THE ARMAAN FAMILY FINALE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY:90*
*THE ARMAAN FAMILY FINALE*
*JIDDAAH BARKUM*
————
Felicia ta share hawayenta da bayan hannunta, amma hakan bai hana wasu sabbin hawayen saukowa ba, ta kalli Zayd da jajayen idanuwanta, muryarta tana rawa sosai, “I’m pregnant…” Zayd bai motsa ba, ya ci gaba da kallonta, kamar kalmar da ta fito daga bakinta ta zo masa da wani yare ne da bai fahimta ba, Felicia ta kalli takardar da ke hannunsa, sannan ta sake kallonsa, “I’m pregnant, Zayd…” Hawayenta suka ƙara zuba, “Wayyo Allah…” Ta rufe fuskarta da hannuwanta, ta fashe da kuka, “Me zan yi yanzu? Wallahi Mum za ta kasheni…”
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe su a hankali, fuskarsa babu wani abu da za a iya karantawa a kanta, Felicia ta kalle shi ta cikin yatsunta, “Zayd…” “Please say something,” Zayd ya ɗaga takardar a hankali ya sake kallon sakamakon, sai ya ɗaga idanunsa ya kalleta, Felicia ta sauke hannunta daga fuskarta ta share hawayen tana jan ajiyar zuciya, “I think… we only have one way out now,” Zayd ya ɗaga gira kaɗan, Felicia ta ja numfashi mai nauyi, “Kawai mu yi aure,” Zayd ya tsaya yana kallonta kamar ya ga wani sabon abu, “Abin da nake nufi kenan,” ta yi saurin ƙara bayani, tana share hawaye, “Iyayenmu za su iya yin fushi saboda ba mu sanar musu ba, ba mu yi da yarda da amincewarsu ba amma daga baya za su huce, they will understand.”
Zayd bai ce komai ba, “Saboda wannan…” Ta nuna cikinta da hannunta mai rawa, “This is our only option now,” ta sake share hawayenta, “Idan ba haka ba, ya za a kalle mu? Musamman ni da nake mace, what will people say about me? What will happen to my reputation?” Zayd ya ɗan karkatar da kansa kawai yana zuba mata idanu, Felicia ta kalle shi cikin tsoro, “Please, Zayd, ka taimake ni,” ta haɗiye yawunta, “Ba wai ina son na matsa maka bane… but what else can we do?” Zayd ya sauke takardar a hankali zuwa cinyarsa, Felicia ta tsaya tana kallonsa, tana jiran ya yi magana, seconds suka wuce, sai Zayd ya ɗaga idanunsa ya sake kallon ta, kallon da ya mata ya kasance kamar na mutum da aka gaya wa wani abu mai matuƙar ban mamaki, amma har yanzu yana ƙoƙarin tabbatar da cewa mutumin da ke gabansa yana sane da abin da yake faɗa kuma yana cikin cikakken hankalinsa.
Felicia ta ga kallon nasa, sai ta daure fuska, “What?” Zayd bai amsa ba, “Why are you looking at me like that?” Felicia ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta sake magana cikin kuka, “I’m serious, Zayd,” ya ɗaga kansa kaɗan sannan ya amsa a nutse, “I know,” “Then say something,” Zayd ya sauke numfashi a hankali, idanunsa har yanzu a kanta, “Felicia…” Ta jira, “Are you sure this is what you want?” Felicia ta kalli cikinta, sannan ta kalle shi, “Yes,” ta gyada kai da ƙarfi, “Yes, Zayd, I’m sure,” ta sake matsowa kusa da shi, “Maybe… maybe this is the only way everything can be okay.” Zayd bai amsa ba, Felicia ta sauke kanta, tana kuka a hankali, “Please…” Zayd ya kalle ta na wasu seconds, a ƙarshe, ya sauke idanunsa zuwa takardar da ke hannunsa, PREGNANCY — POSITIVE, ya sake karanta kalmomin, sai ya yi shiru, daga karshe ya mike tsaye a hankali, har yanzu yana riƙe da takardar a hannunsa, fuskarsa ba ta nuna komai ba, amma idanunsa sun tsaya kan Felicia, “If that’s what you want…” Ya ɗan dakata, “Then let’s go to the hospital, mu tabbatar.”
