RANTSATTSEN RABO

LOKACI CHAPTER 2

by @fulani32

***

⌛🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARR KI KARYMAT BASHEER (An karime karime na)

   FULANI ❣️ 
***

⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
      PAGE 2️⃣ 

Kuka take da dukkan ƙarfin ta amman babu mai zuwa ya cece ta dan daga ita sai shi a cikin gidan, idan kuma maƙota sun shigo suma su samu nasu rabon na cin mutunci hakan yasa ko zai mata dukan mutuwa babu wanda zai shigo dan ya kawo mata ɗauki, saida ya gaji dan kan shi yayi cilli da belt ɗin ya barta a yashe a wajen.

Da ƙyar ta samu taja jikin ta ta miƙe ta shiga ɗakin dake kusa da nashi, zama tayi akan kujera tana ta sauke ajiyar zuciya na wadda taci kuka ta ƙoshi, tabbas ta gaji da auren kuma tana buƙatar haƙura da shi, amman idan ta tuna abinda zata fuskanta akan mutuwar auren sai jikin ta yayi sanyi, ta ɗanɗani zawarci taji yanda yake dan haka bazata so ta koma mishi ba, Bama wannan ba idan auren nan nata ya ƙara mutuwa ya zatayi da mahaifiyar ta? Ya kuma zatayi da maganar ƴan uwan ta? Uwa uba ya zatayi da maganar ƴan unguwa???


★★★

Shiru tayi ta rasa abinda zata cewa mahaifiyar tata, tunani take akan mai ya kamata tace mata, bata kai ga samo amsar ba ta jefo mata warin takalmi ya same ta a ƙirjin ta, ƙasa ta ƙara yi da kanta duk da yanda ƙirjin nata yake mata zugi dan sosai jifan ya shige ta, ita kanta wani lokacin rashin maganar ta yana damunta toh amman ya zatayi a haka halittar ta take, damuwa da kuma zaman kaɗaici yasa shirun nata ya ƙaru fiye da yanda take, jin yanda take ta mata masifa akan shirun nata ne yasa ta fizgo maganar da ƙyar "Mahmah ni ban fahimci akan me yake magana ba" daga haka ta tsuke bakin ta dan dagaske bata fahimta ɗin ba.

Mahmah sakin baki tayi tana kallon ta cike da takaici, tsabar rainin hankali wai bata fahimci abinda yake nufi ba, tunda bata fahimta ba ita bara ta fahimtar da ita "jiya baban ku ya neme shi a masallaci akan yana so ya taimaka ya aure ki, idan har ya amince zai aure ki shi kuma sai bashi auren ki sadaka, yanzu kin fahimta?" Ta ƙarasa mata bayanin da tambaya a ƙarshe.

"Haba mahmah dan Allah yanzu kamar aunty zahra za'a ce za'a bada auren sadaka? Gaskiya wannan abin bai dace ba" cewar salma cike da jin haushin abinda iyayen nata suke wa yayar ta ta. "Dan uban ki idan ba auren sadaka ba me ya dace da wannan ƙatuwar guzumar duk sa'annin ta da ƙannan ta faɗa min wanda baiyi aure ba, nace ki faɗa min? Ƙannan ta guda biyar duk suna ɗakin mijin su da ƴaƴan su itafa? Bata da aiki sai cewa ta fita aiki, ni na san babu wani aiki da take zuwa a da dai tana zuwa aiki amman yanzu nasan yawon ta take zuwa? Taya za'a ce ƙatuwar mace ƴar shekara 35 batayi aure ba kuma bata damu ba, idan ba yawo take ba me take nace ki faɗamin salma" ta ƙarasa cike da hargagi.

Daga Salman har aunty zahra kuka suke har ana jin sheshsheƙar kukan ta, ita kuma aunty zahra hawaye ne kawai yake zubo mata masu matuƙar ƙuna da raɗaɗi, ba yau ta fara jifan ta da miyagun kalamai ba amman har yanzu ta kasa sabawa, duk sanda zatayi mata sai sun daki zuciyar ta, inda ace yau bata kama da mahaifiyar ta sak da sak da tuntuni zata saka ayar tambaya akan cewa ba itace ta haife ta ba, toh amma me fuskar su iri ɗaya ce banbancin kawai ita ta manyata ita kuma da ƙuruciya akan tata fuskar, a kallo ɗaya bazaka taɓa can kar shekarunta ba saboda yanayin ƙaramin jikin ta da kuma fuskar ta, shekarun kawai a baki suke amman ba'a jikin ta ba.

