THE JEALOUS HUSBAND
ZAYD ARMAAN
CHAPTER SEVENTY EIGHT:78
THE JEALOUS HUSBAND
JIDDAAH BARKUM
———-
Safina ta sauke wani dogon numfashi, sannan ta gyara zamanta a inda take, muryarta ta yi ƙasa amma cike da seriousness.
"Bari na shirya na fito, sai nazo nan ɗin. Ke ma ki shirya yanzu. Tunda gaskiya a yadda kika labarta min, dole sai an tashi tsaye. Ba wai a zauna ana kallon su kawai ba."
Seeyama ta ɗan yi shiru, tana kallon gabanta da wani irin murmushi mara daɗi. Ta ɗaga gira ɗaya a hankali, kamar ta riga ta fara ganin yadda komai zai kasance.
"Exactly," ta amsa a takaice. "Shi yasa na kira ki. Bana son wani ya shiga min cikin wannan."
Safina ta gyara murya, "Toh shikenan. Ki bani time na shirya, zan taho. Amma Seeyama... Ki tabbatar kin san abinda kike yi. Wannan karon ba abun wasa bane yanzu ne asalin game din zai fara."
Seeyama ta yi wata ƙaramar dariya, amma babu wani farin ciki a cikinta.
"Safina, kin san ni. Idan na ɗauki abu da muhimmanci, bana barinsa halfway."
"Na sani," Safina ta amsa. "Shi yasa ma nake cewa ki jira ni. Kada ki yi komai ke kaɗai kafin na zo."
Seeyama ta ɗan lumshe ido, sannan ta gyada kai kamar tana yarda da maganar.
"Fine. Just hurry up."
"Okay. Zan fito."
Ta katse wayar. Seeyama ta sauke wayar a cinyarta, ta yi shiru na ɗan seconds kafin ta miƙe. Ba ma maganar breakfast ta fara ba. Tun daga farkawa har yanzu, babu abin da ya zo gabanta sai fushi da ƙudurin da ta ɗauka a ranta. Har ledar naman da Zayd ya jibga mata jiya da dare, wadda har yanzu take nan a gefe, bata sake kallonta ba. Kai tsaye ta nufi bathroom.
Bayan ɗan lokaci ta fito cikin simple outfit mai kyau, ta gyara kanta a hankali ba tare da wani ƙarin kwalliya mai yawa ba. Ta buɗe wardrobe ɗinta, ta ɗauki wasu ƴan abubuwa da take buƙata, tana zubawa a cikin handbag ɗinta.
Wayarta dake kan dressing table ta fara ringing. Ta ɗago kai, ta kalleta. Safina. Ta ɗauka tana nufar ƙofar fita.
"Hello kar dai har kin zo?"
"Ehh, nazo," Safina ta amsa daga ɗayan ɓangaren. "Amma wallahi wannan iskan gateman ɗinku ya hana ni shigowa. Wai maigidan yace ba shiga ba fita!"
Seeyama ta tsaya cak. "What?!" Ta riƙe wayar sosai a kunnenta, fuskarta ta canza nan take. "Ya hana ki shigowa?"
"Wallahi. Na ce masa na zo wurinki, amma sai yake cewa ba shi da permission na buɗe gate."
Seeyama ta ja dogon numfashi. "Okay. Stay there." Ta katse wayar.
Cikin taku masu sauri ta nufi entrance ɗin. Da ta isa wajen gate ɗin, ta hangi Safina a tsaye a waje, yayin da mai gadin yake gefe yana ƙoƙarin yi mata bayani. Seeyama ta tsaya cak. Ta kalli Safina, sannan ta juya idonta zuwa mai gadin.
"Why?"
Mai gadin ya ɗan sunkuyar da kai, ya fara magana cikin ladabi. "Madam, wallahi ba laifina ba ne. Boss ne ya ba da umarni tun jiya cewa kar a buɗe gate ga kowa, ba shiga ba fita sai ya ba da permission. Ni dai ina bin umarnin da aka bani ne—"
Seeyama ta ɗan zaro ido. "Are you telling me you refused to open the gate for her?"
