegiyar yarinyar da ya aura, da ƙafafunta zata bar gidana. Ba dai a kanta bane first night dina ya zama kamar na wata wacce bata da kowanne irin gata, a wulakanci ace mijinka, a darenku na farko, ya bar ka a zube a kofar gida a cikin uban sulusulin dare?”
Muryarta ta ƙara daukar wani nauyi, kalamanta suka ƙara nuna fushin da ke cikin zuciyarta, ta ɗan yi dariya mai ɗauke da haushi, “Toh na rantse da wanda ya busa min rai, sai na wulakanta rayuwar yarinyar nan, I will make her life miserable. Shi kuma Zayd zai gane shima.” Ta matse wayar a hannunta, “Wallahi akwai sanda ko numfashi sai ya nemi permission dina zai shaƙa. Sai na juya shi kamar waina a tanda.” Safina ta yi shiru. Seeyama kuwa ta ci gaba, kamar wadda ta riga ta shirya komai a ranta, “I promise myself this.” Muryarta ta yi ƙasa, amma cike take da conviction, “Sai ya durƙusa min akan ƙafarsa yana neman na bashi kaina watarana. Wannan alkawarin da nayi ne, zai gane abinda ya aikata min.”
Safina ta gwalo ido, “Kina nufin a hanya ya juyeki ya tafi?” “Uhmm,” Seeyama ta amsa a takaice, “Ba zaki gane ba, wallahi it’s baffling me how I was taken for granted.” Safina ta ɗan yi shiru kafin cikin mamaki ai su zatonsu nan Zayd daukar Seeyama yayi suka wuce aka sha amarci, muryar Seeyama ta katse mata tunaninta, ta cigaba da magana da wani irin ƙuduri a ranta, “Ke dai kawai ki shirya yau ba sai gobe ba. Ki rakani inda za a min maganin su duka. Kafin kwanaki biyar ɗin su cika, na gama abinda zanyi.” “Saidai ta koma gidan ubanta da takardar saki. Amma ba dai ta tare a gidan nan ba!”