LOKACI CHAPTER 4
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)
*Under Team Yota's Amazing Pens*
SADAUKARWA GARE KI KARYMA BASHEER (AN KARIME KARIME NA)❤️
PAGE 4️⃣
"Ni kike toshe wa hanci nace?" Ganin yadda ran shi ya ɓaci ne ya sa ta magana babu shiri "Ba hanci na toshe ba majina zan share." hararar ta ya yi ya ci gaba da shan sigarinsa, ya sani bata son warin sigari a farkon aurensu, har amai take yi daga baya kuma sai ya fita waje ya sha a lokacin bai gama bayyana mata asalin halinsa ba, daga baya kuma da komai ya gama bayyana a gabanta zai yi idan ta yi amai koya mare ta ko ya hanɓare ta, lokacin da yake ji da tijara kuma har da duka, ganin bai kuma mata magana bane ya sa ta wuce ta yi alwala, daga nan ta shige ganin ba ta da nutsuwar da za ta yi sallah ne ya sa ta zauna akan daddamu tana tuna wani lokacin can baya.
A lokacin da aurenta na biyu ya mutu, sosai ta damu saboda kaf ƙawayenta dama tsararrakin ta babu wanda ya taɓa aure ya fito sai ita, hakan ya sa ta matsu ta yi aure, ba ta damu da ya halin mutum yake ba ita dai kawai burin ta ta yi auren, tana ganin yadda abin yake damun Ummunta duk da ba ta taɓa buɗe baki ta yi mata magana ba, amma tana ganin damuwa a tare da ita a lokuta da dama da kuma yadda take yawan tambayarta har yanzu babu tsayayye a masu zuwa wajen ta, ita fa ba yarinya bace ko da ba ta fito ta faɗa mata ba ta san zamanta babu aure abin yana damun ta.
Ba ta manta lokacin da suka fara soyayya da Auwal babu abin da ba'a ce mata a kansa ba, amma ta ƙarya ta taƙi ji, dan ita ba ta ga ta inda ya yi mata kama da mai shaye-shaye ba, ita a lokacin ko da ma yana yi za ta yadda ta aure shi tun da gwara mai shaye-shaye da mazinaci ana ta tunanin, tana tuna yadda aminiyarta ta dinga ba ta shawara akan ta tsaya a ƙara bincike amma taƙi, idonta ya rufe burinta kawai ta yi aure, ba ta nemi zaɓin Allah ba ido rufe ta amince da aurensa kuma a ka yi.
Ba ta yi wata ɗaya ba a gidansa, ta fara danasanin aurensa, duk da a farko yana ta ɓoye mata halayensa, amma daga lokacin da ya san ta gano shi shikenan komai ya lalace mata, idan ta ce za ta masa wa'azi ko ta nuna masa baya kyauta wa ƙarshe ɗan banzan duka za ta ci a hannunsa. A farkon fara dukan ta tasha yin yaji ta tafi gida sai dai tana zuwa a ranar za ta dawo dan Ummu za ta ce ta yi haƙuri ta je ta ci gaba da zaman aure, ga shi ta yi haƙurin har na tsawon shekara biyu amma ba ta ƙaru da komai ba a cikin sa, da dukkanin zuciyarta take addu'a akan Allah ya nuna mata lokacin da auren nan nata zai zo ƙarshe, dan idan ta ce ba ta gaji da shi ba wallahi ta yi ƙatuwar ƙarya.
Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi ta tada sallah, a wajen ta zauna har aka yi sallar isha'i ta yi sannan ta yi shirin kwanciya, bayan ta yi azkar ta kwanta duk da babu alamun bacci a cikin idanuwanta, ta jima a haka taga ya shigo kamar yana tangaɗi, cikin faɗuwar gaba ta miƙe zaune babu shiri tana kallonsa, dan ta san ba alkhairi ne ya kawo shi gurinta ba, aikam ba ta gama tunanin ba ya faɗo gefen ta yana janyo ta daga zaunen da take, ba ta da ƙarfin da za ta ƙwace kanta, tana ji ta gani yana warin sigari da abin da ya sha a haka ya ziyar ce ta ba tare da yana cikin hayyacinsa ba, yana gamawa ya hankaɗo ta ta faɗo daga kan gadon, wata iriyar ƙarar azaba ta saki dan sosai ƙuƙunta ya bugu a ƙasa.