Felicia ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ja da baya kaɗan, tana watsa masa wani kallo, wani irin kallo ne kamar ba ta yarda da abin da ya fito daga bakinsa ba, “Hospital?” Zayd ya ɗaga gira, “Which hospital?” Ya ɗan kalli takardar da ke hannunsa, “Where should we go?” Felicia ta watsa masa wani kallo, “Wanne asibiti kuma za mu je?” Ta ɗan yi tsaki, sannan ta matso kusa da shi, “Bayan kasan daga can nake,” ta nuna takardar da ke hannunsa, “In fact, ga takardar result ɗin nan ma a wajenka,” kafin Zayd ya sake cewa wani abu, Felicia ta miƙa hannu ta fisge takardar daga hannunsa, ta kalle ta na ɗan lokaci, sannan ta share hawayenta da sauri, “I will go home now,” Zayd bai ce komai ba, Felicia ta ɗaga idanunta ta kalleshi, “You should think about what I said,” “Idan ka gama tunanin… you can reach out to me,” Zayd ya tsaya yana kallonta, sai ta juya, a hankali ta fara tafiya zuwa ƙofar, amma kafin ta kai can, sai ta sake kallonsa na ƙarshe, Zayd bai motsa ba, ba ya cewa komai, bai hana ta fita ba, bai kuma ƙara tambayarta komai ba, Felicia ta buɗe ƙofar, sai kawai ta fita da sauri, kamar tana tsoron idan ta tsaya na wani second, Zayd zai sake kiran ta, ƙofar ta rufe, Zayd ya rage shi kaɗai a cikin falon, shiru ya mamaye apartment ɗin, ya tsaya a inda yake, idanunsa a kan ƙofar da Felicia ta fita ta ciki, sai ya sauke numfashi a hankali ya koma kan abinda yake yi.
Bayan wannan lokacin, Zayd ya yi ƙoƙari sau da dama ya sake magana da Felicia game da zuwa asibiti domin a tabbatar da pregnancy ɗin, amma duk lokacin da ya kawo maganar, sai ta fara dodging, wani lokaci ta ce ba ta da lokaci, wani lokaci ta canza magana, wani lokaci ma kawai ta bar message ɗinsa a seen, Zayd ya lura da hakan, amma bai yi mata magana mai yawa ba, bayan ya yi iya ƙoƙarinsa, sai kawai ya share batunta daga kansa, ya ci gaba da abin da yake gabansa.
Amma kusan sati guda bayan wannan, sai aka samu wani labari da ya dawo masa da sunanta, an kira Zayd aka sanar da shi cewa Felicia ta yi accident, tana asibiti, ba ta cikin hayyacinta, kuma a cewarsu, ba ta da kowa a kusa da ita, Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci bayan jin labarin, a dalilin ba yanda zaiyi dan shi aka Kira a haka, ya shirya sannan ya tashi ya je asibitin, da ya isa, aka kai shi inda take, Felicia tana kwance a gadon asibiti, idanunta a rufe, jikinta ba ya motsi, Zayd ya tsaya daga gefe yana kallonta, bai san dalilin da ya sa har yanzu yake jin cewa ba zai iya juya mata baya gaba ɗaya ba, duk da komai da ya faru tsakaninsu, sai dai kafin ya yi wani abu, likitan ya zo masa da wani labari, Felicia ta yi miscarriage.
Zayd ya tsaya cak, ya kalli likitan, sai ya sake kallon Felicia, a wannan karon, bai ce komai ba, bai tambayi komai ba, bai kuma yi ƙoƙarin shiga cikin rayuwarta fiye da yadda ya kamata ba, bayan ta farfado ya biya bills din aka sallameta, daga wannan ranar, ya sake cire kansa daga cikin harkar Felicia, amma Felicia kuwa ba ta daina binsa ba, ko da bayan ta farfaɗo, har yanzu tana ta neman Zayd, tana kiransa, tana aika masa da messages, idan kuma yayi ignoring ya shareta, sai hau maganganu tana maimaita magana ɗaya— “You took away my pride,” tana kuma zarginsa da cewa yayi dumping ɗinta bayan abin da ya faru, Zayd kuwa ya daina ba ta amsa, a wajensa, abin ya wuce, ko kuma aƙalla haka yake ƙoƙarin gaya wa kansa.
Sai wata rana ta samu kira daga gida, muryar da ke ɗaya gefen wayar ta sanar da Felicia cewa mahaifiyarta ba ta da lafiya, ba ta yi wani dogon tunani ba, ta tattara kayanta, ta bar New York, ta koma gida domin kula da mahaifiyarta, school kuwa ta dakata a wajenta, wannan shi ne abin da ya bawa Zayd nutsuwa, ba don yana ƙin Felicia ba, amma saboda a karon farko tun bayan komai da ya faru, ya samu damar rayuwa ba tare da jin muryarta a ko ina ba, sai dai tafiyar Felicia ba ta sa school ta tsaya ba, rayuwa ta ci gaba, lectures suka ci gaba, exams suka ci gaba, friends suka ci gaba da rayuwarsu, Zayd kuwa ya shiga karatu sosai, shekaru suka fara wucewa, Felicia ba ta dawo ba, kusan shekaru biyu.