"Madam, ba wai na ƙi ba ne. Wallahi idan haka kawai ne zan buɗe amma umarni ne kar na buɗe, boss ya ce—"
"I don’t care what your boss said!"
Mai gadin ya yi saurin ƙara mata bayani, "Madam, please, ku fahimce ni. Ni aikina kenan, idan na buɗe gate ba tare da permission ba, boss zai tambaye ni dalilin da yasa na—"
Seeyama ta zabga masa mari mai ƙarfi a fuska. Mai gadin ya juya kansa gefe saboda marin, hannunsa ya tafi kan kumatunsa nan take. Ya tsaya cak, ya kasa cewa komai na ƴan seconds. Seeyama ta matso kusa da shi, tana kallonsa da wani irin fushi.
"How dare you stand there and tell me rubbish?! Are you mad?!"
"Madam..."
"Don’t ‘Madam’ me!" Ta katse shi a tsawace.
Mai gadin ya sake riƙe kuncinsa, ya sunkuyar da kai. "I’m sorry, Madam. I was only following—"
"Then follow your instructions properly and stop standing here arguing with me!"
Safina kuwa tana tsaye a gefe tana kallon komai, ta kasa cewa komai. Ta san Seeyama tana cikin wani irin yanayi ne da ko ƙaramar magana za ta iya ƙara kunna wutar fushinta. Sai kawai ta kalli Seeyama, sannan ta kalli mai gadin, amma bata ce komai ba.
Seeyama ta yi wani dogon numfashi, ta gyara handbag ɗinta a kafaɗa. "Open the gate."
Sai kawai mai gadin ya buɗe gate ɗin nan take bai sake cewa komai ba. Safina ta shigo, tana ɗan kallon Seeyama da wani irin expression.
"Wallahi yau kin tashi gidan nan da wuta," ta faɗa a hankali.
Seeyama ta kalle ta gefe ɗaya kawai. "Let’s go."
"Where?"
"Parking lot."
Ta juya kai tsaye ta nufi parking lot ɗin gidan, takunta cike da sauri da fushi. Safina ta biyo bayanta, tana kallonta ba tare da ta ƙara magana ba. Da suka isa parking lot ɗin, Seeyama ta tsaya gaban motar, ta ciro key ɗin daga handbag ɗinta. Ta buɗe motar, ta jefa handbag ɗinta a back seat, sannan ta shiga driver’s seat. Safina ta zagaya ta shiga kusa da ita a passenger seat.
Seeyama ta ƙuna motar, ta riƙe steering ɗin da ƙarfi, tana kallon gabanta da fuskar da har yanzu take cike da ɓacin rai. "Seat belt," ta faɗa a taƙaice.
Safina ta yi saurin ɗaure nata, sannan ta kalle ta. "Okay... yanzu ina zamu?"
Seeyama ta yi wata ƙaramar murmushi mara daɗi. "Somewhere we can talk properly." Ta saka gear.
Motar ta fara motsawa daga parking lot ɗin, yayin da fushin Seeyama bai ragu ko kaɗan ba. A zahiri ma, abinda ke cikin ranta ya fi yadda Safina ta sani.
Raihana ta haɗe rai tana kallon Zayd, fuskarta cike da takaici. "Ina zaka kaini? Meye haka? Ya zamu fito tare da ita amma ka koreta, sannan ka wani shigo? Ni don Allah ka saukeni. Wallahi ba zan iya binka ko ina ba."
Zayd bai ce komai ba. Ya yi mata banza kamar babu wani mai rai a cikin motar. Raihana ta ƙara haɗe rai, ta zuba masa ido na ƴan seconds, tana jiran ko zai ce wani abu. Amma shiru. Ta shaƙi takaici, ta juya kanta gefe, sannan ta sake kallonsa da harara. "Ka ji abinda nake cewa kuwa?"