★★★★
Sai da ta gama jifan ta da mugun kallo sannan ta ce "Wallahi idan ba ki je ba Fatima mai raba ni dake a cikin gidan nan yau sai Allah, wuce ki ba ni waje" da sauri ta sa ka kai za ta fice daga gidan dan ka da ta canza shawara. "Big sister ba ki ci abinci ba za ki fita?" Salmah ta tambaye ta ganin zata fita babu abin da ta ci, ga shi jiya ma da ta dawo babu abin da ta sa ka wa cikinta. "Zan ci a can baby sis" tana faɗar haka ta fice daga gidan.
Juyowa Salmah ta yi aikam karaf suka haɗa ido da Mahmah da take ta zabga mata harara, yi ta yi kamar ba ta gani ba tana murmushi ta ce "Mahmah uwar gida kuma amarya a gidan Baffanmu" jin daɗin kirarin Mahmah ba ta san sanda ta yi murmushi ba, dan indai Salma ce haka take ko da za ta dake ta, tana hararar ta ta ce "Munafuka" ta bar wajen ta shige kitchen, "Allah ya kawo miki mafita babbar yaya"
Tana fita da ƙafa take tafiya dan sai ta fita daga layinsu ko da za ta samu napep, tana cikin tafiya taji ana kiran sunanta, hakan ya sa ta tsaya dan yarinyar maƙotansu ce, gaisawa suka yi zabta wuce ta ƙara tsayar da ita "Wai Zahra yaushe za ki aure?" Ta jefa mata tambayar tana tsare ta da ido. Murmushin yaƙi ta ƙaƙalo ta ce "Lokacin da Allah ya nufa." "Gaskiya babu wani lokaci kawai dai ba ki yi niyya ba Zahra, duk ga shi muda l mu ka yi niyyar auren duk mun yi har da yara, amma ke kin ƙi, ko da yake an ce aiki kike a restaurant ko?" Ba ta jira cewar ta ba ta ɗora daga inda ta tsaya "Babu ma ta yanda za ki yi aure a yanzu ai Zahra, na san kina haɗuwa da manyan mutane a can ko?"
Gaba ɗaya da farko rasa abin da za ta ce mata ta yi, sai kuma ta aro jarumta ta yi murmushin mai ciwo ta ce "To ke da kin sani har kike tambayata?" Sakin baki ta yi tana kallonta, tana shirin buɗe bakinta ta yi magana ta zagaye ta wuce, sosai taji wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ƙirji ta daɗe da sanin kallon da mutanen unguwa har ma da ƴan'uwan ta suke mata kenan, toh ma tun da uwar da ta haife ta ba ta yadda da ita ba waye zai yadda da ita a duniya babu ta bawa kanta amsa, har ta fito layinsu ba ta kula ba saboda yawan tunanukan da suka sha kanta, tafiya kawai take sai da ta fito babban titi ta tsaya tana kallon inda take, ajiyar zuciya ta sauke ta tsayar da napep ta ce ya kai ta Nassarawa, duk sanda zabta je aiki ko ta dawo ta riga ta saba hawan napep drop dan haka yanzu ma shi ta hau, har suka zo tunani kawai take a ranta amma ba ta bari hankalin ta ya bar jikinta ba tana kallon hanya, a daidai bakin restaurant ɗin ya tsaya ta sauka
*DARA RESTAURANT &BAKERY*
Restaurant ɗin babban wuri ne mai kyau mai suna "*DARA RESTAURANT & BAKERY*" Yana nan a Nassarawa daga gefen titi, saboda ya yi kan idon mutane ne ya sa mutane suna yawan shiga da fita.
A gaban restaurant ɗin akwai babbar ƙofa ta gilashi, sannan a jikin ginin akwai sunan restaurant ɗin da aka rubuta da manyan haruffa. Akwai ƙaramin parking space a gaban sa.
Da zarar mutum ya shiga, zai ga reception da cashier a gefe ɗaya, sannan akwai kujeru da tebura masu kyau a tsakiyar hall ɗin. A gefe kuma akwai wani ƙaramin sashe da aka ware domin takeaway da snacks.