Amma hakan bai hana ta kasancewa a rayuwar Zayd daga nesa ba, wani lokaci sai ya ga message daga gare ta, wani lokaci call, wani lokaci voice note, tana tambayarsa yadda yake, tana gaya masa yadda mahaifiyarta take, tana magana kamar babu wani babban tazara da ya taɓa shiga tsakaninsu, Zayd kuwa yana amsawa ne kawai idan ya ga ya dace, ba ya sake buɗe tsofaffin maganganun, ba ya tambayar ta komai, ba ya kuma nuna mata cewa yana jiranta, lokacin graduation ɗinsa ya zo, Felicia ba ta nan, ta rasa graduation ɗin, Zayd ya gama karatunsa, ya rufe wannan chapter ɗin rayuwarsa, sannan ya koma gida, Felicia kuwa, saboda kasancewarta yar Edo, ta yi ta cewa za ta zo ta same shi a Kaduna, ta yi ta maimaita hakan sau da dama, sai da Zayd ya yanka mata babban warning, ya gaya mata a sarari cewa kada ta zo, ba ya son ta zo masa Kaduna, ba ya son wata hayaniya, ba ya son ta sake shiga rayuwarsa kamar yadda take yi a baya, kuma saboda yadda Zayd ya yi maganar cikin seriousness ɗin da ba a saba ganin sa yana amfani da shi ba, Felicia ta fahimci cewa wannan karon ba wasa yake ba, ba ta zo ba.
A lokacin da Zayd ya dawo Kaduna, bai daɗe da dawowa ba sai wani babban al’amari ya afkawa gidan Armaan, mahaifinsa, Alhaji Arman, ciwon ciki na dare ɗaya ya ɗauke shi, mutuwar ta zo bazata, ba wanda ya shirya mata, ba wanda ya zata, kuma labarin ya girgiza kowa, a cikin Armaan family, babu wanda ya iya ɗaukar mutuwar cikin sauƙi, Inno ta koma Yola bayan mutuwar ɗanta, tana cewa ba za ta iya ci gaba da zama a Kaduna kamar da ba, gidan da ya taɓa cika da muryar Alhaji Arman ya yi shiru, mutanen gari ma sun shiga alhini, domin Alhaji Arman ba mutum ne da aka san shi da dukiya kawai ba, mutumin kirki ne, mai taimako, mai tallafa wa mutane, mutumin da ya taimaki waɗanda ba su da, mutumin da ya riƙe ayyukan alheri da dama a ƙarƙashinsa, foundation, orphanage, taimakon marasa ƙarfi, ayyukan da ba kowa ke gani ba, yanzu kuma babu shi, kuma duk wannan ya sauka kan kafadar ɗansa, Zayd, a matsayinsa na babban ɗa, a matsayinsa na namiji a gidan, a matsayinsa na wanda ya kamata ya riƙe abin da mahaifinsa ya bari, harkokin kamfani suka hau kansa, foundation ta hau kansa, orphanage da sauran ayyukan mahaifinsa suka hau kansa, abin da da can yake kallon mahaifinsa yana yi, yanzu shi ne yake zama dole ya ɗauka ya ci gaba da shi.
Zayd bai yi gunaguni ba, bai nuna wa duniya nauyin da ke kansa ba, ya ɗauki komai, ya nutsu, ya yi aiki, ya girma cikin lokaci kaɗan, kuma wannan shi ne lokacin da mutane suka fara ganin wani sabon Zayd, ba kawai ɗan Alhaji Arman ba, ba kawai matashin da ya dawo daga New York ba, amma Mr Zayd Arman.
A gefe guda kuma, Seeyama tana nan, son Zayd ya fara ne tun tana ƙoƙarin basarwa, ta yi ta cewa ba ta damu ba, ta yi ta nuna kamar ba shi da wani matsayi a zuciyarta, amma lokaci ya wuce, abin ya ƙara zurfi, har ya kai matsayin da kusan kowa ya sani, kowa ya san Seeyama tana son Zayd, sai dai Zayd? Kallon ma ba ta ishe shi ba, bai taɓa ba ta wani alamar da za ta sa ta yi tunanin yana kallonta a matsayin mace ba.
A lokacin da ayyuka suka fara cinye Zayd gaba ɗaya, Felicia ma ta dawo, ta dawo school a lokacin da kusan duk classmates ɗinta sun gama, ta dawo daga baya, amma dawowarta ba ta hana ta neman Zayd ba, ta sake fara calling, ta sake fara texting, har wata rana ta kira shi tana roƙonsa da ya zo mata graduation, “Please, Zayd,” “Come for my graduation,” Zayd ya yi shiru, “Everybody will be there,” bai amsa ba, “Please,” ta ci gaba da matsa masa, “Just come,” Zayd ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, ya riga ya san Felicia, ya san idan ya ce no, za ta ci gaba da kira, za ta ci gaba da messages, za ta ci gaba da matsa masa har sai ya gaji, daga ƙarshe, saboda tsananin nacinta da kuma yadda ta ci gaba da roƙonsa, Zayd ya amince, “I’ll come,” Felicia ta yi farin ciki, “Really?” “Yeah,” “Promise?” Zayd ya ɗan yi shiru, ta san ba zai yi magana ba kuma sai ta yi dariya, “Okay, okay, I’ll see you there.”
Kuma kamar yadda ya yi alkawari, ya je, ba tare da sanin cewa wannan tafiyar ba za ta kasance kawai zuwa graduation ba, ba tare da sanin cewa a bayan wannan ranar akwai wani abu da zai sake buɗe wani tsohon chapter na rayuwarsa, shine har abinda ya faru ya faru, har zuwa inda rayuwarsa ta sake sauyawa gaba ɗaya.
Wannan kenan daga tarihin Armaan family.