Zayd ya ci gaba da kallon hanya, hannunsa a kan steering, fuskarsa calm kamar babu wani abu da ke faruwa. Raihana ta sauke numfashi da ƙarfi. Ta miƙa hannu zuwa ƙofar motar, tana ƙoƙarin buɗewa. Amma sai ta ji locked. Ta sake gwadawa. Nothing. Ta kalli ƙofar, sannan ta kalli Zayd. "Ka kulle?"
Zayd bai amsa ba. Ta sake jan handle ɗin, wannan karon da ƙarfi. Still locked. Takaicin ya gama isarta. Ta koma ta zauna sosai, ta haɗe hannayenta a ƙirjinta, sannan ta fara zabga masa harara kai tsaye. Ta wani irin haɗe rai, tana kallonsa lokaci-lokaci kamar tana son ya gane da kansa cewa tana jin haushi.
Zayd kuwa? Kamar babu Raihana a motar. Ya ci gaba da driving ɗinsa cikin nutsuwa. Har suka isa wani traffic light. Motocin suka tsaya. A wannan lokacin wasu samarin da suke wanke glass na motoci suka fara zagayowa tsakanin motocin, duk da wasu drivers ba sa son a wanke musu glass ɗin. Ɗaya daga cikinsu ya zo wajen motar Zayd, ya fara wanke front windshield ɗin da sauri. Raihana tana kallon abin ne kawai ba tare da wani interest ba.
Bayan ya gama, Zayd ya ɗauko kuɗi daga aljihunsa, ya sauke glass ɗinsa kaɗan ya mika masa. "Thank you," yace a taƙaice. Yaron ya karɓa yana murmushi ya juya. Zayd ya ɗaga glass ɗin yana shirin maida shi ya rufe. A dai-dai lokacin ne wani saurayi da ke kan bike ya tsaya kusa da motar, sannan ya juyo zuwa wajen Zayd.
"Morning, boss."
Zayd ya juya kansa ya kalle shi sai ya ɗan daga gira kamar bai yi tsammanin ganinshi a nan ba. "Morning Haris. Where to?"
Raihana dake kallon can gefe ba tare da wani abu a ranta ba, jin muryar mutumin kawai sai ta juyo a hankali. Idanunta suka sauka a kansa. Da farko kamar ba ta gane shi ba. Amma da ta kalleshi da kyauuu, zuciyarta ta yi wani mugun bugawa. Idanunsu suka haɗu. Na ƴan seconds, komai ya tsaya mata. "...Haris!" Ta furta sunan a ƙasan muryarta, kamar ba ta yi niyyar faɗar shi da ƙarfi ba.
Haris shi ma da mamaki ya bayyana a fuskarsa, kawai sai ya tsaya kallonta. Shi ma bai ce komai ba. Kallo kawai. Wani irin kallo ne mai ɗauke da mamaki, kafin ya ɗauke kansa a hankali ya koma wajen Zayd, kamar bai ga komai ba.
Zayd kuwa ya ci gaba da magana da shi. "Ko ka fita shan iska ne?"
Haris ya ɗan daidaita zaman da yake kan bike ɗin, sannan ya amsa cikin ladabi fuskarsa da ɗan murmushi. "Farmland, sir."
Zayd ya ɗan jinjina kai. "Okay."
"Alright, sir."
Zayd ya amsa da ɗan jinjina kai. A dai-dai lokacin ne aka basu hanyar tafiya. Haris ya matsa bike ɗinsa gaba, ya wuce.
Raihana kuwa har yanzu idanunta suna bin shi. Ta kasa motsawa na ƴan seconds. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta, sannan ta mayar da kallonta gaba. Zayd ya saka motar gaba. Bai tambayeta komai ba. Bai ko kalli fuskarta ba. Ya ci gaba da driving gently, hannunsa a kan steering, fuskarsa calm kamar babu wani abu da ya faru. Kamar babu komai a duniya da zai iya damunsa.
Har suka isa guest house ɗin, Raihana har yanzu bata dawo hayyacinta ba daga shock ɗin abinda ya faru. Zayd ya san Haris. Not only did he know him, daga yadda suka gaisa ɗin ma, a fili yake cewa ba ƙaramin sani suke da juna ba. "Morning, Haris. Where to?" "Farmland, sir." Wannan conversation ɗin ta ci gaba da maimaituwa a cikin kanta. How does Zayd know Haris? Kuma me ya sa Haris yake kiran shi boss?
