RANTSATTSEN RABO

LOKACI CHAPTER 7

by @fulani32

***

⏳🕛 LOKACI 🕛⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER❣️

FULANI
***

     ⏳🕛 LOKACI 🕛⏳

        PAGE 7️⃣

Kamar wadda aka hankaɗo haka Mahmah ta faɗo ɗakin da waya a hannunta, mugun kallo take watsa musu su duka biyun, Salmah na ganin haka ta koma bayan Aunty Zahra ta tsaya tana rarraba ido.

"Kin dawo bance miki komai ba, duk da yanda zuciyata take raya min na ɗauki mummunan mataki akan ki. Shine yanzu kuma zaku kira min yarinya tana gidan auren ta ku ɗaga mata hankali? Kome ki kai Zahra ba zan yi mamaki ba dan ba ki auren ba, kuma baki san daɗin shi ba. Daɗin gantali kawai kika sani bana aure ba.."

Tamkar an janyo Salmah daga bayan Aunty Zahra ta fito tama manta ɓuya ta yi. 
"Haba Mahmah dan Allah, wai ya kike so Aunty Zahra ta yi ne? Kince sai ta je gidan ƙanwarta tayi mata aiki ta je kuma ba ta tsira ba. Ita ma munafukar data kira ki bata faɗa miki nice na kira ta ba?" Hannunta Zahrah ta riƙe idonta cike da hawaye.

"Salmah nice uwarki ko kuma Zahra?" Mahmah ta jefa mata tambayar a fusace.

"Babbar ya uwa ce, kuma ni gaskiya kallon uwa nake mata.." tsit ta yi ta dafe bakinta jin wani irin raɗaɗi daya ziyar ce ta a baki. Wani dukan Mahmah ta kawo mata. Cikin zafin nama Zahra ta ture ta dukan ya sauka a jikinta. "Ni za ku nunawa haɗin kai?" Ta tambaye su tana nuna kanta.

"Wallahi Wallahi Wallahi sai kin yi danasani a yau Zahra sai kin gwammace daman bani ce na tsugunna na haifeki ba."

Zubewa ta yi a wajen ta fashe da kuka, bayan fitar Mahmah. Salmah kanta kuka ta ke danasanin kiran Sadiya na kamata ta ɗorawa kanta laifi tana ganin duk abin da ya faru ita ce sila.

Sun jima a haka kafin ta share hawayen ta, ta nufi kitchen, tuwon semovita ta shirya da miyar taushe, dan tasan yan da Mahmah har ma Baffan suke so sosai, musamman ma idan ita ce ta haɗa musu, bata ɗauki lokaci mai tsayi ba ta gama, a flask ta zuba, sannan ta saka guda biyu a flet da miya ta nufi ɗakinta, dan ta san yau idan ba ita ta lallaɓa auta ba, bai zama lallai taci abinci ba.

"Zonan muci abinci Autar Mahmahn ta" yanda ta yi maganar tamkar babu abin da yake damunta, nan kuwa da za'a bincika irin bugun da zuciyarta take tsaf za'a tsora ta. Ajiye wa tayi ta zauna a gaban ta.
Salmah kwanon tuwon semovita da aka shirya cikin tsafta. Miyar taushe mai ɗan kauri ta lulluɓe tuwon, ana iya ganin ƙananan yankunan nama da kifi soyayye a gefe. Yayin da albasa da tattasai su ka ƙara mata ƙamshi, sai kuma ɗan ƙamshin daddawa da ya ke tashi ya ba miyar wani irin ƙamshi na musamman.

Sosai take kallon abincin miyan ta yana tsinkewa. Ta ɗauki cokali na farko, ta kai bakinta, sannan ta lumshe ido. "Wayyo Allah na Aunty Zahra ta wallahi har yanzu ban taɓa ganin wanda ya kai ki iya abinci ba, Wallahi mijinki yana cikin alkhairi."

Murmushi tayi bata ce mata komai ba, ɗibowa tayi ta kai bakinta "haa big sister" kamar ƙaramar yarinya haka Salmah ta nufi bakinta da tuwon, buɗe wa tayi ta saka mata, a haka suka ci abincin Salmah na bata a baki, bayan sun gama Salmah ta fita da flet ɗin ita kuma ta shiga wanka, bayan ta fito cikin riga mara nauyi ta shirya ta kwanta tana danna wayarta.