Bata iya ci gaba da tsayuwa a wajen ba taja ƙafafuwan ta ta nufi ɗakin ta, har ta shiga tana jin yanda Muryar Mahmah take ta shi a sama tana ci gaba da jifan ta miyagun kalamai, gaban mudubi taje ta tsaya hijabin jikin ta ta zare tana ƙarewa kanta kallo, kwata kwata bata ga wata makusa a tare da ita ba, indai kyau ne Allah ya bata tamkar ita ce ta zana kanta, a dirin jiki ba'a cewa komai bata rama ko kaɗan, duk da tana da tsayi amman komai a jikin ta daidai yake da tsarin jikin nata, meyasa toh ta riga da tasan komai yana da *LOKACI* toh ita yaushe ne nata *LOKACIN* zai zo? Wannan itace tambayar da take yawan yiwa kan ta ita wadda bata da amsa.

Zama tayi ta zuba wa ɗan yatsanta manuniya ido, zobe ne me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, a kallo ɗaya bazaka fahimci wani irin zobe bane saidai idan kasan kan su sosai, ƙasan zoben zallar azurfa ce golden, saman kuma akayi mata ado da farar tagulla, sosai zoben yayi kyau a hannun nata ya kuma haska zara zaran ƴan yatsun ta, hawayen ta ne yake ɗiga akan zoben yayin da zuciyar take bugawa da ƙarfi "abubuwa sunyi min yawa best friend bani da abokin shawara, babu wanda zan faɗawa damuwa ta best friend kowa baya fahimta ta, Mahmah ta kasa fahimta ta mutanen unguwa kowa yana jifana da duk kalmar da tazo bakin shi, gaba ɗaya ƙannaina sun rainani, kowa gurguwar fahimta yake min best friend kai kaɗai ne kake fahimta ta kai kuma kayi min nisa bansan kana ina ba bare na faɗa maka damuwa ta kana ina besty" yanda take wa zoben magana bazaka taɓa tunanin bada mutum take ba, kuka take wanda duk wanda zai ji yasan daga ƙasan zuciyar ta yake fitowa, a da da iyayen nata suke cewa zasu bada ta sadaka, tana ganin kawai barazana ce, sai gashi yau sun tabbatar mata da zihiri ne ba barazana ba, sosai zuciyar ta tayi mata nauyi a haka wani irin wahallen bacci yayi gaba da ita.

★★★

Da ƙyar ta samu ta kammala wankin kayan shi da take, bayan ta gama gyaran gidan tayi ta ɗora abinci dan duk tijarar Auwal baya barin ta da yunwa yana bata abinci a wasu lokutan ma idan da ƴan mutunci a kan shi har nama ko kifi zai siyo mata, saidai kawai idan yana ji da tijarar shi zai kafta mata ita hankali kwance, bai ɗauki dukan mace a bakin komai ba haka zagin ta da cin mutunci, shi gaba ɗayan shi ma zata iya cewa bashi da alƙibla, baza ka taɓa fahimtar halin shi kai tsaye ba, shiyasa duk yanda zatayi ƙoƙarin ganin ta kauce wa yi mishi laifi sai tayi, wasu lokutan ma garin kiyayewar ne take mishi laifin.

Bayan ta gama girkin ta zubo a flate ta zauna da niyyar ta ci, saidai me ta kasa kai ko loma ɗaya duk kuwa baƙar yunwar da take ji haka nan taji abincin ya fice mata a rai, tagumi tayi ta zubawa waje ɗaya ido, a auren da tayi guda biyu wannan na uku bata taɓa haɗuwa da irin Auwal ba, ko wanne da irin ta shi matsalar amman ta Auwal tayi mata girma, gaba ɗaya jikin ta tabon duka ne wanda yayi mata, tun bata saba ba har tazo ta saba, babban abinda yake ƙara ɗaga mata hankali iyayen ta sun san a halin da take ciki kuma zasu iya cire ta, amman sun ƙi yi mata komai a kai, Ummu tace lallai sai ta zauna ta gaji da irga mata aure da ake, dan haka tun da bata rasa ci da sha ba dole ta zauna, koda ma ace babu abinci a gidan da dai ace ta dawo mata gwara Ko yaushe ta dinga kawo mata ita, ta yarda ta ciyar da ita har mijin da dai ace ta dawo mata gida da sunan zawarci.