Tana cikin wannan tunanin ne Zayd ya fito daga motar. Bata ma lura da lokacin da ya sauka ba. Ya zagaya zuwa side ɗin da take, ya buɗe mata ƙofar, sannan ya tsaya yana jiran ta fito. "Hey, come down."
Sai Raihana ta ɗago kai a hankali. Ta kalleshi. Shi kuwa ko a jikinsa. Fuskarsa calm, babu ko alamar cewa wani abu ya faru a hanya. Kamar bai ga Haris ba, kamar bai lura da irin kallon da Raihana ta yi ba, kamar komai normal yake. Raihana ta kure shi da kallo. Ita kanta ta san wannan ba irin kallon da ta saba yi masa bane. Tun da take rayuwarta, duk lokacin da za ta kalli Zayd, kallon gefen ido take masa. Ko idan yana kallonta, sai ta kau da kai. Amma yau? Ido da ido take kallonta. Ba tare da kunya ba. Ba tare da ta ɗauke kanta ba. Kamar wacce take jiran amsa.
Zayd ya tsaya yana kallonta cikin nutsuwarsa. Bai ce komai ba. Raihana kuwa bata motsa ba. Bata da niyyar fitowa ma. Bayan ƴan seconds, Zayd ya ɗan daga gira ɗaya, har yanzu idanunsa a kanta. "Are you coming down, or do I have to come get you?"
Raihana ta ɗan ƙara haɗe rai. Sai Zayd ya sake cewa cikin nutsuwa, "Zaki fito ko na fito dake?"
Ta ɗauke kallonta daga kansa, ta kalli gaban motar kawai. Ta yi shiru na ƴan seconds. Sai a hankali ta ce, "Ba zan fito ba."
Zayd ya ɗan yi shiru. Raihana ta ci gaba, har yanzu tana kallon gaba. "...sai ka faɗa min meye haɗinka da Haris."
Zayd ya zuba mata ido yana kallonta na ƴan seconds. Sai kawai ya haɗe rai, ya sauya yanayin fuskarsa zuwa irin na “I couldn’t care less”. "Ban san wa kike magana akai ba." Ya faɗa a taƙaice, kamar maganar bata ma da wani muhimmanci a wajensa. Sai ya ɗan karkata kansa zuwa ƙofar. "Fito daga motar nan."
Raihana ta zuba mata ido na ƴan seconds, kamar ta kasa yarda da abinda ta ji. Raihana ta shaƙi takaici, ta haɗe hannayenta a ƙirjinta, sannan ta juya masa baya gaba ɗaya, tana kallon can gefe. Zayd ya tsaya yana kallonta. Ya ɗan tauna lower lip ɗinsa a hankali, har yanzu idanunsa a kanta. Bai sake magana ba. Bai kuma bata lokaci ba. Kawai ya miƙa hannu zuwa gare ta, ya ɗauke ta daga cikin motar a sauƙaƙe.
Raihana ta buɗe baki da mamaki. "Me haka?!"
Kafin ta fahimci abinda yake yi, jikinta ya riga ya samu waje a hannunsa. Tsoro ya ratsa ta saboda ba ta shirya ba, sai kawai ba tare da dogon tunani ba ta ɗaga hannayenta biyu ta kewaye wuyansa, saboda gudun kada ta zame ta faɗi. "Put me down!"
Zayd bai ce komai ba. Ya rufe ƙofar motar da ƙafarsa, sannan ya fara tafiya da ita zuwa entrance ɗin guest house ɗin kamar babu wani abu na musamman da yake faruwa. Raihana ta fara motsa ƙafafuwanta, tana ƙoƙarin saukowa daga hannunsa. "Let me go!" Amma ya ƙara riƙe ta sosai. "Stop moving." "I’m not moving! I’m trying to come down!" "Then stop trying." Raihana ta sake ƙoƙarin sauke ƙafafuwanta, tana durƙusar da su ƙasa, amma Zayd ya ci gaba da tafiya bai tsaya ba.