Tana jin sallamar baffa gabanta ya yanke ya faɗi ta duba lokaci a wayarta, 9:45pm. Yau ya daɗe bai shigo da wuri ba ta ayyana hakan a ranta....


★★★★

Sosai Khairiyya ta sake tana rayuwarta, a cikin gidansu tamkar bata da wata matsala, dan ma ciwon jikinta yana hana ta rawar gaban hantsi, tun tafiyar Aunty Maryama tana parlow a zaune tana kallo, ko alwalah zata yi a toilet ɗin parlown take yi tare da sallah a parlown, har dare bata bari sun zauna da Ummu ba dan ma kar tace zata lallaɓata ta koma gidan Auwal, dan taci alwashin ita da gidan nan har abada.

Tana cin abinci Ummu ta shigo ta zauna a kusa da ita. Kicin kicin tayi da fuska dan ma kar tayi mata maganar. "Khairiyya fushi kike dani?" Ta tambayeta cikin sanyin murya. Shiru tayi taƙi magana, sannan ta kasa ci gaba da cin abincin.

Hannunta ɗaya Ummu ta riƙe "Khairiyya idan har kashe auren ki zai baki farin ciki, bazan taɓa hana ki ba, saboda duk wanda zai so farin cikin ki a bayan ni mahaifiyar ki ne, ki sani ban taɓa farin ciki da rayuwar da kike a gidanki ba, kar ki manta niɗin mahaifiya ce. Yau bazan ƙi ace kaf duniya kinfi kowa yin dace da rayuwar farin ciki a gidan aurenki ba. Ina jin zafi sosai a cikin raina Khairiyya, saidai ina son ki sani babu rayuwar auren da babu ƙalubale a cikinta, zan goyi bayanki ki kashe auren Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi, kawai dai..."

Shiru tayi ta ƙara matse hannunta, wanda hakan yasa ta ɗagowa ta kalli fuskar Ummun, sosai ta marairaice fuska, dan idan har idonta bama gizo yake mata ba kamar hawaye ne a idonta. "Kawai dai me Ummu?." Ta tambayeta kamar an mata dole.

"Babu komai kar ki damu." Ta share hawayen da ya zubo mata. "Taya zaki ce min babu komai bayan kuma kina kuka Ummu da komai faɗa min menene?." A tsorace take tambayarta, sai dai babu yanda zata yi dole ta tambaya dan bata son damuwarta ko kaɗan.

"Ina tunani yanda za'a ci gaba da kallonki ne Khairiyya, idan wannan auren naki ya mutu na uku kenan. Amman kar ki damu babu komai na ɗauki ƙaddara, a cikin ƴaƴan Hajiya babu wadda ta taɓa koda yaji ne bare zaman zawarci, haka a cikin ku, toh kinga dan ke kinyi ai bazan damu ba saidai ma nagode wa Allah da yasa a iya kan ki abin ya tsaya, baƙin cikina kawai za'ayi ta ƙirga miki aure, Alhamdullah ma da ba tara ƴaƴa kike ba, yanzu kizo Alhajin ku yana kiranki, ina bayan ki yau dole auren nan ya mutu, sai kiyi zaman gidan kiyi rayuwar farin ciki Khairiyya."

Tana kaiwa nan ta zare hannunta ta fice tana goge fuskarta.

Wani irin kuka ne ya ƙwace mata na tausayin kanta, a taƙaice Ummu ta tunasar da ita abinda ta manta. Tabbas duka ƴaƴan babansu babu wadda ta taɓa yaji bare zawarci sai ita, sau biyu aurenta yana mutuwa, idan wannan ya mutu na uku kenan. Gadai shi Ummu tace tana bayanta, toh amman bayan ta gama mata hannun ka mai sanda meya kamata tayi? Duk abin da ta saƙa a madadin mafita sai taga hakan ba mafita bace. " Ya Allah ka kawo min mafita." Ta furta a fili cikin muryar kuka.

★★

"Ya akai Ummu ina Khairiyyan take?." Cewar dattijon dake zaune a kujera yana kallon Ummu da ta shigo ranta a haɗe.

"Gatanan zuwa kasan na faɗa maka ta faɗi kuma ta bugu a ƙugunta." Ta bashi amsa tana zama tare da yin tagumi da hannu bibbiyu. "To kuma menene naga duk kinyi wani iri ko da wani abu ne bayan ciwon da ta ji?." Ya tambayeta yana maida hankalin shi kan ta.