Tana shiga ta tsaya suka gaisa da mutanen reception ɗin, daga nan ta wuce kitchen ɗin dake bayan restaurant ɗin ta ciki, dan a can take aiki, har taje suna gaisawa da mutane, da yawan mutane suna tunanin aikin ta karɓar customer's, amman ba haka bane aikin ta a restaurant ɗin shirya kayan snacks, duk wani snacks da ake a restaurant ita ce take yi, kitchen ɗin guda biyu ne akwai babban kitchen a nan ake shirya manyan abinci, kamar shinkafa, chicken, soups da sauran meals.
Sai ƙaramin kitchen wanda a nan take ita kuma take snacks akwai Oven,Gas cooker, Frying pans, Mixing bowls, Trays, Refrigerator, Work tables, Flour, sugar, eggs, butter da sauran kayan haɗi. A gefen kitchen ɗin akwai babban shelf da ake ajiye snacks ɗin da aka gama, kafin a kai su wajen sayarwa. Kullum da safe ita ce ke fara shirya snacks a wajen duk da tana da masu taimaka mata, amma kamar ita ce shugabar su a part ɗin gaba ɗaya,
Meat pie, Sausage roll, Samosa, Spring roll, Doughnut, Puff-puff, Cupcake, Chin-chin, Cookies. Waɗan nan sune abubuwan da kullum take yi.
Suna yawan samun order na snacks a restaurant ɗin saboda yanda ta iya, hakan yasa da an samu order manager yake sanar da ita, koda tana gida haka zata zo tayi.
Tana shiga ta ɗora apron akan doguwar rigar jikin ta, sannan ta saka Hairnet a kanta, duk da suna da unifoam ita bata fiya sakawa ba, hakan yasa koda fita zata kamata za'a gane ita ma'aikaciyar kitchen ce ba waitress ba. Akwai ƙaramin glass window tsakanin pastry section da hall. Ta wannan window customers za su iya ganin yadda ake shirya wasu snacks ɗin.
Tana gama shiryawa ta fara haɗa snacks ɗin cikin nutsuwa da nishaɗi, a kaf rayuwar ta abinda yake saka ta nishaɗi ta ganta tana girki, duk wata harkar kitchen tana son ta, tana tuna lokacin da Mahmah da Baffa suka tsaya mata akan koyan girki da kayan snacks ganin yanda take so, a lokacin da rayuwar ta bata juya mata baya ba, murmushi tayi kawai ta girgiza kanta, ta cigaba da aikin kafin kace me taci ƙarfin aikin tana yi su kuma sakawa a oven, dan haka suka gama da wuri.
Tana aikin tana duba lokaci dan tana da gudun zuciya duk da basu gama aikin ba, lokacin da tace wa Mahmah zata tafi gidan Sadiya nayi ta cire kayan jikin ta ta nufi office ɗin manager, da sallama ta shiga bayan sun gaisa tace mishi tana da uzuri zata tafi gida. "Amman Zahra kin san ba'a gama aiki ba, kuma anyi min waya ana son arder yau ya za'ayi kenan?"
"Afuwan aiken Mahmah ne dole zanje, amman idan nagama da wuri zan iya dawowa idan kuma ban samu dawowa ba gasu sister hindu nan zasu iya yi ai" ganin yanda ta ƙara kame fuskar ta, duk da daman can ba sakin fuska take a wajen ba, yace taje kawai, sallama tayi mishi ta wuce ta fita.
Hanyar bata wani bauɗe mata ba, daga Nassarawa zuwa hotoro, napep ta tare ya kai ta har ƙofar gidan, knocking tayi taji shiru ba'a buɗe mata ba, wayar ta ta ciro a jaka ta kira ta, sai da tayi mata 3 misscalled sannan ta ɗaga "ina ƙofar gidan ki kizo ki buɗe" tana faɗar haka ta kashe wayar ta. Tafi 30 minutes a tsaye duk ƙafar ta ta gaji, ga rana ta take saboda lokacin ƙarfe 1 da wani abu na rana, jin kanta ya fara ciwo ne yasa ta juya da niyyar komawa gida duk da abinda hakan zai iya haifar mata.
FULANI
***