Ta kalleshi daga kusa, fuskarta cike da takaici da mamaki. Shi kuwa kallonsa yana gaba, babu ko ɗan alamar damuwa a fuskarsa. Kamar ɗaukar ta haka ba wani abu bane. Raihana ta sake gwada sauke ƙafafuwanta, amma ya ƙi cika ta. "Wallahi ka sauke ni!" Zayd ya yi mata banza.
Sai da suka isa entrance ɗin, ya buɗe ƙofar ya shiga da ita. Raihana kuwa har yanzu hannayenta a wuyansa, saboda duk ƙoƙarin da take yi na saukowa bai yi tasiri ba. Da suka shiga falon, ta kalli wajen, sannan ta dawo da kallonta kansa. "Now, will you put me down?"
Zayd ya kalleta a karo na farko tun bayan da ya ɗauke ta. Fuskarsa har yanzu a haɗe. Sai ya ci gaba da tafiya. Sai da ya kai ta kujerar ƙarshe da ke cikin falon sannan ya sauke ta a hankali. Ya tsaya a gabanta, yana kallonta da wani ɗan iskan kallo daga sama har ƙasa, fuskarsa babu ko ɗan murmushi.
Aikuwa da ya ajiye ta, Raihana ta miƙe tsaye nan take. Ita ma ta zuba masa ido. Ta ɗan gyara veil ɗinta, daya zame sannan ta buɗe baki cikin tsiwa da ɓacin rai, muryarta cike da masifa. "Dama na sani! Wallahi kaine ka rabani da Haris. Kaine nan ka shirya abinda ka shirya ka rabamu!"
Zayd bai motsa ba. Ya tsaya kawai yana kallonta. Raihana ta ƙara matsawa kusa da shi, fuskarta cike da takaici. "Ka san me? You don’t even care how much we loved each other!" Raihana ta sauke wata ƙaramar feshin numfashi, kamar maganar ta fito ne daga zurfin zuciyarta. "Ka rabani da shi bayan dashi na shirya gabatar da rayuwata. Duk wani tanadi, shi na yi wa."
Ta ɗan girgiza kai, idanunta suka ƙara cika da ɓacin rai. "Komai da muka tsara... komai da muka yi planning ɗinsa, dashi ne. You just decided to cut everything off like it meant nothing!"
Zayd har yanzu yana tsaye yana kallonta. Bai ce uffan ba. Amma wannan karon, kalamanta sun samu inda suka dosa. Adam’s apple ɗinsa ya motsa a hankali yayin da ya haɗiye abinda ya taru a makogwaronsa. Raihana kuwa bata lura da hakan ba. Tana cikin fushi ne kawai.
"Ka yi deciding ɗaya kawai, ka datse alakarmu dashi. Without even asking me. Without even giving me a chance to say anything!" Ta ɗan ɗaga hannu cikin takaici. "Why? Saboda kai ne Zayd Armaan, dole sai komai ya tafi yadda ka ce?"
Zayd ya ci gaba da kallonta straight to the eyes. Raihana ta yi shiru na ɗan lokaci, numfashinta yana fitowa da ƙarfi. "Ni ban taɓa cewa ina son ka ba. Ban taɓa ɓoye maka ba." Muryarta ta yi ƙasa kaɗan, amma har yanzu cike take da ɓacin rai. "Then why did you do it?"
Zayd ya runtse idanunsa na ɗan second. Sai ya buɗe su. Kafin Raihana ta ankara, Zayd ya matso. Ya kama hannayenta da hannuwansa biyu, ya ja ta zuwa gare shi da wani irin sudden movement, har bayanta ya haɗu da bango. Raihana ta buɗe baki da mamaki. "Zayd..."
Ya tsaya a gabanta, hannayensa har yanzu a kanta. Idanunsa suka makale cikin nata. Straight to the eyes. Babu murmushi. Babu bayani. Sai dai wannan kallon nasa mai nauyi wanda ya sa Raihana ta kasa ci gaba da maganar da take yi na ƴan seconds.