"Raina ne a ɓace Alhaji.." shiru tayi kamar me tunani. "Uhm ina jinki meya ɓata miki rai?." Yace har lokacin yana kallonta.

"Ahmad ne daga zuwa ɗaukar ta sukayi faɗa da mijinta har da dambe, abin ya ɓatamin rai Alhaji yanzu dan Allah idan a sanadiyar haka auren nata ya mutu sai kuma yace me?." Shidai kallon ta yake da mamaki, can dai ya ce "dambe kuma da mijin Khairiyyan?." Ya tambaya kamar mai tantama.

Shiru kawai tayi sai ƙafarta da take girgizawa, alamun abun ya kai ƙoluluwa wajen ɓata mata rai. Shima shiru yayi yana tunani.

Tana sane bata faɗa mishi da Aunty Maryam aka je gidan ba, dan tsaff zata faɗa masa duk abin da ya faru har akayi faɗan, shi kam Ahmad a irin warning ɗin data buga masa, tasan koya tambaye sa bazai ce komai ba, sai dai ya ɗauki laifin. Har yanzu Alhaji baisan wani irin zaman aure Khairiyya take a gidanta ba, duk wata ƙofa da zaisa ya sani ta toshe ta.

Sallamar Khairiyya ce ta katse musu zaman shirun, shi kaɗai ya amsa, Ummu kuma ido ta zuba mata tana son ganin yanayin ta, ajiyar zuciya ta sauke dan taga rauni a tare da ita, wanda tana da tabbacin maganar ta ce ta kawo mata hakan.

"Barka da dare Alhajin mu" ta ce bayan ta zauna a gefen sa. "Barka Khairiyya ya jikin naki?." "Dasauƙi" daga haka tayi shiru dan batasan dalilin kiran ba. "Meya haɗa ɗan uwanki faɗa da mijinki?" Ya tambaye ta dan shidai har lokacin mamaki yake.

Ummu ta kalla ita kuma ta ɗauke kanta, murmushin takaici tayi kawai, dan wannan tambayar ta shi ta nuna mata Ummu bata faɗa masa komai ba. Shiru tayi kanta yana ƙasa tana ƙoƙarin maida hawayenta. "Baku da gaskiya keda Ahmad tsabar wulaƙanci yaje har gidanki yayi dambe da mijinki, zai zo ya same ni." Sosai yake faɗa ta inda ya shiga batanan yake fita ba, gaba ɗaya ya ɗora laifin akan ta da Ahmad.

Jin yana kiran waya ne yasa ta zuba mishi ido ba tare data sani ba, gaban ta yana faɗuwa. Bata ƙara shiga fargaba ba sai da taji Muryar Auwal yana gaida shi cikin ladabi. A lokacin kam kasa tsaida hawayenta tayi, jin yanda Alhajin su yake ta bashi haƙuri akan abin da ya faru, ba tare da ya binciki ainayin abin da ya faru ba, tana jin yanda shima Auwal ɗin yake bada haƙuri. Bata tsinke da lamarin ba sai da taji Alhajin yace yanzu nan zata dawo gidanta, yayi haƙuri. Daganan ta dena gane komai har suka gama wayar, ya gama mata nasiha ya bata kuɗi, sannan ya sallameta akan taje a cikin yayyanta wani ya mayar da ita gida.

Babu yanda zatayi haka ta tashi ta nufi waje, bata jima ba Ummu ta shigo ta sameta, ta buɗe baki zatayi magana ta dakatar da ita. "Lah Ummu basai kince komai ba zan koma idan da rabon kinzo kin ɗauki gawata wata rana zaki fahimci abin da..." Kasa ƙarasawa tayi jin yanda ƙirjin ta yayi mata nauyi.

Juyawa tayi ta fice jin ana mata horn, duk da jikin Ummu yayi sanyi da maganar mutuwar da tayi tana fita ta sauke ajiyar zuciya, itadai tun da ta koma ai shikenan, burinta ya cika. Har suka je gidanta tunani take kala kala a cikin ranta, yana parking ta fito ta nufi cikin gidan, abin da ta gani ne yasa wani irin mamaki ya rufeta.....

FULANI 
***