A lokuta da dama tana yunƙurin kashe auren saidai idan ta tuna abinda zata fuskanta dolen ta, ta rarrashi zuciyar ta ta zauna, kamar yanda shima tunda ya fahimci yanda bata son auren ya mutu da kuma duk abinda yake mata iyayen ta basa ganin laifin sa sai dai suka ga nata, hakan shi yake ƙara bashi lasisin yi mata duk abinda yaga dama dan yace komai zai mata yayi wa banza kuma zama da shi ya zama dole, sosai tayi zurfi a cikin tunani har bataji shigowar shi ba.

"Masoyiya tunanin me kike haka?" ya tambaye ta yana ɗora hannun shi a kan ta, sai a lokacin taji maganar shi da kuma hannun nashi da ke kanta, ɗagowa tayi ta kalle shi suka haɗa ido, janye idon ta tayi daga kan shi idon ta na tara hawaye, tsugunnowa yayi a gaban ta ya matsar da abincin gefe hannun ta ya riƙo guda ɗaya a cikin nashi, cikin kwantar da murya ya ƙara ce wa "me kike tunani haka masoyiya?" Kan ta kawai ta girgiza mishi a zuciyar ta tana raya yau ƴan mutunci ne akan shi kenan. 

Kallon abinci yayi ya kalle ta ya kuma ce wa "ko abincin ne bakya so? Idan akwai abinda kike sha'awa faɗa min naje na siyo miki" nan ma bata ce mishi komai ba sai kanta data ƙara girgiza mishi, tana ƙoƙarin mayar da hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata.

"Shikenan jira ni bara naje na nemo miki wani abin bar abincin" bai jira cewar ta ba ya fice daga cikin ɗakin. Wani irin kuka ne ya ƙwace mata na tausayin kanta, haka nan a duk lokacin da bai sha komai ba zai zo mata kamar cikakken mutum, a kuma lokacin da ya sha yake ji da tijar zai zo mata a tantiri mara mutunci, a yanzu a wannan fitar ta shi ba'abin mamaki bane ya dawo mata a buge ya ɗora daga inda ya tsaya.

Tananan inda take bata tashi ba ya shigo da leda guda biyu a hannun shi, zama yayi a kusa da ita ya buɗe mata, gashashshiyar kaza ce sai rufaidah yughurt da ya haɗo mata da ita, kai tsaye tace mishi bata ci amman ganin irin kallon da yake mata babu shiri ta saka hannun ta a ciki ta fara ci, saida ta ƙoshi sannan shima yaja sauran ya cinye, tashi yayi ya fita babu jimawa ya dawo da kaya marasa nauyi a jikin shi, tashi tayi zata fita daga ɗakin ya janyo hannun ta ta faɗo kan shi, tana ji tana gani yayi yanda yake so da ita ya gama ya tashi ya bar ta.

Kukan baƙin ciki ne ya ƙwace mata, dan wallahi ta gaji babu inda baya ciwo a jikin ta gashi shima yazo ya ƙara mata wata gajiyar, ya dake ta tayi wanki yanzu kuma yazo ya karɓi haƙƙin shi bayan ya karɓa kuma ya fice ya barta a wajen shikenan amfanin ta ya ƙare a wajen shi, sosai take addu'a a cikin zuciyar ta akan Allah ya kawo mata ƙarshen zaman ta da wannan bawan na nashi.

Lallaɓawa tayi ta tashi taje ta tsarkake jikin ta dan tasan nan da lokacin kaɗan za'ayi kiran sallar magriba, tana cikin shiryawa ta fara jiyo warin sigari na tashi a cikin gidan, kanta kawai ta girgiza ta ci gaba da shirin ta, amman sosai warin yake takura mata har yanzu ta kasa sabawa da jurar shaƙar warin ta, bata son warin sigari ko kaɗan sai gashi Allah ya haɗa ta zaman aure da me shan ta, Alwalah ta fito zatayi ta ganshi zaune da gajeren wando yana busa hayaƙin cike da nishaɗi, duk yanda taso daurewa ta kasa har saida ta toshe hancin ta.

"Ke dan uban ki ni kike toshe wa hanci?????

FULANI
***

***