Zayd ya zuba mata ido na ƴan seconds, idanunsa suka fara yin ja sosai, alamar maganganunta sun taɓa wani wuri da bai ji daɗi ba. Muryarsa ta fito ƙasa, amma tana ɗauke da wani irin nauyi. "Da aurena kike magana to my face...?"
Raihana ta ɗan haɗiye yawu, amma bata sauke idonta daga kansa ba. Zayd ya ƙara matse jaw ɗinsa, yana kallonta straight to the eyes. "Dashi kika tsara rayuwa?" Ya yi tambayar a hankali, amma kowace kalma ta fito kamar ana jefa ta cikin zuciyarta. "With him?"
Idanunsa suka ƙara yin ja. "After you got married to me, you’re standing here telling me to my face that you had already planned your life with another man?"
Raihana kawai hararsa take duk da yanda kirjinta ke sama da ƙasa a tsorace. Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta cikin wani irin disbelief. "I think baki san aure ba, ko?" Muryarsa ta ƙara yin nauyi. "Ko kuma har yanzu baki fahimci cewa kina magana da mijinki ba?" Ya yi shiru na ɗan lokaci, idanunsa har yanzu a kanta. "Because if you did... you wouldn’t stand in front of me and tell me that another man is the one you planned your life with."
Zuciyar Raihana na bugawa da bala’in tsoro. Ta taɓa ganin Zayd cikin fushi sau da yawa, amma ba haka ba. Wannan kallon nasa ya sa numfashinta ya ɗan tsaya na ƴan seconds. Idanunsa sun yi ja, fuskarsa ta yi tsauri, kuma yanayin jikinsa gaba ɗaya ya nuna cewa maganganunta sun taɓa masa rai. Amma duk da tsoron da take ji, taurin zuciyarta bai bar ta ta ja da baya ba. Sai ta murguda baki cikin tsiwa, tana ƙoƙarin ɓoye yadda zuciyarta ke bugawa. "Ai you caused it." Ta faɗa cikin ƙaramin murya, amma cike da stubbornness.
Zayd bai ce komai ba. Raihana ta ƙara kallonsa. "Me yasa zaka rabani dashi?" Ta ɗan daga gira, kamar ita ce mai tambayar sa. "Why did you have to separate us? Idan ba kai ka shiga ba, da komai ya ci gaba da tafiya normally." Ta sauke numfashi, idanunta har yanzu a cikin nasa. "Ni ban nemi ka raba ni da shi ba, Zayd. Kai ka yanke wannan decision ɗin da kanka ko na taɓa neman taimako ne ina neman wanda zai rabani dashi?" Ta ɗan haɗe rai. "So don’t stand there and blame me for something you caused."
Zayd ya tsaya cak a tsakiyar falon, wani irin zafaffen shiru ya biyo bayan kalaman nata, wanda ya fi komai tsorata d ita. Idanunsa da suka riga suka yi ja suka kafe a kanta, suna haskaka wani irin wuta na tsananin kishi da ya ki rufuwa. A hankali, ya sauke hannayensa da suka riƙe hannayenta, amma bai janye jikinsa daga wnn uban closeness din daga gare ta ba. Hannuwansa biyu suka sake landing suka riƙe qugun ta gam, yana matse ta jikinsa sosai kamar yana tsoron idan ya sake ta za ta bace masa.
Raihana ta kalli inda hannayenshi suka sauka sannan ta ɗago ta kalle shi tana zuba masa wata hararar amma kamar an rufe mata baki ta kasa magana. "You think this is a joke, don’t you?" ya faɗa a raɗa, muryarsa na fitowa da wani irin nauyi wanda ya sa kafafuwan Raihana yin wani irin sanyi. "What is this..." ta fara magana tana ƙoƙarin ja da baya, amma ƙarfin da ya riƙe ta da shi ya fi na ta nesa ba kusa ba. "Listen to me very carefully," ya katse ta, fuskarsa kusa da tata sosai har suna jin zafafan numfashin junansu. "The moment you signed that marriage certificate, your life, your past, your thoughts, and everything about you became mine. Wancan wawan da kike magana akai? He doesn’t even exist in your vocabulary anymore. If I ever catch you whispering his name or looking at him the way you did today again… I won't just separate you two, I will destroy anything that reminds you of him."
Idanun Raihana suka cika da hawaye saboda tsananin baƙin ciki. Ta wani zuba masa harara tana kallonshi kai tsaye cikin ido, zuciyarta na bugawa, amma haka ta buɗe baki cike da tsiwa. "Duk abinda za kayi kayi! An faɗa maka ina tsoro ne, ko dan kawai ina baka haƙuri ka dakeni, ka hanani kuka? Kayi min laifi, ka rabani da wanda nake so, amma ka nemi maida laifi kaina? Dan Allah ba destroying anything that reminds me of him zakayi ba, zuciyata zaka ciro ka datse a nan ai dama na faɗa maka gangar jikina ka aura amma ruhina na ga Haris!"
Zayd yayi still yana kallonta da mugun mamaki. Ita ma ta haɗe rai tana kallonsa bata ko kiftawa. Ya ɗan karkatar da kansa, idanunsu na kallon na juna—ba zato ba tsammani, taji yayi wuff da ita! Ya ɗage ta sama, bai direta ko ina sai a kan doguwar kujerar dake bayanta, sannan ya bi ta ya kwanta a jikinta yana sauke numfashi. A mugun razane ta fara magana, tana tura ƙirjinsa da hannuwanta biyu: "Stop all this meye haka ne?!"
Zayd yayo ƙasa da kanshi in a slow motion yana kare wa fuskarta kallo itama kallonshi take a razane gashi ya sake mata nauyinsa gabadaya tana jin ma da ƙyar take janyo numfashinta daga hunhunta sabida azabar nauyinshi da take ji ba zato taji saukar lips dinsa ya haɗe bakinsu da wani irin zafaffen kiss mai cike da zafin rai da kuma mallake komai. Kiss ne da babu ko alamar laushi ko sassauci a cikinsa kawai wani irin hukunci ne da yake nuna mata cewa ita tashi ce, kuma babu wani ɗan adam da ya isa ya gifta tsakaninsu. Raihana ta runtse idanunta, hawaye suka fara zubowa daga fuskarta yayin da dukkan wani ƙarfi ya ƙare a jikinta, ta shiga cikin duniyar da Zayd kaɗai ke da ikon sarrafa ta.
A hankali ya ciƙata yana kare mata kallo kamar wanda yake son haddace yanda fuskarta yake cikin daƙiƙaƙiyar muryarshi yace "Me nace miki akan fita ba izinina?" Raihana tana sauke numfashi, taƙi kallonsa, kawai sai ta sake runtse idanunta dan wallahi uban kusancin dake tsakaninsu ta san ƙaryane ta iya buɗe ido amma sai ya ce cikin wata murya "Ke! Buɗe idanunki." Da sauri ta buɗe tana ɗauke kai gefe. "Answer me," ya sake tambaya a cikin murya mai cike da umarni.
Cikin ƙasa da murya tace, "Ai Ummie ce ta aike mu. Kuma naga kaima a ƙarƙashin ikonta kake." Zayd ya zuba mata idanu yana ɗage gira. Sannan a nutse, da muryar da ita kaɗai za ta iya ji ita ɗin ma dan tana daff da shi, ya ce: "Maybe na barki ne, still kina kallon kanki kamar wata ‘yarinya budurwa. Let me make you mine completely today." Ya ɗora hannunshi a kan boobs dinta ya wani matsa da mugunta yana kallon cikin idanunta. Da sauri ta runtse idanunta tana juyar da kanta gefe. A mugun razane ta fara magana, tana tura ƙirjinsa da hannuwanta biyu: "Wallahi ba budurwa bace matar aure ce ni! Ina da aure, dan Allah kayi haƙuri!"